Fentin Zina Page 19 Hausa Novel
*****Dakyar Ameena ta bude baki murya na rawa tace watan can ne inna.Yi mun bayani watan can ya? Kin gani wannan watan?.Girgiza kai tayi cikin tashin hankalin da ke cinta a zuciya.Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Allahumma ajirni fi musibati wa’akhlifni khairan minha Ameena kin cuce ni Ameena kin ci amanata. Inna take fada dafe da kirji hawaye na taruwa a idanunta.Dakata rukayya kada bacin rai ya saka ki fita hayyacin ki har ki furta kalmar da zata tarwatsa rayuwarta kada ki manta ke uwace duk kalmar da kika furta a kanta zatayi tasiri akanta ki bari mu tabbatar don duk wannan zargine da muke fatan kada ya kasance.Dan Allah Kada ki hana ni magana goggon su yanzu ace yarinya kamar wannan tasan tayi wani ciki kuma ma ubanwa ya mata shi, ta fada da zafi tana mikewa ta hau waige waige inda zata ga abun duka.Goggo ta fahimci hakan shiyasa tace bafa zan barki ki taba lafiyar jikinta ba, ki kwantar da hankalin ki bari malam din ya dawo sai mu tafi asibiti ayi gwaji ko mu bari sai gobe da safe.Ai gara muje yanzu din musan gaskiyan lamarin domin bazan taba samun natsuwa ba har sai na san gaskiya.Daidai nan baba malam ya bugo sallama a tsakar gida fateema ta amsa tana mai sannu da zuwa ya amsa yana tambayar inna tace tana ciki tare da goggo, yace toh toh.Sallama yayi, inna ta amsa masa ya dago labulen ya shigo ya soma bin ko wannen su da kallo Yace.Meke faruwa na ganku cikin yanayin dake nuna rashin natsuwa.Alhamdulillah tunda ka dawo zoka zauna sai muyi magana.Baice komai ba yazo ya zauna saman side drawer yace ina jinku.Gata nan, goggo ta nuna Ameena da yatsa tace so muke mu kaita asibiti ayi mata gwajin ciki.Tun kafin ta karasa baba malam yace ciki? A gidannan, ya girgiza kai yace a’a kuma dai Ameena kuke nufi, bazan iya yarda Ameena zata aikata makamancin wannan kuskuren ba domin kowa yasan babu wanda yakai ta natsuwa duk fadin gidan nan kai harma da mutanen waje kwatance akeyi da kyawawan halayenta.Malam yanzu ba lokacin musu bane, kawai ka bada kudi muje asibiti domin tabbatarwa, goggo ta fada.Ameena wani irin dana sani da tausayin iyayenta ne ya shigeta nan take idanunta suka fara zubar da kwalla ta kasa ce musu komai sai kasa da tayi da kanta cikin fargaban halin da zata jefa kanta da iyayenta a ciki.Yamma tayi yanzu amma bazan hanaku zuwa ba domin bazan zame daya daga cikin masu kokarin marawa barna baya ba, ya dubi Ameena yace ina fatan kada zargin da suke akan ki ya tabbata.Kara sunkuyar da kanta tayi yayinda shi kuma ya ciro kudi a aljihunsa ya mikawa goggo yana cewa Allah ya tsare kana yasa kai ya fita daga dakin.Wani matsiyacin kallo inna ta jefi Ameena dashi tace kin dai ji abunda malam yace hm kiyi kuka da kanki, taja kwafa tace goggonsu barin dauki hijabi sai mu tafi.Ba domin bata san me sakamakon zai nuna ba saidai tana a matukar tsorace da baba malam da ita kanta inna shiyasa zuciyarta keta zillo kamar zai faso kirjinta ya fito waje.Bayan sunje sunyi gwaji a lab din kamar yanda likitan ya basu umurni suka dawo da sakamakon suka mika masa karba yayi ya duba sai kuma ya washe baki yana kallon inna yace mama ina taya ku farin ciki zaku samu baby wato dai tana da shigar ciki a jikinta.Daga tsayen da inna take sai ji akayi timmmm……Ta fadi kasa, tuni likitan ya kwalla kiran nurses suka daga ta a gadon tura marasa lafiya suka nufi emergency da ita aka soma bata taimakon gaggawa.A reception Suka zauna Ameena sai kuka take yi kamar ranta zai bar gangar jikinta.Gogo tace kinji kunya, wato dai ta tabbata maganar hausawa da suke cewa ba’a yabon dan kuturu sai ya shekara cur da yatsunsa, kike nuna fuskar salihai ashe barna kike aikatawa a bayan kasa, yau wa gari ya waya ace kinyi sanadin kwanciyar mahaifiyar ki a gadon asibiti Wawuya shashasha.Kukanta ne ya tsananta wanda yayi sanadiyar daukewar numfashinta cak yayinda bayanta ya jingina da jikin kujerar.Goggo bata lura da halin da take cikiba ta ci gaba da sababinta sai watace dake bayan kujerar Ameenan tace haba baiwar Allah ya kinata fada kuma baki lura da halin da take ciki ba.Kedai barni in fadi abunda ke raina akan wannan ballagazar.Gaskiya ki sassauta mata haba yarinya ce fa kuma bakiga ta suma bane?.Sai a sannan ne goggo ta dakata ta matso kusa da ita ta jijjigata sai ta zame ta karasa kwanciya a kujerar babu numfashi a jikinta.Dayar matar da tawa goggo magana ne ta nufi office din likita da gudu suka dawo tare yasa itama nurses su dauketa su bata gado.Haka dai aka kwantar dasu a dakin jinya na mata gadon su na gab da gab, goggo ta kira baba malam ta sanar dashi abunda ke faruwa salati yayi juwa ta debeshi dakyar ya kai ga dafa bango ba don haka ba daya fadi.Bai zo asibitin ba domin baya so yayi tozali da fuskar Ameena wacce yakewa kallon bakin kumurcin maciji sai kawai ya tura fateema dake tsaye ta ji duk abunda ya wakana don haka itama cikin tashin hankali take.Dukkansu basu farka ba har yanzu bacci sukeyi, fateema ce mai zaune kusa da ameena goggo kuma gurin inna.Ameena ita ta riga tashi kwakwalwar ta na tariyo mata abubuwan da suka faru, kuka ta sake tana dafe da kai.Ki mana shiru malama domin kukan nan naki bazai amfane ki da komai ba dubi halin da kika jefa gidan mu. Wallahi indai kikayi sanadin eani abu ya samu inna baza kiji dadi ba. Duk wannan maganar da fateema takeyi fuska a daure take yin shi Kuma tana kallon gefe.Kuka ne ya kara kubcewa Ameena tana tunani a ranta sosai, wai yau ace ita kanwarta zata duba ta dinga jifa da irin maganganun nan lallai ta yadda laifi laifi ne komin kankantar sa, kuma ta yadda zina masifa ce bala’i da kuma anno ba duka sannan tana zubar da kima da mutumcin mai yinsa ta yadda babu wanda zai dinga ganin martabar ka, yau gashi tana gani da idanunta tana kuma ji da kunnuwanta, abun da bai taba faruwa tsakanin su ba shine yau take fada mata duk abunda yazo ranta kawai don ta aikata ZINA, istigfari takeyi a zuciyarta a hankali kukan nata ya lafa ta mika hannu da nufin kamo hannun fateema ta wapce, ta kara mikawa ta tashi daga gurin ta koma ta daya bangaren, Ameena ta rasa meke mata dadi kamar ta hadiyi zuciya ta mutu ta huta.Inna ce ta fara motsi alamar tana gab da farkawa.Duk maida hankakalin su sukayi kanta.A hankali ta soma bude idanunta har ta ware su sosai akan fateema dake tsaye akanta ta maida kallonta ga goggo dake tsaye a gefenta kana ta tsaida idanunta akan Ameena dake kwance a gadon kusa da nata da karin ruwa a hannunta.Wani irin jijjiga tayi tana neman mikewa. *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️


