Uncategorized

Maganin Kaikayin Jiki Da Mara Ga Maza Da Mata

 

A mafi yawan lokuta idan muka yi wanka kaikayi kan damun jikin, hakan kansa mu rasa inda za mu saka kanmu, ko kuma ƙaiƙayin mara wanda mafi yawan wannan matsalar ta fi shafar mata, to yau insha Allahu zamu kawo maku yadda za ku magance wannan matsalar da ikon Allah sai dai a sani cewa shi magani sababi ne na waraka.

Ga mahaɗan maganin kamar haka don haka sai a natsu a karanta:

  1. Na farko a samu ruwa kofin shayi Uku
  2. A samu citta danya ko kuma wadda ta bushe
  3. A samu garin kanunfari karamin cokali
  4. A samu tafarnuwa curi ɗaya ma’ana kwallo ɗaya a daka ta.
  5. Sannan abu na karshe shi ne a samu garin kurkur shima cokali ɗaya.

YADDA ZA A HADA MAGANIN

Wannan ruwan kofi Uku za a ɗora shi a wuta, sai a samu citta kamar guda biyar da tafarnuwa kwallo ɗaya, amman ya zama cewar cittar da tafarnuwar an daka su, sannan sai a dauko garin kanunfari da kurkur a haɗe su duka a tafasa. Bayan sun tafasa sai a tace. A raba ruwan gida Uku asha da safe bayan anci abinci sannan asha da rana sannan sai da daddare.

AMFANIN WANNAN HAƊIN

Kafin mu fara faɗar amfanin sa bari mu yi wani ɗan bayani akan haɗin, shi dai wannan haɗin ana son ka samu kamar wata Biyu kana yi, 

  • Yana maganin sanyi mai sa tattare fatar jiki kuma ta yi baƙi.
  • Maganin sanyi mai sa kaiƙayin matse-matsi.
  • Maganin sanyi mai sa yawan fitsari.
  • Maganin sanyi mai sa tsattsagewar matse-matsi.
  • Maganin sanyi mai sa ƙaiƙayin ido.

DOKA

Kada ka sha har sai ka ci abinci, sannan kowa zai iya sha amman banda yaron da bai kai shekara Uku ba.

Allah Ya bada sa a ya biya mana buƙata.

Back to top button