*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_
_*BY ZAINAB LALUH📲*_
~(Oumm Imam)~
Book 2
Bonus Page 19*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
……..Tuni jirginsu yay landing har an daukesu Matan na gidansu Fanan angwayen kuma na a Guest house d’in Dad dinsu Fanan nan da nan aka fara shirye shiryen event d’in da za’ai wato Indian Night, Misalin k’arfe Goma na dare aka fara d’aukar Mutane zuwa inda za’ayi wanda katafaren Hall ne acikin wani tsadaddan Hotel wanda na Mahaifin Fanan ne had’in gwuiwa da wasu Abokansa turawa, Wow! Wow!! Wow!!! Just Speechless abun ba’a cewa komae sai wanda ya gani Hall d’in ya k’awatu matuk’a kai kace a India ne koda yake indiyawan ne sukai decorating Hall d’in da taimakon Mommyn wata Friend d’in Fanan da suka yi karatu tare suma indiyawa ne amman a Lagos suke zaune duk ita ta tsara komae furanni kota ina, zuwa k’arfe 11 na dare duk an hallara Matan sun sha sari kala kala wasu masu wando wasu dogayen riguna wasu na nad’awa yayinda mazan ma ke sanye da nasu wanda yawanci fakistan ne na Maza, Farar fata kawae kake gani a wurin bak’ak’en yan k’alilan ne irinsu Abbas suma sai sukai kaman bak’ak’en indiyawa gashi dama Lagos badae fararan fata ba sun taru wurin sosae dama suna da wannan had’in kan sai dae basu ji ba har turawan duk shigan kayan indiyawan sukae can Ango da Amarya suka shigo Tubarakallahu ma sha Allah har saida Alk’alami na ya su6uce ba tare dana ankare ba saida zan ci gaba da rubutun na fahimci hakan, gaba d’ayansu shigan Red sukae Haisam na sanye da Pakistan riga red sai wandon golden brown haka takalmanshi ma red ne anyi masu adon golden brown tamkar na sarauta sumar nan tasha gyara sai salki take wuyanshi rataye da scarf irin wanda indiyawa ke sawa shima golden brown wohoho ba ka ta6a cewa ba ba’indiye bane tabbas da Fatuu tazo wurin nan zuciyarta na iya bugawa ganin ta rasa zuk’ek’en miji kamar Haisam yayin da Amarya Fanan aka sha rantsattsan Sari ja tun daga kafarta har wuyanta gwala gwalai ne ta fito sak ba’indiyyar Amarya masu Arziki don kuwa ba kananun kud’i bane a jikinta to d’iyar Hajiya Maryam face yar kasuwa ta kirki data san kaya masu daraja, su kansu kayan Haisam d’in da wad’anda Abokansa su Abbas suka sa duk daga India aka kawo su aka rarraba masu different colours and designs, a bayansu Haisam d’in su Hajiya Maryam ne dasu Laila harda kakarsu Fanan ta wurin uba baturiya da wasu daga cikin danginsu, su Farha ansha sari riga da wando yellow da fari sai faman yauk’i take, fuskar Haisam a sake suka shigo Fanan kuwa sai fara’a take fuskarta cike da tsantsan farinciki komae yayi mata yadda take so suna shigowa Friends d’inta suka hau watsa masu furanni, bayan duk an zauna an natsu MC wanda yake ba’indiye ne amman yana jin turanci sosae ya fara gabatar da abunda aka zo yi in yayi da indiyanci sai ya fassara da turanci, babbar kawar Amarya wadda mamanta ta tsara wurin ita ta fito tay ma kowa sannu da zuwa ta bada tarihin Amarya da indiyanci bayan ta gama sai khairat data sha sari maroon ta fito tayi da turanci bayansu sai aka bukaci babban Abokin ango Abbas ya fito cike da shak’iyanci ya bada da turanci yana yi yana kwa6awa da indiyanci gaba d’aya yaba Mutane dariya bayan ya gama aka kira k’awayen Amarya indiyawa harda khairat don da ita akai rehearsal d’in rawar da za’ayi aka sakar masu wak’ar indiya suka fara cashewa cikin gwanancewa ba tare da suna missing steps ba abun ba k’aramin nishadantar da mutane yay ba bayan sun gama aka bukaci Amarya da Ango su fito su taka Fanan ta mik’e dama ta shirya ma hakan amman sai Haisam d’in yak’i tashi don shi baya rawa balle kuma rawar indiya shi gaba d’aya program din ma baiso ba kawae don yaga tana so ne ya biye mata amman kuma shima abun ya k’ayatar dashi, ita kadae aka kunna ma wak’ar ta fara rawa a nutse tana yi tana zagaye haisam wani lokacin ta duk’a gabanshi ko ta sak’o kanta ta gefen kanshi kota d’aura fuskarta saman gashinshi yadda take bin wak’ar kai kace ita ta rairata sai k’arar sarkokinta ke tashi kowa sai murmushi yake saki hardae sarkin jin kai saida ya d’an murmusa wato Sameer, wak’ar na zuwa k’arshe ta kama hannuwan Haisam alamar ya mik’e ta rungume shi gaba d’aya aka sa tafi da sowa, haka aka ci gaba da gabatar da abubuwan nishad’i ana raba ma Mutane lemuna, har Abbas da Najeeb saida sukae rawa da yan Matan da sukae, oh su Abbas an yada mata a Abuja anata fantamawa🙄, can bayan wani lokaci aka bada damar cin Abinci kowa abunda yake so za’a zuba mashi yawanci duk Abincin indiyawa ne 6angare 6angare, Bangaren shinkafa akwae su chicken Briyani,Veg Briyani,Briesd beef rice,Butter chicken rice, bangaren kaji kuwa akwae su, Chicken Masala,finger chicken,chicken grilled,chicken prame, haka bangaren Salad akwae su Antipasto salad,chicken salad,crispy salad,ponir mix salad da sauransu dae haka lemun ma akwae su Orange juice,Apple,grape,pine apple juice da sauransu kowa saida yaci yay hani’an nima dae ba’a barni a baya ba naci na sha Alhamdulillah😋,wadanda suka ce bazasu zo ba kun ma kanku ai ☹️
Sai wurin biyun dare aka tashi kowa ya koma masaukinsa masu bacci sukayi masu hirar abunda akayi suka dasa, Washe gari kuma aka hau shirin komawa Abuja, kai Jama’a masu kud’i na abunda suka gadama dama iya abunda yasa aka zo Lagos d’in fa kenan🤔, Wuraren sha biyu wasu suka tafi yawanci Haisam ne da Abokansa dasu Nana da wasu daga cikin k’awayen Fanan d’in su kuma sai da akayi La’asar dasu Hajiya Maryam da dangin mahaifinsu lokacin sun gama duk wani shiri suka tafi don a Abuja hidiman take.
Suna komawa ranar aka hau shirin yin Ethiopian Night wanda Laila ta matsa sai anyi har Mahaifiyar Haisam d’in ma tana so ayi dole Haisam ya bada had’in kai ba yadda ya iya, bayan sallar Isha duk an gama shiri danginsu na Ethiopia dasu Laila su Jidderh harda su Amal Amarya Fanan da wasu daga cikin kawayenta duk sunyi shigar kayan gargajiya na Ethiopia wato habesha khamis kala kala duk dogayen riguna Matan suka sa farare masu adon golden mazan ma riga da wando ne farare sai gaban rigunan anyi adon golden, wasu adon maroon, green da sauransu har iyaye su Mahaifiyar Haisam d’in da Hajiya Zainab da sauransu ba’a barsu a baya ba abun ya matuk’ar bada citta su Fanan dasu Jidderh har iyayen duk anyi masu irin gyaran gashinsu ya bud’e d’innan kaman fanka, ba wani wuri aka je ba a cikin gidan akai program d’in anata d’aukar hotuna a wurare daban daban har a saman staircases suka jere abun gwanin k’ayatarwa daga baya aka ci aka sha, Washe gari Alhamis Arabian night akayi a tsadaddan Event center nan ma da taimakon danginsu Laraba aka tsara komae ya tafi daidai su Ango da Amarya dasu Abbas an sha shigan larabawa anci dabino ansha tea an kuma sha Fruit dasu Alkubzu can na hango wasu daga cikin yan Comment section su Bahillot,husnarh,Ma’ulee,munah bature,Boss bature,Bajatu,sis Asma,Maman Amir,habibty, shafa adili,Angel love,Aisha da sauransu dae anata kwasan saura ana ci ana zubawa a jaka wasu harda dabinon k’asa suke tsinta an fake da ba’a murna da bikin kuma anzo ana k’walama lol🤣,
FRIDAY…..
Juma’at babban rana Allah ya kawo mu Abuja ta kar6i bak’uncin Manyan Mutane na gida da kasashen k’etare don halartar d’aurin auren jarumin mu, hidima ta kacame acan cikin gidan bak’i ta ko ina sai zuwa suke banda wad’anda dama sunzo tuni, tun safiyar ranar aka fara sanya anko, Abokan Haisam gaba d’aya na a wani apartment na Senator dake a cikin layin nan aka sauke su har shima Haisam can ya koma yayin da Senatorn kuma da bak’inshi na a katafaren Guest hause d’inshi, Ana gama sallar juma’a a Central Mosque dubban Mutane suka shaida d’aurin auren ENGR. HAISAM ALEE ADAMU ZAKEE DA DR. FANAN MOHAMMED ABRAHAM akan sadaki Naira 500k, Haisam yaga kara Al’umma ko ta ina ba K’aramin dad’i yaji ba, su babansu Haulat duk sun zo haka yan wurin aikinsu babbar Mota suka yo mata da maza har yan gym dinsu ma ba’a barsu a baya ba mata da maza harda Anah duk sun zo kai wasu ma shi kanshi Haisam d’in bazai tuna inda ya sansu ba sai zuwa ake ana gaisawa dashi ana mashi fatan Alkhairi fuskarshi cike da annuri yasha babbar rigar Farar shadda haka sauran Angwayen ma duk Farar shadda suka sa, to a can gida ma dae duk farinciki ake kar ma Fanan taji sam bakinta ya kasa rufuwa kamar ta zuba ruwa a k’asa tasha ba wata kunya da take ji sai faman godiya take ga Allah daya nuna mata wannan rana cike da murna ta kira Haisam lokacin sun nufi Hotel da za’a yi reception yana d’auka ta fashe mashi da kuka tana fad’in at long last ta zama matarshi Murmushi kawae yake saki kafin yace mata shima yana farincikin hakan su Abbas dake gefenshi suka fara mashi tsiya yace zai kira later, daga cikin manyan bak’in dake zuwa yin Allah yasa Alkhairi harda Hajiya Kubra ta Comment section dama Abuja tasu ce can na hangota cikin shiga ta Alfarma ta zo harda iyalinta aka kar6esu hannu bibbiyu ba kamar data gabatar da kanta a matsayin Fan d’in Haisam, bayan wani lokaci tace zata tafi Hajiyar Sanata tace ya kamata ta tsaya aje dinner dasu anjima tace to zasu je anjima zasu sake dawowa ta bukaci sanin time d’in da za’a yi dinner d’in aka fad’i mata,
Jama’a wai ya Fatuu????
Gaba d’aya ranar ta k’ara harmutsewa sanin yau ne d’aurin auren Haisam k’arfin hali kawae take a Makarantar amman ko daga yanayin fuskarta zaka fahimci ba daidai take ba, ba abunda haulat ke gani kan fuskar tata face tsantsar tashin hankali, bayan an tashi suna zuwa bakin lungun gidansu Haulat tace mata gida zata anjima zata zo kasa dakatar da ita haulat d’in tay ta bita da ido har tay nisa, tana zuwa ta bud’e gidan ta maidashi ta datse tun a bakin kopar daki ta saki jakar ta fizge hijab dinta ta nufi gado da gudu sai lokacin ta samu damar sakin kukan dake ta cinta, sosae ta shiga rizgar kuka tana cikin kukan ta mik’e taje ta jawo drawer chest ta mirror d’inta ta curo IV d’in bikin ta koma kan gado tana kallo tana cigaba da rizgar kuka har time d’in da akasa za’a d’aura Auran yay tana a hakan sai ma abunda ya k’aru ma daga kukan duk ta fita hayyacinta fuskarta tay jajir can kuma a fusace ta fara Magana tana fad’in “nasan na rasa ka yanzu bazan ta6a samunka ba Ya Haisam kayi Aurenka ka barni cikin mawuyacin hali ko kirana ma ka daina yi to nima na daina sonka,na daina na daina na daina…….”.
Haulat na komawa gida ganinta ita kadae yasa innarta tambayarta Fatuu tace mata ta wuce gida ta d’aukko abu, bayan tayi wanka tay salla taje wurin innarta a d’aki tace a bata Abincin Fatuu zata kai mata tana kallonta tace “to ba zata dawo ba?” Yan kame kame ta fara yi tace “eh amman tace sai anjima” shiru innar tayi sai kuma tace “wai kodae wani abu na damunta ne naga duk ta canza kamar tana cikin damuwa ko?” Yan kyafcen kyafcen idanu haulat ta hau yi murya na d’an rawa tace “a’a… ba wani abu kawae dae har yanzu tun ciwon data yi kwanaki bata ida warwarewa ba ta koma kaman da” gyad’a kai innar tay tace Allah ya bata lpy da sauri ta amsa mata da Amin, bayan ta zuba Abincin haulat tasa Hijab ta nufi gidansu, tana isa kopar gidan ta iskeshi a rufe ta fara buga kopar shiru shiru ba’a bud’e ba kuma tana da tabbacin Fatun na ciki, can ta aje yar warmer d’in a gefe taci gaba da bugawa amman shiru har gabanta ya fara faduwa ta fara tunanin kar dae wani abu ya samu Fatun wata zuciyar kuma tace ko dae ba gidan ta dawo ba, ta kuma raya mata to ina zata tabbas tafi tunanin tana ciki, cigaba da bugawa tayi da k’arfi can ta tuna da Fatun nada waya ai da sauri ta fara kokarin kiranta har saida ta kira sau biyu tana niyyar tura kira na ukku taji ana bud’e kopar har saida taji wani sanyi a ranta a hankali ta d’an bud’e kopar ta lek’o da kanta suka had’a ido da Haulat ganin itace yasa ta idasa bud’e kopar haulat din ta d’an waro ido tana kallonta da Al’ajabin ganin yadda fuskarta ta koma idanuwanta sun kumbura gaba d’aya ma fuskar ta kumbure da gani ba d’an k’aramin kuka ta sha ba, a sanyaye haulat ta shiga bayan ta d’aukko Abincin ta tsaya tana kallonta tace “Fatuu ya zaki lahanta kanki akan…” Bata k’arasa ba Fatun ta fad’a jikinta tana fad’in “Haulat na daina son Ya Haisam daga yau, yayi Aurenshi ya manta dani inata wahala” nan da nan idanun haulat suka kawo kwalla cike da k’arfin hali ta d’ago ta tace shikenan su shiga ciki hannunta cikin nata bayan ta rufe gidan suka nufi d’akin Fatun, a gefen gado duk suka zauna Haulat ta aje Abincin k’asa kafin ta d’ago ta kama hannuwan Fatuu tace “Haka yakamata, ki daure ki daina sonshi tunda kinga yanzu yayi Aurenshi yana can yana farinciki shida matarshi ke kuma kina nan zaki ma kanki illa kuma ki sani duk abunda ya sameki kece a wahala iyaka kawae nasan bai wuce su kira ki a waya suyi maki sannu an k’ure ya turo kud’in magani, ki daure ki cije Fatuu ki raya mafarkin ki na son zama Doctor kinga jarabawa ke tunkaro mu bada jimawa ba kuma tattare da ita ne zaki raya burinki ko ki kashe shi ki duba irin d’awainiyar da gwaggo ke maki Fatuu kan karatunki Saboda rayuwarki ta inganta ta baro ki da garinku ta kawo ki nan ya kike tunanin zata ji in kika kashe mata kwarin gwiwar da take da a kanki? ki yi hakuri ki bar ma Allah komae kinji?” Kai ta d’aga mata duk tayi sanyi sai kace ba Fatuu ba, hannu Haulat ta kai ta d’aukko kulan Abincin tace “ga Abinci na kawo maki zaki ci ko?” Kai ta d’aga mata alamar eh, tace “to kin ma yi salla kuwa?” girgiza mata kai tayi cikin disasshiyar murya tace “banyi ba amman yunwa nike ji sosae” yadda tay Maganar gwanin ban tausayi, bud’e mata kulan haulat tay tace to taci in ta gama sai tayi Salla tace to haulat na kokarin zuwa ta d’aukko mata spoon a Kitchen taga ta sa hannu ta fara ci ta koma ta zauna tana kallon yadda take tura Abincin da gani ba k’aramar yunwa take ji ba dama ko da akayi break a makaranta bata ci komae ba wani irin tausayinta ne ya kama haulat ta mik’e taje ta daukko mata ruwa ta kawo mata saigashi ta cinye Abincin tass cikin d’an lokaci Haulat na d’an murmushi don taji dad’in yadda ta ci Abincin ta mik’a mata ruwan shima ta shanye shi tass haulat tace to taje tayo Alwala suka mike tare tana kokarin daukan kulan Haulat tace ta barshi ita ta d’auka suka fita, bayan ta gama sallan da kanta tace bari tayo wanka har saida haulat ta rakota bakin toilet kafin ta koma d’aki tana ta juya abun a ranta tana kuma Addu’ar Allah ubangiji yasa ta daina jin son nashi ko kuma ta rage tunda tasan ba abune da zai yuwu lokaci guda ba sai a hankali, bayan ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atampa ta d’an fad’a daka kalli wuyanta amman dirin ta na nan yadda yake, falo suka koma suka kunna kallo saidae ita Fatun idonta ne akan tv d’in amman zuciyarta na duniyar tunane tunane sai faman imagination take akai akai Haulat ke juyowa ta kalleta su had’a ido ta sakar mata murmushi itama sai ta d’an yi mata na yak’e.
Bayan isha aka shiga shirin tafiya Dinner zuwa k’arfe tara aka fara kwasan Mutane, wohoho Jama’a kuzo Kuga tsaruwar wurin dinner d’in Naira tasha kashi a wurin iya decoration d’in wurin abun tsayawa kallone, Ango yasha tsadaddun suit bak’ak’e yayin da Amarya Fanan ke sanye da wedding gown fara tun daga kunnanta wuyanta hannunta da yatsunta duk Diamond ne mai d’an karan tsada haka takalmanta da yar jakar hannunta masu d’auke hankalin Mutum ne, Angwayen ma duk shigan suit sukae haka k’awaye da yan’uwan Amarya ansha ankon rantsattsan leshi jama’a ina masu sana’ar lalle da d’inki ku zo ku dau style iri iri wani d’inkin sai kace na Aljanu gaba d’aya an watse karamar leshin, ina ganin Farha na hau tunanin yadda akai tasa fitted gown d’in jikinta k’arshe dai na yanke a raina k’ilan a Jikinta aka d’inka ta, Ma sha Allah an ci an sha an kuma nishadantu can na hango Hajiyar Sanata da Hajiya kubra suma duk sun sha leshi ashe dae ta dawo da gaske to Momy muna godiya Allah ya bar zumunci, su Fanan a banza an kadaddabe Haisam balle yanzu da igiyan Aure ya shiga tsakani sam bata barshi ya wataya ba tabi ta k’ank’ame abunta amman banga laifinta ba mijinta ne halak malak, sai wurin d’aya aka tashi Haisam duk ya gaji da hidindimun don shi ba mai son hayaniya bane, Washe gari Asabar akai Mother’s eve wanda yazama tamkar Walima don a cikin gidan akayi shi ranar ankon shadda aka sha abun dae sai dae ace ma sha Allah, sai bayan isha taro ya watse masu tafiya suka tafi Misalin k’arfe goma da wasu mintuna Haisam na tare da Abbas a gaban parking lot basu dad’e da shigowa ba daga wurin sauran bak’in su da basu kaiga tafiya ba don wasu duk sun tafi tun jiya Sameer ma sun tafi yau da safe, zaune suke a saman boot duk suna sanye da shadda dinkin sen style duk basu da huluna akan suna cikin fira wayar Haisam dake ajiye gefe ta fara ringing ya kai idonshi kanta Amarya ce tay kira hannu ya kai ya dauka kafin yay picking call d’in ya kara a kunne tun kafin yace wani abu ta riga shi da tambayar inda yake taje part d’inshi bai nan ya bata amsa da inda yake daga haka tay cutting call d’in ya maida wayan inda take Abbas na murmushi ya tambayi Amarya ce ya d’aga mashi kai kawae, bada jimawa ba sai gata ta 6ullo ta baya jikinta sanye da wata matsiyaciyar fitted gown ta atampa super daga k’asa ta bud’e sai tay kaman kifi mermaid kanta tayi fav d’aurin kallabinta wato Zaraah buhari tana sanye da fashion d’an kunne da yan hannu hannunta ruk’e da wayarta yayinda kafarta ke sanye cikin flat shoes sumarta ta linkata ta yadda ta dawo daidai tsakiyar bayanta, wani kalan fitinannan kamshi mai narkar da zuciyar wanda ya shaka take saki ba a kayanta ba ba kuma a Jikinta ba don ba k’aramin gyara tasha ba tun daga cikin jikinta zuwa kan fatarta ita kanta tana jin canji a jikinta sosae ta tsumu da yawa, tunda ta tunkaro su idon Haisam na kanta haka Abbas ma sai sakin murmushi yake tun kan ta k’araso kamshin ta ya rigata isowa tana zuwa gabadaya ta fad’a jikin Haisam ta d’aura kanta a saman shoulder d’inshi don a zaune yake, wani kalan lumshe ido yay ya d’an juyar da kai yana kallonta daga yadda take ta gaishe da Abbas dake zabga murmushi ya amsa yace “Amarya ya gajiyar hidima?” K’asa k’asa tace “akwae shi don am completely exhausted” d’ago kan tayi idonta akan Haisam sukae ma juna kallon cikin ido seductively ta furta “I ave been looking for u since nayi trying no d’inka bai shiga ba sai yanzu” kallonta kawae yake yadda take Maganar underneath his breath ya furta”What’s it, do u have any problem?” K’ara kwantar da kan tayi ba tare data ce komae ba, Abbas yace “baka ji tace she’s exhausted ba I think she needs some fresh air ko ta rage gajiya ya kamata ta d’an ga gari ai ansha hidima da yawa?” daga yadda take tace “u’r right Abbas” wani kallo Haisam yay ma Abbas d’in ganin dariyar da yake yasa ya fahimci da biyu yay Maganar da yayi sigh yay yace “aiki ya sameka sai ka shiga kai driving muje” wata yar iskar dariya Abbas yay yace “aiki ya same ni ko ya same ka ko kana nufin mun gama ma hidiman bikin Matan ma mu zamu yi maka dawainiyar ta in zaka tashi kai aikin matarka ka tashi ni wllh ba in da zani zuwa ma zanyi in kwanta don nima a gajiyen nike” daga haka ya diro ya aje mashi car key d’in yay gaba yana dariya yana fad’in sai sun dawo, Abbas na tafiya ya kai hannu ya d’ago da face d’inta suka k’ura ma juna ido Fanan sai faman lumshe ido take shima nashi a d’an lumshen suke duk sun cika juna da k’amshi, dirowa shima yay ya kama hannunta ya zagaya other side d’in Motar ya bud’e mata ta shiga ya kai bakinshi ya manna mata kiss a cheek d’inta ta wani kalan lumshe ido bayan ya rufe Motar ya zagaya driver side ya bud’e ya shige bayan ya tashi Motar ta kai hannu ta kama hannunshi guda daga haka yaja suka nufi hanyar gate suna isa aka bud’e masu suka fice…………..
.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.