Hausa novels

Halysaah Page 133 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 133…Khaleesat na fita compound taga Ajay zaune a daya daga chairs din dake compound din kusa da flowers yana danna wayarsa, ta sunkuyar da kai ta tafi har inda yake zaune sannan ta daga kai ta kallesa, sai a sannan shi ma ya kalleta, tana da fingers dinta wasa …..tada maka haka ne don ka kawo ni, ka zata da gaske nake? Ai na dawo gidanmu kenan” Tana kai wa na ta juya ta fara tafiya, ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, after a while ya mike ya bi bayanta, Aunty Farida na zaune parlor bayan taje kitchen tayi ma Nenne magana cewar Junaid zai shigo, Nenne aka bude akwati da sauri aka ciro tsadadden gyale ta fesa turare ta yafa ta fito ta zauna parlor ta kora su Mama Zubaida da Mama Shatu wai baza su zauna parlon da yakunannen hijabin jikinsu ba, haka nan duk suka shiga dakin Mama Shatu don da gaske hijab din nasu duk a yakune yake kamar an kwato bakin kura, Khaleesat na shigowa Nenne tayi kasa da murya tace “Ke dai anyi gantalalliyar yarinya mara seti, dama a waje kika bar Yarima guda tun daxu baki gaya mana ba? Babban mutum haka don kin samesa a banza zaki gantalar a kofar gida?” Khaleesat ta hade rai tace “To ai nace masa ya shigo yanxu” Tagumi Aunty …..Farida tayi, banda ma dai ta ga Junaid din mingnikal almost 40 mins, da sallama Ajay ya shigo parlon kansa a kasa, Nenne ta amsa cikin nutsuwa tace “Sannu da zuwa Yarima, sannu da zuwa, Bisimillah ga kujera zauna, sannu da zuwa” Bai zauna kan kujeran ba ya zauna kan Carpet din parlon kawai, Nenne tace “A’a Ahmadi kayi zamanka saman kujera kar ka bata farin rigar ka, dama ga yara na ta taka cafet din” Ajay dai ya gaishesu yana dan murmushi, Nenne ta amsa da fara’a, Aunty Farida tace “Fatan kun sauka lafiya Junaid?” Yace “Alhamdulillan Aunty, ya muka same ku” Aunty Farida tace “Lafiya lau Junaid” Nenne tace “Ai duk bamu san kana waje ba wallahi, yarinyar nan Khaleesat bata gaya mana ba, duk farin cikin ganin yan uwanta yasa ta rude ta manta bata ce mana tare ku ke ba, sai daga baya ta farga duk hankalinta ya tashi wai ta bar ka a waje, mu ma duk bamu ji dadi ba wallahi” Ajay kawai yayı murmushi still not raising his head, Umma ta shigo parlon suka gaisa sannan ta koma dakinta, Aunty Farida ta tafi kitchen ta dauko masa ruwa da drinks da aka tanadar ta kawo masa parlor, Ajay bai …..koma kenan Ahmad?” Khaleesat ta wani kalli Nenne, Ajay yace “A’a anjima zan dawo” Nenne tace o ba laifi, Allah ya kai mu anjiman” Kofa ya nufa bayan ya fita Aunty Farida ta daure fuska tace “Shashasha baza ki tashi ki raka sa ba” Khaleesat ta mike ta bi bayansa fuskarta babu walwala, nan Balcony ta makale har taga ya fita daga gate din gidan, bayan minti biyar ta juya ta koma parlor yanda Aunty Farida bazata gane bata rakasa ba. Da yammacin ranan Khaleesat na parlor tare da Nenne da Aunty Farida, su Mama Zubaida da Mama Shatu ma duk suna zaune parlorn, sai Harira da ta sake dawowa gidan, almajirai ne suka yi sallama bakin kofar parlon, Nenne tace “Lafiya?? ba nace maku ba sadaka yau ba sai gobe?” Almajiri daya ya shigo da babban Gallon din Man gyada cikin parlon yace “A’a kaya ne aka ce mu shigo da su wai” Nenne tace “Kaya? In ji wa?” Yaron yace “A mota aka sauke kayan abincin yanxu aka ce mu shigo da su” Saig wani almajirin …..taliya carton din wasu cous cous, Indomie, Maggie har da carton din satchet Tomatoe paste, Khaleest dai sai kallon kayan abincin take, Nenne ta gyara zama tace “Ikon Allah, wannan dai aikin Yarima ne” buhunhunan shinkafa uku almajiran suka shigo da su parlon, su Mama Zubaida da Mama Shatu suka kalli juna, Nenne ta mike tace “Ai ciccibosu za ku yi mu kai store, komai na son sirri” Almajiran suka bi bayanta da kayan abincin zuwa kitchen. Kwanakin Khaleesat uku a gidansu suka bar garin Kano, kuka sosai tayi don bata yi tunanin just 3 days za ta yi a gidan nasu ba ga kuma damuwar Bauchi da za su je, ko sunan garin ma bata son ji saboda fargaba, a kwanaki ukun da tayi gidansu kusan yini biyu tayi a gidan Neighbor dinsu Hajiya Zaliha da ta tabbatar duk wani salon gyaran jiki babu wanda bata yi mata ba in and out, a nan unguwan nasu aka yi mata gyaran gashi a saloon, sannan Hajiya Zaliha ta hada mata abubuwan gyara da zata tafi Bauchi da su, Umma raba dare take da …… Khaleesat tana mata nasiha da bata aniki tana using kanta as reference, ita dai Khaleesat bata cewa komai wani lokacin haka bacci zai daukata Umma bata gama magana ba. Karfe uku da rabi na yamma Khaleesat suka isa gidan Sarki, kasancewar Mai martaha na da baki yasa Ajay ya nufi part dinsa directly, Khaleesat dai na biye da shi cikin sanyin jiki har suka shiga parlon sa, everywhere was sparkling clean kamar akwai mutum a bangaren, ga wani daddaden kamshi in each and every angle, a hankali Khaleesat ta zauna gefen kujera tana kallon Ajay da ya dau remote zai rage AC din parlon don ko ina yayi sanyi sosai, Bedroom dinsa ya shiga ta bi sa da kallo, wani sai yayi tunanin prison aka kawo Khaleesat don from her facial expression zaka gane she is really disturbed, not long after Ajay ya fito daga dakinsa ya fita daga parlon ya kulle kofa, Khaleesat tayi tagumi tunani iri iri na yawo a ……dawowa uakın wajen kane piyar da rapi ya wuce Bedroom dinsa, ita dai har sannan tana zaune parlor ge abinci iri iri da Yakumbo ta kawo masu parlon, ana kiraye kirayen sallan Magrib Khaleesat ta mike a hankali ta nufi Bedroom dinsa ganin bai fito ba tunda ya shiga, slowly ta tura kofar tana kallon cikin dakin, kwance ta gansa kan gadonsa idonsa a lumshe, ta juya ta koma parlor. Sai bayan isha’i suka tafi babban parlon sarki don gaishesa, bayan sun gaisa Mai martaba na kallon Ajay cikin nutsuwa yace “Amma ka kai ta sun gaisa da mutanen gidan gaba daya kuwa?” Sarki yayi wannan tambayar ne sanin halin Ajay, Ajay ya sauke kansa yace “I will do that in sha Allah ranka shi dade” Ita dai Khaleesat kanta na sunkuye a parlon, Mai martaba yace “Ok do so today” Ajay yace “In sha Allah” Mai martaba na kallonsa yace “Baka jin dadi ne? You don’t look okay?” Daga kai Khaleesat tayi tana kallon Ajay, ya girgiza ma Mai martaba kai yace “A’a i am fine, stress din driving da nayi ne from Kano” ….anik bangaren Aunty Ajay ya fara nufa ba don ransa ya so ba, ita kanta Khaleesat faduwa gabanta yake amma da ta tuna abinda Umma tace mata da ta gaya mata tana faduwar gaba idan ta ga Aunty kawai ta fara addu’o’i kamar yanda Umma tace ta dinga yi, suna ta zaune parlon Aunty for almost 15 minutes, kuma tun shigowarsu Jakadiyarta ta tafi ta sanar mata, lokaci lokaci Khaleesat ke daga kai ta kalli Ajay da ya jinginar da kansa jikin kujera idonsa a lumshe, Walid ne ya shigo parlon, budewar kofar parlon yasa Ajay ya bude ido, Walid ya karaso cikin parion ya zauna kan kujera yana kallonsu yace “Sannun ku da zuwa, ashe kun dawo” Ajay dai kallonsa kawai yake wondering if da su yake cause it’s strange and unusual, after some seconds Ajay yace “Mun dawo” Walid ya kalli Khaleesat dake gaishesa ya gaisheta shi ma yana mata kallon cikin ido, sai kuma ya mike yace “Bari in ma Mama magana ai tana ciki” …..zaman minti asnırın a parion Ajay ya mтіке, Khaleesat na ganin haka ita ma ta tashi da sauri, ya nufi leía ta bi bayansa a ranta har dadi taji da Aunty taki fitowa, bangaren da Hajiya A’isha take Ajay ya nufa, nan ya tarar kilishi ma na parlon, tun da suka shiga parlon Hajiya Misha da Kilishi ke kallonsu, ya zauna ya gaishe su, Khaleesat ma ta zauna kan kujera ta gaishe su, a dakile suka amsa ma Ajay gaisuwansa iya shi kawai, kilishi ta dinga kallon Khaleesat ta gefen ido, wato suna kan kujera ita ma ta zauna kan kujera tsabar raini, ko ya hanya basu masu ba balle su ji sanda suka dawo, after some minutes Ajay ya mike yayi masu sallama, Khaleesat ta tashi ta masu sallama ita ma sannan ta bi bayansa, suka bi ta da wani kallo, cousin sister din Mai martaba Hajiya Habiba dake gidan ita ma Ajay ya karasa dakin da take don gaisheta, tana kallon Khaleesat dake zaune kasan carpet ganin she is elderly tace “Wannan ce matar taka kenan?” Ajay yayi shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace “Eh” Hajiya Habibah tace “Ba shakka” Khaleesat dai ta hakka ….anik suka fita daga parlon Khaleesat da kallo, can ta gyada kai a hankali parlon tana biye da shi, ta bi tace “Sai yanxu na kara fahimtar A’isha” Ajay yaki shiga wajen sauran mutanen dake gidan kawai ya tafi part din Mami…. Tun da suka shigo parlon jikin Khaleesat yayi sanyi sosai jin karisnin turaren Jay, ta nemi kujera ta zauna tana wasa da yatsun ta kanta a kasa, mintin su biyar zaune parlon Mami ta fito daga dakinta, Khaleesat ta zamo kasa a hankali ta zauna kan Carpet, bayan Mami ta zauna Ajay ya gaisheta tace “Lafiya lau, ya hanya” Yace “Alhamdulillah” Khaleesat bata dago kanta ba ta gaida Mami ita ma, yanda Mami ta amsa ma Ajay ita ma haka ta amsa mata, daga haka babu wanda ya sake cewa komai a parlon, after a while Ajay ya mike yayi mata sallama, Mami tace “Allah huce gajiya” Khaleesat ta tashi ita ma ta mata sallama, yanda Mami tace ma Ajay ita ma haka ta ce mata, Khaleesat na biye da Ajay kafin ya bude kofar fita daga parlon Jay ya rigasa budewa, Ajay ya koma gefe ya basa hanya bayan sun hada ido, Jay ya shigo parlon, tun su ….yace “Evening Halysaah” Kasa amsa gaisuwan nasa tayi har ya karasa cikin parlon, Mami dai dukana kallonsu, tuni Ajay ya fita daga parlon, Khaleesat na tafiya a hankali ta bi bayansa. Har karfe goma sha daya na dare Khaleesat na zaune parlor ita kadai, don tun bayan üa suka dawo Ajay ya shiga dakinsa bai fito ba har zuwa yanxu, mikewa tayi ta nufi dakin ta dan bude kofar a hankali tana leka ciki ta gansa kwance kan gado ya rufe har kansa, tafi minti biyu tana kallonsa kafin ta shiga cikin dakin ta karasa kan gadon ta zauna gefe, kawai ta kai hannu ta sauke duvet din tana kallonsa, sosai ta ji jikinsa da zafi duk da ba wai taba sa tayi ba but she could feel how high his temperature is don duvet din ma was hot, lokaci daya ya bude ido, kawai taga ya koma dayaangaren gadon ya sauka kasa ya kwanta leaving the bed for her don yayi tunanin kwanciya zata yi, ita dai tana ta zaune gefen gadon sai kuma ta tashi ta zaga ta inda ya kwanta ta duka kusa ….kusa da shi tace “Are you sick?” One could sense the disturbance in her voice, ya mayar da idonsa ya ufe sai kuma ya juya mata baya, ita dai tana ta zaune wajen, after a while taga ya sake tashi ya koma kan gadon alamar he is not comfortable on the Carpet, ya kara rufe har kansa da Duvet, ita dai kallonsa kawai take, can ta tashi ta sake komawa gefensa ta zauna ta sauke bargon tace “In kawo maka shayi?” Bai bude ido ba a hankali yace “You are disturbing me” Tayi shiru bata sake cewa komai batashi tayi daga karshe ta fita daga dakin ta tafi parlor ta bude flask din da aka kawo na ruwan zafi ta hada masa shayi, ta sake komawa dakin, ta tarar har ya kara rufe kansa da bargo, ta zauna kusa da shi ta bude bargon tana ….felt how hot his hand was, yayi sip daya kawai ya ajiye kan bedside drawer ya koma ya kwanta, ta sak dauko shayin tana kallonsa tace “To ai baka sha ba” Bai ce mata komai ba kuma bai bude idonsa ba, tace “Ka ji?” A takaice yace “Na sha” Sai kuma ya juya mata baya, tayi shiru tana kallonsa kafin ta ajiye shayin kan bedside drawer, tana ta zaune kusa da shi har karfe daya na dare ko baccin ma bata ji tana ji ba, sai juye juye yake and his body was getting hotter minute by minute, da ya fara baccin yake farkawa cause he was jolting now and then, sauka tayi daga kan gadon ta fita daga dakin, tana tafiya a hankali ta bar parlonsa, ta kusa minti diyu tsaye dogon corridor din da zai yi leading dinka away from his part kamar me tunani, can dai ta ci gaba da tafiya, after walking for 5 minutes ta iso bakin kofar ta bude a hankali ……ta ji a bude, shiga cikin parlon tayi tana bin ko aniki halin cewa “Ni ce” Mami ta fito daga dakinta don dama tana zaune ne kan darduma da carbi a hannunta, ta karaso cikin parlon tana kallon Khaleesat da mamaki fuskarta tace “Lafiya?” Khaleesat na wasa da yatsunta tace “Dama bashi da lafiya ne” Mami tace “Junaid din?” Kinaleesat ta gyada mata kai, Mami tace “Me ya samesa?” Khaleesat ta sauke idonta tace “Tun dai da muka dawo ne” Mami bata sake cewa komai ba ta tafi ta dau wayarta ta zauna kan kujera sannan tayi dialing number Jay.

Back to top button