MATA
1} Zuwa ga zaɓin zuciyata, ina fatan kasha ruwa lafiya? Ina fatan izuwa yanzu nutsuwa ta game jikinka, ishiruwa ta gushe daga makoshinka? Ina kuma fatan lada ya tabbata a gare ka. Fatan ka sha ruwa lafiya? Ka Huta Lafiya.
2} A dukkan lokacin da na ga darenLailatilkadari, zan kasance mai rokon Ubangiji Ya mallaka min kai a matsayin mijina uban ‘ya’yana, ina fatan kai ma zaka kasance mai tsawaita tsayuwa cikin kowane dare domin ganin cikar burinmu? Ina Son Ka.
3} A lokuta da wurare daban-daban ina ganinka kana yi min gizo, ina ganin ka a lokacin da idanuwana ke a rufe ko a buɗe. Ba na iya yin komai ba tare da tinaninka ba. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya.
4} Jin muryarka na sakwan guda, na jefa ni cikin kogin tinaninka, na tsawan lokacin da idanuwana ke kasancewa a buɗe. Barka Da Shan-ruwa.
5} Irin kulawar da kake nuna min a kullum na saka ni tinanin irin yadda rayuwarmu za ta kasance a nan gaba. Zanbzamo tamkar sarauniya a gidanka, kai kuma zaka zamo sarkin da babu wani mai irin masarautarsa a duniya ta kowace fuska. Ina Son Ka.
Na bar addinin musulunci na koma addinin Budda~Muneera Abdulsalam
CBN Zai Hukunta Bakunan Da Ke Karbar Yagaggun Kudi
Daɗaɗan Kalaman Soyayya Na barka Da Shan-ruwa Ga Samari Da Yan Mata
6} Zuciyata ba za ta taɓa canja matsayin da kake da shi ba a cikinta. Murmushina gare ka ba zai taɓa yankewa ba. Son ka a cikin zuciyata ya yi kafuwar da ba zai taɓa goguwa ba a cikinta na har abada. Barka Da Hutawa.
7} Da a ce zan iya zama komai, da na zama ruwan hawaye a gare ka, a haife ni a cikin idanuwanka, na rayu a saman kumatu na mace a saman laɓɓanka. Ina son ka so mara misaltuwa. Barka Da Shan-ruwa.
8} A dukkan lokacin da kake bukatar wani ya taya ka hira, karda ka manta kana da ni, ka nemo ni domin ɗebe maka kewa a cikin kowane irin yanayi da lokaci. Fatan Ka Wuni Lafiya? Ya ya Ibada?
9} A lokacin da na tino irin rayuwar da na yi a baya, na kan hango irin asarar da na yi, na kasancewa ta ni kaɗai ba tare da kai ba, yanzu na same ka, ina ji na a matsayin wata wadda ta fi kowace mace sa’a a rayuwa. Ina fatan na kasance a tare da kai na har abada. Barka Da Shan-ruwa.
10} Ba zan taɓa mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wanda nake so ya nuna min soyayyarsa a fili, ba kowa bane face kai hasken idaniyata. Ina son ka. Barka Da Hutawa. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya?
Karanta>>> Zafafan Kalaman Soyayya Na Yan Mata Da samari 2024