Kannywood

Rikicin Hadiza Gabon Da zaharaddin Sani Na kara daukar zafi daga bangaren magoya baya.

Rikicin Hadiza Gabon Da zaharaddin Sani Na kara daukar zafi daga bangaren magoya baya.

Tun bayan da Jarumi Zaharaddin Sani ya fito yayi kausasan lafuzza ga Jaruma Hadiza Gabon kan wata shawara da ta bawa mata masu sha’awar shiga harkar film ake ta cece kuce har ta kai kowa yana ta tofa albarkacin bakin sa inda wasu ke ganin Hadiza fa gaskiya ta fada ba komai ba kuma shawara kawai ta bada a matsayin ta na wacce take da abin cewa akan abin da aka tambaye ta kuma ta fadi abin da ta sani kuma take ganin shine daidai a tunanin ta.

 

Yayin da a bangaren zaharaddin Sani ma akwai masu ganin shi ma fa zancen sa akwai kamshin goskiya, bazai yiwu ace bayan ka gama shan inuwa sai kayi kashi a qurin dan kar wani ya zauna ba dan haka ko kowa zai fadin aibun Kannywood bai kamata irin su Hadizot da kowa ya shaida irin rufin asirin da suka samu a harkar su kushe ta ba.

 

Sai dai kuma wasu na ganin ba ta hanyar da ya kamata Zahraddin din ya kamata yayi mata gyara din ba kenan duk da ma dai magana ce da alamu suka nuna daga wani group dinsu ana tattauna maganar a cikin gida aka fito da da ita.

 

Lamarin dai ya zamo fadan ku ne na manya wa yake shiga domin da dama an yi zaton Hadiza Gabon zata mayarwa da Zaharaddin din martani ko ta dauki matakin shara’a a kan sa sai dai har kawo iyanzu shiru kake ji musamman kasancewar ansan fada ne na rigimamme da rigimammiya domin kamar yadda Zaharadin din baya barin ko ta kwana haka itama bata barin ko ta kwana da zarar an tabata to za a jita sai dai wala’allah kamar yadda maganar ta faro daga cikin gida an koshe ta a cikin gidan.

 

Mafi akasarin masu yiwa Hadiza gabon marfani nayine da cewa dan ta samu wata madogarar ne sabanin Kannywood shiyasa take sukar harkar wasu ko na maimaita batun zaharddin din da cewa in ma harkar ta baci to da sa hannun su yayin da shi Zaharddin masoyan Gabon din ke zargin sa da cawar’ ba komai ne yake damun sa ba face Hassada wasu ko suce dan bata kira shi tayi hira da shi bane wasu ko suce ai talauchi ne yake damunsa.

 

Mufeeda Rashid da ake kira da Yar kosa a dandalin Instgarm ita kuwa tana tsagin Hadiza Gabon inda ta mayarwa da Zaharaddin din martani inda ta rubuto cewa…

 

Wani daga cikin manyarn yaran Zaharddin Sani ya aiko da sako zuwa ga tashar Tsakar gida da ke cewa shi yana mamakin masu cewa hassada ko talauci ne suka sa Zaharaddin sani yin wannan maganganu domin kuwa suna mantawa da cewa shi din fa Shugabane na jaruman Kannywood a Kaduna. Doka ta bashi damar yin korafi kan duk wani jarumi mazaunin Kaduna har ma dana wani yankin.

 

Batun Hassada kuwa ai tana faruwa ne tsakanin talaka da mai kudi ko wanda yafi wani a cewar Abba Zaharddin ya sami duk wata daukakar da ake nema a Kannywood tun duniya na kwance kuma motocin sa da gidan da yake zaune girman gidajen da kuma Unguwar da suke susa kowa yasan cewa masu wannan tunanin basu san komai game da zaharaddin ba.

 

Abba yaci gaba da cewa power bike kawai da yake hawa yana zaga gari yafi kodin wata motar dan haka batun hassada. ko kyashi bai taso ba Zahraddeen Sani mai kudi ne dan me kudi dan da kudinsa ya shiga film so kuma har yanzu da kudin sa gadkiya ce ko akan waye tazo sai an fade ta.
Daga bangaren Fablous G na Kaduna ya mayarwa da Hadiza Gabon Martani inda ita ko Sadiya Haruna ta mayarwa Zaharddin Sani inda suke cewa

Back to top button