Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 24 By Ayshercool

Duk da cikin matsanancin tsoro da tashin hankali ta bashi amsar, amma ta tattaro jarumtarta ta dake, ta ƙi kallonsa.”Ai ɗago kai zaki yi ki kalle ni, ki bani amsar da ki ka faɗa yanzu”Ta yi shiru, tana jiran yayi mata duk abun da zai yi mata.Ya ce “Dama ba ni na kawo ki gidan nan ba, kuma ba ni na ce a kawo ki ba, idan kin gaji ki tafi dama kin isheni, kuma idan ki ka kuma zuwa kaina ki ka tsaya ki na kuka, sai na ɓarar da ke”. Gabanta ya faɗi, a buge ta tarar da shi yana bacci, ya aka yi ya san duk abun da ya faru, sai dai kalmarsa ta ƙarshe da ya ce a kawota ba, ta yi mata ciwo.Ta zata zai yi mata tijara, da ta ce ta zubar, sai kuma ta ga ya tashi ya nufi hanyar fita, kawai ta fara kukan da ba ta san na menene ba ma.Waiwayowa ya yi yana kallon ikon Allah, da ta samu bai casata ba, da ta ɗebe masa kaya,ta ce ta watsar kuma ya san ƙarya take yi ba ta zubar ba, shi ne saboda samun wuri har da ɓare baki tana kuka.Sosai yarintarta ta fito, yadda ta tura baki tana kuka, tamkar irin ‘ya’yan madarar nan shagwaɓaɓɓu.Kawai ya girgiza kai ya fice, kafin ta fusata shi.Rahila da Zakiyya kuwa sai shewa suke yi, tare da farincikin yadda shawarar da suka yanke ta yi amfani.Zakiyya ta ce “Ni fa na zata yadda yake ɗin nan, ana kaita ya korota tun da ba son auren yake yi ba, amma dama na san ko zai daketa ya cinye abu ne mai wahala ta faɗa ko tayi yaji, juriya ce da ita kamar dutse shegiya”.Rahila ta ce “Shi ɗin me? A duniya akwai namijin da zai ce ba ya son mace ne, ke ban da abun makirci wannan yarinyar son kowa ƙin wanda ya rasa, wa zai ce ba ya so, dan ma ƙarama ce, gashi ai sati biyu kenan sun yi luf daga shi har ita”.”Wallahi na zata ba zai saurareta ba, ƙila ma ya korota, a yadda ki ke bani labarin yadda ya zama, da kuma rashin jin da yake yi”.”Ba fa mahaukaci ba ne, idan ta iya zama da yaron nan, ba lallai ki ji kansu, ai duk wannan bala’in da nake yi da tashin hankali a kansa, wasu lokutan shi da ‘yar uwassa yana yi mata abu, ke har magana shahida take gaya mini a kansa”Cikin mamaki zakiyya ta ce “Kai haba dai?””Wallafa Allah, ba suna school aka yi auren ba, sai da na kusa dukan yarinyar nan, ƙiri-ƙiri wasu lokutan take nuna in daina takurawa ɗan uwanta, aikuwa ubanta nake ci”.”Gaskiya kar ki zauna a kanta, ita ana neman mafita tana shirme? Ni kam yanzu menene abun yi ne? Ƴan uwan Alhajin nan fa sun zo, wai ayi aure ayi visa ta bi shi china”Rahila ta ce “Aikuwa sai dai a lahira idan ana zuwa”.”Aikuwa, wai yanzu ya fasa dawowa nan da watan ɗayan ba, ina nan dai ina ta lallaɓa uban, a kan ya haɗa shi da hafsa”.”Ai ba iya lallaɓa shi ba, malamai zamu cigaba da yi, in sha Allah sai abub nan ya tabatta, ita waccan ai an gama da babinta”.Zakiyya ta ce “Haka ne kam, to Ubangiji Allah ya amince, ni dai ko nawa ne zan kashe, idan ta aure shi na san zan mayar da kuɗina”.”Kar ki damu ai ba zama, za ayi duk mai yiwuwa, hafsa zata auri mutumin nan”.***”Ku yanzu a ganinku ya dace mu na ji mu na gani, baƙo ya zo unguwarmu ya saka mu yi masa mubayi’a? Baƙo ne fa, mu kuma a nan aka haife mu muka girma, muka kafa sabgar nan, kuma ace sai dai mu bi shi, ba dai ya bi mu ba?””Wallahi nima dai haka na gani, abun yayi mini ciwo, guduma ya fi kowa bani haushi shege, ai wallahi sai dai a rabu biyu, ayi ta zubar da jini, har sai ya yarda ya bi mu, ba wani shege da zai shigo arearmu ya buɗe mana ido, mu zagaya mu ji ta bakin sauran, mu ji su waye suka bi, kuma suwaye za su yi tawaye”.Ɗaya matashin, ya hurar da hayaƙin wiwi ya ce “Mu tabattar da suwaye a tare da mu tukuna, zamu yi masa sara na warning, idan ma ta kama, mu kawar da shi da ga sararin nan, ba wani ɗa da zamu yi wa biyayya, tun da muka yi wa iyayenmu ma tawaye”.Suka cigaba da tattaunawa a kan yadda za su ɓullowa lamarin, su yi maganin Al’amin.*****Kamar masu kasa gyaɗa, haka suka kewaye farantin wiwi, suna naɗawa a takarda. Suka mayar da wata ƙwaya garri, suka haɗata a cikin wiwin, ita ma suka ɗaura ta daban.Matasa ne suka din ga shigowa da ɗai ɗai, suna karɓa, suna zube balance, suna karɓar kaya.Liti ya shigo cikin ɗakin da Al’amin yake, da robar abinci, ya zauna ya ce “Taso ga abinci”Ya tashi zaune ya kalli miyar kan abincin, sai ya ji ƙyanƙyamin abincin, miyar sam ba ta ji mai ba, ga ta ba ta soyu ba, ba irin wadda waccan taɓararriyar yarinyar take bashi ba.Guntun tsaki ya ja, Walid ya ce “Lafiya?”.”Na ƙoshi””Meyasa?”Ya girgiza kai ya ce “Bakomai”.”Ka ce mini kawai, abincin amarya zaka je ka ci, wai mu ko sau ɗaya ba zaka kawo mana abincin na ta mu ci ba? Sai dai ka yi ta ci kai kaɗai?”.Kai tsaye ya ce “Ba zan kawo ba””To ka ƙarata, ku ci ku kaɗai, dama ni naga kamar haushina ma take ji, ban san me nayi mata ba”.Ya tashi yana fatan Allah ya sa ya je ya tarar ta yi abinci. Sai kuma ya tuna kukan da tayi kan ya fito, ƙila ma ba ta yi girkin ba.Sai dai kafin ya ƙarasa gidan, aka tsuge da ruwan sama, dan haka ruwa yayi masa duka, yayi ta sauri ya ƙarasa gida, ya san ƙarshenta ruwa yau ma ya shigar mata falo.Sai dai yau aka yi sa’a, ruwan bai shiga da yawa ba, sai dai tsakar gidan ya cika da ruwa.Tana ɗakinta tana salla, ya fara cire kayan da suka jiƙe, ta shigo da sallama, sai dai cikin matsanancin hanzari, tayi wani irin burki, ta juya.Shi mamakin ta yake yi, sam ba ta da zuciya ba ta fushi.Ba tare da ta waiwayo ba ta ce “Ina da ruwan zafi a flask, na kawo maka ka yi wanka, sai ka ci abinci kar ka yi mura saboda ruwan da ya dake ka?”.”Kawo” sumi-sumi kamar mara gaskiya.Ihunta ya jiyo a tsakar gida, bai san ya aka yi ba, sai ganinsa yayi a tsakar gida, cikin hanzari yana zaton wani abun ne ya sameta, tayi jifa da flask ɗin a gefe, Allah ya sa na silver ne tana ihu, ta maƙale a jikin bango.”Ke menene? Meyafaru?””Kwaɗo ne, zai riƙe mini ƙafa”Ji yayi kamar ya ƙarasa, ya kwaɗeta, wai kwaɗo take yi wa wannan ihun.”Zaki rufe mini baki ki zo ki wuce, ko sai na zo na tumurmusa ki?”Jauhar ta ce “Tsoro nake ji wallahi” tayi maganar tana ɗagowa, idanunta har sun yi ja.Sai dai mayar da kanta ƙasa tayi, da sauri, tana tsuma saboda babu riga a jikinsa, wani irin gashi ne a jikinsa, tun daga ƙirjinsa har saman cibiyarsa.”Ke ba na son gulma, miƙo mini flsk ɗin, idan ya so ki dauwwama a wurin”Cikin shagwaɓa ta ce “Wallahi da kwaɗo a cikin ruwan nan, tsoronsa nake ji” tayi maganar idanunta na bayyanar da tsantsar tsoro da tashin hankali.Cikin ruwan ya biyo, ya zo ya ɗauki flask ɗin, zai bar kitchen ɗin ya bar ta, ta saka hannu ta riƙe masa wando, tana ihu.Sai yanzu ya leƙa ya ga kwaɗon ne da gaske, amma girmansa ba wani ƙato bane take wannan ihun, shi bai taɓa jin wai ana tsoron kwaɗo ba, sai yau.A ransa ya ce ‘Laifin iyayeki ne da suka zaɓa miki wannan rayuwar’Kwaɗo ya tsalla yayi waje, ita kuma jikinta sai rawa yake yi, cike da tsoro.”To ai sai ki cikani, tun da ya tafi ko?”Cikin tsananin jin kunya, ta sake shi, ta koma gefe.”A nan wurin zaki dauwwama kenan?”Ta ce “A’a idan ruwan ya bushe, na wuce, ka duba ɗakina akwai man zafi a kan mudubi, idan ka yi wankan ka ɗan shafa kar ka yi mura, abincinka yana ɗakinka” kallonta yake yi, yana son gane nature ta ce a haka, ko kuma iya shege ne, amma yadda take ƙifta ido a tsorace ya tabattar masa da gaske take.Ba ta yi tsammani ba, ya saka hannu ɗaya ya ɗago ƙugunta, hannunsa ɗaya kuma da flask taku kaɗan yayi, ya direta a tsakiyar falo.Kallonsa take yi da mamaki, shi kuma ya nufi ɗakinsa.Har ɗan tsalle ta yi, dan ta tabattar ta na da nauyi ne, ko ba ta da shi, da ya ɗauke ta kamar wata ‘yar teddy.Ta fi mintuna sha biyar tana cigaba da mamakin yadda ya ɗagata kamar a bar banza.Tuwon shinkafa ta yi da miyar taushe, kamar ya cire kunne dan daɗi, ga katifarsa ta saka sabon bedsheet, ɗakin yana ta ƙamshi, amma hakan bai hana shi goge mata hannu a jiki ba, ya gama ya miƙe yana bacci, kayan na sa ma sai ƙamshi suke yi.Leƙawa ta yi ɗakin nasa, ya mimmiƙe a kan katifa, bai saka rigar ba yana bacci ta lallaɓa ta shiga da sanɗa zata kwashe kwanukan.Yanayin garin da sanyi saboda ruwan da aka yi, amma ya takure yana bacci.Ta fitar da kwanukan, ta ɗaukko bargo daga ɗakinta, ta zo zata rufe shi, ɗan ƙura masa ido ta yi. Al’amin ba shi da wata makusa, da yake baccin nan ma he looks very innocent and calm.Kasa rufe shi ta yi, ta tafi tunanin ya aka yi ya fara shaye-shaye, ya aka yi su mama suka samo shi ma, suka aura mata? A ina yake ina ne gidansu? Duk take tambayar kanta.Tashi ya yi zaune kamar aljani ya ce “Meye ne kin zo kin sakani a gaba kina kallona”Zabura ta yi ta ce “Yi haƙuri, na zata bacci ka ke yi, ba kallonka nake yi ba, na ga kamar kana jin sanyi ne, bargo na kawo maka” tayi maganar tana tsuma.Ya miƙa mata hannu, ta bashi bargon, ya ware shi ya lulluɓa, ta fita tana mamakin al’amin idan yayi wani abun mamaki yake bata, har da ajiyar zuciya ta ji yana yi alamun baccinsa yayi nisa, amma kawai ta ganshi a zaune.***”Allah ya taimaki maigida””An gaisheka, ya ake ciki?””Komai normal, ba wani abu””Yaya za ayi? An kama Ja’afar da kaya, hukumar nan sun ƙi sakinsa, ba zan matsa ba, amma ina buƙatar a musanya shi da wani””Oga ba zan iya sakinsa kai tsaye ba, amma dole za’a samu wani a kama shi da kayan, sai a saki jafar a kama shi, ka san wannan karon shugaban namu, yana da sanya ido sosai””Shikenan, ayi abun da yakamata kawai””Ok sir”.Cikin ikon Allah, matar nan tela, tana biyan jauhar, duk da ba wani kuɗin kirki take bata ba, amma tana jin daɗi sosai da sosai, ta sayi katin tara kuɗi, ɗan abun da tayi cefane, sauran sai ta saka a kati, kuma Allah ya saka mata albarka a ciki.Yaran maƙwabta idan sun shigo, tayi musu tsifa da kitso, babu ko sisin iyayensu.Ta duƙufa tana aikinta, ba ta ji motsinsa ba, sai jefo mata bargo yayi a ka.A razane ta tashi, bargon kuma ya cukuikuyeta.Ya ce “Zaki taka kwaɗo” Ihu ta saka ta samu ta cire bargon da ƙyar, tana dube-dube, yana tsaye yana kallonta, kamar ba shi yayi maganar ba.Ta ce “Ina kwaɗon?” Ya yi shiru bai ce komai ba.Ta kalli yadda stone ɗin ya zube kamar ta yi kuka ta ce “Kalli yadda ka saka na zubar da kayan sana’ata.” Ta durƙusa za ta kwashe, sai kuma ta yi sauri ta hau kan kujera, ta maƙale ƙafafuwanta ta ce “Ina kwaɗon ya shiga ne?”Haryanzu shi dai bai daina mamakin yadda kwaɗo ya zama abun tsoro ba.Hanyar fita ya nufa, ta gane tsokanarta yake yi, nan ta ƙara jinjinawa ƙi faɗinsa, har ya iya ya tsokaneta, amma ya sha kunu ba fara’a.”Master” ta kira shi. Ya tsaya bai waiwayo ba.”Dan Allah idan Allah ya yassare, ka taho da omo, zan yi mana wanki”.Yanzu ma bai yi magana ba ya fita, ta naɗe bargonta, ta cigaba da aikinta.Zakiyya kuwa, kamar zata zare, Rahila na ta janta wuraren malamai kala-kala, yadda za su samu, Hafsa ta auri Alhaji mu’azzam da zarar ya dawo.Har sha ɗaya na dare, jauhar na aikin jera stone ɗin ta a kan gadonta, dan tun tana jin tsoron zaman gidan, har ta saba, sai da ta ji bacci yana kama idonta sosai, sannan ta tashi ta ajiye kayan, tayi wanka ta fito tana shirin kwanciya.Ji ta yi ana buɗe ƙofa, dan haka ba ta damu ba, ta san mai gidan ne, sai dai bayan wasu mintuna ta ji kamar yayi jifa da wani abu a falo, yana ta haki mai kama da kakari, gabanta ya faɗi ta fito da sauri, ta tarar da shi ya riƙe hannunsa yana ta nishi, hannunsa an yanke shi, da ƙafarsa ta hagu, kasancewar da wuta, ya sanya ta ga yadda yake zubar da jini, a gigice ta ƙaraso cikin matsanancin tashin hankali ta ce “Master faɗa ku ka yi da wani? Ya aka yi ka ji ciwo haka?” Yayi shiru yana fesar da iska daga bakinsa.Da gudu ta shiga ɗakinta, ta ɗaukko zani ta danne masa na hannunsa da ya fi zubar da jini, ta rikice ta rasa me za ta yi, kawai ta nufi hanyar fita.Ya ce “Ina zaki?”Cikin tashin hankali ta ce “Maƙota zan je, a samo abun hawa a kai ka asibiti kar jininka ya ƙare”.”A haka kuma zaki fita?”Sai a lokacin ta ga, ko hijjabi babu a jikinta, ta koma ɗaki, ta ɗaukko hijjabinta sai kuka take yi, tana dawowa falon ya ce “Kar ki fita””Meyasa? Jini fa ka ke zubarwa”Ya ce “Ki ƙyale ni, zai daina zuba ne”Cikin kuka ta ce “Ni dai dan Allah ƙyale ni, sai wani abun ya same ka, idan jininka ya ƙare fa mutuwa zaka yi” ba ta ma jira me zai ce ba, ta kasa da gudu, tayi waje. Ta din ga buga gidan maman halimatu, malam lawan ya buɗe, ya tsaya yana tambayarta menene?”.”Dan Allah baban su halimatu, ka taimaka mini, na ga kana da babur, mijina ne aka sare shi dan Allah a kai shi asibiti, sai zubar da jini yake yi”Ya waro ido ya ce “A daren nan, haka kurum garin taimakonku, wani abun ya same ni, shi ma idan ya samu wani haka zai yi masa, sai da safe” ya rufe ƙofarsa.Haka ta din ga buga gidajen layin nan, na ƙarshe ne mai gidan ya biyota, sai dai ba shi da abun hawa, suka zo ya tsaya a ƙofar gidan, ta shiga ciki.Yana zaune, ya kashingiɗa ya lumshe idonsa, yana jin yadda raɗaɗi yake ratsa wurin saran.”Master, taso mu je”Bai buɗe idonsa ba ya ce “Ina?”.”Wai meyasa ka ke haka, asibiti mana” tayi maganar hawaye na ta ambaliya a fuskarta.Ya miƙe yayi waje, ya tarar da maƙwabcin na su a tsaye, suka gaisa Al’amin ya ce “Malam ka rabu da ita dan Allah, ka je ka kwanta, ba wani abu in sha Allah”Ya ce “A’a ga jini kana ta zubarwa, ni bani da abun hawa, na kira wani ƙanina, a nan titi chemist ɗin sa yake, ko taimakon gaggawa sai a baka”Tayi farat ta ce “Yauwwa mun gode Allah ya saka da alkhairi”Haka suka tafi, ya kira ƙanin nasa, ya buɗe chemist ɗin babban wuri ne sosai.Ya fara yi masa ɗinki, saboda raunin na hannunsa yayi zurfi sosai da sosai.Sai dai shi da ake ɗinkewa kamar ƙwarya ko a jikinsa, ita kuwa sai uban kuka take yi, tana yi masa sannu.Kawai bin ta yake yi da ido, har mamaki yake yi, yadda take nuna matuƙar damuwarta a kansa.Mai Chemist ɗin ya ce “Dan Allah ki daina kukan nan, ba wani abu, ba ki ga shi jarumi bane?””To jininsa ba zai ƙare ba, ya zubar da jini sosai tun a gida”Ya ce “Ba zai ƙare ba in sha Allah, idan ma ya ƙare sai mu saka masa naki”.”Ki daina yi mini surutu a ka kin cika mini kunne” yayi maganar a ƙule. Haushi ne ya cika masa rai, kamar ya kife mai chemist ɗin da mari.Ta ce “To na daina sannu” tayi maganar cikin kulawa.A ka gama ɗinki, ya ce zai ɗan saka masa ruwa, saboda ya taimaka masa ya zubar da jini sosai, amma fafur ya ce ba ya so.Ya haɗa masa magunguna, ya ce ya din ga zuwa ana wanke ciwon, jauhar ta ce “Sai dai ka bani kayan dressing ɗin, ba zai din ga zuwa ba”.Mai chemist ɗin yayi dariya, ya haɗa ya bata, ta ce “Nawa ne kuɗin maganin? Da abun da aka yi masa?”.Maƙwabcin ya ce “A’a kar ki damu, Allah ya bashi lafiya, ni zan biya”.Jauhar sai da ta risuna, ta din ga yi masa godiya, sannan ta ce “Tashi mu tafi” ya miƙe tsam ta bi bayansa.Suka baro maƙwabcin na su a can, suka nufi gida.”Sannu, ka na jin jiri ne? Idan kana jin jiri mu tsaya ka huta, ko ka dafa ni” kallonta ya yi ya ga me zai dafa. Ya dai yi shiru bai yi magana ba.Suka isa gida, ya shiga ɗaki ya zauna, ta fito ta hau aikin wurin da ya ɓata da jini, dan a buɗe su ka bar gidan ma.Ya zauna ya ci abincin da ya tarar a ɗakinsa, ta ga ledar omo ce da sabulu da ta ce ya sayo, su yayi wurgi da su.Ta dawo ɗakinsa, ta tarar ya jingina ya lumshe ido, “Sannu master, yana yi maka zafi ne? Ga magungunan nan ka sha kan ka yi baccin”.Ya girgiza mata kai alamar ta ƙyale shi, gumi ya fara tsatstsafo masa, saboda allurar ta sake shi, zafi ya fara ratsa shi.Saboda kar ta takura masa da surutu, ya kwanta ya hau baccin ƙarya.Ta fita ta ɗaukko mafici ta dawo, ta zauna a gefensa, ta hau yi masa firfita.Sai dai lokacin kusan ƙarfe biyu ne na dare, ta din ga zabga hamma, yana kallonta, har bacci ya ci ƙarfinta, ta saki maficin.Ya buɗe idonsa fes a kanta, har mamaki take bashi, yadda take nuna matuƙar damuwarta a kansa, kuma komai zai yi mata ba ta jin haushi.Hakazalika bai daina mamakin yadda aka yi, iyayenta suka yarda suka aura masa ita ba.Ya ciro wayarsa a aljihunsa, ya kira walid, uku sauran nan, ya ɗaga.”Walid””Maza, ya aka yi ne?”.”Ka san akuyancin da yaran nan suka yi mini?”Walid ya ce “Wane yaran, suwaye?”.”Na baro chamber, na shigo cikin unguwa, kawai na ji sara a hannuna, sun kai su bakwai, suka hau ni da sara, kasheni suka so yi”Walid ya zabga ashar ya ce “Suwaye?”.”Bari na yi wa ɗaya shaida, haryanzu ba su san waye ni ba, na karya biyu, sauran sun gudu, sun yi mini rauni a hannuna da ƙafata”.”Yanzu kana ina?””Ina gida, ni wallahi yarinyar nan ta fara takura mini, komai kuka, duk ta tashi hankalinta, iyayenta ba su yi mata adalci ba, ni fa ba zata hana ni rayuwata yadda nake so ba”.Walid ya ƙyalƙyale da dariya ya ce “Mai dogon zamani, da uban waye ya damu da ka ji koma menene mana, tana da tausayi ne kawai da alama, ka dai daina yi mata muzurai da zare ido kawai”Yayi tsaki ya ce “Ka saka liti ya nemo mini suwaye yaran nan””Shikenan, zamu faso gobe in ga jikin naka, sai da safe”. Ya ajiye wayar ya kalli fuskarta, tana ta bacci a zaune.Hannunsa ɗaya ya saka, ya janyota ta kwanta a kan katifar, shi kuma ya jingina da bango ya cigaba da bacci.Kasancewar ba salla za ta yi ba period take yi ya sanya, tana ji ana kiran sallar asuba, ta cigaba da baccinta, sam ta manta a ina take.Ƙaurin da ya isheta ne, ya sanya ta fara tari, tayi juyi ta buɗe ido, da fuskarsa ta fara tozali, yana busa sigari. Ta tashi tana kallon ɗakin, sai yanzu ta tuna ta shigo tana yi masa fifita.Ta hau soshe-soshen cizon sauro.Ƙura masa ido ta yi, ya kawar da kansa gefe.A raunane ta ce “Master”Idonsa ya ɗago ya kalleta.”Dan Allah ka daina, ba na so zuciyata ba ta yi mini daɗi, kuma zaka cutar da kanka, kalli yadda ka je aka yi maka rauni, ka zubar da jini, haba master manya ba sa haka” tsuke bakinsa yayi yana sakin hayaƙin, a ƙoƙarin sa na hana maganganun ta yin tasiri a zuciyarsa.Ta girgiza kai ta ce “Shikenan, ya jikin?”.Yayi mata banza, ya cigaba da busa sigari.”Dan Allah ko ba zaka daina ba, ka rage mana, lafiyar ka fa”.”Ke, ki koma in da ki ka fito mana, ko na ɗaure ki na ce ki zauna ne? Tashi ki bar mini ɗaki”.Ta gyaɗa kai ta ce “Abun har da gori, Allah ya baka haƙuri” ta miƙe idonta fal hawaye.Tana kitchen tana aikin karin kumallo, aka buga ƙofa, ta saka hijjabi ta buɗe ƙofar, ta ga walid d wasu matsa su biyu, suka gaisa suka ce mata, wurin mak dogon zamani suk zo.Ta haɗe rai ta ce “Sunan shi Al’amin, bari na yi masa magana”.Tana shiga ta tarar da shi a falo ya fito.Ta ce “Ka zauna sai su shigo su ganka, amma ka ga da rauni a jikinka” tayi maganar tana sunkuyar da kai, tana jiran ya gaya mata baƙar magana.Idonta ya ɗan yi ja, saboda kukan da ta yi.Ya nemi wuri ya zauna, ba tayi tunanin zai yadda da hakan ba.Ta je ta leƙa ta ce musu su shigo.A falo suka tarar da shi, gida sai ƙamshi yake yi, gashi dai ba wani haɗaɗen gida ba, amma ta gyare gidan tsaf.Suka zauna a falo, Walid ya ce “Maza wallahi ka more, mu ma Allah ya tsamo mu, dan Allah ji wani ƙamshi kamar a gidan masu kuɗi”.”Duba ni ka zo yi, ko munafunci ka zo yi?”Walid ya ce “Duka, amma dai ya jikin? Kut ka sha ɗinki kamar ƙwarya, za su ci ubansu yaran nan, kan yamma an gano su in sha Allah”.Suna ta zuba, tana jiyo shi yana saka baki sama-sama, da ita ce dai ba zai yi hira ba, amma yana magana.Tayi sallama suka amsa, ta zo ta ajiye musu kofuna, da cokula da flask ɗin shayi, ta koma ta kawo jallof ɗin taliya a faranti, sai ƙamshi take yi.Liti ya ce “Allahu Akbar, sannu amarya, wannan hidima haka? Ai da mun sani tuntuni mun zo” Al’amin kallonta yake yi, da jinjinawa ƙarfin halinta, har ta ƙar sanwa, ta yi girki da su.Suka kewaye, suka din ga cin taliyar nan, liti ya ce “Kalarta kalar girkinta, abincinta mai daɗi, ita kuma ‘yar beauty, wallahi maza ka more, ga gida mai ƙamshi”Ji yayi ya kasa haɗiye abincin, maimakon ya ji daɗin yabon suka yi mata, sai ya tsuke fuska ya tsame hannunsa daga kwanon abincin.Har suka gama santin, bai sake cewa komai ba, Walid kuma yana ankare da shi, dan haka da gayya, ya cigaba da kunna shi, suka gama abun da za su yi, suka fita tsakar gida suka din ga yi mata godiya.Walid ya ce “Wai ba zaka fito ka raka mu ba?”Tayi farat ta ce “A’a ba shi da lafiya ai”Walid ya ce “Au, to Allah ya baku haƙuri, Allah ya ƙara afuwa ya bar ƙauna”.Bayan fitarsu ta kwashe kwanukan, ta wanke, tana ta aikinta, yana kan doguwar kujera a kwance, sai dai ba ta kula shi ba.Kusan kwanaki uku, jikin master yayi kyau, ba shi da ƙan jiki, ba zai sha magani ba sai ya ga dama, dressing kuwa cewa yayi ba ya so.A kwanakin nan jauhar na jin ciwon kai, da ciwon jiki, sai dai ba ta wani damu ba.Duk yadda ta so hana master fita, da ‘yan dabaru sai da ya saka ƙafa ya fice, ya tafi nasa garari.Cin abinci ne yake dawo shi, ko sau ɗaya bai tambayi yadda take samun yin cefane ba, sai da ya zo ya ci.Tun da ya dawo gidan ya ji shiru bai ji motsinta ba, kuma bai ga abinci ba, sama da awa guda, saɓanin da, da ya shigo za ta fito.Kasa kwanciya hankalinsa yayi, ya nufi ɗakinta.A kwance take a kan gadonta, amma bai tabattar da idonta biyu ko bacci take yi ba.Ya ƙarasa gaban gadon, sai dai ya manta sunanta, Fatima zahra kuma yayi masa nauyin da ba zai iya faɗa a bakinsa ba.

Ayshercool 08081012143

Back to top button