Uncategorized

Auren Jaruma Zahra Diamond ya mutu itama tabi sahun su Rahama Hassan Saura dawowarta masana’antar Kannywood.

Labarin da muke samu shine fitacciyar jarumar da tayi aure watanni shida zuwa bakwai da suka wuce wato Zahar Diamond ita ma tabi sahun su Rahama Hassan, Maryam ceeter, Hafsat shehu, da sauran su da sukayi auren sirri kuma suka fito daga baya, wanda cikin wayannan zamu iya cewa RahamaH ce auren ta yayi ƙarko da har ya haura shekaru 5 amma sauran baya wuce yan watanni cikin hukuncin Allah ake ganin su sun fito.

Da fari dai tsawon wani lokaci kenan Zahra diamond ta bude shafukan sada zumunta na Instagram da TikTok  tana wallafa yan abubuwanta na nishadi sai dai a kwanakinnan ne abubuwan suka chanza salo inda take wasu video da kananan kaya kuma ba dan kwali tana kuma raye raye.

Kasancewar an san jarumar ta dauki mataki na daina amfani da duk shafukan sada zumunta kafin auren ta, hakan yasa alamomin tambaya kan kasantuwar auren nata, domin abin da mamaki a farkon aure ta daina wallafa koda hoton ta na asali ma ta goge dukkan shafukan ta hatta masu shafukan masoya wato fans page sai da ta roke su dasu goge hotunan ta, amma Sai aka ganta ta bude shafin tiktok tana tikar rawa daga baya.

Mun fara bincike kan al amarin inda wata majiya ta tabbatar mana da jarumar auren ta ya dan kwana biyu da mutuwa, kawai dai bata bayyana bane wanda hakan yasa muka tuntubi wani producer dake da alaka da jarumar mai suna Sunusi Multimedia da zummar ya bamu number ta ko ya hada mu da ita, sai dai jarumar ta bada sako a gaya mana cewa a sanda ta tashi auren ta ba dan jaridar da ta gaya wa da haka bataga dalilin da zaisa yanzu a dame ta da auren ta ya mutu ko bai mutu ba!!!?

Da fatan Allah yasa haka shine mafi Alkairi.

Back to top button