═─✿ HADIN TANTABARA YAN SHILA DON KARIN NI’IMA ═─✿
Bayani akan hadin tantabara yan shila don karin ni’ima ba sabon abu bane kusan kowacce mace tasan amfaninsa domin akwai tabbacin yana hada dankon soyayya tsakanin miji da mata bayan ni ima da dandano yana saka gaban mace ya ciko wannan an dade ana amfani dashi kuma yana aiki idan kinason koya to ga yanda zakiyi.
Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi
Da farko dai ga abubuwanda ake bukata ki nema.
1️⃣ Za ki samu Tanbaru amma yaya ba iyayeba (Mace ko Namiji)
2️⃣ Habbatus-Sauda (teaspoon)
3️⃣ Garin Raihan (teaspoon)
4️⃣ Ridi (Cokali uku)
Danna Bulun Rubutunan Domin Karanta Abubuwan Dake Haifar Da Tusar Gaba Da Hanyar Maganceta
5️⃣ Ya’yan Zogale (teaspoon)
6️⃣ Cosbara cokali (teaspoon).
7️⃣ Garin baure (cokali daya).
8️⃣ Kanimfari da citta ko wanne (teaspoon)
Karanta>>> Yadda Zaki Kara Ni’ima Domin Jin Dadin Zamantakewar Aure
Duk wadannan anaso kidakasu su zama gari saiki ajiye bayan kin fara dafa wannan tantabarun sama sama saiki tace ruwan sannan ki zuba wannan garin saiki saka duk wani kayan hadi da kikeso sannan ki zuba ruwa kadan ki mayar kan wuta ki barshi ya dahu sosai sannan ki sauke kuma dukkansu akeso ki cinye ke kadai ki jarraba wannan ko amarya ko uwargida zaku sha mamakin wannan hadin tantabara yan shila don karin ni’ima.
Karanta>>> Yadda Zaku Kula Da Fatar Jikinku A Lokacin Sanyin Nan
Karanta>>> Hanyoyin Da Zaku Bi Domin Karin Kiba Ba Tare Da Kunsha Maganin ba
Shawarwari guda goma da ya kamata mace me fama da kuragen fuska tayi amfani da koda daya ko biyu daga ciki
(1) Da farko ana so awa biyu ko uku kafin ki kwanta barci sai ki shafa man goge baki a fuskarki, musamman wuraren da kurajen pimples suke da yawa. kuma Ba kowane irin man goge baki za ki shafa ba, ana so ki shafa farin man goge baki ne. Idan kin ga dama za ki iya wanke fuskarki idan man goge bakin da kika shafa ya kai minti 30, idan kin ga dama kuma za ki iya kwantawa da shi har zuwa wayewar gari. Za ki rika maimata hakan har zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi hakan za ki ga canji a fuskarki.
(2) Ki kasance mai yawan shan ruwa yawaita shan ruwa ba wai zai sanya miki laushin fata ba ne kawai, a’a, zai taimaka miki wajen yaki da kurajen pimples din da suke fuskarki. Haka yana da kyau ki guji yawan cin abincin gwangwani, kasancewar suna dauke da wasu sinadarai da za su rika sanya kurajen fuska. Ya kamata ki yawaita cin ‘ya’yan itatuwa da suka hada da su abarba da lemu da ayaba da kankana da sauransu.
(3) Ki rika amfani da grem irinsu (Jane Iradale) da (Neutrogenia Rapid Clear) da (Acne Eliminating Spot Gel) da sauransu, hakan zai taimaka miki wajen daidaita man da ke fatarki, wanda masana fata suka ce idan yayi yawa yakan haifar da kurajen fuska.
(4) Ki kasance mai amfani da man (Cornmeal) a fuskarki, yakan sanya kurajen fuska su motse sannan a hankali su bace, misali man shi ne (Intagilo Clear Sal Cleanser.) Sannan ki rika amfani da man da ke hana yaduwar kwayar cutar bakteriya, irin wannan man yakan ratsa kofofin da suke fatar fuskarki da ma jikinki gaba daya, sannan yana yakar kwayoyin cutar da suke fatarki, a lokaci guda ya daidaita miki yawan man da yake fitowa daga fatarki. Zai kuma cire miki kwayoyin halittar da suka mutu a cikin fatarki. Misalinsu; (Phytomer Gommage) da Luffa-0.
(5) Yana da kyau ki ware wata rana ko wadansu ranaku a cikin mako ba tare da kin shafa kayan kwalliya a fuskarki ba, hakan zai bai wa fatar fuskarki samun‘yancin shigar da kuma fitar da iska ta kofofinta ba tare da wani cikas ba. Haka idan za ki shafa kayan kwalliyar a fuskarki, to kiyi amfani da kayan kwalliyar da basa toshe kofofin fatar fuska.
(6) Ki kasance mai shafa mai domin fatar fuskarki ta kasance cikin danshi kasancewar wadansu kurajen fuskar sun fi bata fuska idan fuska tana bushe.
(7) Yi amfani da man (Tea Tree’) domin ba wai kawai yana baje kurajen fuska ba ne, a’a yana rage karfinsu da kuma kalarsu. Za kisami ire iren wadannan man a shagunan sayar da kayan kwalliya na zamani.
(8) Ki kasance mai yin taka tsan tsan wajen amfani da ire iren man shafawar da kike amfani da su a gashin kanki, ma’ana kada ki sake ya rika taba fuskarki hakan zai iya haifar miki da kurajen fuska, kasancewar wadansu sinadaran an yi su don su taimaka wa gashin kai ne, don haka idan suka shiga kofofin fatar fuskarki sai su haifar miki da matsala.
(9) Ki kasance mai gasa kurajen fuskarki Duk lokacin da kurajen pimples suka fito miki sai ki samu wani kyalle mai tsafta, sai ki tsoma shi a ruwan zafi, ba wanda ya tafasa ba, bayan kin tsoma sai ki fito da shi sai ki rika dora shi a kan wajen da kurajen suke, sannan ki rika gogawa a hankali, zafin kyallen yakan sa kurajen su motse daga nan su mutu.
(10) Ki guje yin amfani da hannunki wajen fasa kurajen da suke fuskarki, domin hakan yana kara yawansu hade da sanya fuskarki ta kara cabewa.