Page 60
*Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
Wani mugun kallo rumaisa ta yi masa, ta ture hannunsa da yake gyara mata zaman alkyabbar jikinta, ta ce “Ba ruwanka da ni, kuma ka zo ka mayar da ni gidanmu”.
“Ni na kawo ki? Sai ki fita ki koma ai, tun da bani na ɗauko ki ba”.
“Kuma wallahi sai na tafi, ko ka sani ko ba ka sani ba”.
Hannunsa ya saka, ya matse mata kumatu, ta saka hannunta ta riƙe hannunsa, saboda azabar zafin da ta ji.
Ya sake kallonta ya ce “You better behave yourself, a gidana ki ke, fita ki bar mini ɗaki, wancan ɗakunan zaki ɗauki ɗaya, da safe zan saka a kwashe miki tarkacenki, a mayar miki can” ya ƙarasa maganar yana sakar mata baki.
“Ba in da zani, tun da dai na ga kayan da aka sai mini ne a ciki”
“Kayanki ne, amma gidana ne, sai na kwashi kayan naki na mayar haraba, ki je can ki ƙarata” ya yi maganar yana wucewa cikin bedroom ɗin.
Ya rage kayan jikinsa, ya shiga banɗaki.
Har yayi abun da zai yi ya fito, rumaisa tana tsaye, tana kuka.
Ya je yayi salla, ya wuce ta ya je kitchen, ya dawo amma tana tsaye. Nan ya sake sarawa taurin kan rumaisa.
Har ya gama cin abun da zai ci, tana tsaye ƙyam, ta juya masa baya, ya kashe fitila, ya kunna A.C, ya kwanta, gajiyar biki da zirga-zirga ya sanya yana kwanciya bacci mai nauyi ya ɗauke shi.
Rumaisa gajiya ta yi da tsayuwa, ga tsoro da ta fara ji saboda duhu, ga sanyin A.C yayi mata yawa, dan ba ta saba ba, ta nemi wuri ta kwanta a ƙasa, ta duƙunƙune a cikin alkyabbar ta hau bacci.
Mama kuwa yadda ta ga rana, haka ta ga dare, dan babu wani abu mai kama da barci da yayi shirin ɗaukar ta.
Haka ma ƴan mazan nan, Aliyu cewa yake “Allah ka rufa mana asiri, Allah ya sa kar yayi mata wani, abu yarinya ce ƙarama wallahi”.
Usman ya ce “To yanzu mu kake gaya wa ko yaya?”
“A’a addu’a kawai nake yi”
Mai sunan baba duk da yana cikin damuwa, amma jin abun da suka faɗa da ya haɗa ido da Abubakar, kawai Abubakar ya tuntsire da dariya, mai sunan baba kuwa murmusawa yayi, tare da basarwa kamar bai ji me suke faɗa ba, haka suka kai har wurin ƙarfe biyu, suna hira yadda biki ya gudana, da kuma jimamin ya rumaisa za ta kasance a gidan aure.
Samha ma haka daren nan yayi, ta kasa rintsawa, duk da sun yi chatting da Fauziyya, tana ta rarrashinta, ta tura mata hoton bikinsu Adam.
Amma kasa tsayawa ta yi ta kalla, saboda yadda zuciyarta ke matuƙar tafasa da wani irin masifaffen kishi.
Ko lokacin da ya auri Aisha, ba ta shiga wannan yanayin da take ciki a yanzu ba.
Sai da aka kusa idar da sallar asuba, sannan Adam ya farka, a gaggauce ya shiga banɗaki, yayi alwala, sai da ya ga ba zai samu salla ba ko ya fita, dan haka ya ce bari kawai yayi sallarsa a ɗaki.
Ba tare da ya kunna fitilar ba, ya tayar da salla, bayan ya idar ya din ga jin kamar numfashin mutum, har gabansa ya faɗi, dan ya ɗauka irin razana shin da aka saba yi ne, ya tashi ya kunna swtich ɗin ɗakin, mai zai gani, madiga ce a kwance take ta uban baccinta, abun ka da a gajiye take dama, duk ta cukuikuye alkyabbarta.
“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, ke wai a nan ki ka kwana?” Yayi maganar yana taɓa ta.
Oho bata san yana yi ba, bacci kawai take yi.
“Tashi, ki je ki yi salla” nan ma bata tashi ba.
Toilet ya shiga ya ɗebo ruwa, ya dawo ya zuba mata a fuska.
A rikice ta tashi tana faɗin “Huzaifa meye haka wai?”.
“Na hauzaifa bane Adam ne, ban ce miki ki bar mini ɗaki ki tafi ga naki can ba”
Maimakon ta yi magana, sai ta haɗe rai tana kallonsa, kamar mafarki take yi ma ba a zahiri ba.
Ganin ta tsareshi da ido, ya sanya ya tashi, ya riƙe hannunta ya yi waje da ita, ɗaya bedroom ɗin ya kai ta, ya juya ya tafi ya barta.
Kallon ɗakin ta yi, wasu furnitures ɗin ne a ciki ba nata ba, amma sun yi kyau sosai da sosai.
Ta cire Alkyabbar, ta shiga ta yi alwala, ta fito babu hijjabi. Ta koma ɗakin da aka fara kai ta, wato ɗakin da Adam ya ce nasa ne, ta buɗe drower ya ɗau hijjabi, yana zaune yana kallonta, sai murguɗa baki take ita kaɗai tana harare-harare.
Ta koma ɗakinta, ta yi salla, ta idar ko addu’a ba ta yi ba, ta je ta haye kan gadon, ta ji katifar gadon, mai tauri, ta kalli ɗakin sai ƙamshi yake yi, ta tashi ta yi tsalle a kan katifar, amma taga ba ta lotse ba.
“Allah sarki, zan cewa mama ta dawo gidan nan mu din ga kwana tare a kan katifar nan, su yaya Abubakar kuma sai su ɗauki ɗakin ƙasa, ko shi baban sabir ya koma ƙasa, su dawo saman bene, mu yi zamanmu” ta yi maganar tana kwanciya, saboda baccin da yake kanta.
Sai da ta yi mai isarta, sannan ta tashi daga baccin, ta sauko daga kan gadon, tana son ta wanke bakinta, amma babu komai a toilet ɗin.
Ta fito ta shiga zazzaga saman benen tana kallon yadda gidan yayi kyau, aka tsara shi.
Shiru ta ɗan yi tana tunanin mama, da su Huzaifa, ba ta yi aune ba sai hawaye, wani na bin wani, ta din ga gogewa ta ce “In sha Allah sai na fita na koma gida”.
“Sai zuwa yaushe zaki yi wanka ki sauya wannan kayan, baƙi sun fara zuwa na ce bacci ki ke yi, na dakatar da su a ƙasa, kin tashi kuma baki san ki yi wanka ki canza wasu kayan ba”.
Muryarsa ta ji a bayanta, dan haka ta juya da sauri, ta sha kunu ta ce “To ina ruwanka da ni, ai ni yarinya ce, a gidanmu wanka ake yi mini, ban fara yi da kaina ba”.
Mamaki ne ya kama shi, baƙar magana rumaisa ta gaya masa.
Wata irin fincikowa yayi mata gabansa, ya tsuke fuska sosai ya nuna ta da yatsansa ya ce “Nan gidana ne, kuma fadata, kuma dole ki bi umarnina, da duk abun da nace, ko na yi umarni, idan ina magana, kina mayar mini da abun da ki ka ga dama, zan yi miki abun da ba kya tunani, wuce mu je”
“To, zan yi wanka ba soso da sabulu ne?”
“Wuce mu je na ce” ya faɗa a kausashe sumi-sumi ya sakata a gaba zuwa ɗakinsa.
Ya nuna mata banɗaki ya ce “Ki wuce ki shiga ki yi wanka, ki yi brush, ki fito ki karya, mutane na ƙasa suna jiranki”.
Sai da ta gama kalle-kallenta a banɗaki, sannan ta kalli kayan wankan, ta ga soson a jiƙe, alamar yayi amfani da shi.
“Wallahi ba zan yi wanka da soson da yayi amfani da shi ba”
Ta murza sabulu, ta yi wankanta, ta mayar da kayan da ta cire, ta fito.
Yana zaune a gefen gado yana jiranta, ya nuna mata mai a kan mudubi ya ce ta shafa, ya buɗe wardrobe ya ɗauko, kaya ya tsaya ta gama shafa man.
Ya kalleta ya ce “Ga kaya nan ki canza”.
Ta karɓa ta ce “To a gabanka zan canza kayan?”.
“Ai yarinya ce ke, ba yanzu ki ka gama cewa yi miki wanka ake a gida ba, da ban yi miki wankan ba, ai sai na saka miki kaya ko?”
Zare masa ido ta yi, ya ce “Ki wuce toilet ki canza ni ba in da zani”
Har mamaki rumaisa take, yadda yake ta hantararta.
Riga da skirt ne na lace, har da undeas, ta canza kayan ta fito.
Tana ta kakkare jikinta, kar ya kalleta.
Fita ya yi yana waya, ta tsaya a gaban mudubi, tana kallon kanta, lace ɗin yayi mata kyau sosai. Ba wani iya ɗauri ta yi ba, dan haka kawai ta ɗora ɗankwalin a kanta.
Dawowa yayi tare da iman, tana ganin iman ta fara murmushi.
Iman ta ce “Amaryar takawa, ina kwana”
Haka kurum sai ta ji kunya ta kamata, ta sunkuyar da kanta.
Ya kalli iman ya ce “Ta yi a haka?”
“Yes, ka san komai na ta mai kyau ne, bari ta karya, a ɗan yi kwalliya sama-sama”.
Rumaisa ta ce “Ni fa bana son wannan kwalliyar, haryanzu ta bikin nan jin fuskata nake a ɗaɗɗaure kamar ba ta wa ba”.
Iman ta ce “Ai ba da yawa za ayi ba, bari na kawo miki abinci nan ki karya”.
Abinci ne na alfarma, ammi ta saka aka kawo musu.
Rumaisa ba ta iya ci da yawa ba, dan babu abun da yake yi mata daɗi, Adam kuwa cin abincin sa yayi, bayan sun gama, iman ta shafa mata powder, ta saka mata jambaki, ta ɗaura mata ɗankwali.
Adam ya ce “Ki je ki ce musu su hawo, ta tashi” Iman ta jinjina kai ta fita.
Ya kalli rumaisa ya ce “Akwai familynmu, da naku duk sun zo, idan ki ka kuskura ki ka yi making any rubbish scene, sai na rufeki a gidan nan, ba mai sake zuwa wurinki, kuma ba zaki sake fita ba”.
“Kidnapping ɗina zaka yi kenan?” Ta yi maganar tana kallon sa.
“Eh” ya bata amsa, yana mamakin ita duk abun da aka faɗa tana da amsar bayarwa..
Ta yi shiru, tana kallon awarwaron hannunta.
Mintuna kusan biyar, ta suka fara jiyo hayaniya sama-sama a falon saman benen.
Iman ta shigo ta ce “Yaya ku fito”.
Ya ce “To, muna zuwa”
Ya sake kallon rumaisa ya ce “Ina sake gaya miki, kar ki sake ki yi wani abu a gaban mutane, da zai sa kin janyo mana magana, you should behave yourself”
Ta yi ƙuri da ido tana kallonsa. “Am talking to you” yayi maganar a ɗan kausashe.
“To” ta amsa a hankali.
Miƙa hannu yayi zai riƙo nata, ta janye a ɗan razane.
Ta girgiza kai ta ce “Ka daina taɓani, ni bana son a din ga kallona, kuma kar in je su Yaya sun zo, su ga ka riƙe mini hannu”.
Ajiyar zuciya ya yi ya ce “Ikon Allah, to mu je” da ƙyar ta yadda suka jera, suka fita.
Suna fita aka din ga rafsa guɗa, ana yi masa kirari, haka nan rumaisa ta ji ta takura.
Suka ƙarasa suka zauna, ya zauna a kusa da rumaisa, masu addu’a na yi, masu shewa na yi, ita dai ta yi ƙuri, ji take kamar ta tashi, ga adam ya wani matseta a kan kujerar.
Wata mata da rumaisa ba ta san ko wacece ba ta miƙawa adam hannu ta ce “Ban ga ka fito da ƙyalle ba, dan mu tabattar da me ka aura”.
Ya ce “Haba jakadiya, wannan al’adar ai an daina ta, ko lokacin da na auri Aisha, ai ba ayi haka ba, kuma wannan sirrinmu ne kawai ko Mimi?” Yayi maganar yana kallon rumaisa.
Sororo rumaisa ta bishi da kallo, tana tunanin wacece mimi kuma a wurin, ko ba da ita yake ba?.
“To ai ita aisha tamu ce, kuma ka san ji muka yi an ce, ta shafe watanni shida a hannun masu garkuwa da mutane, kuma mun san ba a bawa kura ajiyar nama, shiyasa muka buƙaci gani, kar mu je saura aka kawo mana”.
Duk da rumaisa ba ta gane kan zancen ba, amma jikinta ya bata ci mata mutunci ake yi.
Sai da ƙirjin Adam yayi wani damm, amma ya basar ya kalli rumaisa, ya ce “Kamar kowacce mace, za ta yi alfahari da daren jiya, za ta yi proud sosai da hakan”
Ji ta yi kamar ta ce da ka koreni daga ɗakin, na kwana a ƙasa, meye wani abun alfahari.
Ƴan uwansu rumaisa kuwa, jin zancen suka yi ba arziki, suka din ga sunkuyar da kai, Gwaggo ta ce “Dama ɗaki muka dawo mu gani, mu anjima zamu koma gida”.
Da sauri rumaisa ta ce “Haba dai Gwaggo, to wai ya baku taho da mama ba, ban ga su yaya bama”.
Adam ya ce “Bai kamata ku tafi yanzu ba, Yakamata a ɗan tayata zama”
Gwaggo ta ce “A’a, ai gaka nan, mu mun tafi, ga saƙonki nan babarki tana gaishe ki”
Tashi rumaisa ke ƙoƙarin yi, amma ya riƙeta, ya hanata tashi.
“Gwaggo dan Allah karku tafi ku barni, dan Allah ku dawo, lawisa kema ba zaki zauna ba?” Ta yi maganar tana kuka.
Adam ya zura hannu a aljihunsa, ya bawa iman, ya ce ta bawa su gwaggo.
Ya ce Gwaggo mun gode sosai da sosai, sai mun zo gida yin bangajiya”
Ta ce “Babu komai, Allah ya sanya alkhairi”
Ya ji daɗin tafiyar su gwaggo, ko ba komai, ba za a cigaba da cin mutuncin rumaisa a gabansu ba.
Ɗago fuskarta yayi, yana goge mata hawayen fuskarta, yana faɗin “Is ok, yi haƙuri kukan ya isa haka”
Ƙoƙarin ture hannunsa take yi, amma yayi mata kallon kashedi, a dolenta ta ƙyaleshi.
Baba uwani sai shiga take tana fita, tana koɗa yadda gida yayi kyau.
Hajiya Lubabatu wato maman Jabir ta ce “Abun dai ya bawa kowa mamaki takawa, bamu taɓa zaton zaka auri ƙaramar yarinya kamar wannan ba, kuma ma dai abun da mamaki, ace wannan ƙaramar yarinyar ce ta kuɓuta da Sabir, daga hannun ‘yan bindiga”
“Ai babu mamaki a ikon Allah, ƙanƙantarta kuma ba zai hana a aureta ba, tun da bai saɓawa shari’a ba”.
Ta kalli rumaisa ta ce “Sannu ƴar nan, sannu da shigowa familyn gidan sarauta, kin zo babban gida, Allah ya baki wuyan ɗauka”
Rumaisa dai ba ta kulata ba, sai kuka da take yi, na tafiyar Gwaggo da kuma rashin ganin mama.
Haka Adam ya zauna tare da ita a wurin, dan kar ya tashi su ci zarafinta, ita kuma ya san ba kunya ce ta wadaceta ba, tsaf zata iya yi musu fitsara.
Sai wajen azahar suka ragu, bayan sun gama faɗe-faɗen maganganun su, da yada habaici.
Da azahar ɗin kuma, Nusaiba ce ta zo da kayan abincin rana.
Sai dai rumaisa taƙi cin abinci, duk surutun nata kuma ta yi shiru, taƙi kula kowa, Iman sai rarrashinta take yi.
Takawa baba uwani ya saka, ta kwashi akwatunan rumaisa, ta kai mata ɗakinta, da sauran kayanta, ya ce ta shirya mata wasu kayan a cikin wardrobe ɗin ta, ga su iman nan, su tayata a haɗa mata ɗakin.
Sai dai Iman ta din ga bin baba uwani da kallo, har sai da ta tsargu, tana ta yi wa rumaisa surutu tana tsokanarta, amma rumaisa ba ta ce komai ba, sai kallonta kawai da take yi.
Tana ƙoƙarin fara shirya mata kayan, rumaisa ta ce “Bar shi, zan yi da kaina”
Kallonta suka yi gaba ɗaya,Nusaiba ta ce “Ki bari ya shirya miki, ke ga gajiyar biki, idan ya so sai ki gaya mata yadda ki ke so”
Rumaisa ta girgiza kai ta ce “A’a, idan ma ta yi sai na sake, kawai ta bar shi”.
Nusaiba ta ce “To shikenan, baba uwani ƙyale mata”.
Adam ya shigo ɗakin, yana tambayarta ko an shirya mata kayan.
Nusaiba ta ce “A’a ta ce a ƙyale mata, za ta yi abun ta da kanta”.
“Shikenan, ku ƙyale mata abun ta, tun da ba ta san gwaninta ba, idan an yi sallar la’asar sai ku tafi gida, ba sai an kawo abincin dare ba”.
“A’a dan Allah kar su tafi, shikenan sai kowa ya tafi ya barni?”.
Tausayinta ya kama iman, amma takawa ya tsare gida ya ce “Do as i said”
Baba uwani ta yi mamakin yadda ƙiri-ƙiri rumaisa ta ce ba zata shirya mata kaya ba, ta so ta saki jiki da ita ta shigeta, saboda ta din ga samun wasu bayanan, da za ta din ga kai rahoto, amma mursisi rumaisa taƙi. Sai ta bar shi a rashin sabo ne, amma tayi alwashin shiga jikin rumaisa, tun da a ganinta yarinya ce ba ta da wayo.
Sannan ta yi mamakin yadda suka haɗu da rumaisa, amma ba ta san ita ce wadda Adam zai aura ba, ta fara tunanin ko dai ammi ta ganota ne, ya sanya ta fara ɓoye mata wasu abubuwan.
Kan su ƙarasa gida, ta ce a ajiyeta a hanya, za ta je wani gida, suka ajiyeta su kuma suka ƙarasa gida.
Tun da suka koma, ammi ke tambayarsu, ya suka baro rumaisa, iman ta ce “Wallahi tana ta kuka ammi, gwanin ban tausayi”.
“Allah sarki rumaisa, za ta saba ne in sha Allah, na san dama za a sha daru”.
Iman ta ce “Ammi kin san me?”
“A’a sai kin faɗa”.
“Wai jakadiya, da maman su jabir, suka saka takawa a gaba, wai ya basu ƙyalle su san me ya aura, sun samu labarin watanta shida a hannun ‘yan bindiga, wai ba a bawa kura ajiyar nama”
Ammi ta yi shiru ta ce “Daga kawo yarinyar jiya, shi ne za su fara wannan abun? Bakomai Allah ya fi su, kuma auren Adam da rumaisa, sai ya bawa mara ɗa kunya in sha Allah”.
Nusaiba ta ce “Suna da matsala, daga zuwanta jiya za su fara nuna hali, kuma wallahi wataƙila Mummy ce zata saka su, ai daɗinta maman Sabir ɗin ma ba kanwar lasa ba ce”.
Baba uwani kuwa, gulma na cinta kasa jurewa ta yi, but ta faɗa sashin Mummy, Aikuwa aka yi sa’a Samha tana nan, suna ta kitsa tsiya.
Mummy ta kalleta ta ce “Ya aka yi?”.
“Daga gidan muke, aikin da aka bani dama na yi shi, ba wata matsala, amma jakadiya sun tambaye shi ƙyalle, ya ce wannan tsohuwar al’ada ce, kuma kamar kowace mace, za ta yi alfahari da daren jiya, nake tunanin ko dai ya….
Samha ta ce “Dakata, ƙarya yake yi wallahi, ai shi da ita sai kallon kallo, ƙarya yake babu abun da ya faru”
Mummy ta ce “Haka ne, ke dai ki yi duk mai yiwuwa ki saka ido sosai, ki din ga kawo mana rahoton duk wani abu da yake faruwa, kuma idan muka baki aiki, ki tabattar kin yi shi yadda ya dace”.
Ta risuna ta ce “In sha Allah uwar ɗakina”.
Tun da su iman suka tafi, ya rage daga ita sai Adam a gidan ta cigaba da kukanta, ta window ɗakinta ya hangota, tana shirya kaya tana kuka, bai kulata ba ya koma falo, yana gwada kayan kallo.
A haka rumaisa ta shafe kwanaki uku a gidan Adam, ko ƙasan bene bata taɓa sauka ba, sai dai ba ta gajiya da kuka, mussaman yadda ƴan gidansu babu wanda ya nemeta, gashi ko an zo mata ta ɗan rage damuwa, da yin la’asar kowa zai watse, shi kuma Adam ba abun da ya iya banda bayar da umarni, ko ya hantareta.
A kwana na huɗu ya lura, tana gujewa haɗuwarsu, idan ta ji motsinsa ko falo ba za ta fito ba, ya lura abincin ma ba ci take yi ba, ta takura kanta sosai da sosai.
Bayan sallar magariba ya shiga ɗakinta, ya tarar ta yi salla tana zaune a kan sallaya ta yi shiru.
Ɗaga kai ta yi ta kalleshi, yayi mata alamar ta zo. Ba musu ta taso yana gaba tana bin sa a baya.
Ƙasan bene ya sauka, ta bi bayansa, tun da aka kawota, yau ta fara sauka ƙasan benen.
Harabar gidan suka fita, ya nufi motarsa, ya buɗe gaban motar ya ce ta shiga.
Ta shiga ta zauna, tana kallon cikin motar sabuwa da ita fil, ga tsofaffin nasa da ta san shi da su a harabar.
Sai a yanzu ta lura, har da burgar dawakai a gidan, da dokuna manya guda huɗu, ga wani murgujejen kare, da shi ma ba ta san da shi ba a gidan.
Security light duk ta haske ko ina a gidan.
Ba ta san in da zasu tafi ba, ita dai ta ga suna tafiya.
Sai da suka je gidan, ta gane gidansu Adam suka je.
Ammi na ganin rumaisa ta rungumeta tana murna, ta ce “Takawa, baka bari ta gama hutawa ba ka fito da ita”
“Ta isheni da koke-koke, shiyasa na kawo ta”
Ammi ta ce “Haba rumaisa, kukan bai isa haka ba, ai yakamta ki kwantar da hankalinki haka” Rumaisa ta sunkuyar da kai, ba ta ce komai ba.
Nusaiba na ganin rumaisa ta fara murmushi “Amarya ba kya laifi, yau da kanki”
Rumaisa ta ce “Shi ne baku kuma zuwa ba da ke da Iman”.
“Yaya ne ya ce kar mu sake zuwa ai”
“To ni kaɗai nake zama a gidan fa, kuma shi ba kulani yake yi ba, sai dai in wuni ina kuka”
Ammi ta kalli Adam, ya sunkuyar da kai, ta kalli rumaisa ta ce “Haba Yarinyar kirki, zai din ga kulaki kukan da ki ke yi ne baya so, gobe in Allah ya kaimu za’a baki hadimai mutum biyu, da zasu din ga yi miki aiki, sa din ga ɗebe miki kewa, abun da ma kin kusa komawa makaranta, wani satin za a koma makaranta”.
Ammi ta yi maganar baba uwani ta fito, ɗauke da Sabir a hannunta.
Murmushi rumaisa ta yi ganin sabir, Adam ya karɓe shi, Baba uwani ta ce “Amaryarmu, sannu da zuwa ya gida, bamu san da zuwanku ba ai da an sheƙa girki na mussaman”
Rumaisa ta ce “Mata ina wuni”
Baba uwani ta ce “Tuba nake, ai ni yakamata na kwashi gaisuwa”
Sabir kuwa rumaisa ya din ga miƙawa hannu.
Adam ya ce “Kai, kwana huɗu baka ganni ba, amma baka ta tawa, Mimi zo ki ɗauke shi”
Waiwayawa ta kuma yi, taga da wa yake, sai kuma ta tuna abun da ya ce washegarin kai ta.
Ta tashi ta je ɗaukar Sabir, yayi ƙasa da muryarsa ya ce “For the second time, idan na ce mimi da ke nake, ba zan so Sabir ya tashi ya ji ina faɗar sunanki ba” ta jinjina masa kai, ta karɓi Sabir.
Ta kalli Ammi ta ce “Ammi, sai a haɗo mini kayansa, na tafi da shi ko?”
Ammi ta ce “A’a, ke da zaki koma school, za’a din ga kawo shi, juma’a da yamma, sai a ɗauko shi ranar lahadi, saboda ki samu ki yi karatunki a nutse, sannan bayan hadimai biyun nan, baba uwani za ta zauna da ku, saboda ta saka ido a kan yadda zasu din ga gudanar da aiki a gidan, idan komai ya daidaita sai ta dawo, saboda ita ce amintacciyar hadimata”.
Babu tsammani rumaisa ta ji gabanta ya faɗi, ba ta son baba uwani, kamar ma tsoronta take ji!.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.