Description/Story:
Gobe da labari Complete Document Written By Batuul Mamman
Description
Alhamdulillah da Allah Ya nuna min lokacin nan da zan rubuta wannan labari. Ina addu’ar Yasa mu ga karshensa lafiya. Alkhairi da albarka su danne sharri da fitina. Sadaukarwa ga duk wani dan Arewa mai kishin kasa.
Bismillahir Rahmanir Rahim
Shimfida
Tabbas garin Abuja da ake yiwa lakabi da birnin tarayya yaci sunansa idan aka yi duba da yawan kabilun dake cikinsa. Kaso mafi yawa na ma’aikatan kasar sun fito daga jihohi daban daban ne. A cikin al’ummar da garin ya tara ne zamu tattaro manyan jaruman da zasu ja ragamar labarin nan mai suna GOBE DA LABARI COMPLETE DOCUMENT.
Indai mun yarda ba a fafe gora ranar tafiya, to wajibi ne tanadin ruwan wanke tukunya domin tuwon gobe. Kullum muna fatan ganin da kyau, to amma wane yunkuri muke yi domin tabbatuwar hakan?
***
ZABABBU
52 Mike Akigbe Way
Jabi, Abuja
The Nordic Villa
A duk lokacin da wani abu ya tunkaro dan Adam yana yi masa barazana da rayuwarsa, sai yaga kamar duk duniya babu abin da ya kai shi mahimmanci. A inda imani ya yi karanci ko wahala ta kaiwa mutum wuya ma babu abin da ba zai iya ba domin kawar da matsalar. Misali, tsadar kayan masarufi da karancin albarkar gona yana sa mutane ganin kamar abinci shi ne jigon rayuwa. Bullowar annoba, yajin aikin likitoci da rashin wadatar arzikin neman lafiya idan ya taso mutum a gaba sai ya rantse kowane mai lafiya sarki ne. Wanda talauci ya hana kumbar susa gani yake kamar yafi kowa shiga halin kaka-nika yi. Amma a yayinda rashin TSARO ya zama labarin yau da gobe a wani yanki, to lallai sai ya mayar da duka wadancan lalurorin nafila. Sai kana cikin ahalinka kake tunanin yunwa, talauci da rashin lafiya. Tattauna wadannan batutuwa shi ne makasudin bayyanar wadansu motoci guda bakwai farfajiyar The Nordic Villa da karfe goma sha daya na daren lahadi. A jere suka shigo, kowacce da tint a jikin gilasanta ta yadda na waje bai isa yace ga matukinta ba balle fasinjoji. Sha daya da minti goma daidai duka kofofin motocin suka dinga budewa ta hagu da dama. A lissafi mutane goma sha daya ne cif suka fito. Mata uku, maza takwas kowanne fuskarsa sakaye da takunkumin fuska bak’i (face mask). Daga yanayin suturun jikinsu da ma tafiyarsu ake gane su din wasu ne ta fannin aljihu sannan kuma da alamun sun zarce shekarun samartaka.
Haske ya wadata kayataccen koridon da wani matashi wanda ke sanye da shirt mai sunan hotel din da bakin dogon wando ya nuna musu. A jere kamar masu yin layi suka bi bayansa har cikin wani madaidaicin dakin taro (conference room). Daki ne mai fadi da dan tsayi wanda babu komai na kyale-kyale a cikinsa sai abin bukata kamar firij, dispencer da wani madaidaicin kabinet dauke da kwanuka (plates) da kofuna. A tsakiyarsa akwai katon tebur mai fasalin kwai (oval) wanda yake da kujeru goma-goma suna fuskantar juna hagu da dama. Kujerun dukkaninsu iri daya ne masu kyau. Sai guda daya daga tsinin tebur din ce ta bambanta da sauran a girma da kala. Wannan yake nuni da cewa nan ne mazaunin shugaban taron wanda kuma mamallakinta a wannan zaman da ya riga ragowar jama’ar isowa yake zaune a kanta. Fuskarsa a bude take ya janyo tasa facemask din kasan habarsa ta rufe sajensa mai sirkin bakin gashi da furfura yana rubuce-rubuce. Sanye yake da suit ruwan toka da riga ‘yar ciki ruwan madara. Wuyansa da necktie mai ratsin layi layi baki da ruwan toka. A dan murmure yake na rashin yunwa amma babu kiba ko kadan sai tsayi. Bafullatani ne na ganin ido ko bai yi magana ba. A bayansa wani dan karamin tebur ne wanda aka dora laptop din da aka jona mata wayar majigi (projector). Wani mutum ne wanda shekarunsa basu kai nasa ba yake aikin daidaita fuskar majigin domin duka mahalartan su gani da kyau idan sun zauna.
Bayan duka baƙin sun zazzauna, kusan a tare su ka dinga bayyana fuskokinsu ta hanyar janye facemask dinsu. Shugaban taron ya dubesu ɗaya bayan ɗaya ya yi murmushi. Bai yi zaton samun hadin kan duka ministoci ‘yan asalin arewa ba. Sai gashi sun bashi mamaki ta hanyar amsa gayyatar da ya yi musu baki ɗayansu.
“Ina yi muku barka da zuwa” Ya nuna mutumin da ya gama hada majigin “Bamu da isasshen lokaci duba da cewa wannan taron na sirri ne saboda haka ba tare da ɓata lokaci ba zan bawa Dr. Yunus Enejo damar gabatar muku da komai.”
Juya kujerarsa ya yi ta kalli bangon da majigin ya fuskanta kamar sauran. Mutumin da yake zaune a wurin tebur din da laptop din take ya danna slide din farko. A nan kowa yaga taken zaman nasu wanda a gayyatar da suka samu sun sami tsakuren bayani.
IDP CITIES REFORM
Aka rubuta da manyan harufa akan shafin. Dr. Yunus ya fara da gabatar musu da kansa a matsayin Permanent Secretary na ma’aikatar lafiya (ministry of health) duk da kowa a wurin ya san shi. Daga nan ya nausa cikin bayani mai gamsarwa game da dalilin kiran da Minister of Health, shugaban taron Dr. Mahmud Barkindo ya yi musu.
Matsayinsa a ma’aikatar ta lafiya yasa yana daga cikin wadanda suka fi saurin jin duk wani labari mai dadi ko kishiyarsa da ya shafi lafiyar al’ummar Nigeria. Idan aka ture rashe rashen lafiya da jama’a suke yi a gidajensu, halin da kasar take ciki a yanzu abin dubawa ne. Tsaro dai na rai da dukiya babu shi. Ga uwa uba bullowar cututtuka masu wuyar magani da saurin yaɗuwa. A gefe guda tsadar rayuwa ta jefa jama’a da dama cikin halin ha’ula’i. A halin da ake ciki ba a jima da sake yakar cutar Lassa fever a wasu garuruwan arewacin kasar ba. Ga dungurungum Covid-19 wadda zuwanta ya girgiza duniya baki daya. A karshe kuma ga ƴan gudun hijira wadanda ƴan ta’adda suke ta rarakowa daga muhallansu. Wadannan mutane galibi sun tashi ne cikin iyalansu suna kuma gudanar da ayyukansu na yau da kullum. Lokaci guda aka dakatar da komai tare da sauya musu faifan rayuwa tamkar mai karatu ya bude sabon shafin littafi. Kullum karuwa suke sannan babu wani tartibin abu da ake yi domin killace rayuwarsu ta yadda radadi da bakincikinsu zai ragu. Wadannan sune jiga-jigan matsalolin da ya tunatar dasu.
“Al’ummar Najeriya da duniya ma baki daya suna bukatar gani a kasa. Your Excellencies, masu girma ministocin ƙasar nan. Lokaci ya yi da ma’aikatunku zasu nuna kawunansu. Ba a banza bayan shugaban kasa da gwamnoni ba aka warewa kowannenku wata ma’aikata wadda ke kula da wani bangare mai mahimmanci aka ce ya zama jagoranta ba.”
“Ina da magana”
Hankalin kowa ya koma kan Minister of Works and Housing wanda bayan ya yi wancan furuci ya mike tsaye. Banufe ne dan asalin garin Bida ta jihar Niger.
‘Yan uwansa ya nuna ya ce “bana jin akwai wani cikinmu nan wanda bai gamsu da bayanan Dr. Yunus ba. Abin da ban gane ba shi ne dalilin da yasa baki dayanmu nan ‘yan arewa ne. Me duniya zata fassara wannan yunkurin namu tunda munyi kaurin suna wurin rigimar kabilanci da addini?”
“HUMANITY!”
Shiru mai ratsa zuciya ne ya sauka a dakin sai ka rantse babu mai zukar iska.
Numfasawa Dr. Mahmud Barkindo ya yi da ya tabbatar kalmar ta sami damar ratsa kunnuwansu ta kuma zauna a cikin kawunansu. Cikin nutsuwa da kwarewa ya cigaba da sarrafa harshe yana magana da turanci. Amma kuma kowane harafi yana fita da karfin mashi yana sukar inda ya dace.
“Da Humanity duniya zata fassara duk wani yunkurinmu domin shi ne yaren da kowane mai addini yake son a alakanta addininsa da shi. A halin da muka tsinci kanmu wajibi ne kowane yanki a kasar nan su fara daga kawunansu kafin azo maganar hada hannu a ciccibi kasar gabadaya. Bana jin za a sami wanda zai kalubalanci wani magidanci idan ya tafi neman ‘yan kwana-kwana a dalilin gobara ta tashi a gidansa. A takaice ma rashin neman taimakon shi ne babbar wauta da zalunci da mutum zai yiwa kansa. Arewa ita ce gidanmu kuma ta kama da wuta. Zamu zuba ido ne wutar ta cinye dakunan da suka fara kamawa ta zo ta kama gidan gabadaya?”
Kawuna suka girgiza. Daya daga cikin matan ‘yar Kwara harda hawaye. Matsalolin arewacin Nijeriya sun fara shallake tunanin dan Adam. Lamarin kullum dada lalacewa yake. Kana bude shafukan sada zumunta labarin kenan dai. Nan anyi kaza can anyi kaza. Labarai marasa dadi wadanda baki baya son dorar dasu a gaba. Kisa, garkuwa da mutane da tsantsar kuncin rayuwa sune carbin da talakan yankin yake ja kullum.
“Kuna sane da cewa gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin a killace duka ‘yan gudun hijira a manya manyan sansanin da tayi guda uku? Duka ragowar za a tayar dasu ya zamana ukun nan sune kadai wurin ajiyesu. Muna so mu zabi daya daga ciki mu fara daga nan. Yunkurinmu zai zaburar da shugaban kasa da gwamnoni akan yin kwatankwacin abin da muke shirin yi a sansanin a cikin garuruwansu.”
File Name | Gobe Da Labari… Hausa Novel Doc. |
Title | Gobe Da Labari Complete |
Author | Batuul Mamman |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Fiction Story |
Published Date | 25/09/2024 |
File Size | 900KB |
Format Size | TXT |
Book Price | Free |
Phone No |
Download Gobe Da Labari Complete Document By Batuul Mamman
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.