Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 43 Hausa Novel

Ta ɗan jima tsaye jikin ƙofan tana tunanin ta shiga ne ko kar ta shiga? Da kyar ta tattaro kuzarinta ta ɗan yi knocking kan ta tura kofar ta shiga gabanta na tsananta faɗuwa.Hasken ɗakin ba shi da wani yawa don haka tsaf take kallonshi zaune tsakiyar gado jingine da pillow gabanshi system ne yana kallo, idanu ya ɗan zuba mata tana tahowa a hankali har ta isa jikin gadon ta ɗayan side ɗin inda shi kuma yana jingine ne da side ɗin da ya saba kwanciya.Muryarta na fita a hankali cikin tsoron faɗan shi ta shiga furta “Na na..zo ne mu yi sallama na ji wai za kayi tafiya, kuma ina so ne in baka haƙuri wlh ban san kalmar ba zata yi maka daaɗi ba. Don Allah kayi haƙuri.”Tun da ta shigo ya ɗauke kanshi daga kan system ɗin ya zuba mata ido sauƙar muryarta a kunnuwanshi ya sa Ya ɗan lumshe idanun ya sake buɗewa a kanta. chan ƙasan muryarshi yace”Zo nan.”Bai cigaba da kallonta ba sai ya mayar da idanunshi kan system dake aiki gabanshi wanda kallo yake na wani horror movie, tun da yayi shirin kwanciya tunaninta ya so ya dameshi sam shi bai ma san me yake damunshi ba daga dan kusancin da suka samu kwana biyu shikenan kuma sai a ta shiga lokacin hutawarshi ta hana shi hutawa da tunaninta? System ya jawo ya fara kallon dole sai kuma Allah ya jefo ta.A hankali ta hau gadon kamshinta na dukan shi har yana jin bugun zuciyarshi na sauya wa.Idanunshi ya kai ga kallonta ganin tana chan nesa ya ce “Matso nan”Ya taɓa gefenshi, a ɗan tsorace cikin bugun zuciya ta matsa tana dana sanin zuwanta ɗakin don ji take kaman zuciyarta za ta fito daga madaukarta don tsabar bugu, inda hannunshi yake ta matsa kaman an ce ta kalli fuskan computern aka nuno wani abin tsoro da ya firgigita don ta tsani film mai abin tsoro za ta gudu ya riƙo tsintsiyar hannunta babu zato sai gata bisa kirjinshi daga gefen kafadanshi ya mayar da hannunshi na wurin ta bayanta inda tayi saurin binne kanta a kirjin nashi sihirtaccen kamshin shi na sake shiganta yana ƙara bugun zuciyarta, baya baya yayi ya jingina da gadon yana sake kara kusantar da ita jikinshi.Bai ce komai ba ya cigaba da kallon yayinda tayi shiru kawai tana sauraran bugun zuciyarshi, sun kwashe sama da awa guda a haka ko da ya gama ya ɗan ɗago ta zai yi magana kawai ya ga tayi bacci, ya san kwanakin tana ƙoƙari kuma bata samun isashen bacci yadda baya yi itama bata yi, gwara ma shi da safe ya kan taɓa amma ita ko da safen baya ganin tana yi sai zirga zirga.Hijabin ya zare mata ya jefar ya zubawa fuskarta idanu yana kallo, bai san me ya riƙe shi a fuskar ba ya dai tabbatarwa kanshi da she’s Drop-dead gorgous wanda bai taɓa fahimtar fuskar ba irin yau, kallon natsuwa yake binta dashi da ya rasa dalili a hankali ya furta “what’s wrong with me?”Ya kai hannunshi ɗaya yana jin zuciyarshi na pounding har sound ɗin na iya shiga kunnuwanshi…Yana so ya kwantar da ita akan pillow amma sai ya ji ba zai iya ba don haka ya gyara kwanciyarshi ya gyara mata ta yadda rabin jikinta na a nashi ya lumshe idanu ga mamakinshi tunaninta ya cigaba da yi Dukda gata jikinshi da kyar bacci ya ɗauke shi.Basu farka ba har aka shiga masallaci suratul Fatiha da ake karantawa shi ya farkar dasu duk su biyu lokaci ɗaya ta yi saurin Miƙewa zaune tana ɗan matsawa kanta ƙasa, ya ɗan kalleta kadan yadda tayi kaman wacce aka kama tana sata ya sa ya ɗan yi murmushin da bai fito ba ya sauka ya shige toilet, hijabinta ta ɗauka ta sauƙa ta gudu.A bayi ta tsaya tana kallon kanta, bacci fa ta sake yi a jikinshi comfortably? Wayyoo Allah ta ayyana a ranta tana dafa zuciyarta, gashinta da tayi parking cikin messy burn ribbon ɗin ya fice bata ma san ta baro a ɗakin ba, da kyar ta haɗa tunaninta wuri guda tayi alwala tazo tayi sallah ta kwanta a wurin, sai Eight ta fito a shirye cikin Abaya Grey da yayi mata kyau sossai hula ne a kanta kai tsaye taje ta dubo abincin taga wanda zai iya ci ne ta kwaso ta kawo sashen nasu ta shirya dining ta saka turaren wuta a parlorn don a gyare yake tsaff yana kyalli ta juya zata koma ya buɗe kofa ya fito, kallonshi tayi yana sanye da wani Army Green riga tare Black wando da ya amshe shi, rigan ya kama shi ya fitar da kirarshi sossai bai mishi ruwa ba sam sai taji wani nauyin shi ya rufeta ta mayar da kanta ƙasa, ya kalleta ya ɗan shafa gashin kanshi kaman zai yi magana kuma sai ya nufi dining kawai.Binshi tayi sai da ya zauna tace “Ina kwana?””Kin tashi lafiya?”Ya bata amsa ko numfashi bai bari ta ƙarasa saukewa ba idanunshi na akan fuskarta sai kawar da ido take daga kallonshi wanda hakan ma dariya ya bashi amma ko a fuska bai nuna alamu ba, ta haɗa mishi abin kari da yau English breakfast suka yi a gidan ta tura mishi, bata so ta tafi tayi laifi don haka ta ɗauki omlet ɗaya ta haɗa tea ta ja kujerar da take zama chan nesa dashi ta zauna tana karyawa, bai ce mata komai ba itama bata ce ba.Bayan ya gama ya miƙe ya koma ɗaki ta bishi da kallo tana ɗan taɓe baki mutum kaman hawainiya, tattare wurin tayi tsaf kaman ba’a ci abinci yanzu ba ta wuce nata ɗakin, monday za ta fara waec don haka dole ta fara duba takarda kafin taje ta faɗi sai ta fara lalabo takardunsu na makaranta ta ɗauko wayanta ta fara bincike akan past questions da take son fara dubawa.Shi kam kusan sai da ya gama haɗa duk abin da zai buƙata lokaci lokaci yana dan daakatawa ya tafi nazari kaman wanda baya kaunar tafiyar kan ya ɗauki keyn mota da wallet ɗin shi ya fito sanye da wata White sneakers da ta sake fito da shigar tashi idanunshi ya rufe da baƙar space sai ya zama kaman wani model ya san kan wanka ba laifi, a babban parlor ya samu su Abeeha suna ganinshi kuwa suka miƙe tsaye don dama sun shirya saboda sun sanshi yadda ya washi jira sai dai a jira shi…Har sun nufi kofa yace “Ina take?”Duk tsayuwa suka yi Abeeha na so ta tambayi ita wa amma fuskar shi da ba’a sake ba yasa tace “Afeefah ina ga bata san da ita za’a yi fitan ba bari na ƙirata”Ta ƙarasa tana nufan sashensu a ranta tana adu’ar Allah ya sa ita yake nufi kafin ya fara mata masifa, sai taga ya fice daga parlorn jannah ta bi bayanshi. Zaune ta sameta hankalinta kwance “Tashi maza ɗauki gyalen ki muje””Ina za mu?””Shopping Ya Rayyan ya riga ya fita yi sauri kafin ya hasala””amma ni ba abinda nake bukata fa Adda Abee…””Ke wlh tunda ya neme ki sai kin je, gwara kin tashi”Bata fuska tayi don wlh bata son zuwa ko ina, kai Abeeha ta gyaɗa “Ki same mu a mota kuma ki yi sauri”Miƙewa tayi ta chanza Abayar jikinta zuwa wani orange, ta saka farin takalmi tayi wrapping kanta da farin Jersey veil ta ɗauki wayanta ta nufi waje har lokacin fuskarta ba’a sake ba.Tun da ta fito ya zuba mata idanu ta cikin glassses na idanunshi yana kallo, a fuskarta ya tsayar da idanu yadda take dan ɓata ran ya bi jikinta da kallo Dukda ko ina a rufe yake sai da ya ɗan ji wani iri, tafiyar ta kaman tana rausaya Dukda ita sauri take, bai ji haushi ba idan ma zai yi judging wani gefen na zuciyar tashi akan gaskiya zai ce he enjoyed the walking ba tare da ya san dalili ba, tuni su Abeeha suna baya dole ta buɗe gaba ta shiga ya ɗan lumshe idanu saboda kamshinta da ya shige shi ya buɗe tare da tada motar ya fice daga gidan.Su Abeeha sun zaci ba zasu wuce shopping malls da suka saba zuwa ba na nan kusa kusa ko market square ko barnawa shopping complex sai suka ga ya miƙa ma yayi chan unguwar rimi bai tsaya ko ina ba sai Kaduna Galaxy Mall yayi parking suka sauƙa tana shirin sauƙa yace “Ki ji!”Ta ɗan kalleshi tana dawowa ta zauna “Na’am Ya Saraki?”Ya zare glass ɗin ya kalleta sai ta kawar da kanta, kaman zai mata gargadi akan wannan sarakin da take faɗa take motsa mishi zuciya sai ya fasa.”Kina ɓata rai babu abin da kike buƙata ne?”Ta Yi mamakin yadda ya karance ta Dukda tunda suka fito babu wanda yayi magana a cikinsu.”Kin min shiru ina magana?”Ya faɗa ba da faɗa ba…”A’a akwai, za mu fara waec monday akwai abubuwan da nake buƙata na makaranta sai da na fito na tuna”Bayan ta gama bayanin kuma sai ya mata shiru ta ɗan sake haɗe fuska shi baya son shiru amma ya ƙware a yi wa mutane banza, sauƙa tayi ranta ba daaɗi su Abeeha har sun shige ita yanzu ina ta nufa ba zuwa ta taɓa yi ba ganin a kyau da tsarin shi ya bambanta da wanda suke zuwa da Abeeha.Wayanta ta duba don ta ƙira Abeehar ma ta ji inda suke su tafi da ita taga katin ta ya kare ta ɗan yi taku biyu tana furta”Oh! ashe ba ni ma da katin, to yanzu ina zan yi??”A karye tayi maganan tana sauƙe hannunta ƙasa, babu zato babu tsammani taji ya sanya hannunshi na dama cikin nata na hagu ya gimtse, da sauri ta kalleshi kaman ba shi ba dole ta fara Binshi sun zaga sossai har wurin kayan makaranta ta ɗauki duk abinda take so suka dawo wurin turaruka ya ɗauki turarenshi ita bata bukatar komai don kayan aurenta duk babu abinda ma ya dauki hanyar ƙarewa suna nan set set, a wurin biya suka ga su Abeeha.Abeeha da ta hange su daga nesa ta taɓa jannah “Addah Jannah kalli ki ga…!”Jannah ta waiga tana kallonsu suna tahowa sun yi matuƙar kyau da dacewa fiye da yadda baki zai fasalta, da sauri ta ɗaga wayanta ta fara musu hoto tana murmushi ganin zai ɗagota tayi saurin sauƙe wayan tana cewa Abeeha “haƙiƙa ba ƙaramin sa’a Afeefah ta taka ba, samun soyayyar namiji irin Ya Rayyan….Ya Allah i just can’t imagine..”With so much excitment tayi maganan. Abeeha ma tace “Wlh shima yayi dace Mata Kaman Afeefah are very rare sun dai dace kawai duk su biyun they Look so breathtaking”Gab da su ya saki hannunta ya zaro Atm ya biya aka hada musu komai nasu suka nufi mota, bayan ya shiga ya kunna Ac ɗin sai yaji baya ba da iska kaman gas babu tsaki mai ƙarfi ya ja ya kunna motar suka fice yana sauƙe glass a hankali.Kwanciya tayi ta lumshe ido jikin kujera tana sauraron dukar da zuciyarta ke yi, hannunta da ya riƙe throughout ta kaishi fuskarta ta shafa tana sake sniffing kamshin da ya bar mata har lokacin tana jin softness na hannun cikin nata, bata san sun yi nisa ba sai da suka zo last danger na ɗaukar hanyar gidansu ta ɗan buɗe idanu sai taga wasu maza a cikin napep suna kallonsu kaman an ce ya kalli wurin ya sake jan tsaki ya miƙa hannu ya dage glass ɗin ɓangaren ta har sama, ta ɗan kalleshi bai ko kalli inda take ba ana sake su yayi kwana zuwa gida.A yanzu bai ɓata lokaci ba don idan ya tsaya batawa zai iya makara gashi takeoff din nasu 12 ne dot. Wurinta ya fara shiga tana zaune kawai ta ganshi ta miƙe tsaye.”Zan tafi.”Tayi mamaki kwarai don ita yana kasheta da mamaki a tsakankanin.”Allah ya tsare ya ba da sa’a ya kuma dawo da ku lafiya.”Ya amsa da Ameen a kan lips ɗin shi yana kallonta.”Ina fata kina sane da jiya ba yau ba ne, bana son yadda kike fita school anyhow make sure kin saka ko hijabi ko ma Abaya before going in ya so in kin isa ki cire, just focus on abin da ya kai ki. Ki kula sossai don ina da matuƙar kishi akan abin da nake so.”Yana kai nan ya ajiye mata bundle na 1k guda biyu a kan gadon ɗakin ya juya ya fita.neman faɗuwa tayi ta samu wuri ta zauna tana jin kalaman nashi na dawo mata “Kishi akan abin da yake so? Waye yake son?”Da sauri taje gaban madubi tana kallon kanta sai ta girgiza kai ba dai ita ba kila bata ji da kyau ba ko kuma kariyar nashi irin na ya da kanwa ne.Jikin Window taje ta tsaya tana kallonshi yana magana da duka ma’aikatan gidan sama da mintuna biyar kan ya shiga mota wanda ba ma dashi suka fita ba ya ja ya fice daga gidan, saƙon Shigowar message taji ta janyo wayanta sai ta ga kati ne mai yawa aka saka mata ta kama baki ta riƙe mamaki na so ya kasheta da ranta data ta kunna sai taga hoton da Jannah ta ɗauke su ne ta turo mata sossai hoton ya mata kyau har bata san ta saki kyakyawar murmushi ba tana shafa fuskar wayan…

Back to top button