Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 14 Hausa Novel

Ya lalubo lambarta ya danna mata kira, sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ta daga. Murya kasa-kasa tace ‘Hello.’Yace ‘Hello, Khadeeja ba kiyi bacci ba?’‘Na dan yi, farkawa dai nayi kuma naji wayar tana ringing. Ai tun dazu aka gama wankin cikin har na dan ci abinci.’‘Sannu. Wankin cikin ba wahala kenan?’‘Hmmm! Akwai wahala ba kadan ba, kawai dai da an gama aka bawa mutum maguguna sai ya sami relief.’‘Sannu. Afaf ce dama ita da Habibi wai ba zasu iya barci ba sai sun yi miki sannu.’Tayi murmushi mai sauti domin ta ji dadi har cikin ranta, ta tabbatar cewa yaran nan suna kaunarta kuma da zai barta da su komai nasu zai zo da sauki amma shi komai gani yake kamar zata cuce su. Muryar Afaf ce ta katseta bayan da Abbanta ya bata wayar ‘Anti.’‘Na’am Afaf, ya aka yi ba kiyi bacci ba.’‘Babu komai Anti, ya jikin naki? Ke ya aka yi bakiyi baccin ba?Tayi ‘yar dariya tace ‘Yanzu zan yi Afaf, kuma na sami lafiya don likitan ma ya ce gobe za a sallame ni.’Suka dan taba hira sannan tayi mata sallama ta mikawa Habib wayar. Bayan sun gama gaba daya ya karbi wayar ya katse yayi mata sai da safe. Ya yi musu sai da safe suka kwanta, har zai kashe fitilar Afaf tace ‘Abba kada ka kashe mana fitilar, in an jima ka zo ka kashe.’Haka ya bar musu fitilar ya fice.Can bayan awa daya ya gama abinda yake yana so ya kwanta saboda ya gaji ya zo zai kashe musu fitilar, yana kashewa Afaf da Habib suka hada baki a lokaci guda suka ce ‘Abba kada ka kashe fitilar.’Da mamaki yace ‘Kai! Me kuke baku yi barci ba?’Afaf tace ‘Abba to ni dai na kasa bacci, da ma zaka taya mu kwana.’Habib yace ‘Eh wallahi Abba don ni wallahi tsoro nake ji.’Takaici ya kamashi, to yanzu ya zai yi? Taya su kwanan zai yi ko kuwa barinsu zai yi a haka suTakaici ya kamashi, to yanzu ya zai yi? Taya su kwanan zai yi ko kuwa barinsu zai yi a haka suna zare ido yaje ya kwanta? Wannan wacce irin fitna ce a daren nan gashi ya gaji.Baya son barinsu su kadai don haka ya wuce dakinsa yaje ya shirya ya rufo gidan sannan ya dawo nan dakin; katifar Habib karama ce ya san ba zata ishesu ba don haka kawai ya gyarawa Nasreen da Shukra kwanciya ya dan sami waje a gefen gadon ya kwanta bayan Khadeeja ta kwanta a daya gefen. Yayi addu’a ya tofa musu sannan yace kowa ya rufe idonsa kada ya sake jin motsinsu.Tunda ya kwanta yake jin wani dan doyi haka, idan iska ta busa sai ya ji kamar doyin ya buso cikin daki idan iskar ta wuce kuma sai ya daina ji. A haka bai san lokacin da bacci ya daukeshi ba.‘Subhanallahi!’ ya fada bayan yayi firgigit ya tashi, ya kai hannunsa ya taba inda yake kwance daidai duwawunsa yaji shi a cikin ruwa sosai. Ya daga hannun yana kallo da tsananan mamaki ‘Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.’ Ya sake fada a fili.to fitsarin kwance yayi ko me? Gashi yaran duk sunyi bacci balle yace wni ne ya zuba masa ruwa; tunda shi dai ya san baya fitsarin kwance. Motsin Shukra da yaji a kusa da shi ne ya tabbatar masa da cewa itace tayi fitsarin, ya mika hannu ya tabata ya jita a jike amma tana ta baccinta hankali kwance. Ya kai hannu zai janye Nasreen daga kusa da ita ya jita itama a jike ‘Tab!’ ya fada a fili. Kenan duka su biyun suke fitsrin kwance ko kuwa yau suka fara? Don shi tunda Khadeeja ta tare a gidan nan sau daya ya taba ji an ce Shukra ta yi fitsari. Ya kalli Afaf wadda ita tana can ta takure a karshen gadon tana baccinta, ya danna wayarsa ya kalli lokaci yaga karfe biyun dare. Ba zai iya tashin yaran nan ba don haka ya lallaba ya sauka daga kan gadon ya fice ya shiga dakin Khadeeja ya samo zanin gado ya zo ya rufe su saboda kar sanyi ya dinga kadasu ga danshi.Bayan ya gama rufesu ya zo ficewa daga dakin doyin da yake ta ji ya sake dukan hancinsa; wannan doyin ai sai ya kymburawa mutum ciki. Kamar daga bandaki doyin yake fitowa don haka ya koma ya bude kofar bandakin ya shiga, ya karasa ya leka toilet din ya tarar babu komai a ciki duk da haka dai ya danna flushing ya juya zai fita. A daidai bakin kofa daga jikin bango ya ci karo da fo din Shukra wanda dazu Afaf ta cire wandon Shukra mai dauke da kashi ta jefa a ciki. Pant din yana nan da kashin a yanda ta ajiye har ya fara bushewa amma duk ya dumame bandaki da doyi.Ya dan ja baya kamar a firgice, to wa Afaf ta ajiewa wannan kashin? Yanzu ya zai yi da shi gashi duk ya dumame gidan da wari. Ya daga hannuwansa ya zuba a aljihu, danshin da yaji ya tuna masa cewa wandon a jike yake da fitsrin Shukra ce ko Nasreen shima bai sani ba. Yayi tsaki ya fito daga bandakin ya wuce dakinsa yana tunanin yanda zai yi da kashin, gashi a jikin pant yake balle ya sa a toilet yayi flushing.Saida yayi wanka ya canza kaya sannan ya fito daga dakin, yana fitowa yaji warin kashin nan har parlor din saboda ya bar kofar a bude. A fusace ya wuce kitchen ya dauko katuwar bakar leda ya zo ya dauki fo din ya kulle a ledar, ya sake dauko wata ledar ya kara kullewa sannan ya dauki mukulli ya bude kofa ya fice ya jefa a shara; gari yana wayewa zai sami yaro ya fitar masa da sharar. Ya san dai Shukra ta iya hawa toilet yanzu, duk da idan ta so rigima sai tace sai ta hau fo amma shi dai ya zubar don ba zai iya wankin kashi ba kuma ba zai iya bari Afaf tayi ba ta zo ta yi musu jagwalgwalo da kashi.Yana dawowa cikin parlor din ya kalli agogon bango yaga karfe uku har ta wuce, abinda yayi masa saura bai fi awa daya da rabi ba ayi assalatu. Sai a lokacin ya tuna bashi ma da abincin sahur, gashi kuma ko a lokacin ma yunwa yake ji balle yace zai yi dore. Kai tsaye ya wuce kitchen ya dora indomie sannan ya tafasa ruwan shayi; nan da nana ya juye indomie din a plate ya dumama stew ya zuba sannan ya hada shayi, ya kwaso ya dawo dining table ya fara ci.Tun kafin ya hadiye lomar farko ya fara jiyo hayaniyar Shukra a dakinsu, yana zuba loma ta biyu ta budo kofar dakin ta fito tana kuka tana ‘Antiiii..’Ya ajiye cokalin yace ‘Menene Shukra?’‘Shayi zan sha Abba’Har cikin zuciyarsa takaicinta ya kamashi, to amma ya zai yi da ita? Haka ya kirawota ya zaunar da ita a kan kujera, tun kafin ya gama gyara mata zamanta zarni ya cika masa hanci; sannan ma ya tuna tayi fitsarin kwance. Ya gyara mata zama yace ‘Bari na gama sahur sai na hada miki shayin.’Ya dauki cokali ya zuba loma a bakinsa yayinda ita kuma ta fara mutssike ido tana kuka.‘Menene kuma?’ ya tambayeta‘Yunwa nake ji, shaaayiii.’ Ya duba agogon wayarsa, saura bai fi minti goma sha biyar ba a yi assalatu ga shi baya jin zai kai azumin nan idan bai yi sahur ba, ya kalleta yanda take ta kuka kamar wadad aka ciza. Bai taba jin haushin Shukra kamar yau ba, amma babu yanda zai yi. Haka ya juye mata rabin shayin da ya hada zai sha ya saka mata madara da milo ya mika mata sannan ya cigaba da cin abincin.Yana yi yana kallon lokaci saboda kar a akirawo assalatu. Haka ya ci abincinnan yayi sauri ya kwankwade shayinsa rabin kofa sannan ya dora da ruwan sanyi duk a loakci guda. Yana ajiye kofin aka fara kiran assalatu, ya kwantar da kansa a jikin kujerar yana mayar da numfashi.Shukra da take kan kujera tana gyangyadi bayan ta shanye shayinta ta taboshi tana cewa ‘Abba kashi zan yi.’A dan zabure ya dubeta yace ‘Kashi Shukra?’Cikin halin ko in kula tana murje idonta tace ‘Um.’ Ta fara kokarin sauka daga kujerar da take zaune.Ya jijjiga kai cike da takaici; su wai yara ba a hutawa da hidimarsu ne? tunda ya dawo daga asibiti ake abu daya gashi duk yana neman fita daga hayyacinsa amma babu alamar sauki. So yake ma ya sami natsuwa ya turawa Khadeeja message ta whatsapp yaga ko tana online amma basu bashi time ba, a halin yanzu ma kansa ciwo yake ga bacci duk kansa ya cushe bai ma san ta ina zai fara ba.Haka ya bi bayanta har bandaki, Allah ya taimakeshi bata ma nemi fo ba ya taimaka mata ta hau toilet tayi kashinta. Yana zaune a gefen gadonsu yajiyota daga bandakin tana cewa ‘Abba na gama.’Gaban shi ya fadi da ya tuna wai shi take sa rai yayi mata tsarki; ya juya ya kalli Afaf wadda take baccinta hankali kwance. Ya san idan ya tasheta zata yi mata tsarkin to amma fa itama bata kwanta da wuri ba. Ya jijjiga kai ya mike bayan da ta sake maimaita masa ta gama a karo na uku. Haka ya tashi ya shiga bandakin ya wanke mata kashin ya wanko hannunsa ya fito ya canza mata kaya ya mayar da ita ya kwantar da ita a kusa da Habib saboda katifar kan gadon ta jike; zuwa lokacin masallatai duk sun riga sun tayar da sallah.Yana fitowa daga dakin yayi alwala ya tada sallah a dakinsa, yana zaune a kan dadduma yana azkar Nasreen ta turo kofa ta shigo dakin, ta karaso ta fada jikinsa tana cewa ‘Abba na tashi, baka dawo mana da Anti Khadeeja ba?’‘Eh, sai an jima.’ Ya fada yana tureta.‘Ki je kice Ant….’ Sai kuma ya tuna Antin bata nan don haka ya gyara zance yana kokarin mikewa ‘Muje na wanke miki jiki ki canza kaya sai kiyi sallah.”‘Abba ni yunwa nake ji.’Ya bata rai yace ‘Sai an canza kaya kuma kinyi sallah.’Haka yayi ta fama da yaran nan, gashi ita Afaf ma fushi take da shi saboda bai tasheta sahur ba tunda Anti tana tashinta tana yin azuminta. Sai wajen karfe takwas na safe sannan ya tashi ya koma ya roko Baban Ummi ta shigo ta karbi yaran don yana son ya tafi asibiti wajen Khadeeja.Yana shiga dakinsa ya zauna a gefen gado ya dannan mata kira.————

Back to top button