Mejo Najeeb Page 53 By Autar Alheri
“What?? Tunyoshe tafita? Yatambaya cikin tashin hankali. “Yanzunnan sr kuma gashi munfito babu ita. Kukoma gidan kawai zanzo yafaɗa tare da yanke wayar…..mejo wani gidan gona suka nufa bayan Captain jameel yayi Perking shikaɗai yafito yace sujirashi yana zuwa kana yanufi cikin gidan danufin yiwa Hajiya umma gargaɗi taneda Mishi hakan bayaso,,,,sedai koda yashiga bakowa a Perlor hakan yasa yanufi cikin bedroom ɗin dake perlor, tura ƙofar yayi yashiga sedai Bega kowaba, ɗan tsaki yaja tare da juyawa zekoma kawai yaga anrufo ƙofar ɗakin, da mamaki yaɗago yana kallonta sedai cikin sauri ya kauda idonshi yana faɗar, innalillahi wa’innailaihi raji’un astagafurullah wa’stubu alaihi, saka makon mugun ganinda idonshi suka Mishi. Hajiya umma tsaye agabanshi tsirara tana kallonshi…ganin yadda yayi yasa tayi wani shi’umin murmushi kana tace “dana kadena wahalarda kanka my son domin kuwa yau dai seka lasawa mamanka jarumtarka tamori abinda ta rena, taƙarasa zancen tana tunkaroshi cikin sigar karuwanci domin taja hankalinshi gareta. Mejo kam tun lokacinda yayi ido huɗu da ita tunɓur haihuwar uwarta tanemi natsuwarshi yarasa wani irin abu yakeji nataso Mishi tun daga ƙasan zuciyarshi mekamada feeling ba feeling ba kunci ba kuncuba yama rasa awanne matsayi yarasa ɗora kanshiTunkaroshi tayi cikin kissa da karuwanci tana wani shi’umin murmushi ganin takonta tYakama kurciya a nata tunanin, hannunshi tariƙo tare da ɗorawa akan jagwal ɗin nonuwanta,,,, beƙarasa kaiwa ba tasaki wata irin raza nanniyar ƙara cikin azaba da ihu tana gan tsarewa, Sakamakon wata irin azaba dataji taratsa bayanta,,,,da sauri mejo dayayi mutuwar tsaye yajuya yana kallon minene abinda yasamu Hajiya ummar, itamadai juyawar tayi cikin tashin hankali tana kallon kominene hakan yadaketa me masifar zafi da azaba. Da jelar macijinta suka fara cin karo tana wani mirɗeta ta ɗaga ta sama tana shirin koma shauɗa mata ita akarona biyu…ido suka zaro atare suna kallon Isseta wanda azahiri dukkansu isseta suke gani amma a ba ɗini gimbiya mardeeya ce ajikinta. “Ido Hajiya umma tawaro tana kallon gimbiya mardeeya da fuskar isseta wadda ke watsa mata muguwar harara, cikin jin haushin ta tace”Jamila kinyi asara kin cuci kanki kin cuci rayuwarki kisani najeebullah yarigada yayi miki nisa tun lokacinda kika fidda maitarki akanshi kuma ina Miki albishir da cewar Maryama tana kan hanyar zuwa gidan mijinta sa’anan hukuma na nemanki akan miyagun aiyukanki, kinga ko a iya hakan aka tsaya Jamila munyi nasara akanki gimbiya laweesat da gimbiya mardeeya sunyi nasara akan mushirika kuma buɗararriyar bil adama, kisani natsaneki tun lokacin da nasan wacece ke banida burin daya wuce nakasheki kamar yadda nakashe abokin tsafin naki tsijuju domin narage ɓata iri acikin duniya amma bazan kashekiba ayanzu domin inason kigirbi abinda kika shuka dakanki duniya tagama yimiki Gwalo tukunnah kiga ƙarshenki ganin idonki….tunda gimbiya mardeeya tafara magana mejo yadawo hayyacinshi ananne yafahimci tabbas ba little mom ɗinshi bace maybe maah ce ko wadda general Aliyu kebashi labari..Itako Hajiya umma tunda taji kalaman gimbiya mardeeya tanemi natsuwarta tarasa babu abinda kemata yawo irin Maryama na hanyar zuwa gidan mijinta gimbiya laweesat tayi nasara akanta kuma gimbiya mardeeya takashe mata tsijuju hakanne yasa idan takirashi baya zuwa, kenan wata tunuwar asirintane yatsaya ina bazeyuba, tafaɗa abayyane tare da nufar hanyar barin bedroom ɗin agigice seda takai perlor tukkunnah tadawo neman suturar dazata saka domin sam tamanta da tsirara take, abaibaice tasaka kayan ko mayafi babu tafigi mota tafice daga gidan.Se alokacin gimbiya mardeeya ta kalli mejo kana tace “mardeeya ce ƙanwar maah ɗinku kayi sauri kaɗauki matarka kuje gidan Alhaji Khamis domin can Jamila tanufa Maryama kuma na kan hanya ayau komi ze warware amma fa idan kabari Jamila tagudu to tabbas za’akoma kamar bayane, tana gama faɗar hakan tazamewarta daga jikin isseta anan tazube ajikin mejo,,,,cikin sauri yaɗauketa yanufi motarshi batareda ma yatsaya bitakan tafarkaba…yana fitowa Captain jameel yataso cikin mamakin ganinshi da ita tunda yasan batare sukazoba gaya kuma Hajiya umma tafoto itama agigice, buɗe mishi motar kawai yayi yasakata cikin bada umurni yace muje gidan Abba yanzu, aiko cikin sauri Captain jameel yafigi motar sauran security ɗinsu suka mara musu baya.Suna isa gidan ko gama Perking Captain jameel beyiba mejo yaɗauko isseta suka fito tare da nufar cikin gidan, Hajiya mama ce da Munir zaune a perlor lokacinda Hajiya umma tashigo Karaye, hakan yasa duk suka bita da kallo basukai ga samun yin magana ba mejo yashigo ɗaukeda isseta. Cikin mamaki Hajiya mama ke kallon kamin su haɗa baki itada Munir wurin tambayar lafiya???”lafiya mama ina Hajiya umma yatambaya yana kwantarda isseta akan doguwar kujera kusan Hajiya mama. Kafin tabashi amsa Sega Hajiya umma tafito wuri janjan kamar an Korita tanufi haryar barin perlor “inzaki kuma umma? Cewar mejo yana nufota…ka kalloshi batayiba tabuɗe ƙofar perlor domin abinda ke gabanta yanzu yafi gaban na mejo,,,tana buɗe ƙofar ana turota daga waje, cak tatsaya kafin tazaro idonta cikin mugun tashin hankali tace “Maryama seda kuwa kika dawo?? Tafaɗa arazane…Abba dake gaba kafin Ammi dasu jidda dukkansu da kallo sukabita cikin mamaki Abba yace “miye hakan Jamila? Lafiya kuwa? Kafin tabashi amsa suka shigo perlor har Ammi…cikin wani irin farin cikin dake fita tundaga zuciya Hajiya mama tace “anty Maryama kece? Alhaji dagaske dai anty Ce tadawo? Ashe dagaske Ummi keyi alhmdlmulillah Allah mun godema daka muna mana wannan ranar anty Maryama, se kawai tarungumi Ammi tana sakin kuka….cikin ƙarfin hali da soyayyar ƙanwar Tata Ammi tarugumeta back tana shafa bayanta ahanki tace “Safiyya kuka ya isa hakan kika kuka agaban ƴaƴanki uhnm bagani agabankiba haba ƴar ƙanwata….murmushi me haɗe da kuka Hajiya mama tayi tana goge hawayenta. Ammi tabuɗe baki zatayi magana kenan sukaji Muryar Hajiya umma cikin amo marar daɗin sauraro tana faɗar “”inaa wlh sam bazeyuba ƙarya kikeyi wlh keba Maryama bace ƙarya ne wlh Maryama bazata taɓa dawowaba har abada domin tsijuju bazemun ƙarya ba…..ɗib kowa yayi awurin cikin mugun mamaki suna kallonta kafin Abba yace “mikike nufi Jamila bangane ba Maryama bace bazata taɓa dawowaba? Kinsan wani abunne akan ɓatan Maryama dakike wannan magar?? Yatambeta cikin tuhuma. Aiko kamar wata zarriya tashiga faɗar “eh mana wlh ba Maryama bace wannan yaudarar ka ce zatayi Alhaji domin kuwa bakina dana tsijuju yagayamin cewar Maryama tatafi kenan bazata taɓa dawowaba sabida tsafin damukayi mata baze taɓa barin jikintaba cikin sauƙi tayaya za’ace tadawo nayarda? Taƙarasa zancen tana wani zazzare ido kamar zata dakesu…ahasale mejo yazaburo zeyi kanta sedai kafin yakai Munir yarigashi yariƙo hannunta cikin mugun baƙin cikin furucinta yace “umma mikike faɗa hakan wacece Maryama? Kedawaye kuka mata tsafi? Kuma mitayi muku? “Wata irin dariya tasaki kafin ta haɗe rai tamau tace “wai wannan itace Maryama kuma karyane ba itace bace domin Maryama dakaina nasaka mata layarda ta haukatarda ita, Bara kaji abinda tayimun.”Nida Maryama munraso tamkar tagwaye kuma Aminan juna munyi karatu tare munyi rayuwar budurcinmu tare dudda kasan cewar mahaifinta yafi nawa kuɗi amma hakan muke abotarmu,,,,kuma ina zuwa gidansu tana zuwa namu, tun lokacinda nagirma na mallaki hankalin kaina nakeson Khamis wato abbanku kuma Maryama da hakan domin kullun ina gaya mata irin son dana keyiwa Khamis kamar zan mutu. Wai kwatsam se Maryama tazo tana gayamin za’a ɗaura aurenta da Khamis inji abbanta kuma ita bazata iya bijirewa umurninshiba shiyasa take gayamin dan Allah nayi haƙuri idan inason yayanta abdussalam zatayi Mishi magana ya aureni bayan kuma tasan cewar abdussalam akwai wadda yakeso wato Hannah,, dudda naji baƙin jiƙin cikin wannan zancen nata amma Sena nuna mata ba komai kuma nayi mata fatan alkhairi sabida tama renamin hankali zuwamin da wannan zancen idan kuwa hakane babu amfanin nuna mata wata damuwar tunda wadda nake gaya mata tun abaya batayi anfaniba.Hakan nashige gaba akayi komai ba hidimar bikin Maryama dani daga gefe ɗaya kuma ina neman hanyar dazan ɗauki fansar abinda tayimun domin bazan taɓa barinta taci bulus ba wannan alkawarina ne…bayan auren Maryama da mako ukku Mahaɗu dawani boka tsijuju shine yayimun maganin Maryama, alokacinda tahaifi najeeb bada jimawaba yabani laya dana saka mata aƙasan gadonta kuma nazuba mata magani acikin abinsha…hakan yasa cikin dare tsijuju yasamu damar ƙarasa aikinshi ta hanyar kiran maryama wanda yasakata tashi tafita daga gidan babu shiri kuma bada sanin kowaba tabi duniya kuma yayi mun alkawarin bazata taɓa dawowaba muddin nabi sharuɗanshi.Bayan ɓatan Maryama nasaka tsijuju yayimun aikin akan khamis ya aureni domin naga abdussalam nason ya aura Mishi ƙanwar Maryama Safiyya…hakan akayi aurena dana Safiyya babu shiri. Muna zaune anan tsijuju yace Sena karɓi renon yaron Maryama wato najeeb tukkunna aikinmu zetafi yadda mukeso…amma nazo abdussalam yahana abanishi ahakan yasa mukayiwa Khamis aiki babu shiri yatattaramu mukabar Niger muka koma Nigeria daga nan nasaka Khamis yakarɓi najeeb yabani…sedai yadda yake nunawa yaron soyayya baze bari muyi komi yadda mukesoba, hakan yasa tsijuju yafitarwada Alhaji khamis najeeb arai sam yatsaneshi kuma muka hanashi zuwa Niger domin abdussalam zekawo muna cikas a aikinmu….bayan najeeb yacika shekaru 16 duniya tsijuju tabani wani abun danake Mishi anfani dashi wanda kesaka wannan masifaffen ciwon dayakeyi domin wannan ciwon nashi yana ƙara nisantashine daga Alhaji Khamis kuma yana nisanta Maryama daga garesu domin har izuwa wannan lokacin tsijuju yagayamin tana raye….sedai dudda kasan cewar nice silar cinwonda najeeb keyi amma inajin tausayinshi sosai domin tun yana Yaro ƙarami aka jarabeni da sha’awarshi muguwar sha’awa wadda tasa bana iya control kaina akanshi….dana gayawa tsijuju shine yabani maganin danake anfani dashi acikin duka kayan abincin gidannan domin ɗauke hankalin mutanen gidan daga kan abinda zefaru tsakanina da najeeb domin kuwa yace haɗuwata da najeeb ashimfiɗa ɗaya shine ze tabba tarda cikar burina, hakan yasa duk abinda zan yi Mishi bawanda zece komai…hakan yasa nake bibiyarshi har banɗaki batareda yasaniba kuma hakan yasa natsani ƴata mansura domin naga itama shitake hari, duk wannan abun bawanda yasani ko yakula se shigowar wannan tsinanniyar yarinyar cikin gidannan tashiga ruguzamin komai daga tsakanina da ɗana har da mutanen gidan nan tahanyar kwashe duka kayan abincin gidannan da magungunan danake anfani dasu takuma shiga tsakanina da najeeb datemakon wannan muna fukar gimbiya mardeeya, bayan takashemun tsijuju yanzu kuma duk wannan be isheta se a wani ce Maryama tadawo bayan tsijuju yace karba yadda tashigo gidannan wlh sam bazeyuba ƙaryane ƙaryanee wahallahi, tafaɗa cikin ƙara ji ɗaga murya wadda kenuni dacewar tarigada ta haukace….!



