Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 100 Complete Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

SADDEST MOOD,

THE Greatest Lost,

Gingimarin motar nan,na sauka daga kan Motar junaid,drivern dake tuƙinta ya fusgeta da gudun gaske ko waiwaye babu,kafin mutane suyi wani yunƙuri motar junaid ta kama ci da wuta tamkar Bomb ne ya fashe a cikinta,

Wata irin razananniyar ƙara jahad ta fashe da ita,cikin fitar hayyaci ta nufi motar zata faɗa ciki,Mutane duk suka rurruƙeta,kuka takeyi kamar ranta zai fita,idanuwanta sunyi jawur dasu,jijiyoyin wuyanta duk sun firfito waje,Cizo da yakushi ta dinga kaiwa hannun mutanen dake rurruƙe da ita,muryarta adisashe take fadin”Junaid!yana cikin mota!dan allah kada ku bari na rasa shi!dan Allah ku ciro mun ɗan uwana!ina jin sautin kukanshi acikin kunne na,Dan Allah kutaimakeshi wuta tana ƙona sassan jikinshi……..”tana kai ƙarshen maganar,ta yanke jiki ta faɗi asume,Mutane sunyi ƙoƙarin kashe wutar amma sai dai kash babu ruwa a kusa,lokacin da motar ƴan kwana kwana ta ƙaraso,tuni Motar junaid ta ƙone ƙurmus,Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!

Motocin Ƴan sanda ne suka zagaye wurin,tare da ƴan kwana kwanan,sun kashe wutar dake ci a motar tashi but unfortunately,basu samu komai ba dangane da junaid,domin kuwa ya ƙone ƙurmus,sai dai toka,wa’iyazubillah,

Ƴan sandan Sun samu bayani a wurin mai siyar da ice cream ɗin nan,saboda agabanshi komai ya faru,kuma shi ne ya kira Police men ɗin,da kuma motar kwana kwanar ya basu address ɗin wurin,

A bincikensu sun gano cewa,koma waye da gangan ya aikata hakan,saboda guduwar da yayi batare da ya tsaya ba,
Ambulance suka kira,aka shigar da jahad cikin motar,kai tsaye suka wuce da ita,asibiti,
Cigaba da bincike ƴan sandan sukayi,ko’ina na wurin suka shiga dubawa,Anan suka samu ƴar purse ɗin jahad,tare da takalmanta,sae kuma ice cream corn ɗin da tayi wurgi dashi,
..wani Inspector ne ya ɗauki,purse ɗinta,ya zaro wayarta,dake ta ringing acikin jakar,Duba screen ɗin wayar yayi,Sunan Ya Omar ne ya bayyana akan screen ɗin wayar,picking Call ɗin yayi yasa ta Hands free tare da kara wayar a kunnansa,
“Jahad kuna ina ne!har yanzu baku dawo gida ba?nayi trying number ɗin Junaid,but na same ta a kashe,” runtse ido ɗan sandar yayi,jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba,
“Jahad!”Omar ne ya sake kiran sunanta,
Sai lokacin inspector ɗin yace”kana magana da Inspector Mukhtar ne!yarinyar da ka kira wayarta,yanzu haka an wuce da ita asibiti ne,sakamakon motar da suka hau tare da ɗan uwanta,ta hadu da hadari……”

Download>>> Auren Karin Kasa Book 1 Complete Document

Saboda tsabar kiɗima,marshal Omar dake tsaye gaban mirror baisan lokacin da ya saki wayarshi ba,ta faɗi ƙasa,idanuwanshi azazzare yake kallon kanshi ta cikin mirror ɗin gabanshi,tuni jikinshi ya soma kerma kaf kaf kaf,
Saboda tsabar kiɗima hanyar fita daga dakin ya nufa daga shi sai short ajikinshi,sae da ya ruƙo handle ɗin kopar sannan ya tuna cewa babu kayan mutunci a jikinshi,komawa yayi a hanzarce ya ɗauko jallabiya ya zura ajikinshi,sannan ya dauki wayarshi,
Gudu gudu sauri sauri haka ya nufo downstairs,Mojar ya kira a waya tunkan yabar falon,ya sanar dashi cewa,An samu matsala su kasance cikin shiri zasu fita,

Da gudun gaske,motoci goma sha biyar na sojoji suka fuce daga cikin gidan,tare da wata irin jiniya mai sautin gaske,

Tracking layin Jahad su kayi har suka ƙaraso inda Motar junaid take,tunkan su fito daga cikin motar jikin kowannansu,yayi mugun sanyi,

A wani irin sukwane marshal Omar ya fito daga cikin Motar,da sauri mutane suka dinga darewa suna basu hanya don su wuce,Lokacin daya ƙarasa wurin da motar junaid take a ƙarmashe,ta lanƙwashe ta dagargaje,Jikinshi a mace ya zube saman guiwowinshi,komai ya tsaya mashi cak!tsit kake ji,
Girgiza kai ya shiga yi da wata irin razananniyar murya ya shiga faɗin”innallillahi wa’inna ilaihirraji’un”!hannu yasa ya damƙi tokar dake a ƙasan wurin,Nan take ya fashe da wani irin matsanancin kuka,hawaye ne suka soma gangarowa asaman fuskarshi Major dake tsaye akansa,haka zalika sauran Soldiers ɗin dake a wurin kowannansu,idanuwansu cike taf da hawaye,tunda suke a rayuwarsu basu ta6a ganin hawayen Marshal ba sai yau,
Cikin shessheƙar kuka ya furta”ku faɗamun meya faru dasu?ina ƙanina yake?Ina jahad”?
Daƙyar ɗan sandar nan ya iya buɗe baki yace”Yalla6ai,A bayanan da muka samu a wurin mai siyar da ice cream ɗin da yarinyar taje,Sun tsayar da motarsu a bakin titin ne,ita yarinyar itace ta fito daga cikin Motarsu,tabar shi Yaron acikin Motar,ta tsallaka titi,kafin ta dawo ne,babbar mota tabi takan Motar,nan take kuma ta kama da wuta,koda muka iso bamu samu komai daga sassan jikinshi ba,
Hannu Marshal Yasa ya tallabe kanshi,saboda wani irin jiri dake ɗibarshi,sai faman ambaton innalillahi wa’inna ilaihirraji’un yakeyi,Yanke jiki yayi ya faɗi ƙasa a sume,
“yalla6ai!”major ne ya ambaci sunanshi da ƙarfi,tare da zuƙunnawa agabanshi,
Suna cikin wannan alhinin saiga Motar journalists ta ƙaraso wurin,aikuwa tun kafin ma su sauko daga cikin motar,sojojin nan suka koresu daga wurin,a hanzarce suka ja motarsu suka koma,

Sau uku suna yayyafa mashi ruwa,yana sake sumewa,hakan yasa suka cuccu6eshi izuwa cikin Motarsu,don su wuce dashi asibiti,

Jami’an ƴan sandar nan,sunyi ƙoƙari wurin ganin sun gano yadda abun ya faru,har street Cctv aka bincika,amma kash Camera ɗin ta jima da samun matsala,
*Allah yajiƙan junaid,ya gafarta mashi,mutun mai kyakkywar zuciya irinta junaid,munayi mashi fatan dacewa don yayi mutuwar shahada,bawan Allah naji mutuwarshi sosai,don har hawaye saida na zubar,akan laifin da bashi ya aikata ba,Anyi silar mutuwarshi,saboda Soyayyar da akeyi mashi itace taja mashi,babu komai,wanda sukayi silar mutuwar tashi kowa zai ɗanɗani kuɗarshi ne,masu cewa junaid yayi azkhar da addu’a before ya fita,kada ku manta,idan lokacin mutun yayi koda sallah yake cikin yi ko agaban ka’aba ne hakan bazai hanashi mutuwa ba,yakamata mu tuna da wannan,bawa bai isa ya gujewa ƙaddararsa ba,ko da yayi addu’a in dae anan ajalinsa yake dole ya mutu ba makawa😭*

*Boss Bature*

Rishraf,

Gabanshi ne yaji yayi wani irin bugu,ba arziƙi ya zame hannunshi daga saman ƙirjin sehrish,ja da baya yayi,yayin da hannunshi ke dafe da saitin zuciyarshi,hankalin shi yayi mugun tashi,lokaci guda ya rasa natsuwarshi,da sauri ya fuce daga ɗakin,hakan yaba Sehrish damar motsawa,ta ɗauki undi ɗinta dake ajiye a ƙasa,ta sanya ajikinta,wata irin kasalace ta baibayeta ga wani irin faɗuwar gaba da take ji,daƙyar ta lalla6a ta haye saman gadon ta kwanta,hannunta rungume da pillow,

Saukowa downstairs,yayi hannunshi na kerma ya zaro wayarshi,yama rasa wa zai kira gida,yaji kowa yana lafiya,ko wani abu ya faru ne?don yanaji aranshi cewa,Something is wrong,that’s why yake jin bugun zuciyarshi na ƙaruwa,
Layin Marshal Ya kira,a lokacin wayar na a hannun Major,koda yaga kiran Sgr,ƙin ɗaga wayar yayi saboda baisan taya zai fara sanar dashi ba,game da mutuwar junaid,

Almost 3 times,wayar na ringing ba’ayi picking ba,layin junaid ya lalubo ya danna mashi kira,lokacin da aka sanar dashi cewa layin daya kira a kashe yake,nan fa hankalinshi ya ƙara tashi sosai,saboda tunda yake a rayuwarshi bai ta6a samun layin junaid a kashe ba sai yau,a ruɗe ya danna ma Abbansu kira,tana fara ringing,Abbansu ya ɗaga tun kafin ma yayi mashi sallama,muryar Abbansu ta katse shi da cewa”Rafayet!wai meke faruwa ne?ina ta kiran Layin junaid akashe!hankalina yaƙi kwanciya,”

Download>>> Mijin Malama Complete Document

Muryar Sgr,a kasalance yace”Daddy,i don’t know why nima na kira layinshi,switched off,Na kira layin Omar ma,tayi ringing ba’ayi picking ba”
“Dan Allah rafayet,ka bincikamun meke faruwa a gidan nan,Hankalina bazai kwanta ba,in har banji muryar baby junaid ɗina ba,wlh har bacci ya fara ɗaukata amma na farka,saboda nasama raina zai kirani ne kamar yadda ya saba kirana,duk in dare yayi kafin ya kwanta,”acewar Abbansu,
Jikin Sgr ba ƙaramin sanyi yayi ba,daƙyar ya iya cewa”In sha Allah daddy,zan yi ƙoƙari na haɗa ka dashi,”
Daga haka sukayi sallama,zarya ya shiga yi acikin falon gidan,tunanin zuwa Abuja yake yi,don ji yake in har bai sanya junaid a idonshi ba,to hankalinshi bazai kwanta ba,

Ranshi ne ya bashi cewar,ya jaraba kiran layin Haroon may be,yana a gidan,can kuma ya soma tunani Anya ma yana da numbar haroon?tabbas baida ita,layin Major ya kira kaitsaye don ya samu ya haɗa shi da Omar,tunda na hannun daman shi ne,
Lokacin da kiran ya shiga wayar major,suna tsaitsaye cirko cirko a cikin asibitin Sgr,Yana ganin sunan Sgr ya bayyana akan screen ɗin wayarshi,jiki na rawa ya kashe wayar gaba ɗaya,
Abun ba ƙaramin ɗaurewa Sgr kai yai ba,kowa ya kira ba’a picking,shi Major ma kiran ya shiga,daga baya kuma aka kashe wayar,hakan ya ƙarasa shi zargin cewa wani mummunan abunne ya faru,
Komawa Upstairs yayi da sauri bedroom ɗin da Sehrish take ciki,tura kopar yayi ya shiga,a kwance ya sameta rungume da pillow,

“I know u are awake,inaso ki kiramin layin wani daga cikin sisters ɗinki,i wanna talk with them ”
Yunƙurawa sehrish tayi tare da kai hannu ta ɗauki wayarta da ta aje gefenta bayan ta kashe wakar,layin jahad ta lalubo ta danna mata kira,A lokacin wayar na a hannun Major ya kar6eta daga hannun police men ɗin,koda yaga kiran My Own sis ya shigo,ta layin jahad,kin daga kiran yayi har ya yanke,hakan yasa sehrish sake kira,sai ya kashe wayar gaba ɗaya,
ɗagowa tayi tare da kallon Sgr,tun kafin tayi magana,ya riga ta cewa”Switch off ko”?ɗaga mashi kai tayi alamar eh,tare da cewa”Bari na kira layin Hosana,”
Numbar hosana ta lalubo,tare da danna mata kira,tana fara ringing hosana ta ɗaga kiran,muryarta da alamun bacci atare da ita,
“Wai wanene ke kira na”?
Sehrish tace”ke nice,Ina jahad ne na kira layinta a kashe”?
Hosana tace”tun ɗazu da suka fita da junaid shan ice cream basu dawo ba,inata jiransu har bacci ya ɗauke ni,”kafin Sehrish ta ƙara cewa wani abu,da sauri Sgr ya sanya hannu ya kar6e wayar,
tare da karata a kunnansa”Ina Omar yake”?rass taji gabanta ya faɗi,daga kwance take,amma jin maganar babban yayansu yasa ta miƙe zaune,anatse tace”Wlh bansan inda yake ba,ko yana gida ko yana waje oho,ni dai ina ɗakinmu,”
“Go to his bedroom right now,and see if he’s around,”
Mikewa hosana tayi tare da saukowa daga saman gadon,gudu gudu sauri sauri ta wuce upstairs bedroom ɗin Omar,a buɗe ta samu ƙopar,turawa tayi ta shiga daga ciki,ko’ina ta duba,hada leƙa toilet ɗinsa,ganin babu kowa yasa ta sanya wayar a kunnanta,
“Ya Rafayet,na duba ko’ina,amma banga ya Omar ba,”
“Its okey,ki koma ɗaki,”yana faɗin hakan ya katse kiran,
ɗagowa yayi da lumsassun idanuwanshi masu ɗauke da bacci ya kalli Sehrish itama kallon nashi takeyi,duk jikinsu yayi sanyi mika mata wayar yayi”take ur phone,”hannu tasa ta kar6a,
Da sauri ya juya,jikinshi duk babu ƙwari a lokacin idonshi ya sauka kan belt din shi dake akasa,hannu yakai ya dauka ya fara kokarin maida shi jikinsa tare da fucewa ya nufi downstairs,a dai dai lokacin Abusufyan na fitowa daga ɗakin da suka kwantar da Abu,jikinshi sanye da jallabiya,

Download>>> Boss Lady Romantic And Comedian Novel Complete

Yana jin takun takalmi,yakai idanuwanshi wurin,yana ganin Sgr ya tunkareshi da sauri,
“Rafayet!wai kunyi waya da Junaid ne?i ave been trying his phone number,Amma akashe!nayi traying har nagaji,since evening ya sanar dani cewa,zasu fita tare da jahad shan ice cream,inaso naji ko sun koma gida,itama kuma phone dinta akashe”
Ƙarasa saukkowa daga saman benen Sgr yayi tare da kallon Uncle ɗin nasu yace”Uncle nima bansan meke faruwa ba,kowa na kira layinshi switched off,babu mai picking call ɗina,That’s why na yanke shawarar zuwa Abuja yanzun nan zan bi jirgi naje can,” ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin wucewa ta gefen Abusufyan,da sauri ya ruƙo damtsen hannunshi tare da cewa”A’a Rafayet!ka haƙura sai gobe mana ka wuce can ɗin,”acewar Abusufyan
Girgiza kai ya shiga yi tare da cewa”Bazan iya jurewa ba,inaso nasan meke faruwa ne acan ɗin,na damu akan rashin jin muryar Junaid,daddy ma ya kira ni yanzu,yana cikin damuwa,ko don saboda shi inaso naje can na haɗashi da junaid,if not ko bacci bazai iya yi ba,tunda ya sama ranshi son jin muryar junaid,”
“Zanyi magana da yaya hossein ɗin,ka ajiye tafiyar nan dare yayi,sai zuwa gobe da asuba,”
Ba don ya so ba,a dolenshi ya haƙura,komawa sukayi saman sofa suka zauna jigum jigum,Suna jiran tsammani,kowa da abunda yake saƙawa acikin ranshi,

*HAROON*

Around 12 na dare,Yana zaune gefen gadonshi,message ya shigo wayarshi,da sauri yakai hannunshi ya zarota daga cikin trouser pocket ɗinsa,buɗe message ɗin yayi ya soma karanta shi kamar haka,
_Oga Aiki ya kammalu fa!ka duba whatsapp ɗinka,mun tura maka video zazzafan gaske,nasan yau zakayi kwanan farin ciki_
Shu’umin murmushin nan nashi ya saki,jiki na rawa ya shiga whatsapp ɗinshi anan ya samu Video ɗin da suka tura mashi,bayan ya kunna Wi-fi ɗin wayarsa,tunkan video ɗin ya ƙarasa yin loading jikinshi keta tsuma harya ƙagara yaga Videon menene,
Ƙura ido yayi akan screen ɗin wayar,lokacin da video ɗin ya buɗe,motar Junaid ya gani tana ta ci da wuta,ta lomatse ta rakwakkwa6e,Wani irin ihu ya fasa cike da tsantsar farin ciki ya miƙe tsaye yana faɗin”Yess!Yess!!finally Burina ya cika,ko ayanzu na mutu nasan cewa,na gama dasu,na kashe farin cikin da suke taƙama dashi!”
Ya ƙarasa maganar tare da fashewa da wata irin mahaukaciyar dariya,lokaci guda kuma ya dakata da yin dariyar,jikinshi ya soma kerma sakamakon Muryar junaid da tayi mashi gizau acikin kunnanshi
_Ya haroon!burinka ya cika ko?ka rabani da rayuwata,laifin me nayi maka?menayi maka dana cancanci wannan ɗanyen hukuncin a wurinka!yanzu shikenan bazan sake ganin ƴan uwana ba?ka rabani da mahaifina kuma kana farin ciki?haƙƙina bazai ta6a barinka ba_
A tsorace Haroon ya shiga waige waige a cikin ɗakin nashi,ba ƙaramin razana yayi ba,ganin baiga kowa ba,yasa shi sauke ajiyar zuciya,
ɗago da wayarshi yayi tare da Calling layin waɗanda yasa su kashe mashi junaid,tana fara ringing aka ɗaga kiran,
Muryarshi asanyaye yace”dagaske ne video ɗin da kuka turomin cewa kun kashe junaid”?

Karanta>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel – Aihausanovels

On the other hand,mutumin yace”ƙwarai kuwa!Yaron nan babu shi yanzu a doron duniyar nan!domin kuwa da truck muka take motarshi,bayan mun tabbatar yana acikin Motar,Amma ita yarinyar bata acikin motar kamar yadda ka bamu umarni,ta tsallaka titi zata siya masu ice cream……”
Tunkan ya ƙarasa maganar,haroon ya zube saman guiwowinsa,wata irin zufa ce ta shiga tsatstsafo mashi ajikinshi,tuni ta wanke shi sharkaf,
“Ya Haroon!Kamar baka farin ciki?naji kayi shiru”?
Kasa buɗe baki haroon yayi,la66ansa sae kerma suke yi,
“Hello!hello!Oga haroon!kana a kan layi kuwa”?jin shiru bai tanka masu ba yasa suka katse kiran,
Jikin taƙaura yayi la’asar,gaba ɗaya haroon ya shiga ruɗani,Shin farin ciki yake yi da mutuwar junaid ko kuwa baƙin ciki?Tun yanzu ya fara tsorata da gizan da muryar junaid tayi mashi,
_Laifin me junaid yayi mun?na kasa yarda cewa ni da kaina na bada umarnin a akashe shi_
Runtse idanuwanshi yayi sosai,yana tariyo fuskar junaid,mai ɗauke da kyakkyawan murmushi nan nashi,
Guiwowinsa duk sun sage,ya kasa miƙewa tsaye,yayi fiye da awanni zuƙunne batare daya motsa ba……..

*AUNTY BABBA*

Tun bayan da Abra ta gudu daga hotel ɗinnan,Tana fitowa daga wanka,jikinta ɗaure da towel,sam bata kawoma ranta komai ba,duk da tayi mamakin ganin babu kowa,Jinjina kai ta shiga yi tana faɗin”Ko gidan ubanwa taje?bayan na sanar da ita cewa Yanzu zamu tafi,zata dawo ta same ni,”ta ambaci hakan tare da samun wuri gefen gadon ta zauna,tun tana sa ran dawowar abra har ta fara fidda rai,tunawa da abunda ya faru da hayaam a hotel yasa hankalinta ya tashi,tsoranta kar ace itama abra,an samu wani ya ƙurmushe ta ne,hakan yasa tayi firgit ta miƙe tsaye,tare da kai hannu saman bedside drawer ta ɗauki wayarta dake ajiye a samanta,
Yanke shawarar kiran Abra tayi,tun kafin ta shiga Contacts ɗinta,saƙon abra ya shigo cikin wayar,on the top of screen ɗin wayar,
Janyo saƙon tayi ta buɗeshi,a tsanake ta soma karanta saƙon
_Aunty laila sai dai kiyi haƙuri,wlh bazan iya zuwa wurin bokan nan ba!saboda ƙaryar da kika yi mun dangane da hayaam,ashe Aunty hayaam tana kwance rai hannun Allan agadon asibiti,amma kika gudu kika barta saboda kawai tsautsayi ya same ta?ashe dama amfani kike yi damu don ki cimma burinki!baki damu da rayuwarmu ba,Naji tsoro ne saboda nasan cewa nima wata rana in irin hakan ta faru dani zaki gujeni ne,ina mai baki haƙuri Aunty laila,bansan ya rayuwarki zata ƙare ba a Enugu,domin kuwa na kwashe duk wasu kuɗi da muka zo dasu,Na tafi da handbag ɗinki gaba ɗayama,kada ki sha wahalar nemanta Aunty hayaam da aunty Amani ne suka sa nayi hakan a ƙarshe ina maki fatan sa’a_
Saboda tsabar kiɗima a hautsine ta jefar da wayar ƙasa,Dafe ƙirjinta tayi hankalinta a matuƙar tashe,ta furta”kutumar Uba!Ni Abra zata yiwa iya shege!Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!Ya Allah ka rabani da mugun ji da mugun gani!Ya Allah kasa mafarki ne ba gaske ba,Abra ta yashe ni!ta gama dani!na shiga uku na ni yau! Na gama yawo!
Tuni Ido ya raina fata,cizon yatsanta ta shiga yi,tana faman yarfa hannunta,Duk tabi ta ruɗe ta rasa inda zata tsoma ranta,
Zuƙunnawa tayi ta ɗauki wayar da tayi wurgi da ita ƙasa,layin Abra ta kira,unfortunately ta samu wayar akashe!

Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document

“Allahumma Ajirni fil musibati wa’aklifni khairan Minha,Meyasa Abra zatayi mun haka!Nashiga uku ni yau,Wannan wata irin Musiba ce!daga wannan sai wannan?”
Hawaye ne suka soma saukowa daga saman fuskarta,a susuce ta shiga faɗin”Wlh baku isa ba!baku isa ku hanani zuwa wurin bokan nan ba!Wlh sai naje,Allah ya isa tsakanina Da Amani!Munafuka duk ita ta shirya mun wannan,Ita kuma waccen kingin gardawan bamma san ya akai ta farfaɗo ba,don nasan itace ta sanarwa Amani har suka shiryamin wannan tuggun,Wlh bazan ƙyalesu ba…..”Aunty babba fa ta zare sai faman sakin sambatu takeyi,da alama ta fara zarewa,zagaye ɗakin tashiga yi tana safa da marwa,hannunta asaman kanta,
Yanke shawarar bin bayan Abra tayi,a gaggauce ta buɗe trolley ɗin kayansu,ta ɗauko doguwar riga ta zura ajikinta,Ta yafa mayafi buɗe ƙopar tayi,jiki na rawa,haka ta shiga zagaye hotel ɗin tana neman Abra,har wurin receptionists taje,ta tambayesu ita,hada yi masu kwatancenta anan suka sanar da ita cewa,sunga gifcinta a lokacin da take ƙoƙarin barin reception ɗin,Jin haka yasa Aunty babba ta zabura da gudu ta fuce daga reception ɗin ta miƙi hanyar fita daga hotel ɗin,gudu gudu sauri sauri haka ta fita waje gefen titi tana Neman Abra,
Hanya ta miƙa tana tafiya tana sambatu,tana ƙoƙarin ta tsallaka titi wata jibgegiyar Mota ƙirar Range rover tayi Awon gaba da ita,Koda mai motar nan yaga aika aikar da yayi jini har asaman glass ɗin motarshi,aikuwa a hanzarce yaja motarshi da gudun gaske ya bata wuta kamar zai tashi sama yabar Wurin!!!
Aunty babba kuwa sai kwala ihu takeyi tana shure shuren ƙafa asaman titi,
“Wayyo Allah!nashiga uku!na bani Na lalace!Ya kashe ni!Ya gama dani!”
Dandazon mutane ne suka taru a kewaye da ita,sun zuba mata ido suna ta kallonta an ransa wanda zai iya taimaka mata,kowa tsoro yake ji kada ace shine yayi silar mutuwarta,Wannan dalilinne yasa aka rasa wanda zai ta6ata,kuma babu wanda yayi tunanin kiran ƴan sanda don yayi reporting akan Incident ɗin,
Tun tana shure shuren kafarta jini na tsargowa ajikinta,har jikinta ya soma saki alamar rai zai yi Halinsa……..

DAMATURU,

Wuraren karfe 1 na dare,Abba na zaune zugudum tsakiyar gadonsu ya zabga uban tagumi,zuciyarshi sai bugawa take yi,kwakkwaran juyi Alexandra tayi karaf idanuwanta suka sauka akan shi,da ya ke akwai hasken bedside lamp dake a kunne,muryarta adisashe tace”Abban Junaid!lafiya har yanzu bakayi bacci ba,”?

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Hankalinshi atashe yace”taya zan iya runtsawa?kullum junaid ya saba kirana a waya da daddare kafin ya kwanta yayi bacci,Amma yau shiru wayarshi a kashe,wayar Omar a kashe,na rasa wanda zan samu a gidan in kira shi don ya sanar dani halin da junaid ke ciki,”
Jin wannan maganar yasa hankalin Alexandra ya tashi haiƙam,mikewa zaune tayi cike da mamaki tace”nikaina nayi mamakin rashin kirana da junaid,baiyi ba amma ban kawo komai araina ba har bacci ya dauke ni”
Abba na ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,suka ji an ƙwanƙwasa ƙopar ɗakin nasu,
Atare suka haɗa baki wurin cewa”Wanene”?
Muryar Twins ce ta amsa masu”Mommy mune,”
Kallon juna sukayi at same time,kafin Abba yace”Ku shigo ciki,”
Tura ƙopar sukayi atare suka shiga kowannansu sai faman hammar bacci yake yi idanuwansu a lumshe saboda baccin da suke ji,
Aruɗe Alexandra tace”is everything alright twins?me kuke yi har yanzu bakuyi bacci ba”?
Ayaan yace”mommy wlh ba lafiya,mun kasa runtsawa saboda yau junaid kwata kwata bai kira wayarmu ba,Ko text message ɗin da ya saba tura mana yau bamu gani ba,kuma mun bibiyi layinshi a kashe,har ya Omar mun kira muji ko lapia shima a kashe,taya hankalinmu zai kwanta,”yana kai ƙarshen maganarshi jahan ya ɗaura da cewa”Mommy,Daddy Ni da Ayaan mun yanke shawarar komawa gida gobe,dan Bazamu juri rashin junaid a kusa damu ba,”
Tashin hankali,zuba masu ido Sukayi suna kallonsu,kowanne yasha sleeping dress ajikinshi,
“Ku zauna”Abbansu ne yayi maganar tare da nuna masu doguwar sofa ɗin dake acikin bedroom ɗin,Zama su kayi kowa fuskarshi ɗauke da damuwa,
“Mommy!”gabanta ne ya faɗi jin Muryar fawan,da sauri takai idanuwanta bakin ƙopar ɗakin,shigowarshi kenan,idanuwanshi sunyi luhu luhu dasu,ƙarasa shiga ciki yayi daƙyar yake iya ɗaga ƙafarshi saboda bacci,
“Fawan!kaima baka yi bacci ba”?Abbansu ne yayi tambayar,
ɗaga mashi kai yayi alamar eh,tare da cewa”Abba,junaid fa?ko wani yayi waya dashi acikin ku?duk yau bai kira ni ba,kamar yadda ya saba,har text yana turamun kullum amma yau shiru,ko ta whatsapp bai turo man ba,da abun na kwanta yanzu na farka still banga sakon shi ba, layinshi ma a switched off,duk na damu wlh,’
Tashin hankali,abun fa ya fara basu tsoro,wasa wasa one by one su Irfan kowa ya shiga shigowa ɗakin yana tambayar junaid,dayake family house ne,duka danginsu na 6angaren Mahaifinsu,suna acikin katafaren gidan,wanda ya kasance mallakin kakansu,mijin Ammi,
Aranar dukkansu babu wanda ya runtsa,mafi yawancinsu a zaune suka kwana,don sunci alwashin dawowa gida,tun da asussuba,Abbansu yafi kowa ƙagara daya dawo yaga meke faru ne,Ya ƙwallafa rai akan son ganin junaid,don da ace yana da fiffike da ba abunda zai hanashi tashi sama atsakar daren nan yadawo gida! *Allah sarki*

Kamar yarda su Abba suka kwana a zaune,haka Sgr da Abusufyan suka kwana a zaune,cikin falon gidan,babu wanda ya runtsa acikinsu,haƙika ba ƙaramin so sukeyi wa junaid ba,Rashin kiran da baiyi masu ba a waya yasa duk sun tashi hankalinsu,inaga sunji mutuwarshi?mezai faru?kowa fa yasha jinin jikinshi,

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel 

Tunda asussuba Jirginsu Sgr da Armstrong ya ɗaga izuwa Abuja,

*Sehrish*

Bayan sallar asuba,Sehrish ta koma ɗakin Oummansu,har lokacin bata farka ba,Wuri ta samu saman gadon daga gefenta,ta kwanta abubuwa da yawa suna zuwa mata aranta,ita kanta tasan cewa tayi kewar wasu daga cikin mutanen gidan,musamman Su Hosana da Junaid,da Aunty azmee,kowa missing ɗinshi take yi,gashi batasan ranar da zasu koma gida ba,tana cikin wannan zancen zucin nata,tajiyo muryar Oummansu tana sambatu,tana faɗin”kada a ta6a mun ƴa’ƴana,dan Allah abarmun su,su kaɗai nake dasu,sune dangina,sune komai nawa,’
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e Sehrish,miƙewa tayi zaune tana kallonta,a hankali ta furta”Oumma” slowly abu ta buɗe idanuwanta,tare da wurgasu kan fuskar sehrish,wani irin kallo take bin ta dashi,kallon tuhuma,
Murmushi sehrish ta sakar mata tare da ƙoƙarin miƙa hannu zata shafa gefen fuskarta,aikuwa a tsorace Abu ta miƙe zumbur tana ja da baya,girgiza mata kai ta shiga yi tare da zare mata manyan idanuwanta,wai don kada ta ta6ata,.
Jikin sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba,
“Oumma baki gane ni ba?Ni ce fa sehrish!Rishi ɗinki’
A ruɗe ta shirga girgiza kanta tana cewa”a’a a’a Ni bansan wacece ke ba,bake bace rishi ɗina ba,Rishi ɗina ƙarama ce,”
Cikin sanyin murya Sehrish tace”Oumma kallanni dakyau ki gani,nifa ce rishi ɗinki,nasan bazaki manta da kamannin fuskata ba,na ƙara girma ne kaɗan,”
Harara abu ta watsa mata,dama tun fil azal abu mace ce mai taurin kan tsiya ga kafiya,tun tana da hankalinta balle kuma yanzu da babu hankalin atare da ita,
Zubama juna ido sukayi kowa na kallon kowa,taƙi yarda sehrish ta kusantota,da zarar sehrish ta matsa,itama da sauri zata matsa,ganin ta kusa ƙurewa gadon gudun kada ta faɗa ƙasa,yasa Sehrish ta ƙyaleta,
Cikin lallashi tace”Oumma!kin tuna da Hosana?da jahad?
Girgiza mata kai tayi alamar a’a,”Ni bansan su ba,Ni ki ƙyaleni bansan kowa ba,ƴa’ƴana na sani Nemansu nake yi,yace zai kashe munsu,dan Allah akawo mun ƴa’ƴana kusa dani,”
Murmushi sehrish ta saki tana kallonta,tsantsar son mahaifiyarsu take ji kamar kamar me,gashi taƙi bari ko rungumarta tayi,
“Kiyi haƙuri kinji,Babu wanda zai ta6a maki ƴa’ƴanki,idan har kika bani dama,Ni dakaina zan kawo maki ƴa’ƴanki,”
Shiru tayi bata tanka mata ba,Sai ma wani kallo da take bin ta dashi,kallon ban yarda dake ba,wayau zakiyi mun,
Jin sallamarsu Abusufyan yasa tayi saurin amsa masu tare da saukowa daga saman gadon,ta fito daga ƙopar dakin,Su uku ne suka shigo,Baban sadeeq tare da Abusufyan sai Sadeeq ɗansu da suka ɗauko jiya,Anan ya kwana gidan,
Fuskarta ɗauke da fara’a ta gaisar dasu”ina kwananku?Kun tashi lafiya,”
Atare suka amsa mata”lafiyalou,Alhamdulillah,”
“Sadeeq ka ganeta kuwa,”?Baban sadeeq ne yayi maganar yana kallon sadeeq ɗin dake tsaye agefenshi,murmushi ya ɗan saki tare da girgiza kai alamar a’a,yace”fuskarta kamar na santa,amma bazan iya tunawa ba,’

Download>>> Doctor Eesah Complete Novel

Abusufyan yace”Ae zaiyi wuya ya ganeta saboda canzawar da tayi,ba kamar daba da yasanta,yanzu ta ɗan ƙara girma,”
Baban sadeeq yace”Allah sarki,Sadeeq wannan fa ba kowa bace face daya daga cikin waɗannan ƴan ukun na Wurin abu,waɗanda suke yawan zuwa gidanmu su yini wani sa’in ma harsu kwana,”
Cike da mamaki Sadeeq yace”Wai su rishi,hosana,da jahad”?sae lokacin ya ganeta,baki asake yake kallonta,don bazai manta lokacin da suke yawon zarya acikin gidansu ba,musamman in yunwa ta addabesu,wani sa’in ma shi Mamansu ke aikawa gidansu ya kai masu abinci idan tajiyo kukansu,da zarar ya kai masu abincin,Jiki na rawa suke kar6a su zauna suna ci,’
“Rayuwa kenan,banta6a tsammnin rana irin ta yau ba,gani ga rishi,”tuni idonshi sun ɗan cicciko da ƙwalla,haka itama sehrish ɗin
Baban sadeeq yace”ka tuna lokacin da kake kuka saboda mamanka taba su rishi abincinka’?
Fashewa sukayi da dariya gaba ɗayansu,
Kunya duk ta rufeshi daƙyar ya iya buɗe baki yace”Dan Allah Abba,adaina tuna abunda ya wuce,’
“Shikenan tunda haka kake so andaina,”
Wuce wa Abusufyan yayi cikin ɗakin abu,Baban sadeeq ma ya wuce ɗakin da suka sauka,ya rage daga ita sai Sadeeq atsaye,suna fira,
“Yanzu shekarunki nawa’?ya tambaya yana kallonta,
Wurga ido ta ɗan yi kamar mai tunanin wani abu,kafin tace”sha takwas kaifa”?
Hannu yasa tare da ɗan sosa keyarsa yace”Sha tara,” harara ta watsa mashi tana ƴar dariya tace”wlh ƙarya kake yi mun nafa son shekarunka,Allah kamar ma mun girmeka,don ka ganka dogo shiyasa zaka 6oye mun shekarunka ko’?
Murmushi ya ɗan saki tare da nuna mata sofa ɗin dake a falon yace”Mu zauna mana,nagaji da tsayuwa,baccin ma bai isheni ba Allah,naji daɗin sanyin nan ba kamar gidanmu ba,fankar ɗakina ma,6eraye sun lalata mun ita,”ya ƙarasa maganar tare da samun wuri ya zauna,itama ta zauna suna fuskantar juna,
Sae faman bin falon yakeyi da kallo,ƙasa ƙasa yayi da muryarshi ya ambaci sunanta”rishi,”
“Na’am”ta amsa mashi
“Wai wannan mai mutuncin,mai kama dake ɗinnan Yayanku ne”?
“Me hali dai bazai ta6a canzawa ba,ashe har yanzu kana nan da wannan tsegumin naka kamar mace”?cike da zolaya tayi maganar,harararta yayi tare da cewa”Ae tsegumin nawa ku ma yayi maku amfani!ko kinmanta ni ne ɗan leƙan asirin Mamanmu?ita ke cewa nazo gidanku najiyo mata idan kun ci abinci,idan nayi la6e naji kuna kukan yunwa sai in watsa da gudu inje in sanar mata…. ”
Dariya sehrish tayi har haƙoranta suka bayyana,baki asake Sadeeq yace”Wai!madarar kyau!rishi kinga yadda kikayi kyau kuwa da kika washe bakinki Fararen haƙoranki suka fito kamar na Ketrina kef?ba kamar lokacin da ba,Haƙorannan Jawur dasu kona Maclean ma babu,”
ɗaure fuska sehrish tayi kamar ta rufe shi da bugu tace”kai Sadeeq ɗazu fa naji kana cema baban ku,adaina tuna baya,shine nikuma zaka dinga tunamun abunda ya wuce don wulakanci,”
Fashewa yayi da dariya,bin shi tayi da kallo bakowa ya faɗo mata arai ba,fa ce junaid ɗinsu,lokaci guda taji tana kewarshi,
“Sadeeq,mutumin da kake magana akanshi,ba yayana bane,Shi ne mahaifin mu!”tunkan ta taƙarasa maganar ya katseta da cewa”kutmelesi!Amma dai ƙarya kikeyi mun ko?idan shine mahaifinku,Wanccan mai dogon gemun fa?wanene Shi?cike da tuhuma yayi mata tambayar,
Shiru tayi bata bashi amsa ba,tsareta yayi har sai da ta faɗa mashi komai daya faru arayuwarsu,wani Shu’umin murmushi taga yana saki,hakan yasa tace”Wai lafiya”?
“Rishi aike yanzu hajiya ce,Ashe dama ku ƴa’ƴan masu kuɗi ne?Ae wlh bazata sa6u ba,Tunda kunyi arziƙi yanzu sai a ramama kura aniyarta koba haka ba”?yayi maganar yana ɗage mata gira,irin na ƴan duniyar nan,

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Dariya sosai tayi,bayan ta tsagaita da yin dariyar tace”Faɗamun dame dame za’a rama maka”?
Lissafo mata ya shiga yi”Ragowar abinci na da kuka saba cinye mun,tare da ƴan kayan sawa na da maman mu ke kwashewa tana kaima Oummanku don asanya maku kin tuna’?
Shiru sehrish tayi bata bashi amsa ba,bakomai take tunawa ba,fa ce rayuwarsu ta baya,ya tuna mata da lokacin da Maman Sadeeq ke aiko da kayanshi don acanza masu kaya,saboda nasu duk sun yayyage,tun sunayi ma Oummansu kukan bazasu sanya kayan maza ba har suka haƙura ta dinga sanya masu,haka tsoffin takalman sadeeq haka aka dinga kawo masu don su rinka sama kafafunsu,
Ganin hawaye akan fuskarta yasa Sadeeq saurin mikewa ya dawo gefenta ya zauna cikin lallashi yace”rishi nifa wasa nake yi maki,wlh ban faɗi hakan ba,da niyyar in 6ata maki rai ba,kawai inaso in sanyaki nishadi ne,saboda yanzu ta ko’ina Allah ya hore maku,’
Cikin shessheƙar kuka tace”ni baka 6ata mun rai ba sadeeq,na tuna da irin rayuwar da muka yi ne abaya,kaima kasan dole inyi kuka in na tuna,”
“Tunda baki so,mu manta da komai,bazan ƙara tuna maki ba,Yanzu dai faɗamun nawa ne acikin asusun bankin ki?nawa kika tara”?
Fashewa tayi da dariya jin abunda yace,
Da hannu ta nuna mashi yatsunta guda biyar,
“ɗari biyar”?yayi guessing yana kallonta,girgiza mashi kai tayi alamar a’a,
“Dubu biyar”?ya sake canka,cike da sa ran ya faɗi dai dai,
Girgiza mashi kai ta kuma yi,
“To dubu ɗari biyar,”nan ma ta girgiza mashi kai Alamar a’a,tur6une fuska ya ɗanyi saboda ya fara tunanin kamar ƙarya takeson ta shirga mashi,
A ƙule yace”Miliyan biyar”murmushi ta sakar mashi tare da jinjina mashi kai alamar ya faɗi dai dai,
wani kallon rainin wayau ya jefa mata tare da cewa”Alkazzubu haramun,”
“Wlh dagaske nake maka,Ina da kuɗi sosai sunma fi miliyan biyar amma basa a hannuna,duk suna a wurin Daddyn….”kasa ƙarasa maganar tayi,ganin Sadeeq ya sauko daga saman kujerar ya dawo ƙasa saman carpet ya zauna agabanta tare da lankwashe ƙafafunshi zaman cin tuwo,
“Lafiya naga ka dawo ƙasa,”?
Hannu yasa tare da ɗan sosa ƙeyarshi yace”Ae matsayinmu ba ɗaya ba,kefa Millionaire ce,ni kuma Faƙiri mamallakin naira ɗari biyar acikin aljihu,bazaiyiwu mu zauna a saman kujera ɗaya ba,abun ma sam babu ladabi acikinsa,
Fashewa Sehrish tayi da dariya,Yau sadeeq ya sanyata nishaɗi sosai,komai yayi yana tuna mata da junaid,
“Aunty sehrish,kinji nace ina da ɗari biyar ko?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh , “Yawwa,wlh itama Wanki da guga nayi a shagon wani abokina aka bani ita,Nifa nan da kike gani na sai inyi fiye da wata ɗaya babu ko sisi a aljihuna,Babanmu kuwa idan kinga ya bani kuɗi to sai dai fa,idan naje islamiyya ne,haka itama maman mu,ataƙaice dai bari in fito maki a mutun,wlh Sehrish ko abun hawa bandashi,tunda keke na ya samu matsala ba’a ƙara gyaramun shi ba,naje wurin mai gyara yace sai ya ci dubu uku,tun daga nan na jingine shi gefe guda,
Zuba mashi ido sehrish tayi tana kallonshi,yadda kasan ɗan Almajiri haka ya zauna yana zayyano mata matsolilin dayake fama dasu na rashin kuɗi,ta kasa kunne tana sauraronshi,

A 6angaren Abusufyan kuwa,lokacin daya shiga yayi arba Da abu a zaune dirshan saman gadon tana faman zazzare idanuwanta,ba ƙaramin daɗi yaji ba,ƙarasa shiga ciki yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna,zuba mashi ido tayi tana kallonshi,
Murmushi ya sakar mata tare da miƙa mata hannunshi,zuba ma tafin hannunshi ido tayi tana kallonshi,ta gane fuskarshi a matsayin wanda ya taimaketa,ta fito daga hannun masu fararen kayan nan,
“Ina ƴa’ƴana suke”?muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,
“Kada ki damu,ƴa’ƴanki suna atare dani zan kaiki wurinsu,kina so ko”?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
“A ƙarshe dai duk yawace yawacen naki,gashi kin dawo wurina abu,saboda ƙaddararki tana atare dani,kamar yadda kika zama ƙaddarata nima,Ashe da rabon zan sake ganin wannan kyakkyawar fuskartaki”?calmly yayi maganar,tsantsar sonta ne da ƙaunarta ke addabarshi,ji yake yi tamkar ya mayar da ita cikin cikinshi,
“Abu na,Faɗamun har yanzu kina sona kamar yadda nima nakeson ki,”
Wuƙi wuƙi tayi mashi da ido tana kallonshi,sam batasan inda zacen nashi ya dosa ba,
“Kaine ka kashe mun babana ko?kuma ka rabani da ƴa’ƴana ko?Zaka kashe munsu ko”?
girgiza kai Abusufyan yayi tare da cewa”ni bani bane na kashe maki mahaifinki ba abu,Nifa ne Abusufyan ɗinki,uban ƴa’ƴanki,ba zaki iya tunawa ba ko kaɗan,”
Kallon dayaga tana binshi dashi ne ya tabbatar mashi da cewar a harzuke take,jira take yayi yunƙurin matsawa kusa da ita,Yasha bugu,
Dariya ya ɗan yi tare dacewa”kwantar da hankalinki,

 

Karanta>>> Zurfin Ciki Book 1-4 Complete Novel Document

⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫
*_MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI_*

*DOMIN. DAWO DA MARTABAN NONONKI*

Shin ko kinsan nono yanada matukar muhimmanci a wajan mai gida ,? Shin ko kinsan babu abunda namiji yafiso yafi daukar hankalinahi kamar cikar k’irji , ? To nono shine babban Martaban mace a wajan mijinta , don babu namijin da zaiso mace mai yakunannen nono kamar silifas ,wannan yasa Nazo maku da sahihi kuma ingantaccen maganin nono Wanda bashida wata matsala hadin gargajiya ne , acikin lokaci kalilan zakisha mamakin yadda nononki zai ciko sosai Wanda wannan cikowar ita zata bashi damar da zai tashi sosai ta yadda kema zaki Shiga cikin jerin mata masu aji agaban mazajensu ……..kedai hanzarta ki nemi mmn Yusuf mai kayan mata yar mutan sokoto zaki samu ingantattun kayan mata masu tafiyar da hankalin maigida…….don neman Karin bayani 07069711327 ……

Back to top button