Gargadar So Chapter 35 By M Shakur
Kyakkyawan baccin gagaran Khaleel yayi danko 30 minutes baikaiba ahankali yabude idanunshi yana juyowa daga rub da cikin dayayi yana kallon saman dakin baimasan meke damunshi ba, normally yakamata yayi bacci har zuwa 4 na yamma but yakasa baccin tunanin yarinyar chan kawai yake, kaman her sick spirit na kiransa, hannunshi yadaga yakalla da Hawwa ta ciza lumshe idanu kawai yayi yabude sannan yatashi zaune yasauka daga gadon, boxer yacire ya yar awajen yawuce abinsa naked yafada bathroom yayi wanka yafito yawuce walk in closet dinshi dake kama dawani exquisite boutique, shiryawa yayi yazaro Balmain monogram print flowing shirt dakeda kalan black print din kuma white yasaka, yadauko dogon denim wando na Diesel yasaka daya zauna ajikinshi da kyau dasdas, agogonshi yaciro from drawer na designers watch dinshi, yacire Furlan Marri yasaka dayama hannunshi kyau, yadan juya yakalli showglass na takalmansa kaman shago yasa hannu yaciro wani suede flat takalmi na Birkenstock Boston, sannan yadau turarukanshi yashiga fesawa yadauki brush yana taje kansa ya shimfada dadduma yayi sallan azahar sannan yamike yabude kofa yafito yasauka kasa, chan falo yayi yana kallon agogon hannunshi is 1:30 ba kowa afalo probably Mommy ta kwanta ko tana spa nasu ana mata massage, kofa yawuce aka budemai yafita wajen black Mercedes Maybach S class dinshi yayi dake kyalli tsabagen kyau da kudi, da sauri security nashi suka taho wajen yakalli Salman dake budemai motan yace “when did you come back?” Dasauri yace “not quite long Sir everything is sorted babu wani matsala motanta I called auto shop sunzo sun dauka har an fara gyaransa” yatsine fuska yayi kadan baice kome ba ya shiga bayan motan ya zauna, Salman ya maida kofan yarufe yakoma gaba yashiga ya zauna driver shima na shiga mopol dinshi ma haka, anatse yace “hospital” Dasauri driver yace “yes sir” yatada motan suka fita yana kallon hanya chan yace “music” waka aka samai yafarabi yanadan shaking kai yadaga wayanshi yayi selfie yasa a instagram story nashi hankalinshi kwance.*Kansu Ni’ima tayi da plastic chair data dauka dasauri Baban Yaseer yajuya yana sauke Hawwa agadon yajuyo yasa hannu da zafi zai karbe kujeran ta zame tai gefenshi zata rafkama Hawwa dake kallon Ni’ima completely heart broken Baban Yaseer yabude hannuwanshi ya tsaya agaban Hawwa, Ni’ima tace “kama rungumeta idan zakayi amman saina halakata, saina halakata wlh, Allah ya kasheki ya dauki ranki sai inga wazakaso Aliyu? Inaso naga ko zaka bita kabari kuyi soyayya, ba sumbatar juna kukeso kuyi ba kuka ganni kuka wayance? Ka tashi agabana” hannu daya Baban Yaseer yasa ya fizge kujeran daga hannunta yana kokarin ijiye chair a gefe tabi gefenshi zatayi kan Hawwa taji an riketa gam juyowa tayi daidai Ammi na dauketa da mari jikake tasss! Hawwa ta zabura tana kokarin mikewa ganin yanda Ammi ta zubamata mari but takasa tashi, Ni’ima ta dafe kuncinta tana kallon Ammi da jan idanu, Ammi tace “kika kara maganan banza anan saina sake daukeki da wani marin shashasha” Ammi takalli Baban Yaseer dake tsaye yana kare Hawwa cikeda fushi tace “tashi agaban yarinya na bar wajen nan, tashi nace!” ba musu yatashi ahankali yakoma wajen kofa ya tsaya ranshi in yayi dubu yabaci sabida abinda Ni’ima keyi, Ni’ima takalli Ammi idanunta jajir har lokacin kallon Ammi take tace “kika mareni Ammi? Ko uwata bata taba bari naba saike”?Ammi na kallonta jin maganganun datake rai abace tace “saisa ni nake tayata bawa diyarta tarbiya, kika karamin gara gara anan saina sake daukeki dawani marin, you’re very, very and very stupid Ni’ima hauka kikeso kiyi sabida namiji? Eh?” Shigowa Baba yayi zuwa wajen ya tsaya kusada Ammi babu alamun wasa akan fuskanshi yace “meke faruwa Zainab”? Ni’ima Ammi ta nuna tace “Malam Ni’ima tana daya daga cikin dalilan dayasa Hawwa kenan wajen” azuciye Ni’ima tace “menayi? Nakira yarku na yanke alaka da ita, naja mata layi, bansonta arayuwana dayake mayya ce, bakar mayya mara zuciya ce ita wacce tai kwantai haka ta dinga bina tanajan gwuiwowinta akasa tana rirrikeni tana kuka tana karna rabuda ita, nikuma na tattake hannuwan banzan nawuce nayi tafitata” sosai Baban Yaseer ke kallonta hakama Baba da Ammi yanda take magana kaman ba Ni’ima ba, can a sweet person turn monster over night? Sabida namiji? Ni’ima tace “mijina nawane kadai wlh, ba best friend ba ko kanwata ce saina jamata layi wlh, kugayama yarku tafita daga harkan mijina” nuna Baban Yaseer Ammi tayi tace “ga mijin naki nan ai shiya kawo kanshi nan, dau abinki kubar nan” cikeda rashin kunya tace “eh zan dauki abuna amman saina gama, yar iskan yarku kokarin sumbatan mijina take, mara kamun kai da natsuwa, Hawwa zata iyama maza fyade sabida tsabar bukat……” tsawa Ammi daka mata tace “Ni’ima!” Rai abace sosai tace “nasan waye Y’ata! Jedai ki bincike mijin naki, munsan kalan tarbiyan da muka bata” ganin Ni’ima zatai magana tabi Ammi da chachan baki yasa Baba yakalli Baban Yaseer strictly yace “Aliyu dauki matarka kutafi, mungode Allah saka da alkhairi” cikeda tsantsan rashin kunya Ni’ima tace “ba dole kace ka gode ba anci kudin mijina an koshi, yazo yabiya kudin asibiti da kudin magani, mayu kawai kwadayayyu masu neman kai da yars……” fizgota Baban Yaseer yayi yajuyo da ita tai facing nashi ganin abin nata yazama hauka yadaga hannu zai kwasa mata mari Baba yace “kul!”


