Uncategorized

Zuciya Da Kwanji Book 1 Chapter 4

 

ZUCIYA DA KWANJI 
BOOK 1___4

Na Maimuna Idris Sani Beli

Washe garin ranar sai a office ya karya, don sadiya ta dauki zafi sosai da shi, har ya bar gidan bai ga keyarta ba, bayan ya gaji da bugun kofarta ki budewa. Sai wajen sha daya ya daure ya kira wayar fatima, sau biyu tana katsewa yana sake kira, sai ana ukun ta daga bayan ta kusa yankewa. Ba ta ce masa kala ba, shi ma sai ya shiga numfashin jin isa, sannan murya a bace ya ce. “Zan shigo anjima, ko kina ganin nayi zamana kawai?” Ta sha kamshi da kyau,kafin a kasaice ta ce. “Don me

zaka yi zaman naka?”

 Tana rufe baki ya amsa mata “Don kar na zo mu aikata wa juna ba dai dai ba, kina satar hararata, ni ma haka. Idan ta kure ki yi min tsaki….mts! Idan zuwan nawa ba shi da wani muhimmanci na share kawai….”

  Ranta ya yi masifar baci, ita kanta kuma ta rasa abin da ya bata maya ran. tsakin da ya yi mata, ko ma’anar korafinsa, ko kuma rashin ba ta girma da kima? Ya kamata duk ukun, su bata mata rai, amma ta fi jin ciwon rashin ba ta kimar, tasan ko makiyinta na son kallon kyakkyawar fuskarta ko da tana kunshe da abin da ya fi harara, amma me yasa kyawunta ba ya ɗaɗa Abdullahi da kasa? Dole ta tara wadannan kalubalen a zuciyata ta hadiye, murya a bace kamar ana mata  dole ta ce “Na fika ƙin zuwan naka, don akwai ciwo cikin kaskantar da kai na sauraren ka…. Sai dai kana iya zuwa domin zuwan naka yana daga cikin biyan hakkin da muka dauke ka akai”. 

  Ya dan yi jima, tunkunna ya amsata. “To idan haka ne zan dauki hutu akan zuwan, zan komo bakin aiki ranar da ki ka tare….” 

 Ta yi saurin tare shi a tunzure kamar tana a gabansa “Za ka samar da gibi ke nan… A halin yanzu jama’ar gidan nan sun damu da rashin zuwanka…. Za ka zo ne domin su, ba don ni ba, don ni babu abin da zai amfane

ni a zuwanka…. Kashedi na karshe, idan ka zo bana son takura,kar ka yi min irin zaman kunatar da ka yi min zuwanka na farko….”

  Shi ma ya tare ta da cewa “Shi yasa ai na ce na yi zamana kar na zo ki ga bakar fuskata”.

 Daga nan ne ta gane zafinta ba zai ba ta ladabinsa ba, sai ta dan sassauta murya ta ce “Idan ba zaka yi min

zaman kunatar ba ke nan?”

 Ya dan ja fasali Kafin ya tanka ba tare da shakka ba. “Kwarai da gaske, ai ban ga dalilin da zai sa ki dinga daga min hankali ba.ban taba yi miki kallon wata mace da don na raɓeta zan ji abin da kike kokarin yi min katanga da shi ba, watakila da na yi miki kallon cikkakiyar mace ba zan karbi wannan kwangilar ba, don na na munafunci….”

 Tun da fatima ba’a taba fada mata magana mai munin wannan ba, Abdullahi ya ci fuskarta matuka! Ya kuma kara sanyawa zuciyarta ta kullace shi.To me ta rasa? Tambayar da ya kamata ta yi masa ke nan, amma shakkar amsar da zai iya ba ta ta yi mata birki. Ta hadiye yawun takaici, a kausashe ta ce, “Ido kayan wari ko? Inji makaho, Na tabbatar idan na rantse ba

zan yi kaffara ba, ba ka ajiye kyakkyawar mace

kamar ni a gidanka ba….”

 Ya tari numfashin ta a dake. “Ai ba a nan ta keba, wai an danne bodari a ka”.

 Ta yi dif wasu kwalla masu zafi suka fara cika mata ido, ta rasa ma tunanin da zata yi akan wannan mutum wanda wulakanci ya zagayewa numfashin Dukkan KWANJINTA ba shi da tsari a muhallanta. Ace duk kudinta da iya jan zaren mulkinta yau ga wani yana yana keta alfarmarta kuma har yana hada mata da cin mutunci. Kuka ya dan fara fixgarta, ta kashe wayar bayan ta ce masa.

“Abdul ba ka da mutunci wallahi. Na gode”.

 Ya jima yana kallon wayarsa, kalamanta na yawo a kwanyarsa. Ya dan kafa ido alamun son raba hankali fiye da gida biyu, har lokacin da jarumtarsa ta motsa ta danne komai ta ba shi damar tabe baki ya ci gana da harkokinsa.

  Haka Fatima ta wuni da wannan takaicin, da zarar babu idon mutane sai dai ta yi ta faman hawaye. Ta rasa inda zata tsoma ranta ta ji sanyi, bare hanyar da zata bi ta fanshe wannan cin mutumcin da Abdullahi ya yi mata. Wannan bai hanata da $on zuwansa ba, yan gidansu sai hidimar tarbarsa suke kamar wancan lokacin ko ma fiye, tunda yanzu ya zama ahalin gidan. Ita ce dai ba ta wani shiri game da zuwan nasa, har sai da jama’ar gidan suka kwabeta bisa rashin wanka da canja tsari, sai ita da kanta ta ga beken kanta.To mutumin da ka yi kwalliya ma ya ce ba ka da kyau ina ga ba kayi ba? Kawai sai ta

biye wa su safiya, ta yi gayu na garari ta saka kaya wadanda suka lafe a jikinta suka kuma dace da fatarta, ta yi fes kamar mai shirin gasar sauraniyar kyau. A yau babu ma rigakafin wato laffaya, sai wani yalolon mayafi ta yafa irin rufin ‘yammatan zamani.

 Karfe biya dai dai ya rangada mata waya tana ganin sunansa sai da gabanta ya fadi, haka kawai Abdullahi ya fara tsoratata, ga kuma su safiya a wajen bare ta dizga shi. Ta daga wayan da walwala a fuskarta, amma ta

kasa tanka shi, shi ma a takaice ya ce. “Na karaso”.

Ta dinga zabga murmushin dole, ta kasa tankawa, sai ma ta sauke wayar tana ajiyar zuciya. Safiya da shukura suka tafa.

Shukura ta ce, “Tabdijam, wanna gayen ya tafi da imaninki.”

Duk suka fice suka barta tana binsu da kallo, wasu kwalla suka cika mata ido, in banda dole mai Sanyawa a kwana a ido, ai babu dalilin da zai kai ta inda wancan dan rainin hankalin zai ga inuwarta. Har wasu mintuna tana zaune, sai da ya turo mata khalid da kira sannan ta dauro amsa kira. Tana shiga falon suka ƙura mata idanu su duka, musammam Abdullahi wanda yake mata kallo daga sama har kas,idanuwansa na fitar da wasu sakwani wanda zai sa ka tsammaci

tsantsar soyayyar amaryarsa a cikinsu bai tsaya ga tura sakon kawai ba sai ga shi tsaye nuna alamun girmamawa da marhabin. Su salma sun baza mata ido sai ta rasa irin acting sin din da zata karbeshi da shi, don haka ta ji kafarta na hardewa, shi kuwa Abdullahi ya sami distination da nasa

acting din, domin har ya isa gabanta bai bata lokaci ba, ya ware hanununsa ya rungume ta.

Dakin ya fara wantsalata,kirjinta yana

harbawa ta fara kokarin kwacewa lokacin da ta  fara jin shewar su safiya ya hanata da jarumtarsa ta namijin da ya lakanci soyayya, ya dago da kanta ya sumbaci goshinta, sannun a hankali ya bi kunnenta yana rada mata wasu manyan kalamomi masu huda zuciyar masoyi, don haka kwakwalwarta ta kasa fassara mata su. Face wasu ‘yab kwayoyi da zuciyarta ke fada mata kamar sun shafeta.

Wadannan daƙiƙoƙi da za su iya samar da mintoci sun yi mai kama da mafarki, sun dan kwatanta mashi ana samun aljanna a duniya….

Fadima numfashinki na da sanyi da kamshin shaka, kamar yadda jikinki ke tashin kamshi….. Dole ki yi tasiri mai karfi a rayuwar masoyi ko da bai shirya hakan ba….” Ta zama tamkar mutum- mutumi kallonsa kawai take ba tare da tayi magana ba, rike hannunta ya yi ya ja ta zuwa kujera ya zaunar da ita, sannan ya zauna a hannun kujerar, ya dafa kafadarta yana kokarin su hada ido, ya ce “Ki share su safiya, don sun ga kina jin kunya suke miki wannan dan bikin”. Ya juya yafice su safina yana dariya. “Ku je abinku na gode da karramawa”. 

 Ba su bar yi musu shegantaka ba suka fice, A cikin dakikoki da baza su wuce sakan goma ba, dakin ya  dif! Tamkar babu wani mahaluki.

  Kafin kowa ya yunkura. Abdullahi ya mike zumbur ya bayar da baya cikin kankanin lokaci ya canja fuska, kamar fuskarsa ta ranar haduwa, wadda ta dace da munanan kalamansa a waya. Hakan ne ya hadar wa fatima takaici da kaicon mu’amalar da ya yi mata a yanzu, a matsayinsa na baranta da matsayinta a gurinsa na wadda ba ta isa hada kafada da sauran mata ba, kawai sai ta sami kanta da kuka kashirban. Ta dinga kuka kamar ranta zai fita yana tsaye rungume da hanaye, ya juya mata baya kamar kukan nata ba ya damunsa, har dai ya juyo gare ta fuskarsa da alamu tausayawa irin na tsakanin namiji mai imani da mace mai rauni. Ya durkusa a gabanta tare da dago fuskarta muryarsa a raunane ya ce

 “Abin da na yi ya fice yadda yakamata plan dinmu ya ajiye ko? Ki yi hakuri ban yi don na bata ranki ba. Ba kuma wani sabon abu ba ne a cikin dabi’una, dama haka nake don haka ban ga wata hanyar da ba ta kai wannan ba wadda zata nuna farin cikina da kasancewarki amaryata ko da ta a gaibu ne. Ina jin kin ji ciwon haka ne domin kiyayyata da ke cikin zuciyarki…. Ama kuma….” Ta kwace kanta tana share hawayenta, kuma ta tsayar da kukan sai dai zuciyarta ta kara rinewa da takaici.

 A kufulce ta ce masa. “Takaici na ya samu ne ta hanyar ba ni matsayin macen da zata iya shiga gonar soyayyarka ne, ko da kuwa a plan dinmu ne….Ko ka manta ne? Ya kamata ka bi wata hanya wadda zata ba ka damar ci gaba da jadadda abin da ka fada idan dai ba rikidewa na yi daga halittar dutse na koma mace a idonka ba……”

  Muryarsa a tausashe ya tare ta da cewa “Kin kuntata fahimtarki ga magana ta fadima, idan babu soyayyar da zata samar da sha’awa a tsakaninmu me yasa ba zamu samar da wadda zata samar da zaman lafiya a tsakani mu ba? Ki Dube ni a wani dan uwanki, idan ma ba zaki iya hakan ba, yi min kallon baranki amma ki samar da kauna ta tsakanin yaro da uwargijiyarsa”.

  Ta fara sassarfar numfashi, bayan kishiyoyin abubuwa biyu sun hadar mata lokaci guda, takaicin da maganarsa ta samar mata da tsoron janyewar biyayyar Abdullahi da ta fara samu idan ” Na ji, matsa ka ba ni waje”.

 Ya mike yana dariya, ya ce “Shi ke nan zo ki ba ni abinci kar su ce ban ci ba”. Ta dago ta zabga masa harara, ta ce, “Share guri ka zauna ba zan kara zuba maka ba, koda kudinka ka siyo?”

 Ya amsa cikin dakewa. A’a, ni kika sa kudi kika siyo, kuma kanki za ki tsinka, don zasu yi tsammanin mun shagala da wasu al’amura ne shi yasa ba mu tuna abinci

ba”. Da ta dan nutsu sai ta ga kamshin gaskiya a maganarsa, saboda haka ta tashi babu shiri ta ɗebo masa abincin ya ci ya ƙoshi.

 Tun daga wannan rana Abdullahi bai kara komawa wajen fatima ba, bai kuma kara yi mata waya ba, abin mamaki sai hakan ya dinga yi mata ciwo. Ba don takaicin rashin ganinsa ko kuma fassarar da jama’ar gidan zasu yi mata na rashin kulawarsa a gare ta ba, sai din hakan da yayi shaida ce na bai dauke ta a bakin komai ba. Kusan Alh ne ya canje shi, domin da shi ta ke raba dare suna hira a waya tunda babu hali da rana, sannan ya bude mata bakin aljihunsa da kyau, wato ya tura mata makudan kudade asusunta wanda zata yi hidiman bikin da su. Ya so ma ya tura mata kudin Abdullahi na sallama ta ki yarda da uzurin cewa, idan kawu ya ankara kudaden asusunta sun fice kima zai bincike ta, tunda bai barta sakaka ba. 

  A ranar asabar ma’aikata suka je suka kawata mata

dakunanta a gidan Abdullahi, makeken falo mai dakunan bacci biyu kowanne da bandaki, a falon ma akwai ga kicin hade da sito da kuma baranda. Abdullahi mutum ne mai kaunar kawata muhalli don haka girman gidan sa da ƙawar da gidan ya kunsa bai yi kama da nasa ba, musamman idan aka dubi tilon motar da yake hawa alhalin harabar gidan zata ci motoci hudu. Haka cikin gidan ma yana da yalwa, bayan an fitar da sashe hudu irin na fatima sak! Sadiya, Hindatu, shi kuma yake zaune a cikin daya. Akwai wasu empty dakunan saboda baki ko wasu bukata na daban, kai har da karamin wurin shan iska mai kama da lambu. Akwai rumfa gefe da fararen kujeru, can kuma ga bishiyu har da fulawoyi. Wannan ta dan kara daga darajar Abdullahi a idon dangin fatima, duk da cewa sai a saka gidan Abdullahi bakwai a cikin na Alhaji wanda fatima ta baro, amma ba za’a ce fatima ta kastanta ba. Ko kuma tsammanin mamallakin gidan zaiyi sana’ar auren kisan wuta. To haka aka kashe dala wajen kawata mata nata dakunan tamkar ta zo da niyyar zama. Ranar lahadi aka wuni ana shagalin biki da yammaci aka kai amarya gidanta bayan an kaita gidan iyayen Abdullahi har gaban malam ya yi ta sheka mata albarka, kafin ya koma kwarzanta mata angonta nata da irin kyawawan halayensa.

 Bayan sallar magariba kadan kowa ya watse,aka bar fatima da halinta, niyyarta da kuma sake saken wadda zata fissheta. Gidan dif! Kamar babu wani mai rai sai ita. sai gaba daya kadaici ya mamaye ta don ta saba gidansu gidan mutane ne. Haka gidan Alh ma babu laifi, amma wannan kam kamar kufai! Ba ta jima tana kirga mintunan da suka samar da awa daya da ‘yan kai ba, ta ji dirar motar Abdullahi wato bayan sallar isha kadan, kawai sai gabanta ya yi wani mumunan faduwa. Gaba daya ta rikice, sai barin jiki ta ke ta tashi ta koma falo, ta kara lullube jikinta da laffayar da ta ke nade da ita, ta fara duban kofa tana tunanin darenta na farko a gidan Alhaji wanda idan dai irinsa ake wa kowanne irin ango, to Abdullahi ba shi kadai zai shigo gidansa ba a yau. Ta dan fara jiyomaganganu sama sama wanda ta tsinci muryar Abdullahi sai kuma wasu muryoyi biyu wanda ba su yi kama da na abokan Abdullahi ba, domin kamar su na karbar umarni daga gare shi ne. Ama abin mamaki Abdullahi bai nemi dakinta ba har sha dayan dare ta gota, wannan ya sa ta dan saki ranta, sai dai ta kasa ko motsin, iyakacinta dai falon kamar wadda ta zo ci rani. Sha daya da rabi sai ga Alhaji ya kirata a waya ta daga jikinta na bari ko sallamarta Alhaji bai amsa ba ya ce 

  “Fatima ya nemi shigowa wajenki?” Da sauri ta girgiza

kai kamar yana ganinta, tukunna ta ce, “Ko duriyarsa ma ban ji ba”. Alh ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ya ce. “Haba na shiga rudani, tun karfe takwas nake kiran mutumin nan yana watsa kiran nawa a kwandon shara, ina shakkar idan bai yi adding din lambobina to reject list ba, tabbas!”

Cikin fatima ya dauki wani kugi, ta ce “Ko Alhaji? Ni kuma sai nake shakkar da wuya zai yi hakan, kasan rabon da shi tun washegarin daurin aurenmu? Kuma bai taba kiran wayata ba”.

 A matukar gajiya Alhaji ya ce “Toh, Allah ya saya ya ɗore, ki sa wa dakinki key kinji? Kar ki yarda ki dinga barin kofarki a bude”.

 Ta ce da shi cikin bin umarni. “To bari na je na rufe”. Ta kama key zata murza ke nan Abdullahi ya murda handle ya turo kofar. Gabanta ya yanke ya fadi kawai sai ta yi mutuwar tsaye a wajen. Bai ko dube ta ba ya wuce ta zuwa tsakiyar falon yana kare masa kallo kamar wanda ya zo daga kauye. Ta silalo a mugun kasalce ta zube kan kujera bakinta fal da addu’ar neman tsari.

  Ya juyo ya dube ta, fuskarsa sam babu walwala ya ce “Ina ta tunanin kin zo da kaza da kayan sayen baki sai na ji shiru,shi ne na biyo baya” 

  Ta tilastawa kanta karfin hali lokacin da ta ke kallonsa a sakrce, ta ce “Dama akwai wannan cikin sharudanmu?” Ya soke hannu a aljihu ya fara cije lebe, Sannan ya zaro hannu daya yana juyawa ya ce. “Ina tsammanin tana daga cikin sharuda ne masu aiki irin na magani a jikin cuta, kin san ba ko yaushe aikinsu ke tasowa ba, ko kin manta? Ba a zube sharadin zan zo tadi ki ba ni kudin zance ba kike ba ni. Na rike a raina hakan yana da alfanu kamar dai yau,idan ki ka sai bakina sannan ki ka kawo min kaza kamar ko wanne mai KWANJI idan ya yi aure”.

 Ta rasa abin da zata ce masa saboda fargaba da takaici, sai kallonsa kawai ta ke. Tana kifta idanuwa, har sai da ta sami basirar da zata iya fada da tasa basirar. “Idan shi ke nan abin da ya kawo ka sai ka fice na daina ganin inuwarka, ko kai zaka biya ba ni ba. Ba ni da bukatar bakin naka bare ni na yi asarar kudina… Kaza kuma ka manta illarta a tare da kai ne da kake nemanta?…. Mts! Mai tsaurin ido kawai, ka fice ka ba ni guri idan barainin da ka saba ka kawo min yauma shi zan samu ba”.

  Kafin ya yi magana kiran Alh ya shigo wayarta cikin gadara ta amsa wayar. “Ina fatan kin rufe kofar?” Inji Alh.

  Ta dubi Abdullahi wanda ya zuba mata ido a tsorace, sannan ta dubi kofar bakinta na rawa ta ce “Eh, na rufe” 

  Ya ce mata murya a kwance “To sai da safe”. Tana sauke wayar Abdullahi ya dube ta cikin ido ya ce “Me yasa kika yi masa karya?” Ta kawar da kai ta ce. “Ai wani lokacin halal ce….” Ya yi saurin tarar numfashinta, ya ce

“Kin ga ni kuwa ban karɓar halaaccin karya sai ta yi matukar kure min, ko hakan nema sai na kan yi ta a bai bai” Ta kara bata rai, ta ce “Ka yi abin gwaninta, idan ka yi abin da ya kawo ka sai ka fice zan kwanta”. Ya dan ja fasali sannan ya dora cikin nata batun. Akwai saura da yawa”.

Wani wawan tsaki tana.

 Ya yi fuska sosai ya dubi tsakiyar idonta ya ce “Kar ki kara yi min tsaki balle ki fadi wata kalma mai kama da zagi a kunnena, ko ba ki da tarbiyya ne? Ban girme ki ba? Ya kamata ki ce min na yi miki tsaurin ido? Ko kuma ki fada min idan kimar kudi ta zarce ta girma da mutumci…..” Ya dan dakata ya shaki iska kadan sannan ya dora cikin ci da zuci. ” Ba na sayar da girmana da mutumcina akan kudi, idan kina tunanin shi ne tazarar da ke tsaninmu har kika fi ni tsawo. To ki ajiye wannan tunanin zai fi miki kyau”. Ya ba ta damar magana, amma ta kasa ta rasa ma abin da ya cukwaikwiyo zuciyarta, mamaki? Takaici? Ko kuma sallamawa ce? Sai fitar da numfashi da kyar take yi.

 “Sai mu yi bakwana”. Ya katse lissfinata, sai ta saka masa ido kawai ba tare da ta ce kazil ba. Ya yi taku kamar uku da hannu. Sannan ya ce, “Duk ranar girkinki zan shigo kamar wannan lokacin in miki bakwana, ranar da sauran ke da girki zan shigo miki da maraice, sannan duk safiya zan shigo mu gaisa, sai maganar abinci kowacce na girkinta daban ne, idan ina dakinta ta hada da ni,

ke me kika gani a ranar naki girkin?”

 Ta tattare duk masifarta da ke makogoronta akan kalmar da zata fitar. “Ba na bukatar in dora wata tukunya a gidan nan, idan na ci ‘yan kwalam ma sun ishe ni nayi maneji zuwa sati biyun”.    

  Fuskarsa ba ta sauya ba, ya tambaye ta. ” Kin zo da na sati biyun da zaki yi?”

 “Ina ruwanka?” Ta ce dashi cike da tasowa.

 Ya kada kai, ya ce “Babu, sai dai akwai sharadi….” Ta yi sauri dakatar da shi da hannu, sannan ita ma ta miƙe ya ga tsawonta. “Ba ka da wani sharadi da zaka kafa min shi a yanzu, wanda ba ka kullo shi tun ranar da muka shirya ajandarmu ba, saboda haka sharadinka ko wanne iri ne ba shi da muhalli a sha’anina”.

 Ya dinga kare mata kallo sama da kasa, sannan ya kada kai. Karon farko tun shigowarsa murmushi ya bayyana a kuncinsa, ya janyo cofee table ya zauan. Ya zamana ita ce a tsayen, bai dauke ido daga kanta ba ya amsa mata. “Bayan waccan ajandar ce aka kulla min damar jagoranci a cikin sha’aninki da son ranki ko babu…. To wai me kike wa tsoro? Ki jira ki ji sharadin nawa mana don me za ki hau yi min wannan masifar?” Tsaki taso ta yi, amma ga mamakinta sai ta ji zuciyarta na shakkar ta yi masa tsaki, dole ta buge da kada harshe, sannan ta dubi wani wajen daban. Ya kara fadada murmushinsa yana kara nazarinta, ya ce “Sharadin nawa ba fa wani mai tsauri ba ne, dama fada miki zan yi. Nan gidan babu matar da ta ke fita sai da izinina, ma’ana idan kina fita a gidan Alh ba tare da neman izini ba a nan gidan lallai ne sai da yardata, don haka kar ki sake in ga karfarki a waje ba tare da yardata ba”. Bai bata damar magana ba ya kuma dora wani batun bayan ya mike ya nufi kofa. “A karshe ina shawartarki da taƙaita waya da Alh, sannan ki san irin maganganun da zaki yi da shi, saboda gudun bacin rana, har wani cikin gidan nan yasan halin da muke ciki, sannan idan akwai hali ki dan boye wa duniya rashin kaunar da kike min, kin gane ko? Taso ki rufe kofar”. Ba tare da ya jira cewarta v ba ya fice daga falon, binsa ta yi da kallo galala cike da tsabar rudu. Ta rasa makamar da zata rika don fara nazari akan wannan ba’izgilen mutumin wanda ko shakka babu ya riga ya gama ganin damarta, ita ma kuma da alama ta fara sallama masa tunda ta ke jin shakkarsa, koda yake dama can ita ba masifaffiya ba ce, Allah ne kawai yake ɗora ta akan mutane suke shakkarat. To da alama bai dorata akan Abdullahi ba, wanda yake nufin wasu abubuwa masu tsauri a kanta, irin wanda.numfashinta zai iya jurewa da ma wanda ba zai jure ba.

“Kar ki sake inga kafarki a waje…” Maganarsa ke nan da ta bude mata kofar hasashen me Abdullahi yake nufi a kanta? Yana son nuna mata iyakarta ne ta hanye mulkarta don tana cikingidansa ko kuma kawai yana nufin kuntata mata ne don ya sami wannan damar?

 To idan ba ta fita ba me zata ci? Kuma idan ta fita ba da izinin nasa ba me ya tanadar mata? Ba ta iya amsa dukkan tambayoyin da ta yiwa kanta ba, kuma hakan ne ya taimaka wajen raunana zuciyarta, ta barke da kuka. Ta je ta rufe kofar sannan ta dawo ta zauna ta ci gaba da kukanta tana tuno tasirin Alh a rayuwarta, wanda ba ya iya ja da duk wani zabinta ko da kuwa bai yi ma ransa dadi ba, a hakan kuma kullum yake kirarin sauran mata rakota duniya kawai suka yi, amma yau ga ta a gidan da ake faɗa mata ita ta rako matan duniya, har da bita da kullin, takura da wulakanci. Kusan a nan zaune ta kwana a nan falo, sai da aka fara kiraye kirayen sallar asuba sannan wani malalacin bacci ya fara fizgarta, ta daure ta jira sallar asuba ta gabatar da ita sannan ta kum kwanciyar anan falo bacci mai nauyi ya dauke ta.

   A hannu daya sadiya ta fita daga nata kuncin tun shigowar Abdullahi a daren jiya, wanda ko kallon kofar dakin amarya bai yi ba, ya share guri ya zauna kallon wasan kwallon Kafa, har daren ya yi musu asuba ta gari sannan ya waiwaye amaryar shi kamar akan ƙaya, sadiya na duba agogo mintuna ashirin da takwas ya yi ya fito ya shige nasa dakin har wayewar garin nan. Sadiya ta gama yardar wa ranta wannan amaryar har ta fi Hindatu kaskanci a idon Abu Turab, lallai babu wata mace da zata sami rabin matsayin da ta ke da shi a zuciyarsa, wannan ya sa kashi 70% na kishin amaryar ya fice daga zuciyarta, hankalinta kwance ta shari bacci har da saleba.    Wajen karfe goma Abdullahi ya kwankwasa kofar sadiya cikin shirin fita, ba shi da yakinin zata saurare shi, domin jiya da safe kaca kaca suka rabu. Amma ga mamakinsa ko minti daya bai hada ba ta zo ta bude kofar, ba tare da ta dube shi ba ta wuce kai tsaye, ya bi bayanta ya zauna a hannun kujera yana mai fuskantarta, fuskarsa kunshe da walwala ya ce, “Kin tashi lafiya?” 

  Ta kawar da kai tana shan kamshi ta ce, “Kalau”. 

   Ya dan zuba mata ido ya ce, “Ina fatan kin ci abinci kafin ki kwanta wannan baccin naki, bana son zamanki da yunwa”.

Zamu dakata a nan sai Allah Ya kaimu gobe inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Ga masu bukatar Audio kuma za su iya saurara ta hanyar taɓa wannan hoton dake ƙasa. Mun gode da ziyarar Aihausanovels.

Back to top button