Harijin Sarki Page 23 Romantic Hausa Novel
Hankalin Sultan ya ƙara tashi ya koma yana tattaɓa jikin Samha ya rasa ma ta ina zai fara wannan wacce irin jarabawa ce yake fuskanta duk matar da yasa a ransa sai ta mutu ta barshi yanzu idan Samha ta mutu ta barshi ina ya kama? Wace zata iya jigila da lalurarsa? Da wannan ya ɗauketa cak kamar ya ɗauki karmami ya fito aka saita masa mota ya sanyata a ciki ya kwantar da ita Yadam yaja motar suka fice, kai tsaye Royal hospital suka nufa aka shiga da ita aka fara bata taimako amma iyakar bincikensu basu gano wata damuwa ba har sungaji da aunata, likitan ya kalli Sultan yace “Ranka ya daɗe ba muga wata damuwa a tattare da Lalla ba saidai kamar akwai shigar sauyin halitta a yanayin jikinta wannan baccin mun kasa gano dalilinsa baiyi kama da bacci ba yafi kama da suma ko kuma commer ta shiga, zamuyi bakin ƙoƙarinmu”Kansa ya kuma kullewa da wannan bayani na likita ya dago jajayen idanunsa yace “Meye zaisa ta suma har haka asalin zafin zazzaɓin ko kuma wani abu daban?” Sunkuyar dakai likitan yayi yace “Har yanzu bamu gano wannan amsar ba ranka shi daɗe saidai mun fahimci zazzaɓinta bai kai wanda zai ja mata wannan damuwar ba, ayi mana uzuri muna kan bincike” numfasawa Sultan yayi yana me kallon Samha dake shimfiɗe kamar gawa ya jinjina kai ga dukkan alamu akwai wani abu ɓoyayye dole zaije ya tsawaita bincike, da wannan ya tashi ya fita ya nufi gidan nasa a hargitse wannan wanne irin lamari ne me kama da mamaki cikin lokaci kaɗan an gadarwa da yarinya bacci me wuya haka.Yana shiga gidan ya zauna a parlournsa kansa na juyawa zuciyarsa na suya yana jin ciwon abinda bazai iya maganceshi da kansa ba a haka Najjisa ta shigo ta sameshi ta zauna a gefensa tana wani karairaya wai ita mace, ya tashi ya shige dakinsa ya kwanta kawai yana saƙawa da kwancewa abin duniya yayi masa zafi, sake biyosa tayi ta ta zauna tace “Wai ya ina binka kana guduna Sultan meye yake faruwa ne Ni naga kamar yanzu baka sona, do Komai zai faru a gidan nan ina sani amma yanzu bana sanin komai, Ni ban hanaka aurenka ba amma Yakamata muma ka sammana lokaci cikin lokacin daka tattara ka bata” Miƙewa yayi zaune ya zuba mata ido har yanzu bata iya haɗa idanu da Sultan kwarjini yake yi mata da wannan tayi ƙasa da kanta yaci gaba da nazarinta can yaja fasali yace “Duk wanda na kama da hannu cikin rashin lafiyar Samha, zan hukunta shi da hukuncin da sai ya kwammace mutuwa da rayuwa, zan azabtar dashi a kurkukun ƙarshe….” Da wannan ya shige bathroom ta taɓe baki tare da cewa “Kaja mata ai saidai ka rinƙa cinta a haka ita da lafiya in anayi a lahira tayi” da wannan ta tashi ta fice daga ɗakin sukayi turus Jalila ta galla mata harara, Najjisa tayi murmushi tace “Saura ke” ratsewa juna sukayi Jalila ta shiga ta ishe yana bathroom wanka yayi ya fito ta kalleshi shima ya kalleta tace “Ranka ya daɗe yanzu Basrah take sanar dani Lalla Samha babu lafiya tun jiya har kun tafi asibiti anya ba waɗanda suka kashe Nataj da Amrusha ne suke bibiyarta ba itama don sunga hankalinka na kanta?” Kallon ta yayi kallo na nutsuwa ya nemi guri ya zauna sosai ya dawo da tsananin buƙatar mace amma komai ya kwace masa Samha a kwance babu hayyaci? Yamutsa sumarsa yayi yace “Na shiga wasu-wasi na kasa bambamce kaina shin me ke faruwa ne jiya i yanzu ƙalau muke yau tana critical conditions shin me yake shirin faruwa ne”Duk da ba har ranta take maganar ba ta nuna alamun tausayawa sosai da wannan ya tashi zai fita tabi bayansa dole suka tafi asibitin tare, da kansa ya ƙara duba Samha Jalila ta zuba mata ido tana kallon baiwar Ubangiji Samha ta ƙeru, wani kishi ne ya taso mata tayi saurin haɗiyewa, dama an canfata a me baƙin kishi da kuma faɗa kar tayi abinda zata ɓarar da damarta tayi shiri akan yau ɗin idan tayi wani yunƙuri ita zata kwana ciki, da wannan ta matsa jikin gadon da Samha take tace “Ranka ya daɗe wannan aikin bana asibiti bane ka bincika kaji zakace na faɗa maka” zubawa Samha idanu yayi shima ciwon baiyi masa kama dana asibiti ba kawai dai baison yin abinda zaisa a fahimci ya gano damuwar da wannan ya matsa ya tsugunna yayi kissing ƙaramin bakinta ya kama hannunta ga mamakinsa sai yaji tafin hannunta da ɗumi sosai ya dago sai yaga ta buɗe idanunta ya ƙura mata idanu yaga yanda ta kafesa da ido ya matsa da sauri yace “My Dr!” Lumshe idanunta tayi ya sauke ajiyar zuciya ne ƙarfi yace “Alhmdllh sannu inane ke miki ciwo?” Sake buɗe idanunta tayi tana ƙoƙarin motsa jikinta ta kasa magana takeson yi ta kasa cewa komai, tayi iya yinta maganar taƙi fitowa, gashi takasa motsa kowacce gaɓa ta jikinta, da wannan ta cika da mamaki tare da tariyo inda wata inuwa ta hudo gini ta fito ta nufo gadon da take kwance bayan Sanah likitar dake kula da ita ta fita, tana kokarin neman agajin Ubangiji wannan inuwa ta feso mata wani ruwa daga bakinta take taji wata azaba ta ratsa ta fiye da wacce taji jiya data faɗi take ta rasa hayyaci shine bata farka ba sai yanzu…..



