Hausa novels

Fentin Zina Page 31 Hausa Novel

* Tunawa tayi da cincin din da tayi shekaran jiya ta dauko kula daga kitchen mai hannu ta dawo ta zuba mata mai yawa ta bude fridge ta zuba mata soyayyen nama a kai ta rufe ta zauna gefen gado tana sakin ajiyan zuciya dukda tasan ba gwaninta zatayi mata ba amma ita a ranta tana son kyautata mata tare da fatan wata rana komai ya zama tarihi.Ganin lokaci na tafiya yasa ta mike ta fito falo daidai shima ya fito daga nashi dakin cikin shirin shi da hularsa a hannu yana kokarin sakawa, ya kalleta lokacin da yake karasa saka hular yayi murmushi ganinta da kula don ya gane sako zata bashi ya kaiwa mamarsa sai yaji sanyi a ranshi don tana faranta masa ta wannan bangaren yadda take nuna kulawa ga iyayen shi saidai wani lokacin baudadden halinshi da ke hana shi gani.Ta mika mai kular tana cewa ka kaiwa su mama ka kuma gaisheta.Karba yayi yana jinjina kai yace zasu ji sai na dawo.Allah ya dawo dakai lafiya.Ameen yace ya nufi dakin maryam ya shiga ya mata sallama bai zauna ba ya fito yaja motar shi sai gidan.Kamar Kodak yaushe a falo ya tadda su da mama da kannen shi guda biyu sai kanwar mama da bata koma ba har yanzu tun biki, zama yayi ya shiga gaishe su, kannen shi suka gaishe shi suna tambayar amarya? Yace dasu zata zo kwanan nan.Nan sukayi ta hira wanda rabi mama sukar Ameena take yi a cikin zancen saima karamar kanwar shice mai kokarin tare mata.Da yake babu aiki shiyasa bai damu ba ya zauna yasha hirar shi a gurin sai gurin shabiyu da rabi ya mike ya musu sallama ya fita bai koma gida ba a masallaci ya tsaya inda suke sallah karfe daya saida yayi sallah kamin ya koma gida.Ameena ta gabatar mai da abincin dake jere kan dining yace ta sauko dashi kasa anan yake sha’awar ci.Bata musa ba ta sauko da duka abincin yace ta kira maryam, haka ta tafi ta tsaya a bakin kofa ta kirata ta sanar da ita mai gidan na magana, bata jira cewar ta ba ta komo daidai wayar shi na ringing yana dubawa yaga Anas ke kira ya kyabe baki kafin ya daga yasa a kunne.Daga cikin wayar Anas ke cewa tunda kai bazaka neme ni ba gashi ni dana damu dakai na neme ka, ina gajiya?. Hum Abdul yace kamin yace kanka ake ji dama kaine da laifin ai so kai ya kamata ka biyo bayana.Shikenan daga fadin gaskiya sai na zama mai laifi a gurin ka? Ai tunda baka so na daina baza ka kara jin bakina akan abunda ya dangance ka da Ameena ba koda kuwa kaine da kanka ka nemi shawarata akan hakan.Kaga Anas bama zata kawo mu wannan ranar ba ka gane ko.Toh shikenan tunda haka kace sai anjima dama kewar kace naji yasa na kira ka.Ok man nagode sai anjima. Yana fadar hakan ya kashe wayar sa ya ajiyeta gefe yana cewa zuba mana abincin kafin ta fito ina jin yunwa.Ok. Tace ta hau zuba musu, ko kafin ta gama maryam din ta fito suka zauna suka ci.Da yamma Abdul ya dawo gida bayan fitar shi zai hadu da wani friend dinshi. A kofar gate yaga saurayin ranan daya biyo fateema taki tsayawa a tsaye da alama yana jiran wani ya fito ko yaro yazo wucewa ya aike shi ciki don shi a zaton shi nan din gidansu yarinyar daya biyo rannan ce.Karasowa Abdul yayi bayan yayi parking motar shi daga bakin titi yace malam lafiya kana neman wani abu ne? Ko akwai abunda kake jira ne?.Gyara tsayuwa saurayin yayi yace eh toh banace jira ko nema ba wannan sakone daga zuciyata nike son isarwa da masoyiyata.Abdul fa shima tsayuwar shi ya gyara ya harde hannaye a kirji yana duban saunrayin yace ina jinka dame zan iya taimakon ka?.Dadi saurayin yaji yace yarinyar gidan nance wata fara tana da dan tsayi da idanu ita nike so ka mun sallama da idan akwai hali dan Allah wallahi tun ranar da muka hadu zuciyata ta kasa sukuni ina so in ganta akwai maganar da ya kamata mu tattauna da ita.Zuciyar Abdul tuni ta harzuka yayinda wutar kishi ya soma ruruwa a zuciyarshi nan take idanunsa suka kada sukayi jajur kamar garwashi yace matata ce wacce kake magana din akai toh don haka ina umurtar ka daka gaggauta barin kofar gidan nan.Dariya sosai saurayin ya fashe dashi har yasa Abdul ya tsargu ya soma dudduba jikin shi ko zaiga abunda yakewa dariyar.Saurayin ya tsagaita da dariyar tasa ya nuna shi da yatsa yace amma ko kadan bakayi kama da wanda zai iya auren wannan yarinyar ba koma dacewa baza kuyi ba sannan ni bata sanar dani tana da miji ba don haka zan tafi ba domin kai ba amma ka sani zan dawo domin zuwa gurin sahibata na barka lafiya. Daga haka ya haura bakin titi ya shiga motar shi yaja ya tafi ya bar Abdul tsaye a gurin cikeda matsancin fushi wanda hatta da jijiyoyin kanshi saida suka tashi sukayi rudu rudu.Ameena tana gyara kayan walldrop dinta ya banko kofar ya harde hannaye yana kallonta cikin takaici da fusata gaba daya abunda zuciyar shi ke bashi shine “taci amanar ka”. Babu abunda kunnuwansa ke jiyo masa sai yadda saurayin nan ya dinga lissafo kirar matarsa da kuma irin soyayyar da yake ikirarin yana mata. Kalamanshi su suke ta amsa kuwwa a kunnuwansa har yana runtse ido. Sai yanzu ma yake nadamar meyasa bai hada ma saurayin jini da majina ba ya barshi ya tafi.Ameena ganin ya banko kofar a fusace ga irin kallon da yake mata sai ya jefata cikin shakku da tunanin abunda ta masa bayan tasan lafiya suka rabu ya fita waje, rashin sanin takamaiman abunda ya faru ya saka ta fara takowa zuwa gareshi. Firgigit kamar wanda ya tashi daga bacci haka ya dawo hayyacin shi tare da buga mata uban tsawan da ya razanata dama duk wanda yake cikin falon gaba daya.Keeeeee………….Kada ki karaso nan munafuka algunguma ashe dama kin dade kina cin amata ban sani ba? Toh yau Allah ya toni asirin ki wallahi Ameena kinyi asara ashe ke zina ado kika dauke ta? Allah wadaran ki wallahi nayi dana sanin haduwa dake a rayuwata nayi nadamar saninki Allah ya isa tsakanina dake,, ya karashe yana huci sosai.Innalillahi wa inna ilaihi raji’un me kake fada ne haka Abdul me yayi zafi shi ba wuta ba ka mun bayani idan wani laifin na aikata a gare ka kake jifana da irin wadannan kalaman wallahi bansan me nayi ba amma ina rokon kayi adalci gurin yanke mun hukunci.Babu abunda zaki gaya mun munafuka mai fuska biyu ai nasan duk tsayin lokacin nan da gangan kika ki haihuwa saboda ki cigaba da karuwancin ki kada a samu abunda zai miki tsaiko toh anyi walkiya kowa yaga kowa.Dan Allah Abdul ka tsaya mu fahimci juna nifa bansan irin zaren da kake sakawa ba ka bani damar in kare kaina mana ko sau daya ne na rokeka, ta fada lokacin da ta soma karaya da zantukan shi.Fahimtar juna fa kika ce, hum to dawa? Da mazinaciya mai yin zina da auren ta fasika?…Ya isheka….. Ta fada da tsawa sosai tana daga mai hannu tace bansan me kuma zan kara fada maka ba amma ka yanke hukuncin da kake ganin shine daidai saidai kada ka sake kirana da fasika alhalin niba ita bace.Guntun murmushi ya saki yace zaki gani kuwa ya fita a fusace fuu kamar zai tashi sama, jim kadan ya dawo cikin dakin hannun shi rikeda takarda a nade har lokacin bata motsa daga inda take ba saboda rudun da take ciki da kuma madaukakiyar mamakin laifinta da tayi tunanin duniyar nan ta kasa gano inda tayi laifi.Mika mata takardar yayi yace na sake ki saki daya sai kije ki auri wanda ke zuwa yana tsaya mun a kofar gida har yake da tsaurin idon suffanta mun kamannin ki yana so in mishi sallama dake. Dama yace baki sanar dashi kina da aure ba sai kije ku daura daga inda kuka tsaya, saidai abu daya nike so ki sani Allah ya isa tsakanina dake bazan taba yafe miki ba azzaluma.Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, tace ta mika hannu ta karbi takardar ta bude ta karanta kamar haka “ni Abdulmaleek na saki matata Ameena saki daya bayan kamata da laifin ha’intata”. Daga ido tayi ta kalle shi cikin ido lokaci daya taji zuciyarta ta bushe bata jin tsoro ko fargaban komai, tace dashi nagode abunda kayi mun idan mai kyaune Allah ya saka maka idan kuma akasin haka ne Allah ya mayar maka. Daga haka ta juya ta linke takardar ta janyo karamin akwatinta ta debi kaya tasa a ciki tasa takardar sakin a aljihun jakar ta dauki hijab dinta ta saka ta ja ta fita daga dakin don shikam tuni ma ya fita.Ko waiwayen gidan bata yi ba ta tari napep ta shige ta masa kwatance ya fada mata kudin tace muje drop ma kawai zaka kaini idan muka je sai kayi lissafi bana son kara koda minti daya anan…………………. *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️

Back to top button