Haihuwa Da Hanji Page 24 Hausa Novel
Da misalin ƙarfe ɗaya na dare ta jefar da mayafin kanta tare da dira daga saman gadon tana jan tsaki, me salim ke nufi ne? Babanta ya tabbatar mata shirin da aka yi akan shi ba mai sauƙi bane da zai iya resisting amma me ya faru har yanzu bai shigo ba? Ɗaukan maganin da Gaje ta bata a gefen bedside tayi ta jujjuya “To bai ma zo bama bare in sha wannan ɗin” ajiyewa tayi ta janyo wayanta kaman ta ƙira su Gajen kuma sai ta fasa ta nufi parlor, kasancewar sashen nashi ɗaki daya ne da parlor sai kitchen in har dai ya shigo to ba zai wuce yana parlorn ba sai dai idan a waje zai kwana.Shi kuwa salim tun karfe tara ya shigo gidan yanayinshi baya mishi daaɗi sam, fuskarshi babu walwala haka ya tura kofan da sallama ya shigo, yana taka door mat ɗin ya ji kanshi yayi wani diimmmmm jiri na shirin kwashe shi a hankali ya furta “Subhallah!”Ya tsaya a wurin sama da mintuna biyu kan ya sauƙe numfashi ya nufi three seater ya kwanta hannunshi dafe da goshinshi, duk yadda zai yi ya samu sauki ya yi sai dai wani irin tension yake ji, sai juye juye yake Sabrina da a chan ƙasan ranshi ya san bai damu da ita ba sai kai komo take yi a ranshi, bai san adadin lokacin da ya dauka ba shi ba mai bacci ba shi ba ido biyu ba, ko matse shi zaka yi ba zai ce maka ga abin da ke damunshi ba sai jin Fitowar ta yayi.Ganinshi ya sa ta nufe shi.”Ya salim dama ka shigo? Shine kayi kwanciyarka anan ina chan duk tsoro ya rufe ni?”Bai ce komai ba sai ido da ya ɗan zuba mata.”Ka tashi mu je ka kwanta a ciki idan baccin ne ma”Ta faɗa tana riƙo hannunshi, kasa mata musu yayi haka ya bi bayanta kaman rakumi da akala, a bakin gado ta ajiye shi ta shiga rage mishi kayakin jikinshi, wani sashi na zuciyarshi tsantsar mamaki yake na wannan bushewar idon wani sashen kuma na faɗa mishi ba laifi bane, har ta gama cire mishi kayan shi dai bai tanka ba kuma bai motsa ba, hannunshi ta ja wai tunda ba ya jin daaɗi su je ta mishi wankan, tana tura shi bayi ta dawo da baya ta sha wannan maganin da gaje ta bata don ta tabbatar mata yana kusantarta da maganin babu kuma wani abu da zai gane, babu wacce zai gani nan duniya bayan ita.Tun daga chan cikin bayin zancen ya sauya, ita ce ke jan ragamar komai kaman ba amarya ba har dai ta samu nasara a kanshi Dukda ita ce tayi kidinta kuma tayi rawanta abinda zuciya bata so gangar jiki ko an tilasta ta ba zata ba da abinda ake so ɗin ɗari bisa ɗari ba, shi dai ya san bayan nan bacci mai nauyi ya ɗauke shi tana kwance jikinshi tana zabga murmushin nasara.Washegari da kyar ya iya tashi yayi sallah a makare, yana zaune kan sallaya idanunshi na zube a kanta tana ta baccinta, duk ya rasa me yake tunani ko me yake ji kaman an yi blocking kwakwalwarshi da daidaitacciyar tunani, knocking da ake ta yi shi ya ɗaga shi daga wurin ya nufi kofan ya buɗe Samha ce.”Ina kwana yaya?”Kai ya gyaɗa bai ce komai ba.”Gashi in ji Mommy wai in kawo muku”Karɓa kawai yayi ya juya ya koma, ta tsaya tana kallon kofan for seconds kan ta tafi.Shirya abincin yayi kan ya nufi cikin ɗaki ya nufi bakin gadon ya shiga bubbuga hannunta.”Sabreena! Sabreena!!””Uhmmmm”Ta faɗa cikin baccin tana haɗawa da tsaki “Wai menene?””Kin yi sallah?”Ta sake jan tsaki kan ta buɗe idanu tare da Miƙewa zaune “Ka san gajiyar da nayi? Ai koyaushe na tashi zan yi Sallar yanzu ka tashe ni sai in yi ciwon kai ai”Da mita tayi maganar.”Ai in sallah bai tashe ki ba yunwa zai tashe ki, ga abinci chan ki fito mu karya”Yana kai nan ya miƙe ya fice yana ji kawai ya gamsu da something is off with him amma ba zai iya pointing menene ba.Sama da mintuna arba’in sai gata ta fito shirye cikin wasu riga da wando masu fadi, yana zaune yana jiran ta ganinta sai ya fara kokarin sanya musu abincin bata hana ba ya saka plate ɗaya zai saka wani ta riƙe hannunshi “Wannan ma ai zai ishe mu Ya salim mun riga mun zama ɗaya ai ko ba haka ba?”Kai ya gyaɗa yana zame hannun nashi ya ɗauki spoon ya saka, ita ta haɗa musu tea tana wani irin murmushi.Tun daga wannan rana saleem sai da ya kwana bakwai bai fita ko ina ba yana tare da ita, wani lokacin haka za su yini duk abinda tace zai gyaɗa kai kuma zai iya yi mata amma ba zai yi magana ba, itama kuma tana abunta da taku ne, ko sau ɗaya basu sauka sun gaida Mommyn ba suna gida ɗaya abinci kuwa safe rana dare daga wurin mommyn ake turo musu, wayanshi ma kashewa tayi kar ma a kira shi don dama ya ɗan samu hutun aiki.Yau mommy na zaune a parlor tana mamakin wannan sabon hali na Saleem kasa shiru tayi ta kalli Sadiqa tace “Yayanku kam duka cikin daaɗin auren ne za’a kwana bakwai muna gida ɗaya bai iya lekowa ya gaishe ni ba? Daga shi fa har Sabrinar tunda aka haura da ita ban ga keyarsu ba”Sadiqa tayi murmushi”Ai za ki musu uzuri Hajiya mommy kin san sabon shiga, amma na san dai duk yadda ake ciki yau kam kila su sauƙo kin san har da gajiya duka na hidima ya tarar musu”Samha dai bata gamsu ba amma ganin mommy bata sake cewa komai ba sai itama ta share.”Amma mommy ba kya tunanin akwai abin da yake damun Sameera? Yarinyar nan duk ta zama kaman ba ita ba don damuwa?””Toh Sadiqa ya zanyi? Na yi tambayar duniya ta ce babu komai kila ku in kun saka ta gaba zata faɗa muku damuwarta”Sadiqa tace “Wlh ni dai ta ƙi faɗa min ban san ko Samha ba””kawai karatu ne fah! Kin ga tana ta shirin shiga final year abin babu sauƙi”Ba wai sun yarda ba suka bar maganan, Sameeran ce ta fito ta zauna za tayi magana suka ji motsin takowa kaman ana saukowa daga stairs duk ido suka zubawa staircase ɗin sai ga Sabrina da Saleem suna jerowa idanunshi na kallon ƙasa yayin da take murmushi mai faɗi har tsakiyar parlorn suka zo bai ɗago ba, ganin zai fice mommy ta miƙe tsaye “Saleem”Waigowa yayi ganinsu ya ɗan shafa kai “Oh mommy ashe kuna nan, barka da safiya”Speechless ta zama ta kasa furta ko A, Sabrina ta kalleshi “Kayi sauri don Allah Ya Saleem idan ka dawo za’a yi gaisuwar”Ba musu ya juya ya fice, ta juyo tana murmushi ta zo ta samu kujera ta zauna”Mommy barka dai Fatan kina lafiya?”Ido kawai suka zuba mata, da kyar mommy ta kawo musu uzuri a ranta ta zauna tana cewa “Lafiya ƙalau ɗiyata ya zaman sabon wuri?””Lafiya ƙalau mommy ai ba wani sabunta da yake duk gida ne kuma yayan yana kula da ni yadda ya dace”Kai mommy ta gyaɗa, samha da Sabrinar take sa’a da ita tace “kin tashi lafiya?”Murmushi tayi “Lafiya ƙalau ƙanwar mu”Harara ta maka mata Sabrinar tayi wani murmushi tana kallon su sadiqa tana jira su gaisheta.Mommy ce ta musu ido duk suka gaisheta ta amsa kuwa hankali kwance ita matar yayansu “Mommy kin ga ya fita yana sauri ko? Wlh Gaje ce bata ji daaɗi ba kuma Bakinta babu taste kwadayi take ji shine na ce ya je ya sayi kayan kwalam sai ya kai musu gidan ya kuma bata kudin magani”Mommy da kanta ya sake ɗaurewa tamau ta zubawa Sabrina ido sabon salo wai gada a kotu yaushe kuma aka fara hakan? “Ah yayi kyau”Abinda ta faɗa kenan, Sabrina ta miƙe “Bari na koma ciki”Tana kai nan ta haura saman ta Barsu da tunanin me ke faruwa? Sai dai babu wanda ya je da nisa saboda mommyn na mata uzuri kuma tana son ta da Saleem ɗin sai suka kama wani hirar daban.****Yau sunday tun safe Afeefah ke tare da Mammi, hira suke yi kaman ‘ya da uwa kafafun Mammin na kan cinyar Afeefah tana ɗan matsa mata take cewa “Mammi yau ƙafafunki sun kumbura dama yana miki haka?””Yana yi Afeefah, ni kam me ba na gani ne? Yau kam ma na tashi jikin sai a hankali ai ni kaɗai na san me nake ji”Tayi maganan da ‘yar haki tana kishingida.”Sannu! Ko zaki ƙara magani?””Kayya bar zancen maganin nan Afeefah, je ki kira min Yayanku nayi ta gwada layinshi bana samu tun bayan asuba da ya shigo nan muka gaisa ban sake ganinshi ba”Idanu ta ɗan waro gabanta na faɗuwa, Dukda ta san ta inda Sashenshi yake amma bata taɓa gigin shiga ba to me zai kai ta? Yanzu ɗin ma jiki a sabule ta miƙe ta fice daga ɗakin, Abeeha bata nan tun safe taje gidan jiddah za ta raka ta asibiti wai bata jin daaɗi da ko ita zata iya zuwa amma ita har yanzu ganinta baƙuwa a gidan take, ko ba ma haka ba ina zata iya da wannan da ba’a mishi gwanintar? Mutum sai faɗin rai da masifa… Da kyar ta ɗaga hannu tayi knocking kofan parlorn sai dai shiru babu amsa, ta sake yin knocking karo na biyu nan ma shiru, a hankali ta tura kofar da sallama a Bakinta ta shiga yana kishindige very relaxed a cikin kujera, parlorn da hasken shi ba sosai chan chan ba sai tashin kamshi yake, kaman waya yake yi amma ba da wayar da ta saba ganinshi dashi ba gabanshi system ne shima a kunne kaman dai aiki yake yi ya tsaya amsa wayar.Daga ɗan nesa ta tsaya kanta a ƙasa tana jin yadda yake magana wane wani sarki, murmushi tayi a chan ƙasan ranta take raya dole Mammi ta kira shi Saraki don shi komai nashi ya fi yanayi da jinin sarauta, bayan ya gama wayan ya ɗan kalleta ba tare da ya ce komai ba ya ɗauke idanu itama jin shiru ya sa ta ɗago ganin ya gama wayan ta ɗan ƙara taku biyu sai ta rasa me za ta ce.Da kyar ta iya haɗa kalmar sunanshi akan lips ɗinta “Yaya Saraki…”Ɗagowa da yayi ya kalleta ya sa maganar datsewa, bai san ya ɗago ɗin ba don yadda ta kira sunan sossai ya dake shi, bayan Mammi bai yarda ya ji sunan bakin kowa ba amma jinshi a Bakinta sai ya rasa me yake ji ma, haushi ne ko takaici ko bacin rai? Tsam ya miƙe ya nufo ta.Idanu ta shiga zarewa takunshi na tafiya da bugun zuciyarta har ya matso dab da ita yace “Maimaita abin da kika ce?”Shiru tayi ta kasa magana idanunta da suka yi raurau alamun kuka ko wani lokaci ta ɗauke daga kanshi jikinta na tsuma ta ciki, kusan seconds huɗu kan ya ce “Allah ya so ki, da kin maimaita sai na fasa miki baki ke Mammi ce da za ki kira ni Saraki? Wani Yaya Saraki…!”Ya sake maimaitawa yana ɗan harararta.”Me?”Ya faɗa yana dan gyara tsayuwa idanunshi tsamm a tsaye a kanta ko a jikinshi.”Yaya…”Wlh sai ta kasa cewa Rayyan ɗin tayi tsai tsammm sai ma ta fasa kiran sunan da ɗan saurin baki tace”Mammi ce wai ka je!”Ta juya za ta fice yace “Tsaya!””Ba ni da suna ne? Ko da gini kike magana?””Innalillahi wainna ilaihi rajiun…”Ta faɗa kaman za tayi kuka chan ƙasa, sarai ya ji ta “Ga musiba tsaye gabanki ko?”Girgiza kai tayi, tsaki ya ja yace”Bar nan”Da sauri ta fice.Sai da ta ganta tsakiyar babban parlor kan ta dafe kirjinta tana sauƙe numfashi, Rayyan na son kasheta da ranta, yaushe ya iya ma dogon magana haka bata sani ba, shi da komai ko oho ne me yasa zai saka ta a gaba yayi ta razana ta! Jiki a sabule ta ƙarasa wurin Mammi “Wai yana zuwa”Zama tayi kawai bata sake cewa komai ba, mintuna basu wuci uku ba sai gashi gaban Mammin kawai ya ƙarasa ya fara taɓa temperature ɗinta, numfashinta baya fita yadda ya kamata hankalinshi tashi yayi, a take yace su tafi asibiti duk yadda Mammin za ta ƙi ya nace ya dubi Afeefah yace ta ɗauko mata mayafi, da sauri taje ta ɗauko duk sai ta shiga damuwa ganin yadda hankalinshi ya tashi, kuma dai a fili Mammin bata yi tsananin da ya kamata ya ɗaga hankalin nashi haka ba, bata zauna ba itama gyalen da ta ɗaura a kanta na Jersey ta warware ta yafa akan doguwar rigar atamphar dake jikinta ta bi bayansu, a gaba ya saka mammin ta buɗe baya ta shiga suka fice daga gidan.Tafiyar mintuna ashirin ya kai su asibitin shi ya sake kama mammin suka yi inda za’a duba ta don ya riga yayi call, tuni suka karɓeta don a yi mata gwaje gwaje a tabbatar da babu abin da ya sake tsananta ko chanzawa.A reception ta zauna idanunta na kan yatsun ta sai adu’ar samun lafiya take yiwa Mammi mata mai kirki da mutunci, macen da ta zame mata uwa kuma garkuwa a yanzu. “Afeefah…!”Da ɗan karfi ta ji an kira sunanta har bata san ta ɗago a razane ba sai…


