Labarai

Yar Gata Ce Complete

Description/Story:

Yar Gata Ce! Complete Hausa Novel Document Written By Miemie Bee

 

Description

‘YAR GATA CE!

BY MIEMIEBEE Page 01

 

 

_Gidan Alhaji ISMA’IL YUSOUF Unguwar Dutsen Tanshi, Bauchi, Bauchi State._

 

Matsakaicin gida ne ba yabo ba fallasa, na d’an kasuwa meh arziki dai-dai ba irin na hauka d’innan ba, arzikin sa beyi yawa ba be kuma kasa ba. Kalan arzikin Alhj Isma’il Yusouf ake kira da middle class earners. Gidan nasa wanda ya k’unshi sashi biyu, k’arami na bayan ya kasance BQ. Daga babban sashin wata ‘yar yarinya chocolate skinned meh k’imanin shekaru goma sha d’aya (11) ce tafito a gurguje ta nufa kitchen inda ta d’au wani k’warya da magani ciki tafito a hanzarce, tsabagen saurin da take har tafashashshen maganin na zube mata a hannu amman hakan be hana mahaifinta k’olla mata kira a fusace daga ciki ba “MARIAM! MARIAM! Wai d’auko maganin ne har yanzu?! Mschww!” kamar wacce zatayi kuka takaici kwance fal a fuskarta tace, “gani nan zuwa fa Baba” chan k’asa k’asa tace, “haihuwa sekace hauka Ya Allah karkasa Mama ta haifi na mac-” bata k’are maganan ba tayi kacib’us da Baban nata a bakin k’ofa, wani kallo ya galla mata tare da wabje k’waryan maganin ya nufa ciki da hanzari a yayinda Mariam ta juya tayi d’akinsu da k’anwarta YASMIN.

 

“Gashi HAFSAH sha kinji? sannu, sannu ko?” Baba wanda ya kasance dark skinned amman kyakkyawa ajin farko yanada ball eyes da long eyelashes with thick brows, sajen fuskarsa ya had’e da moderate gemun dayake ajiyewa, ya kasance cikakken na miji me tsayi dakuma kauri kad’an, sede ba wani babban mutum bane dududu shekarunsa talatin da takwas (38) ne. Maganar yayi ma fara kyakkyawar matar dake kwance kan turkey bed dake d’akin. Mace ce me shekaru talatin da d’aya, (31.) A very young and beautiful woman. Miqe akan gado take tana juyi da tsohon ciki tattare da ita se nishin nak’uda take duk tabi tayi zufa sede sam yanayinta be hana kyawunta wanda yasamo asali daga tushen Fulani fitowa ba. Gefenta wata ungozoma ce zaune tana mata sannu. A sannu a sannu ungozomar tasamu ta d’ura wa Hafsah maganin har a yanzu Baba na a tsaye kan matarsa hankali tashe yana me addu’a a ransa Allah sa Hafsah ta sauqa lafiya ta haifo masa santaleliyar ‘ya mace. Yake ga ba me kaisa murna in matarsa ta haifi ‘ya mace, ‘ya macen da ze samu yayi wa margayiya beloved sis nasa ZAINAB takwara. Zainab takasance best sibling na Alhaji ISMA’IL cikin yayyun sa mace da miji d’aid’ai dakuma k’annensa mata biyu ciki harda Zainab d’in wacce take binsa dab daga shi se ita. Duk cikinsu ba wacce yafiso suka kuma fi shiri da shaquwa kamar marigayiya Zainab ba, shekaranta d’aya (1) da aure mutuwa yayi halinsa, shekaru biyar (5) da suka wuce kenan yanzu amman Alhaji se gani yake kamar jiya ne rasuwan nata, tun rasuwan ta Alhaji Isma’il yad’au alk’awarin da zaran Hafsah ta sake samun ciki ta haihu muddin mace ce takwaran Zainab sistersa zeyi kodan zena tunawa da alkhairun data masa wanda kad’an daga cikinsu ya kasance na basa jarin fara kasuwancin da yakeyi har a yanzu wanda Allah ya mugun sa masa albarka ciki se bunk’asa yake.

 

Sede kash! tundaga kan Yasmin meh shekaru shida (6) yanzu wacce takasance ‘yar auta cikin yaransa hud’u wanda biyu daga ciki maza ne biyu kuma mata, tun daga nan haihuwa yayi rana wa matarsa mafi so fiye da komai a rayuwansa, yau shekaru hud’u (4) kenan rabuwanta da haihuwa se a shekara na biyar (5) Allah ya azurta ta da wani cikin wanda Alhaji Isma’il yad’au buri da gatan duniya ya aza wa cikin, burinsa a kullum bayyafin Allah yabasa santaleliyar macen da zema margayiya Zainab takwara. 2 months back yaje aikin hajj inda ya riga d’awafi yana rok’an Allah cika mai burinsa.

 

Babban d’ansa IBRAHEEM wanda ya kasance fari ne tas wane mahaifiyarsa Hafsah, kyawunsa kuwa sak na mahaifinsa yanada 13years ayanzu yana matakin JSS 3 a karatu a Havardth School wanda ke kusa da unguwansu da k’afa ma suke tahowa se kaisu ne mahaifin keyi a motansa k’iran Corolla S baqa, dan gudun kada suyi latti. Daga Ibraheem se k’anwarsa MARIAM shekaru biyu (2) ne a tsakaninsu. Mariam wacce takasance 11years kyakkyawa ce itama kamanninta irin na Baba kaman Ibraheem sede ita ba fara kamar mahaifiyarsu bace bakuma baqa kaman mahaifin nasu ba chocolate skinned take tana JSS1 a matakin karatu itama a Havardth. Daga Mariam se OMAR shekara d’aya da rabi (1½) ne a tsakaninsu, Omar is 9½ years yana Primary 5 a karatu shima a Havardth, skin colour nasu d’aya da Mariam sede kaman yad’an fita haske. Daga Omar se Yasmeen auta. Shekara uku (3) ne tsakaninsa da Yasmeen she is 6 years tana matakin Primary 2 a karatu itama a Havardth, tanada haske sosai sede bara a kirata da fara ba.

 

Cike da tashin hankali da tsatsan tausayin Hafsah data kasa haihuwa tin tin d’azu, a kaita asibiti kuma taqi, bana wai haihuwan gida takeson yi. Alhaji ya d’ago kai yana kallon Omar daya sasa yima Mamansu fifita kafin Ibraheem ya siyo petir da za’a sa a engine a tayar.

“Wai a bangon duniya Ibraheem yaje siyo petir d’inne?!” Yayi maganar cikin kakkausar muryan dayasa Omar b’ari ko amsa mahaifin nasu yakasa se fifita Maman su yake da sauri da sauri. “Omar dakai fa nake magana! Ina Ibraheem?”

“Bbb… Bbaba ban sani ba kaifa ka aikesa siyo petir yana han-” be k’arisa maganan ba Ibraheem yashigo da galon na petir a hannunsa tare da yin Sallama “Baba gash-” tunkud’esa Baba yayi tare da wabje galon d’in “se yanzu kaga daman dawowa kabar mahaifiyarka tana jiqewa anan dan zufa ko?!”

“A’a fa Baba yau gidan man da layi ne-”

“Rufa min baki ka wuce kaje kasa ka tayar yanzun nan” ya danqala masa galon d’in a sanyaye yaje ya aiwatar da abinda mahaifinsa ya buqacesa.

 

_30 minutes later…_

A’ee (Ungozoma) ce tafito da jariri nannad’e cikin shawul pink a hannunta batai ko inaba se d’akin Baba inda tayi Sallama, rashin amsawansa yasa kawai tasa kai ta shige, zaune kan Sallaya hannayensa biyu d’age a sama yana addu’a ta tarar dashi. Bayan Sallaman da tayi tanemi gu ta zauna har anan Baba be juyo ya kalleta ba sakamakon kukan jariri dayaji yasa yabar dukkanin abinda yake ya juyo da hanzari “A’ee bade Hafsah ta sauqa ba?”

“Ga santaleliyar ‘yarku nan anan.”

“ ‘Ya mace?!” Yayi maganar cike da k’in yarda tsantsan murna da farin ciki “kina nufin mace ta haifa?!” yayi maganan a lokacinda yake amshe jaririyar daga hannunta, yarinyace kyakkyawa ajin farko hanci tun tana k’arama a miqe ba abinda ya rabata da mahaifiyarta Hafsah illa fari da Hafsah tafita, jaririyar ta kasance tana da haske sosai erin masu golden skin d’innan amman da alama harda hasken jarinta tattare da ita nan gaba barata kai hakan haske ba, kyau de kam masha Allah ga gashi kota ina a fuskarta.

 

“Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah mai iko kai Allah abin godiya azumin bakancen dana yi alk’awarinyi a gobe zan fara in shaa Allah ya Hafsah da jiki?”

“Alhamdulillah ta sauqa lafiya tana wanka ne.”

“Masha Allah! Wannan kyauta haka daga Allah, Hafsah taci kyauta!” nan yayi hud’uba wa jaririyar a b’oye sannan a fili yace, “Allah ya raya ZAINAB, Allah raya Mana ZEEZEE a tafarkin addinin muslinci ya albarkaci rayuwarta AMEEN” shida A’ee suka fad’i a lokaci d’aya. “Toh masha Allah Alhaji Allah ya cika maka burin ka sekaje kaga Hafsah kai mata godiya nikuma barin je in sanar da yaran kyautan da Allah yayi mana gabad’aya” ganin tanada niyyan amshen Zeezee Baba yayi saurin dakatar da ita, “barta kije ki fad’a musu a baki ban gaji da riqe Zeezee ba.”

“Oh! Oh! Oh! Alhaji anya zakazo kayi adalci tsakanin yaran nan kuwa?”

“Ke ina ruwanki?! Matsa min anan” yana kaiwa nan ya miqe yabar mata d’akin zuwa d’akin Hafsah har alokacin Hafsah bata fito daga bayin ba dan haka yayi zaman jirarta a bisa gado se k’are wa Zeezee kallo yake yana taking nata pictures a yayinda take ta mummutsika jiki da hannu which is damn adorable.

 

***

“Assalamu Alaikum gwamnoni da matan shugabannin k’asa” A’ee tayi maganan alokacin da take sa kanta cikin d’akinsu Mariam inda dukansu dasu Ibraheem suka taru sukayi jugum tare da had’a tagumi kowannen su na addu’a a ransa Allah kar yasa mahaifiyarsu ta haifi ‘ya mace, Allah yabata na miji inda hali ma maza biyu su basu damu ba amman de kam banda na mace dan kuwa tun baby’n na ciki basu samu sakat ba ina ace an haifosa yau?

“Samari da ‘yan matan nawa barasu amsa bane?” Tayi maganan tana k’ok’arin zama gefen Yasmeen dake kusa da Ibraheem, se ayanzu hankalinsu ya buga duk suka dawo da kallonsu kan A’ee dake binsu da kallo fuskan kowannensu d’auke da tambaya da tsantsan tashin hankali. Kusan atare sukace “Baaba A’ee meh Mama ta samu?” Dariya ta saki kad’an sannan tace, “meye haka? Sekace dugjal aka haifo maku?” Nanma almost a tare sukace, “dan Allah mana Baaba A’ee meh Mama tasamu?” Kowannensu na me kasa kunne dan jin amsarta. Ibraheem yayi k’wafa yace, “Allah sa ba mace ba” qannensa suka amsa da “ameen” a takaice ciki harda ‘yar Yasmeen, ita yanzu shikenan baby’n da aka haifa zata k’wace mata autanci.

 

“Toh ku kwantar da hankalinku d’a na miji Mama ta samu” ta musu k’arya don ganin reaction nasu, zan so kuga yadda ake sakin hamdala a d’akinga daga meh “yes!!” Se meh “alhamdulillah” semeh “thank god” se me sujjada seda ta barsu suka gama haukansu sannan tace, “lallai kuwa yaran nan! Toh ‘ya mace mesuna Zainab Mamanku tasamu”

Ibraheem ya had’e gira kai “Baaba A’ee banda wasa please.”

Mariam tace, “ai ma wasa take bawani macen da Mama ta haifa na miji ne born boy!” tad’an murmusa.

Omar ya bud’e baki zeyi magana kenan Baba ya k’olla ma Ibraheem kira.

“Ibraheem! kazo nan kai da k’annenka” anan duk suka tabbatar da maganan A’ee gaskiya ne, “shikenan mace ce, wallahi mace Mama ta haifo mana” Mariam tayi maganan tare da dafe kanta. Omar yaja ‘yar tsuka “mace ko jaraba Adda Mariam?” Yasmeen wacce takaici yabi ya ratsa ta tace, “Adda Mariam yanzu banice auta ba??” Ita abinda ke damunta kenan sau dayawa friends nata a school sukan ce mata da zaran an mata k’anwa ko k’ani shikenan nata ya k’are, Mama da Baba zasu bar sonta se new baby. Ganin Mariam batada niyyan amsata yasa Yasmeen karkato da kallonta gareda A’ee cikin sauti cike shakwab’a tace, “Baaba wai Baba da Mama zasu bar sona yanzu se baby?” Dogon sumanta A’ee ta shafa a hankali tana mata murmushi “inji wa? Yasmeen d’in Baba? Har a kullum Baba ze cigaba da sonki keda sabuwar k’anwarki Zeezee kinji?” Badan ta yarda ba ta gyad’a mata kai.

Omar ya miqe tare da fad’in “yanzu duk sallolin daren da muka tayi a iska kenan?” A’ee ta dafe baki in suprise _wato yaran nan har Sallan dare suke kar Mamansu ta haifi ‘ ‘ya mace? Lallai ga dukkan alamu Alhj bareyi adalci tsakanin yaran nan ba._ Tayi tunanin haka a ranta.

“Wai ina kuke neh?” Baba yayi maganar wannan karan a fusace. Firgit duk suka miqe Ibraheem ne a sahun gaba k’annensa na a bayansa suka fice zuwa d’akin Mama inda suka hango Baba ciki suka shige ciki A’ee na mara musu baya. Akan kujerar 3 seater dake d’akin sukayi lining suka zauna according to girmansu suna me kallon Baba dayayi banza da shigowansu se wasa wa ‘yar jaririyan da bata ma san yana yi ba yake.

 

Ganin sunci fiye da minti biyu Baba baida niyyan kulasu Ibraheem yace, “gamu Baba” daidai nan Hafsah (maman su) tafito daga bayi da zani d’aure a k’irjinta, murmushi ta sakar wa ‘ya‘yan nata one by one suka gaisheta da jiki suna faking murnan k’aruwan da suka samu banda Yasmeen data turo baki taqi koda magana da Mama ta gano hakan seta murmusa, dankuwa Yasmeen akwai kishi. “Yasmeen d’ita” cewar Mama. “Zo mamana kinji? Zo auta taa” a sanyaye Yasmeen ta nufa wajen Mama suka k’arisa kan gado inda Baba ke zaune da Zeezee se kallonta yake yana mata wasa suka zauna. Daga d’an nesa Mama ta zauna da Yasmeen a gefenta Baba yayi saurin d’ago kai “haba Hafsah na matso nan mana ko bakisan yau k’ima da darajar ki ya k’aru bane? Matso please.” D’an murmushi ta saki tana wasa da gashin Yasmeen “kai Baban Yasmeen barade kabar halinkan nan bako?”

Gira ya had’e “waye Baban Yasmeen? Na kashe sunan nan daga yau Baban Zeezee nakeso” cike da mamaki kowa ke kallonsa a d’akin harta Mama, a hankali ‘yar Yasmeen tafara kuka Mama ta rungumota tana jijjiqa ta.

 

“Yi shiru kinji Auta ta? Baban Yasmeen wace erin magana kuma kake haka? Yanzu dan an samu Zeezee se a k’i Yasmeen kuma?”

“Toh meh? Yayinta ya wuce ke Yasmeen banason shakwab’a meh haka? Tashi ki zauna! Ke bakisan ke yaya babba ce yanzu ba? Kukuma Ibraheem da Mariam haka ake yi a garinku ko? Harda kai Omar, ba wanda yayi yunk’urin amshe Zeezee yaganta cikinku, an samu k’aruwa amman ko ajikinku kuzo kuga lafiyar abinda aka samu dana Mamanku koh? Ku kiyaye nifah!”

Ibraheem ne yasoma yunk’urin magana Baba yadaka mai tsawa “rufa mani baki! tarbiyyan dana baku kenan koh?”

“A’a Baba kayi hakuri” suka fad’i a tare. Ibraheem ya miqe tare da nufowa gun Baba haka Mariam ma hannu ya miqa ze amshi Zeezee Baba ya bige hannun “seda na tambaya toh banaso barin bada taba matsa min anan!” A sanyaye suka koma kan kujeran suka zauna.

 

“Hafsah ya jiki? Ba inda ke maki ciwo koh?” Baki ta tab’e sannan ta amsa “a’a babu alhamdulillah.”

“Masha Allah, sannu Hafsah ta sannu kin chanchanci a baki tukuici Hafsah.” Cike da mamaki su Ibraheem ke kallon Baba a hihuwar Yasmeen Baba be bada tukuici wa Mama ba se ana wannan Zeezeen?

“Tukuici kuma Baban Yas… Aww Baban Zeezee” ta gyara kanta ganin yadda Baba ke hararta. “Tukuicin meh kuma?”

“Sekin tambaya ne? Na wannan kyautan mana, kap yaran nan bame kyan Zeezee gashi ita kad’ai ke kama dake, kin chanchanchi kyautan dubu hamsin.”

“Baban Zeezee dubu hamsin?” ta zaro manyan idanunta, “In ban manta bafa kace kwana biyun nan bakada kud’i yanzu ga harkan suna ga na dubu hamsin kuma?”

“Kinga erin halinki da banaso kenan inde akan Zeezee ne toh ba abinda barinyi ba in barakiyi godiya bane fine.”

“A’a Alhaji na meyayi zafi? Godiya nake Allah dad’a bud’i.”

“Ameen” yace daidai nan Zeezee tasoma ‘yar kuka. A’ee tanufo gaban Baba dan amshe crying Zainab Baba ya hanata, baki ta tab’e “Alhj anya kuwa zakayi adalaci tsakanin yaran nan?”

“Ke A’ee ina ruwanki? Yaran nan de kowa yasha gata yanzu kuma lokacin Zeezee ne itama a barta taci gatan ta saboda wannan *_YAR GATA CE!_”* Su Mariam de har yanzu sun kasa cewa komai se kallon abinda Babansu ke suke harda wai tukuici wa Mama saboda ta haifi ‘ya mace suna cikin wannan nazari a zuqatansu Baba ya daka masu tsawa “ku kuma yayyun banza kuna jin kukan k’anwarku ko a kolan rigunan ku koh? Banason mugunta fah!” Da wuri Mariam ta doso gun ta miqa hannu zata amshe Zeezee Baba ya bige hannun nata itama “matsa min sekace dagaske Hafsah yi sauri ki karb’eta ki shayar da ita.”

 

Mama dake shafa mai tace, “toh Baban Zeeze yanzu zan gama shafa man ina zuwa.”

“Har sekin gama? Itakuma abarta tana kuka? A dalilin meh?”

“Yo! Alhj barin shafa man zanyi?” tayi maganan baki asake.

“Eh Hafsah bari zakiyi ki amsheta” zata sake magana Baba yayi tsawa “kibari nace!” kowa ya tsaya kallonshi haka Mama ta yanke shafa man ta amshe Zeezee tasoma shayar da ita se anan hankalin Baba yasoma kwanciya ganin yadda Zainab ke tsotsan abincinta a hankali Baba besan lokacinda yasoma sama Hafsah albarka ba.

Kusan minti biyar Mama tad’au ta na shayar da Zeezee, a hankali ta zare Mamanta daga bakin Zeezee take Baba yayi magana “ya haka Hafsah? Har ta k’oshi ne?”

Mama batai magana ba Zeezee tasa kuka “miyar mata, miyar mata nace!”

“Baban Zeezee nima fa inada abinyi zan miqa ta wa A’ee tad’an jijjiqata nan danan zatayi bacci.”

“Akan yinwan? Akan yinwan zatayi bacci nace?”

“Wani erin yunwa kuma Alhj bayan na shayar da ita” har anan Zeezee bata bar kuka ba.

“Hafsah ki miyar mata nace karna sake nanata kai na.”

 

“Oh Allah!” Daga fad’in haka ta miyar wa Zainab mama karap ta chafke tacigaba da tsotsa da zaran Mama tace zata cire se Baba ya hanata haka seda Zeezee tayi bacci Baba ya yarda aka kwantar da Zeezee kan gado anan su Ibraheem suka miqe zasu fice suma.

“Ina kuma zakuje?” Baba ya dakatar dasu.

“D’akinmu Baba” Omar yabada amsa.

“Ita kuma Zeezeen fah? Ita kad’ai zaku bari anan?”

“Baba ga Mama da Baaba A’ee.” Cewar Ibraheem.

“Uwarka nan! Uwarka nace! Dawo kaida Omar ku tsaya akanta kuyi mani gadinta.” Baki wangalau Ibraheem ya bud’e, bashi kad’ai ba harta su Mama.

“Baban Zeezee gadi kuma bayan gani da A’ee a d’akin?”

“Bansani ba yimin shiru kicigaba da abinda ke gabanki.” Ganin Ibraheem be motsa ba har yanzu Baba ya buga musu tsawa “daku fa nake magana!” k’iris yarage Zeezee bata farka ba, a sanyaye suka juyo sukayi kan gadon Ibraheem na k’are wa d’an abar da za’a sasu yima gadi kallo.

 

*ACIGABA…???*

 

 

File Name   Yar Gata Ce… Hausa Novel Doc.
Title   Yar Gata Ce Complete
Author    Miemie Bee 
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/07/2024
File Size    1.48 Mb
Format Size    TXT
Book Price    Free
Phone No
Download Yar Gata Ce Complete Novel Document By Meimei Bee
Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button