Hausa novels

Halysaah Page 117 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 117Sai kusan karfe hudu Khaleesat ta iya mikewa ta bar parlor tana tafiya da kyar ta wuce sama zuwa dakinta tana rike da wayarta a hannu, ta zauna gefen gado ta sake dialing number Ajay tana kallon screen din wayar babu ko kiftawa, yanxu ma dai har ya gama ringing ba ayi picking ba, ajiye wayar tayi ta kwanta gefen gadon tana jin kamar tayi kuka, bata san sanda kukan ya taho mata ba, ita kanta bata san dalilin kukan ba, tayi me isarta ta gaji sannan ta tashi tayi karfin halin shiga bandaki ta dauro alwala ta fito zata yi sallan la’asar, sai karfe bakwai da rabi na dare Khaleesat ta iya sauka downstairs daga kwancen da take zata je kitchen ta dafa taliya, rabonta da abinci har ta mance sai dai ta sha shayi da cookies, ko kuma ta sha lemo da snacks, bata iya ta ci taliyar da ta dafa ba kawai ta rufe don baya mata dadi ma a baki, ta shiga bandaki ta wanke bakinta tayi wanka sannan ta dauro alwala ta fito, ta kwanta kenan wajen karfe takwas da minti sha biyar tana replying message din Ummanta da tayi mata tun da safe sai ga kiran Safiyyah ya shigo wayarta, picking call din tayi ta kai kunne, Safiyyah tace “Ya ciwon kan yayi sauki?” A hankali Khaleesat tace “Alhamdulillah…” Duk da har sannan tana jin ciwon kan ga sanyin da take ta ji tun da ta fito wanka, Safiyyah tace “Ajay din ya kira ki ne?” Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah tace “Hello” a hankali Khaleesat tace “Bai kira ba” Safiyyah tace “Sai yanxu na sake tabbatar da mafarki na” Khaleesat tace “Na me?” Safiyyah tace “Na ce maki da nayi bashi da lafiya mana, kinsan ba sallah nake ba, ai ko tun karfe shidda bacci ya daukeni farkawata kenan, to mafarki nayi da gaske ba shi da lafiya wannan driver din nan me kai ki school ne ke kula da shi don su Stepmom dinsa ma sun tafi da dadewa, daga shi sai Dreba ne a gidan in gaya maki, kinsan ni bana mafarkin banza ko tatsuniya, don haka wallahi idan har abu ya samesa hatta Mai martaba bazai taɓa yafe maki ba don kece ya kamata idan kika ga jikinsa yaki dadi ki kira gida ki sanar masu, yanda aka basa amanarki ku ka taho kasar nan haka Mai martaba ya damka maki amanar magajinsa ko da bai bude baki ya furta ba, amma yau sati biyu da kwanaki baki san halin da bawan Allah yake ciki ba gashi ya dena hawa WhatsApp kwata kwata sannan baya iya daga kira, amma kina apartment din ki hankalin ki kwance tun da ya cika maki gidan da Foodstuffs sannan ya tura maki isassun daloli a account din ki, wallahi ki ji tsoron Allah Khaleesat” Khaleesat da ke ta sauraronta ta ɓata fuska tace “To wai ni ya zan yi ne bayan nace ki rakani gidan kin ki, ko daxu fa sai da na sake kiransa bai daga ba, to ya zan yi?” Safiyyah tace “Aikin banza kenan ai, baki san inda gidansu yake bane da za ki yi ta doka masa kira ki damesa, kila ma bai san inda wayar yake ba yana fama da kansa” Khaleesat ta mike zaune ta jingina da gado looking so disgruntled, Safiyyah tace “Wallahi ki ajiye batun wasa mafarkin da nayi kenan da magariban nan, don haka ki dau wayarki yanxu kiyi order din Lyft ki tafi gidan ki dubo halin da yake ciki, kina ta wani tambayar ya za ki yi sai kace baki san hanyar gidan ba” Khaleesat ta wani bude ido tace “Da daddaren nan?” Safiyyah tace “Kakan dare, karfe takwas da rabi ne dare? As far as zaki samu Uber ina ruwanki da lokaci?” Khaleesat tace “Ni bazan iya zuwa da daddaren nan ba sai dai gobe da safe idan Allah ya kai mu” A ɗan fusace Safiyyah tace “Ke kika sani, dama ba a taɓa baki shawara ki dauka, kuma ni dai babu shegen da zai ce kawarki bata gaya maki gaskiya, i know i am trying my best, rashin lafiya ai ya take komai ko da kuwa mutum enemy dinka ne, amma ke duk yanda za a sa ki a hanya sai kin nuna taurin kai kin maida mutum ɗan banza, ke na gaji da halin ki wallahi, haba na kiraki ina kona ɗan katina amma sai jan magana kike yayi tsayi, idan abu ya samesa nasan hankalin ki zai fi na kowa kwanciya tunda dama mijin wata kika dauka kika makala a ranki” Daga haka Safiyyah ta katse wayar, Khaleesat ta ajiye wayarta a hankali ta koma tayi kwanciyarta, she made up her mind to go to the house tomorrow morning, ta yaya za ta ce mata taje da daddaren nan, after some minutes ta jawo wayar a hankali ta shiga WhatsApp, dubawa tayi ko Umma ta mata reply amma taga bata hau ba, instead sai message din Aunty Farida ta gani tana tambayarta Junaid, ajiye wayar tayi, tayi lamo kan pillow kamar me tunanin, bayan kusan minti goma kawai ta sauka daga kan gadon ta bude press din dakin ta dau hijab dinta har kasa ta dora kan red color Chemise dake jikinta, ta dau wayarta ta fita daga dakin ta sauka downstairs, zaunawa tayi parlor tana danne dannen wayarta, after almost 15 mins ta mike ta kashe wutan parlon ta kunna Flash din wayarta ta nufi kofa ta bude da makulli ta fita daga parlon sannan ta kulle kofar da key din, tana rike da makullin a hannu ta nufi Lyft dake jiranta, ta bude bayan motar ta shiga, wajen karfe tara da minti ashirin suka iso gidan, gabanta sai faduwa yake bayan ta sauka Lyft din ta shiga cikin gidan tana tafiya a hankali har ta isa entrance din parlon, bude babban kofar tayi ta shiga ciki sannan ta tura a hankali ta rufe tana kalle kallen cikin parlon, Laptop dinsa dake parlor a bude take kallo, kamar ance ta juya tayi ido hudu da Legend da yayi saurin shigowa parlorn alamar yaji motsin an shigo, tun bai fara haushi ba ta zaro ido tana kokarin bude kofar da sauri zata fita amma tsabar rudewa yasa ta kasa, da gudu karen ya nufota yana haushi, ta fasa ihu tayi wurgi da takalman ƙafafuwanta har da makullin hannunta da waya ta tattare hijab dinta tun bai karaso kusa da ita ba ta nufi up stairs da gudu yana ganin haka ya bi ta, bata san sanda ta isa part din Ajay ba kawai ganinta tayi a cikin parlonsa ta nufi Bedroom dinsa a guje ta bude kofar jikinta na rawa, Ya fito wanka kenan ko gama goge jiki bai yi ba ya dau rigar pajamas dinsa dake ajiye gefen gado zai saka akan short din jikinsa ya fita saboda haushin da yaji Legend ke yi kawai ta afko cikin dakin ta tafi da gudu ta kankamesa ta baya jikinta na rawa tana cewa “Na shiga uku, wallahi cizo na zai yi, don Allah ka taimake ni ka koresa” Ajay bai gama recovering daga rikon da tayi masa ba bayan ya sake pajamas din hannunsa yana kokarin regaining posture dinsa a kusa da gadon da suke tsaye sai ga Legend har cikin dakin yana haushi, ai kuwa karen na ganin yanda ta rike Ajay ta baya yayi tunanin attacking dinsa ta shigo yi, ya doka wani uban tsalle ya nufi har inda suke tsaye ya cafko dogon hijab dinta, ihu ta dinga kurmawa tana kara makale Ajay at the same time ta tube hijab din jikinta ta cillar, Ajay da duk tayi confusing dinsa yayi saurin juyo da ita suna facing juna ya rufe bakinta da hannunsa cause she is disturbing the peace of the neighborhood with her shout gashi dare ne, ai ko ta kara kankamesa as if that’s the only way she will be saved from the barking dog, loosing stamina dinsa yayi all of a sudden sai ga su tim sun fada saman gado, lokaci daya ya fara kokarin banbareta daga jikinsa yana komawa baya ta yanda she won’t cross boundary ita kuwa sai sake kankamesa take, kasa kora Legend dake ci gaba da haushi yayi don ji yake kamar an zare masa strength din yin komai, amma yana ganin shi ma karen hayowa saman gadon yake kokarin yi still wanting to attack her kawai yayi karfin halin sa kafa ya hauresa sannan ya jawo duvet dinsa dake saman gadon ya rufeta da shi yana rungume da ita jikinsa duk da yayi using arm dinsa as a barrier between them, tsit Legend yayi ya fasa hawa gadon ya fara komawa baya yana kallonsu, Ajay yayi masa alamar ya fita with his other hand, juyawa karen yayi ya fice daga dakin da gudu yana waigosu, everywhere became absolutely silent banda breathing dinsa that was rapid, ita kuwa sai ajiyar zuciya take saukewa jikinta na rawa, rufe idonsa yayi jin rate din heartbeat dinsa na increasing, after few seconds Khaleesat ta bude ido a hankali jin shiru karen bai kara haushi ba, shesshekan kuka ta fara yi, ya fara rabata da jikinsa zai tashi amma ta rikesa gam cikin kuka tace “Nooo plsss” sai kuma ta leko daga cikin duvet din tana zare ido hawaye caɓa caɓa a fuskarta, ganin karen baya dakin ta daga kai ta kalli Ajay with fears written all over her face, sae a sannan taga she was clinging onto his bare body all this while, komawa gefe tayi da sauri ta jawo duvet din ta rufe har kanta da shi ta takure waje daya, har sannan zuciyarta bai dena bugawa da sauri ba, Ajay ya kasa mikewa daga kan gadon, can ya juya ya ɗan kalleta ta gefen ido yaga she is still covering her head with the duvet, komawa karshen gadon yayi, yayi using switch din wajen ya kashe wutan dakin gaba daya, sai a sannan ya mike ya shiga bandaki, bai fito bandakin ba sai bayan minti arba’in, cikin duhun ya samu ya fita zuwa parlor ya kwanta kan carpet ba tare da ya shimfida wani abu a kai ba ya rufe idanuwansa don kansa yayi masa nauyi sosai. Karfe biyu Ajay ya mike zaune daga kwancen da yake duk da ba bacci yake ba, ya tashi walking slowly ya shiga Bedroom dinsa zai dau Jallabiyansa ko sallah ne ya samu yayi, wutan dakin mara haske ya kunna ya ɗan kalli saman gadon ya ganta same exact position din da take kwance tun daxu gashi ta takure waje daya kuma har sannan tana rufe da duvet, ya gama saka jallabiyansa ya karasa saman gadon ya bude duvet din jikinta yana kallonta, hannu ya kai forehead dinta jin yanda duvet din ya dau hucin zafi, bai san sanda ya zauna kusa da ita ba ya dagota yace “Are you alright?” Sosai ya ji jikinta yayi zafi, ta bude ido da kyar zata koma ta kwanta yaki saketa yana kallonta yace “Me yake damun ki?” Bai jira amsarta ba ya fara tattara mata tulin gashinta that was scattered all over don babu hula a kanta, ya jawo pillow ya dora kanta a kai sannan ya cire duvet din jikinta ya mayar gefe, kamar zata yi kuka tace “Sanyi nake ji” Ya mike ya dau remote ya kashe AC din dakin, ya dawo kusa da ita ya zauna yana kallonta yace “What’s wrong with you?” Ita dai bata ce komai ba don duk jikinta ke mata ciwo, tashi yayi ya tafi banɗaki ya jiko karamin towel ya fito ya dawo kusa da ita ya dora mata a forehead dinta don ko pain reliever babu a gidan, ta matsa daga kusa da shi da sauri bayan ta cire towel din daga goshinta, sai kuma ta juya masa baya a hankali tace “Bana so, ni bacci nake ji” Kallonta ya dinga yi, after some seconds ya mike ya mayar da towel din bandaki ya fito, jin saukan numfashinta alamar ta koma bacci ya kashe wutan dakin ya fita ya koma parlor ya kwanta saman kujera ya lumshe idanuwansa. Da Asuba Ajay ya sake komawa dakin, ya kunna wuta ya koma kusa da ita yana kallonta, baccinta take comfortably ga dogon gashinta duk yayi scatterring all over the pillow, ya duka ya kai hannu kusa da forehead dinta yaji temperature dinta is normal babu zafin jiki, bin ta da kallo ya dinga yi don red Chemise din jikinta is just above her knees, dai dai sanda ta bude idonta a hankali suka hada ido, ta wani ɓata fuska tayi stretching din hannunta tana miƙa kamar mage, ya dauke idonsa a kanta sai kuma kawai ya fita daga dakin, zaro ido;;tayi ta jawo duvet ta rufe jikinta da shi ganin kayan bacci ne kawai jikinta…

Back to top button