Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 21 Hausa Novel

“Sulaiman?? Har za ka ja da maganan Yaya a kan yarinyar? Aaa lallai, yo ko mahaifinka ya isa ya sauya maganan nan?”Kawu Zubairu ya katse shi a hasale.Shiru Sulaiman yayi sai dai idanunshi tamkar garwashi, zuciyarshi yake jin ya wani matse ya mishi nauyi wane dutse aka ɗora mai, kawai don kawu bai da hali sai a hana shi auren Afeefah? Me laifin ta? Ita me tayi? Har suka shigo Kaduna bashi da natsuwa, da kyar ya kai kowannensu gida suna ta kushe wannan neman auren nashi haka ya nufi gida ko da ya shigo a parlor ya samu Umma, ganin yanayinshi kaman zai faɗi ta miƙe da hanzari ta riƙe shi”Sulaiman! Menene? Lafiya kake kuwa? Ko wani abin ne ya samu Afeefar?” Girgiza kai Yayi yana neman inda zai zauna ta ja shi kujera suka zauna tare, Baaba jummai ma da tun safe take ta adu’ar dacewa ta fito, ruwa ta je ta ɗauko mishi Umma na tsaye kanshi tana ta tambayar shi duk ta rikice ta sanshi da masifar migrine in ya fara kuma baya jin magani, ruwan ya karɓa ya sha sossai tamkar zai fasa ihun kuka yace wa Umma”Umma wai su kawu ba za su nema min aurenta ba, wai ba za su hada zuri’a da ita ba, Umma idan kenan kawunka bashi da halin kirki sai aka ce kaima haka kake? Me Afeefah tayi na kin aurenta? Don Allah ki yiwa Abba magana ya samu Yayanshi zan nemi Afeefah! Zan neme ta duk inda take ni dai don Allah ya bar ni in aureta a haka nake son ta”Duk sun kasa gane inda ya dosa, Abba da shigowan shi kenan ya ce “Ba da Miyau na ba kam, sai dai kuma idan kai zaka nemawa kanka aure wannan kam zaka iya amma tunda har Yaya ya kirani ya tabbatar min gidan chan ba gidan neman aure bane ba zan taɓa sake tado maganar ba don na san ba karya ya yi ba, da kai aka je ai ba da wani ba kuma kaima shaida ne”Idanun da suka sake rinewa sossai ya zubawa Abban yace “Abba ita wallahi ba haka take ba, nitsatsiya ce kuma tana da tarbiya daidai gwargwado, Abba aka auri karuwa da ta tuba ma bare Afeefah? Abba ko ladarta ba za ka bari na samu ba? Korinta fa suka yi bayan sharri da ƙage da aka lankaya mata a garin”A yanzu kam hawaye sai da suka zuba mishi.”Ko ma menene Sulaiman ba a zuri’ar mu ba, ban taɓa saɓa maganan Yayana ba kuma ba zan fara a kan ka ba Sulaiman, ku fara shirye-shiryen auren shi za’a hada da na Munir”Umma ta ɗago da sauri ta kalleshi “Alhj wata ɗaya fa kacal ya saura na Munir yaushe ya gama warke wannan ciwo da zai yi aure?””Ke kenan kike goya mishi baya yayi abin da yake so ko? Toh shikenan kar yayi”Yana kai nan ya wuce abin shi.Baaba jummai kam har hawaye take yi, bayanin abin da duk ya faru yayi musu bayan ya gama ya kama hannun Umma “Don Allah umma ko auren za’a yi min ki taimaka ki saka baki a hada da Afeefah wlh ina son ta, tausayinta kuma yanzu ya sake kama zuciyata har ina jin kaman zai fashe”Duk sun tausaya mata, Baaba jummai ta sha kuka sai Allah ya isa take yi a madadin ta, abin da ya dame su ma kasancewar yanzu ba’a san inda ta dosa ba.”Yanzu ka je ka sha magani ka huta sai ka je ka nemo mana ita in har muka sameta komai mai sauƙi ne, rayuwar ‘ya mace a haka hatsari ne komai zai iya faruwa, imma a yi mata mugun abu ko kuma ta jefa kanta halaka”Duk sun gamsu, Miƙewa yayi ya nufi Sashenshi cike da tunanin ta ina zai fara nemanta?*****Saleem a Washegari aka sallameshi ya koma gida, shi ne ma ya matsa saboda ya damu da halin ko in kula da Mahaifiyarshi ke mishi, ƙannenshi kam ba ya kula su bayan ya dawo wanka yayi ya fito, har kicin ya shiga Talatuwa ta bashi abinci ya zo ya ci kan ya nufi ɗakin Mommy, sossai yake kokarin danne damuwar da yake ranshi saboda Rayyan da yayi ta ƙoƙari wurin ganin ya manta Afeefah ya cire ta a rayuwarshi.Zaune ya sameta bakin gado tana danna waya, sallamar shi kawai ta amsa amma ko ɗago ido bata yi ta kalleshi ba, a gaban kafafunta ya je ya zauna”Ban taɓa tunanin akwai ranar da zai zo da zan yi rashin lafiya har in kwanta na tsawon kwana daya gadon asibiti Mommyna bata zo ta duba ni ba, na san na miki laifi mai girma ne shiyasa na kasa bari in samu lafiya na nemi a sallameni don in zo in nemi yafiyarki, kiyi haƙuri in shaa Allahu na cire Afeefah daga raina…”Ya faɗa a raunane “Duk kuma abin da kike so zan cigaba da so matukar bai saɓawa shari’a ba ko da kuwa zai cutar da ni ne, ki yi haƙuri Mommy”Ɗagowa tayi ta kalleshi sai zuciyarta ya karye, wani sashe na cewa bata yi mishi adalci ba, wani kuwa na bata ƙwarin gwiwa a kan abin da ta aikata ɗin ai taimakonsu ne gabaɗaya.”Zan yafe maka in manta irin rashin kunyar da ka yi min matuƙar ka bi umarnina na karshe a gareka”Ta faɗa cikin tabbatarwa.”Mommy ko me kike so ki faɗa ni kuma zan cika miki ko da bana so””Zan aura maka Sabreena nan da wata guda”Da sauri ya ɗago ya kalleta amma sai harshen shi ya mishi nauyi, uffan ya kasa cewa sama da mintuna uku kan ya ce da kyar “Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi””Ita ce ma Alkhairin naka”Kai kawai ya gyaɗa ya miƙe ya fice fuskar shi babu walwala sam, a parlor ya ga Sameera na zaune, ido ya ɗan zuba mata ganin ta mishi rama kuma ta yi zuru zuru ga damuwa nan fal a fuskarta, kaman zai yi magana kuma sai ya wuce abin shi.****Ta ɓangaren Afeefah ta tashi Washegarin jikin da kwari sossai, wanka tayi ta saka kayanta ta samu wuri ta zauna don bakunta ne fal cikinta da kuma tsoro, har yanzu Mammi bata san wacece ita ba shin wani abu zai chanza in ta san wacece ita? Anya shi ma Rayyan ya san wacece ita kuwa? Tunanin da yake ta kai komo kenan a ranta har ta ji an tura kofan an shigo.Ɗaga kai tayi tana amsa sallamar Abeeha.”Alhamdulillah jiki yayi sauƙi sossai Aunty Abeeha”Ta amsa mata bayan ta jefa mata tambayar yaya jiki, Zaro ido Abeeha tayi “Lallai Afeefah ni ce Auntyn taki? Kin ga kirani Abeeha na bana wani son Aunty na san ko da zan girme ki ba zai wuci da shekaru biyu ba”Afeefah ta ɗan yi murmushi “Toh ai ko da kwana ɗaya ne kin cancanci na ce miki hakan bare har shekaru biyu””Ni dai bana so na bar miki”Ta faɗa da dariya, Afeefah ma tayi murmushi “Kin karya kuwa?”Abeeha ta tamabaya don ita ta tafi lectures 6 yanzu kenan dawowanta 9 ɗin nan.”Eh sun kawo min har nan na karya, ina dai so in je in duba jikin Mammi ne kuma ban san ta inda zan ganta ba””Nima chan nayi daga nan, na fita duk kuna bacci. tashi mu je”Miƙewa Afeefah tayi Abeeha na cewa rigarta ya mata kyau tayi murmushi tana mamakin saukin halin Abeehar da saurin sabon ta.Sai kallon gidan Afeefah ke yi tana ƙara yabawa abin da ya fi burgeta yadda ko ina kalkal sai kamshi da sanyin Ac ke tashi, ga nan chandliers design daban daban masu kyau kowanne da kalar hasken shi da tsaruwarshi, silifas ɗin kafafunsu mai taushi kaman ka nitse ciki take ta jin daaɗin shi don duk basa yawo kafa banza a cikin gidan da lofas ɗin su masu kyau itama kuma har ɗaki aka kai mata saboda sanyin tiles, ɗakin Mammin suka tura da sallama suka shiga.A kan kujera suka samu Mammi gabanta fruits ne masu low potassium tana sha shima kuma in portion ne akwai yawan da ba zai yiwu ta sha ba, Daga kan gadonta Rayyan ne yana cikin bargo Dukda ba bacci yake ba idanunshi lumshe yana tunanin maganan da Mammi ta gama faɗa mishi yanzu, numfashi ya ɗan sauƙe ya buɗe idanunshi ya kalli inda suke a lokacin Afeefah ta kai ƙasa Mammi na ce mata “Tashi! Tashi a ƙasan nan Afeefah ga kujera zauna ko ki zauna bakin gado ina ke ina zaman wannan sanyin”A bakin kujera ta ɗan dosana tana gaishe da Mammin, Mammin ta amsa cike da kulawa tana tambayarta jiki ta ce ta ji sauƙi, Abeeha ma ta gaisheta tana tambayar karfin jikinta duk adua suka dinga yi wa Mammin tana amsawa, sam Afeefah bata kula da Rayyan ba Mammi da ta kosa ta ji Afeefar daga ina take kuma ina danginta tace “Afeefah ki yi haƙuri da tambayana, ba wai zan tambayeki bane saboda mun gaji dake ko muna so ki tafi ba, yana da kyau ne tambayar saboda mu san asalinki mu san me ya rabo ki da danginki, in kika duba yadda wannan zamani ya zama har wasu tsoron taimakon suke saboda dayawa an fi janyo su inuwa su tura mutum rana. Idan har baki shirya sanar da mu ba kuma za mu hakura mu cigaba da zama dake har ki ji kin gamsu kina son sanar da mu ɗin. Na yi ta tambayar Saraki bai ce min komai ba”Afeefah ta ɗan muskuta gabanta na tsananta faɗuwa ta ce “Mammi don Allah ki daina ba ni haƙuri, ya zama dole in sanar da ku wacece ni! Ina tsoron saka ki cikin damuwa alhali ba lafiya ce ta ishe ki ba don labarina bashi da daaɗi, bashi da abin burgewa ko karsashi, babu abin da ke ciki sai tarin baƙin ciki, kuka da damuwa, Mammi Sunana Afeefah kamal na buɗi idona ne kawai na tsince ni gaban kakata wacce ta haifi babana….”A hankali ta cigaba da basu labarinta tun daga farko har ƙarshe, ta gaji da kuka a kan labarinta hakan ya sa a yanzu ta danne kwarai bata yi kukan ba sai idanunta da suka rine matuƙa gaya, bayan ta gama ta ɗago ido tana kallon expression na su Mammin gabanta na faɗuwa zuciyarta na duka da ƙarfin gaske….

Back to top button