DA BAN SAN SHI BA
DAGA FAUZIYYA D. SULAIMAN
Sai gab da magariba suka fara isa cikin gine-genen binni, basu da suke ido biyu ba hatta masu bacci ma sai da suka farka, domin jin yanda sauran ‘yan’uwa suke ihu da shewar ganin manyan gine-gine abin da basu taoa gani ba, su yara ne k’anana da yawan su basu ta6a zuwa binni ba, iyakacin su babban garin dake kewaye dasu wanda babu ginin bene ko daya a cikinsa, banbancin sa da garin su ginin bulo ne kawai, domin suna gine-gine da bululluka sa6anin k’auyen su wanda da bulon k’asa kawai suke yin gini. Sai da magariba suka isa cikin garin kano kano wanda nan ne inda yaji malamin nasu yana sanar dasu zai ajiye wasu, sai dai abin da ya bashi mamaki bai wuce ganin an fara sauke wasu daga cikin su a wasu makarantun ba, sai yaji malam Habu d’in na yana fad’in da kad’an zai tafi zai bar sauran nan, domin shi can wajan zariya zaiyi, a can makarantar su take, cikin wad’an da aka sauke harda abokin sa Idi hankalinsa ya tashi kwarai da gaske sanda yaga an sauke Idi a wata makaranta, ya kalli mal. Habu cikin rud’ani yana fad’i. Malam don allah ka barni anan nima, ka barni tare Idi. Mal. Habu yayi masa dakuwa yana fad’in kaci gidan ku, kaine zaka sanar dani abin da ya dace nayi, kalli ya wan ku, ya yazan iya barinku guri d’aya, ni kaina bazan iya rike ku duka ba balle shi da zai mini alfarma. Haka aka wuce dasu yana hangen idi yana hawaye, dukkan abubuwan burgewa na binni da suka fara sanya su farin ciki yanzu sun daina burge shi yanzu kwata-kwata. Tafiyar su kayi tsakanin inda aka suke idi da inda suka kara tsayawa bubu nisa, ANSAMU MATSALAR SHAFI. Malamin ya kallesu da kulawa ya shafa kansu yana fad’in masha allah, kar ka damu malam habu zamu rik’esu kamar yanda ka bayar dasu za’a kula da karatun su insha allahu, ubangiji yataya mu rik’o. malam habu ya kad’a kai da gamsuwa yana fad’in amin summa amin.
Sannan ya sanya hannu cikim aljihunsa ya mik’awa malamin, ya kalli su alu yana murmush. To yara ayi kartu sosai, idan lokacin saduwar ku da iyayan ku yayi zanzo na d’auke ku kowa ma kai shi ya gansu, baku da kowa anan sai wannan bawan allah. Ya nuna mal. Sadau da hannusa muza mu wuce sai allah ya k’addara saduwar mu kuma malam. Rabe ne ya iya amsawa da amin alu kam bin sa yayi da kallo idon sa na zubda hawaye yana rumgume da buhun kayan sa, har mal. Habu ya jiya ya fara tafiya ya nufi motar dake tafe dasu kai tsaye ya shige, mal. Saudau ya kalle su. “Yaya sunayen ku yake ne? Rabe ne ya fara fad’ar sunan sa sai alu shima ya fad’i nasa, ya girza kai da gamsuwa, yana fad’in to daga yau nine baban ku kuma babar ku, dukkan abin da ya dame ku ni zaku gayawa, zaku kai kayanku waccan rumfar ku sami guri ku ajiye ta, annan zaku dinga kwana, tun da asuba ake fara karatu idan gari yayi haske sai ku fita ku samarwa kanku abin da zaku karaya, wajan k’arfe goma na safe zaku fara zama karatu sai k’arfe d’aya zaku fita bara
Nan ma zaku samu abinci rana karfe hud’u za’a k’ara zama a makaranta sai karfe shida za’a tashi, bayam karfe tara na dare za’a kara zama sai karfe goma shad’aya za’a tashi idan ba’ayi ruwa ba kenan, idan kuma anyi ruwa ba’a karatun dare, duk karshen sati kowa zai kawowa malam kudin laraba, watarana kuma za’a tafi gona ta can bayan gari ayi noma, ai daman kun iya noma ko?
Gabadaya suka amsa da eh yayi murmushi daidai lokacin da aka fara kiraye-kirayen sallahr magariba ” yauwa maza ku tafi ku ajiye kayan naku ku d’auro alwala ku wuce masalaci kuyi sallah.
Ya wuce da sauri ya fara tafiya suka bishi da kallo Rabe ya fara tafiya “Zomu tafi mana. Rabe ya fara tafiya Alu yayi tsaye kamar bazai motsa ba sai kuma ya fara tafiya yabi bayan Rabe, har suka isa cikin rumfar, Rumface da aka rufe saman ta da kwano sannan aka zagaye ta da katakwaye, amman guraren da yawa sun cinye don haka aka toshe suda tsummokaran kayan almajiran, akwai akwatina zube da buhunan da gana must go a gurin, k’aton guri ne da kusan mutum hamsin zasu iya kwanciya,
Akwai wasu almajiran wad’an da basu tafi masallaci ba, akwai tarin alluna a gurin da yawa, Idi da Alu suka k’arasa suka tsaya suna karewa gurin kallo, yaran da suke cikin gurin suka bisu da kallo, wani k’olo ya iso zai shigo ya tsaya yana kallon su sai ya kaiwa k’eyar Alu duka yana fad’in ” kuwuce mana kuyisami guri ku zauna.
Alu yayj taga-taga kamar zai fad’i amma bai fad’in ba, Rabe ya wuce da sauri ya sami guri ya zauna, Alu ya isa ya zauna a kusa da shi, abu na farko dake damun su shine yunwa gashi ance zuwa zasu yi su nemo abincin dazasu ci, suka tsaya suna kallon kowa yana harkarsa, wani daga cikin almajiran wanda bai wuce shekarun su ba ya k’arasa ya zauna a kusa dasu yana fad’in.
Sannun ku, yanzu aka kawo ku? Suka daga masa kai alamar eh, yayi murmushi yana fad’in “sunana Isa kuna jin yunwa ko? D sauri suka k’ara daga masa kai alamar eh, azaton su abinci zai ce musu gashi amman sai suka ga ya k’ara murmushi yaci gaba d magana. Sanda aka kawoni nima haka naji yunwa kamar zanmutu gashi bansan kowa ba,
Kuma bani da ko kwabo haka na kwana da yunwa ban san daga zuwan mutum zai fara bara ba, nayi tsammanin wanine zaizo yabani, idanzaku bara ku taso mu tafi.
Alu yayi jagale yana kallon yaron, Rabe ya mike da sauri yana fad’in “Taso muje.
Suka mik’e da sauri, Alu ya kalli kayan Rabe sannan ya kallesu.
“Kayan kaka kuma fa? Ya tambayi Rabe “meza’ayi d kayansa, kaima ka aniye naka anan babu wanda zai d’aukar maka, baka ga kayan mu anan gurin a ajiye ba muma. Yaron ya bashi amsa ya nufi wani gurin wani buhu ya bud’e ya d’auko roba k’ok’on bara ya kifa akansa, ya kalle su “ku taho mu tafi.
“Amman bamu da kwano famu. Rabe ya sanar dashi. Kuzo muje mu samo a can sai ku dinga yi da barar kwano idan muka shiga gida.” Suka kad’a kai suka bishj a baya, har lokacin Alu ya kasa sakin jikin sa, tinanin Innar sa yana dumun sa a ransa, yana jin dama ya sani daya tsaya sunyi sallama bai falla da gudu ba, ya taho bai yi sallama da ita ba.
Also Read:
Da Ban San Shi Ba Book 1 Chapter 1
Da Ban San Shi Ba Book 1 Chapter 2
Jama’a suna ta sallah su kuma suna yawon bara, tun da suka fara tafiya garin ya fara had’ewa da hadari aka fara iska, Isa ya kallesu yana fad’in.
[Kunga hadari ya had’o gashi ba’a samun abincin a irim wannan lokacin da sauri, nizan dinga shiga idan na shiga gidan faruko kai sai kashga na biyu kai kuma ka shiga na uku. Yan magana yana nuna su, suka amsa masa da daga kai alamar to, haka d’in suka fara yi sai dai bai fi gida uku suka shiga ba aka fara ruwa, isa yafito daga gidan da yake da gudu yana fad’in ku tuho mu koma kada ruwa yayi mana duka. Ya fara gudu suka rufa masa baya suna gudu, suna gudu ruwa yana k’aruwa, har suka isa rumfar su suka shige, abin da ya basu mamaki bai wuce ganin rumfar ta cika da mutane ba, kowa yana neman gurin kwanciya, ga ruwa yana shugowa ta gefe da gefen rumfar, Alu da abokansa suka fara k’ok’arin neman gurin daza su raba su kwanta, sai dai abin ya faskara domin duk inda suka raba sai a hankad’e su, daga k’arshe Rabe da Isa suka sami gurin suka ra6a amman Alu bai samu gurin kwanciya ba sai can karshen bakin kofar ya samu ya rabe amman gurin bai isheshi kwanciya ba sai zama yayi, rabin k’afafunsa ruwa na fesowa suna jikewa haka ya zauna shuru yana karewa daran ubangiji kallo. Acan kasan zuciyarsa tinanin innarsa yake yi, kota kammala abincin dare, ko ta sami wanda ya iza mata wuta, ko a wane halitake yanzu, wannan shine abin da ya sanye bai jin dukan ruwan dake sauka a rabin jikinsa, har zuwa sanda bacci ya d’auke shi. Ya waye gari asuba tayi an fara tash cikin gaggawa kamar masu shirin zuwa lahira, wasu na nufar gidaje barar ruwa domin basu da ruwan sai sun bara tukun, wasu kuma na tsugunnawa gaban ruwan da ya taru cikin dare suna alwala da wanke bakuna su, shi kam ba zai iya amfani da ruwan k’asan ba, ga shi kuma bashi da robar dazai barato haka ya zauna shuru har aka fara karatun asuba, babu sallah balle wanke baki shima ya shiga sahun karatun, sai dai yunwa ta sanya shi bai fahimtar dukkan karatun da ake masa, ga kuma tinanin innarsa, wannan itace rayuwar da mahaifinsa ke sanar da shi zaiyi mai dad’i a binni, shi dai baiga wani abin dad’i cikin wannan rayuwa bayan bak’ar wahala ba, yana zaune yana karatu yana kuka. Yana jin kamar ya gudu ya koma gurin innarsa wacce bai san halin datake ciki ba a yanzu, amman yasan babu hali yin hakan domin bai san inda zai bi ya sadu da garin suba.
AKWANA A TASH…
Wata guda ya k’are ga Alu, dukkan yanda yaso ya saba da wannan rayuwar ya kasa, idan akwai abin dake wahalar da rayuwarsa bai wuce rashin abin da zai ci ba, da yake damuna ce mutane masu gidajan kan su ma suna fama gurin samun abin dazasu sanya a bakin salatin su balle almajirai, sai dai ya fara sabawa da rayuwar wahala da kwarzaba manyansu da jama’ar gari, ya fara fahimtar karatun sosai, ya fahimci dalilin da yasanya mahaifinsa ya dage ya taho, wato idan mutum yana jin matukar yunwa yafi dagewa yayi karatu, amman a wani 6angaren yana ganin kamar bashi da gata. yau an wayi gari cikin mamakon ruwa daya hana kowa fita, hatta kasuwa a ranar ba’a cita cikin dadin rai ba, domin mutane da dama sun yi zaman su cikin gidajan su, wannan ya sanya dukjan wani mara gata zai shiga garari gurin neman abin da zaici da makwancin dazai dora hakarkarinsa, kasancewar ranar juma’a babu makaranta haka Alu ya wuni yana gararanba a gari gurin neman abin da zai sanya a cikinsa, dama tini sun raba gari da Rabe, domin shi ya tare a gidan katuwai idan ya tashi daga makaranta can yake zuwa yayi musu aikace-aikace kamar wanki da siyan taba da wanke-wanke suna bashi abinci da kud’ad’e, Alu ya fara bin sa da farko sai dai daga baya daya kula da abubuwan dake faruwa a gidan ya tabbatar w kansa ba zai iya ci gaba da zuwa ba ya watsar, ya gwammace yayi tabi gada-gida yana bara da neman abincin da zai sanya wa uwar hanjinsa.
Magariba ta kawo kai babu komai a cikinsa sai ruwan koko d aka bashi a wani gida tuni da farar safiya, ya dawo makaranta ya zauna cikin abokan karatunsa yana ware ido ko wani zai yi masa tayi ko ya rege ya bashi, sai dai babu kowa a gurin kowa ya kama gabansa sai tilin kayan su dake zube a gurin, ya zauna shuru cikin rawar jiki da ciwon kai, ga zazzabi yana neman saukar masa. Ya dai kula zaman na shi bashi da amfani don haka ya k’ara fita cikin ruwan marka-markan ya fara bin gidaje yana barar, ya shiga gida ya kai goma amman bai sami komai ba, ya shiga Gida na shadaya kafarsa ta fara nauyi saboda gajiya da wahala, gadan babu kowa sai cha6ali, fitila ta dallare tsakar gidan ya fara rere waka irin ta Almajirai.
“Iya Allazi wahidin, Iya ina sadaka, Iya ko d’an k’anzo ne, Iya yunwa nakeji ki taimaka mini dako gaya ne, Iya yunwa bata da hankali.” Kusan minti d’aya yana ta kala bara babu wanda yace masa ko kanzil, ya yanke k’auna ya juya da zummar barin gidan saiyaji muryar wani yaro ya kwala msa kira.
” Kai almajiri zoka amsa.” Dad’i ya cika shi ya nufi cikin gidan d gudun sa har yana tuntube, bai kula da cabalin dake tsakar gidan ba ya nufi kofar dakin daya jiyo muryar yaran.
“Gani. “Alu ya fad’i cikin zumud’iwata mace ta leko daga cikin dakin hanzari tana duban Alu.
Yaya akai yi ‘Dan malam? Alu ya durkusa cikin sauri. Ina wuni Inna?
“Lafiya lau” ta amsa cikin gaggawa gami da k’ara kallonsa cikin tuhuma ta hasken kwan lantarki daya dallare tsakar Gida.
“Yaro ne ya kira ni, yace nazo na amsa daman.” Alu yayi magana cikin rawar baki da neman taimakon ta.
“Anan gidan? Ta k’ara tambayar Alu cikin gatsali. Alu ya daga kai alamar eh, matar tayi murmushi gami da fad’in. “Shkiyanci ne irin na d’an baba haka yake yiwa alamajirai, mu kammu bamu koshi ba balle muyi k’ok’arin baiwa wani, Allah ya baka hakuri d’an malam.
Jikin Alu yayi sanyi ya mike salo-salo yayi hanyar fita, domin ya sanya rai kwarai da gaske, zuwa yanzu ya fara jin yunwa kamar zai fad’i, haka ya lallaba ya fice daga gidan.
Haka yaci gaba da gararamba amman bai da ce ba, har dare ya fara yi shu ya fara d’aukewa, cikin ransa ya fara tsanar jama’ar garin domin ya kula basu da tausayi, dukkan halin dayake ciki babu wanda ya taba tausaya masa.
Wajan k’arfe goma shad’aya ya koma makaranta, kusan dukkan almajiran sunyi bacci, sai wasu matasa guda biyu dake zaune suna hira suna cin gurasa da nama a takadda suna ta dariya,
Sune manyan a makarantar tasu, ya karasa kusa dasu ya tsugunna daga gefe su yana lasar baki, fatan shi su yadda takaddar ya d’auka ya sid’e domin yasan ko yafi k’oda naci baza su bashi ba, suna kallon shi sarai suka ci gaba da hirar suna cin abinda suke ci.
Wasu matasan guda biyu daga cikin samarin suka k’ara shugowa, suka hago sauran suna cin nama da gurasa suka nufesu da gudu suka dasawa abin wawa, gabad’aya suka 6ata gurin yayi kaca-kaca rabin gurasar ta zube a kasa, Alu ya hango wata datayi gefe ya nufeta da sauri ya mik’a hannu zai d’auka ashe daya daga cikin samarin ya hango shi ya bish da sauri ya take hannunsa gami da hankad’eshi gefe, Alu ya fasa Ihu gami da rike hannun nasa yana kuka.
Wanda ya taka masa hannun ya bishi da harara yana fadin “Shige dan uwar ka mu sa’annin kane da muna cikin abu zaka sanya mana hannu! Cikin gunjin kuka Alu yace “Yunwa nakiji, tunda safe ban ci komai ba.”
Wanda yake gefansa ya k’ara masa wata harara yana fadin “Ina ruwan mu da rshin cin abincin ka, muma da gumin mu muka samo, ubanwa ya hana ka kasamo abinda zaka ci?
Na ukun yace “Wallahi yaran nan kukan dad’i ma suke yi, sanda muna kamarsa mun isa mu shiga gardawa har mu sanya musu hannu cikin abinci, da kuka samu bamu cewa ku barato mana abincin ko?
Wai baku kula shi ba? Wannan yaron tun ranar aka kawo shi yak’i sakin jiki da kowa, wad’anda yake bi d’in ma ya daina binsu yanzu, bashi da aiki kullum sai kuka, yaro na gaya maka kuka yanzu ka fara domin nan ne gidan ku, nan ne gurin rayuwar ka har abada.”
Alu yana jin dukkkan bayanan su yana kuka, ya rarrafa yaja jikinsa ya koma gefe ya kwanta, jikinsa ya fara zafi, ga yunwa ga taka hannu da aka yi masa, ga kuma uban sanyi, tinanin Innar sa ya dinga dawo masa, shi yana cikin wannan halin ita ko yaya take ciki.
Yana daga inda yake yana sauraran Garadan suna ci gaba da hirar su, sai yaji d’aya daga cikinsu yana fadin.
“Nifa yau bazan 6ulla tashar nan ba, domin na sami abin da zan kashe daga nan har sati guda.”
Na biyu yace “Wai ku Bala baza ku daina wannan abin ba, kanku kuke cuta f, iyayan ku sun kawo ku karatu amman kuma neman lalata rayuwar ku.
Na ukun yace “Ai sun riga ma sun gama lalatawa, ni ina tausaya musu duk randa malam ya gane halin da suke ciki wallahi sun shiga uku.
Wanda aka kira Bala ya mike yana huci “Sai me don ya gano, daman nagaji da zaman gurin nan idan naga zai mini zara sai na bar shi, nifa yanzu ina da wanda zai iya bani gurin da zan zauna har karshen rayuwata, kuma ba don na samo ba kwa kwaci nama da gurasar nan, dare daya fa zai baka naira d’ari, har d’ari da ashirin badawa yake yi mutumin nan”
Na farkon yace ” Kaji Banza meye Naira d’ari d’ariko dubu d’aya yabaka a banza, ya kamata dai wallahi kusan Annabi ya faku.
“Bala ya fashe da dariya ” Baza ku gane abin da muke nufi ba, ni yanzu can zan zagaya ma, nasan cikin daran nan zan iya samun dari biyar bayan an cika min ciki da abinci da lemo mai sanyi, waye zai rakani?
Su biyun suka kalleshi suna fad’in Allah ya sauwake, kaine d’an wahala, sai kaje kayi tayi.”
Na ukun kuma cewa yayi ” Na gaya muku bazan 6ulla ba yau, ma had’e gobe.”
Bala ya nufi haanyar fita yana dariya, gami da fad’in “Babu damuwa abokina.
Alu dake kwance cikin rawar d’ari yana jin dukkan abin dake faruwa, a ransa yana ta sak’awa da kwancewa, me Bala yake yi yake samun wannan kud’in a dare d’aya, idan har zai iya samun ko da abinda zai dinga ci kullum ne ai shi zai iya yin abinda nan, domin fatan shi a yanzu ya sami inda za’a dinga bashi abinci ko dasaud’aya ne ma arana, yayi ta yawo yana neman gidan da zai yi aiki bai samu ba, amman yana jin kamar yabi Bala ya gwada irin aikin da Bala d’in yake yi, ba tare daya kammala yanke shawarar da zuciyar saba ya mike domin jin Balan na yin nisa da inda yake, sauran gardan basu kula da shi ba domin sun ci gaba da hirar dune kawai.
Ya fita da gaggawa daga cikin rumfar sai ya hango Bala yayi nisa ya nufi can hanyar bayan gari, koda yake yaji daman yace tasha zaije, ya taba zuwa tashar bara sau biyu, ya dinga bin bayan bala wanda bai san yana bin saba suka dinga ratsa unguwanni har suka fita wajan gari suka nufi tasha kai tsaye.
Tashar babu kowa sai kukan tsintsaye da karnuka da gyare, babu tsoro Bala ya kutsa kai ya shiga, Alu yana biye da shi , kai tsaye wata rumfa wacce aka zagayeta da kwano ya nufa ya tura yana kallon inda Bala ya shiga yana sak’awa da kwancewa, gurin babu wadatar haske sai kad’an-kad’an, ya sami guri ya zauna yana jiran yaga Bala ya fito shima ya shiga, domin bai son Bala yasan ya biyo shi don kada ya dake shi, yana nan zaune cikin tsananin tsoro da fargaba, domin babu mahaluki ko guda ya hango Bala ya fito daga cikin rufar yana mik’a, sai yaga ya tsaya yana kirga kud’i masu yawa a hannunsa daga inda yake yana iya hangen kudin daga d’an hasken dake ratsa gurin ‘yan goma-goma ne, Bala yayi murmushi ya fara tafiya yana cigba da mik’a, Alu yana le6e daga inda yake yana hangensa har yayi nisa, zuciyar shi tana sak’awa da kwance wa aka ya tashi ya shiga gurin ko kuma kada ya shiga, amman yunwar da yake ji da halin da yake ciki suka tinzira zuciyar sa ga shigar, ya mik’e ya nufi gurin yana waige-waige ya tura kofar..