Haihuwa Da Hanji Page 27 Hausa Novel
Washegari friday har ta je school ta dawo bata daina tuna irin faɗar shi na jiya ba, ita kam ba don mammi ta tabbatar mata da sai ta je ai shi zumunci yake so da ita ba tsiya ba, wanda yake sonka da arziki kuwa ya gama maka komai da babu inda zata je ai zama lafiya ya fi zama ɗan sarki.Ko da ta dawo da ɗakin Mammin ta fara ta duba jikinta suka ɗan yi hira kan ta wuce ɗakinta aka biyo ta da abinci, sai da ta ci kan ta shiga tayi wanka da alwala ta zo tayi sallah, a gaban mirror ta zauna tana kallon kanta a yanzu ko ita ta san ta yi kyau, ta ɗan yi ƙiba skin ɗinta na wani irin yalki don man da Abeeha take shafawa ita ma shi ta saya mata kuma skin tone ɗin su ɗaya, ta sake cika tayi kumatu kaɗan sai ya mata kyau, kwalli ta zana a idanunta bata cika sakawa ba amma ta san yana mata kyau kawai dai bata son sakawa ne don yana sa idanunta hawaye sai wani ruwa ya kwanta ciki kaman mai, dama gasu da girma masha Allah, lip gloss ta shafa ta miƙe ta tafi gaban wardrobe.Abaya ta ɗauko wani blue da adon fari egyptian ne ya amshe ta sossai ta saka farar hula don farin gyale yake da shi sai ta yafa gyalen ta yi kyau sossai sai ta ji nishadi a ranta, wa zai ganta ya ce Afeefar Dutsen-wai ce, Mayya kuma annoba? Wa zai ce tagayyara aka so tayi Allah ya dube ta ya tallafi rayuwarta? Malamin islamiyyarta na makaranta na cewa Allah zai buɗe ma bayinsa kokafofin rahama da sauƙi cikin ko wani tsanani muddin ka saka tsoronshi da tawakalli cikin ranka, sannan zai buɗe maka kofofin arziki ta inda baka yi zato ko tsammani ba ko a mafarki bata zaci ganinta cikin irin wannan gida tana rayuwa ba, tayi tunanin za ta tabbata a bauta da wahala a kasakance amma da Allah ya ce ba hakan bane ga inda ya kawo ta a yanzu.Da kyar ta bar gaban madubin wurin Mammi ta nufa.”Masha Allah Daughter ta tayi kyau tabarakallah!”Murmushi tayi tana zama gaban Mammin “Mammi zolaya ta fa kike ina kyau anan? Ko fa powder ban shafa ba”Mammi za ta yi magana kenan Abeeha ta shigo kaman ta jima da Dawowa don ba da kayan da ta fita ta shigo ba.”Afeefah Dr. Sulaiman ya kira yana harabar gidan nan”Mammi tace”Abeeha gobe dai tunda saturday ne ku je ki nema mata waya mai kyau”Murmushi Afeefah tayi tana Miƙewa “Sai kun dawo a gaishe su, sannan a kula. Abeeha kar ku jima kin san Yayanku”Da Toh duk suka amsa suka fice daga parlorn.Ta jima sossai tana tuna Afeefah a ranta kan ta sauke ajiyar zuciya tana Miƙewa da kyar cikin yanayin rashin ƙarfi da cikakken lafiya ta shiga cikin ɗaki.A harabar gidan kuwa suna fitowa Rayyan na parking, gaban Afeefah ne ya faɗi zuciyarta ya shiga doka wa da ƙarfin gaske, a natse ya buɗe murfin motar ya sanyo jikinshi waje Farar jallabiya ce da daga ganinta zaka san tana da tsada sai maiƙo take yi kirar Kasar dubai don tana da wani ado mai yanayi da rubutun larabci daga gefen kirjinshi kaɗan har karshen hannun hagunshi, hirami ne baƙi mai layi layi fari ya mishi wani ɗauri a kai yadda Larabawa suke yi ya zauna mishi sossai yayi kyau, kafafunshi sanye da halfcover Milano baƙa, hannunshi na daure da wata silver agogo yayinda zoben azurfan dake yatsar shi na kusa da ƙarshe ke ta daukar idanu.Kallon duk a seconds biyar ta yi mishi don fargaba da ta kan tsinci kanta a duk arean da yake, baƙar shade na maƙale a idanunshi ba za ta san ya ko kalli iskar da ya kwaso su ba yau ko Sulaiman dake zaune cikin mota bai kalli sashen da yake ba ya shige gidan kamshinshi na buso musu, Abeeha ce ta iya yi mishi “Sannu da dawowa”Hannu kawai ya ɗaga mata wai shine amsar ya shige abunshi.Motar Sulaiman suka isa Afeefah ta shiga gaba Abeeha ta zauna baya suka fice daga gidan suna sake gaisuwa.Har suka isa shi ne yake hira da Abeeha ita kam tana zaune shiru, shi ya musu iso har cikin gidan Baaba ta taso ta rungume Afeefah dake ta murmushi a ƙasa ta zube tana gaishe da mahaifiyar shi Umma ta miƙa mata hannu ta je kuwa ta kama sai ta zaunar da ita gefenta tana ɗan rungumeta kaɗan “Ina ta jin labarin ɗiyata sai yau Allah yayi zan ganta! Barka da zuwa barka da zuwa”Murmushi Afeefar ke ta yi hakika ta ji matukar daaɗin irin tarbar da ta samu, kayan kwadayi da su drinks aka cike musu gaba da su ita dai kunyar Ummar take ji yadda take ta jansu da hira shi Sulaiman ya fice Sashenshi da a cikin gidan yake.Sun jima sossai har aka yi la’asar suka je suka gabatar suna dawowa parlorn Su Fauza suka fito shirye don wucewa islamiyya suka yi sallama akan su ma za su zo musu suka fice, basu jima da fita ba sai ga Sulaiman da matarshi sun shigo, kyakyawa ce kuma fara tasss bata da wani girman jiki a shekaru kuma da kaɗan za ta iya fin Afeefar kila su yi sa’a da Abeeha, zama tayi tana ce musu sannu.Gaisawa suka yi kadaran hadaran, tunda ya ce mata da Afeefah yake ta zuba idon ganin Afeefar da bata santa ba amma ta yi matuƙar haddace sunan saboda yawan Ambaton da Sulaiman ke yi musamman in tayi wani abu, sai ta ga Afeefar ma ba wai kyau ta fita ko ado ba haɗiye abin da take ji tayi ta yi musu sallama ta fice.Baaba ce ta kawo zancen su kawu tana tambayar Afeefah me yasa suke kiranta annoba? Shiru ta ɗan yi kan ta shiga basu labarinta daga farko har ƙarshe, Baaba da Umma sun sha kuka umma ta sake rungumeta tana cewa”Sannu Afeefah… Sannu! Allah ubangiji ya ƙara miki karfin zuciya da imani ya wanke miki duk wannan wahalhalun”Ta amsa da Ameen tana murmushi don a wannan karo bata yi kukan ba illa iyaka Adu’a da tayi ta bin iyayenta da Aunty zee.Sulaiman dai bai iya ya ce komai ba a ranshi yake ayyana Dole ta sha piya-piya don kashe kanta, dole ta samu saukar jini don damuwar, ya so da ita ce a ɗakin shi a yanzu matsayin matarshi ya bata duk wata kulawar da ta dace amma gani yake lokaci ya riga ya ƙure, Dukda haka zai zauna matsayin yayanta zai bata duk wani gudumawar da ya dace a rayuwarta daga yanzu.Karfe hudu ya maida su sun bar gidan da tsaraba niki niki daga Umma ta kuma roki Afeefar da ta dinga zuwa mata, har cikin gida ya dawo dasu suka yi mishi godiya suka nufi ciki.****Karfe 3:40 ya fito ya wuce masallaci sai wuraren 4:20 ya koma cikin gidan kai tsaye sashen Mammi ya nufa don ya duba ta, tana zaune kan sallaya sai dai kanta na kife ne a bakin gado, da ɗan hanzari ya isa gareta “Mammi! Lafiya kike kuwa?”Ta ɗago ta sakar mai murmushi ya runtse ido da ƙarfi, da gaske murmushi take sai dai a cikin murmushin wani irin ciwo yake hanga da damuwa haɗe da gajiya, a idanunta wani abu mai wuyar fassara yake karantowa, tausayi da rauni suka rufe shi wanda basu ɓuya ba sam don a kan Mammi baya iya danne damuwarshi.”Saraki..! Ina lafiya, ka zauna za mu yi magana”A gabanta ya zauna kasancewar akwai turkish center carpet mai tsananin taushi da tsada dake malale tsakar ɗakin.”Ina muka kwana da zancen mu? Saraki babu lafiyayyen namijin da zai iya dawwama ba tare da mace ba, aure na sani ba dole ba ne amma babbar sunnah ce ta ma’aikinmu sannan akwai wani hadisi da Manzon Allah yayi magana akan bayan mutuwar mutum komai nashi zai tsaya chak sai abu guda uku, sadaka mai gudana, ilimin da ya samu ya kuma bayar da shi sai ɗa nagari mai mishi Adu’a ashe baka Fatan ka ajiye ‘ya’yan da za su yi maka Adu’a bayan baka nan? Bana so in sake ji ka ce min ba zaka taɓa aure ba wanchan kuskure aka samu da akasin rashin sanin nagarta da kyaun halinka… Ba duka aka taru aka zama ɗaya ba”Kallonta kawai yake idanunshi duk sun sauya sun zama red har jijiyar kanshi na tashi, sam baya so baya son jin zancen wani aure daga bakin Mammi, a baya dai ya so yi amma bai san mummunar taɓonshi zai sa a hana shi aure ba, bai san za’a iya kallon cikin kwayar idanunshi a faɗa mishi kalmar da har abada ba zai taɓa mantawa ba, baya so a maimaita baya so samm.”Mammi…””RAYYAN…!”A razane yake kallonta jin yadda ta katse shi, ta katse shi da asalin sunanshi da bata taɓa ƙira ba… Gabaɗaya sai hankalinshi ya sake tashi a raunane ta ce “Rayyan kana so in mutu ban ga ka samu cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali ba? Kana so in tafi wurin ubangiji ina tunanin rayuwar ka zai iya taggara bayan babu ni? Kana so in tafi in barka ban cika alkawarin da na ɗauka wa rayuwarka ba?””Yaaa ilaihil alameen…”Ya faɗa a rikice sai ya miƙe tsaye don wani irin tashin hankali yake ji, taku biyu yayi gaba ya juya yayi biyu baya yana shafa kanshi zuwa fuskarshi ji yake kaman ya tsala ihu ko zai fahimtar da Mammi abin da yake ji a cikin zuciyarshi.Zama yayi ya kalleta “Mammi saboda ke don ke kaɗai zan amince da zancen aure! Amma ban san kuma ta yadda zan je in cewa mace ina sonta ba, ban ma san menene son ba, ban san ta ina zan fara ba kuma… Na bar miki, na bar miki wuka da nama duk abin da kika yanke ni mai karɓa ne”Shiru tayi tana kallon shi, ya riƙo hannunayenta “Mammi kin san yadda na ɗauki alƙawari, na miki alƙawari zan yi iya kokarina a duk abinda za ki yanke a kaina, wanene ni da ba zan miki biyayya ba a duk abin da kike so? Ki kawo ko wacece zan zauna da ita yadda kike so matuƙar hankakinki zai kwanta, matuƙar za ki daina yi min zancen tafiya ki bar ni… Mammi kika ci gaba zuciyata za ta iya tarwatsewa”Hawayenta ne suka zubo, ta gimtse hannunshi dake cikin nata tana murmushi a lokaci guda ko babu komai zai tuna da ita ta zaɓar mishi mata, zai tuna da ita ya yi mata adu’ar alkhairi a duk sadda zai ga wannan mata ya ji farin ciki, in shaa Allahu ba zata yi zaɓin nan da kanta ba za ta bar wa Allah, za ta tsaya tsayin daka ta roƙi ubangiji yayi mishi zaɓi da kanshi ta san sai ya fi dacewa duniya da lahira…Anan suka bar maganan ya miƙe ya fice, ta bishi da kallo ta tabbatar yau bacci rabi da rabi zai yi hannu ta ɗaga sama tana cewa “Allah ga bawanka nan Rayyan! Allah ka sassauta mishi Allah ka yaye mishi matsalarshi Allah ka sada shi da duk wani farin cikin wannan duniya ka bashi dacewa a ƙiyama…”Ta shafa.Daga wannan rana Mammi ta dukufa adu’ar neman zaɓin Allah, ko sau daya bata yi tunanin wata mace ba damuwarta kawai Allah ya zaɓa mishi mafi alkhairi cikin mata, ya zaɓa mishi matar da za su tabbata har a aljannah wacce zai so ta, wacce idan ta tashi barin duniyar za ta kular mata dashi ta yadda ba zai yi kukan rashin ta ba don har a yanzu jin Rayyan take kaman yaro ƙarami da kan riƙe hannunta yayi kuka yayi kuka matuƙa idan an faɗa mishi abin da ya taɓa zuciyarshi, har yanzu ganinshi take kaman wannan dakakken yaron mai tsananin juriya da ƙarfin hali wanda duk wani abin da zaka mishi baya bari a ga rauninshi sai in yana gabanta.Ta ɗauki tsawon sati biyu tana wannan roƙon Allahn a cikin uku bisa ɗayan dare lokacin da Allah ya ce mu roƙe shi zai amsa mana, lokacin da ubangiji ke sama na ɗaya yana neman bayinshi masu roƙon shi ya amsa musu babu hijabi, a yau daren Alhamis safiya juma’a bayan ta gama nafilfilunta ta kwanta kaɗan saboda dan ciwo dake damunta a ciki, dole bacci ya lallaɓa ya dauƙeta ana ƙiran farko na assalatu ta farka a ɗan firgice ta miƙe zaune, a hankali ta saki murmushi mai kyau kan tayi Adu’a ta miƙe ta nufi bayi don gabatar da Alwala.



