Uncategorized

Kishin Bal-Bal Complete Hausa Novel By Jamila Umar Tanko

          NA

JAMILA UMAR TANKO (JUT)

Matashiya:

Assalamu alaikum wararahamatullah. Tsofaffi da sababbin masoyana masu bibiyar rubutuna. Ina yi muku Albishir da fitowar sabon labarina mai tafe da sabon salo, mai fadakarwa da nishadantarwa wato KISHIN BAL-BAL part 1, 2 and 3.

Ina fatan za ku biya domin samun ci gaban wannan qayataccen labarin akan kudi naira 5️⃣0️⃣0️⃣ kacal.

 Na gode sosai. 

0023843938

Unity bank 

Jamila umar tanko 

Whatsapp 

08037196708

Godiya:

Bismillahi Rahmanir Rahim 

Na fara da sunan Allah mai rahama mai jin qai. Dukkan godiya ta tabbata ga ubangijin talikai mai kowa mai komai. Ina addua yadda Allah Ya bani ikon farawa Ya bani ikon kammalawa lafiya. Allah Ya dora alqalamina akan rubuta daidai ya kiyayeni da rubuta kuskure.Amin.

Sadaukarwa:

Ga dukka matan da suke yiwa mazansu uzuri, su ka iya danne da saita kansu wajen fito da mugun kishi. 

An fara rubuta shi ranar 24/06/2022. 

Qarfe 8:30am.

FREE PAGE

0️⃣1️⃣

      A yau na yi kwalliyar da na dade ban yi ba, gidana sai  qamshi yake a gyare tsaf. Jikina qamshi ni kaina ban san adadin humra da turaren wuta na jiki da na tufafi da na tsugunnon da na dinga tuqaqawa jikina a ciki da waje ba.

         Mai yin kwalliya na gayyato ta zo da kit dinta na make up ta yi min a fuskata na biya ta kudi da yawa, daman a gidan qunshi da kitso na wuni. 

       Leshin da na saka shine na sallah ta da ban samu na saka ba saboda aikin suyar nama. 

      Sannan na danqare kan dining table da irin abincin da abin shan da ya fi so a rayuwarsa, fresh juice na Banana milk shake, fruits salad, farfesu kayan ciki da fried rice.

       Dukka wannan shirin na yi ne saboda mai gidana abin qaunata Usman. Auren shekara takwas yau na sabunta shi, sai ka rantse amaryar kwana takwas ce.

         Na kora yara dakinsu su yi wasan acan har bacci ya kwashe su, dan bana so su bata min falona su katse mana soyayyarmu.  Na tanadi kalaman da zan zayyano masa a cikin kunnensa da kuma wadanda zan fada masa ido cikin ido.

      Na je jikin mudubi na kalli kaina da kaina wallahi ko hasidin iza hasada sai ya yabe ni, yau kam na yi kyau- na yi kyau over ma. Na juya gaba da baya na kama qugu na canja tafi kala-kala irin wacce zan yi masa wato kamar dai fasshion perret daman gani  doguwa , siririya, fara tas Alhamdulullah. Mijina yana yabon qirar jikina kamar taliya, haihuwa hudu amma bani da tumbi.

        Misalin qarfe takwas da rabi na dare daidai, na ji ana danna qararrawar qofar falon na tabbatar sarkin da yake mallake da birnin zuciyata ne ya iso wato Dan Usmanuna, dan haka na taso cikin rangwada na bude masa.  

       Na yi farfari da ido yadda zai ga eye lashes da eye shadow sosai. 

        Cikin wata siririyar murya na ce ” abin alfahari na barka da zuwa….”

       Ban kai qarshen maganata ba labari ya canja, dan a cikin sakan guda aka cire ni daga cikin wannan duniyar na ji an cilla ni wata duniya mai jujjuyawa, kaina ya koma qasa qafafuwana a sama. Ji na da ganina ya dauke, hankalina ya gushe,  radadi da zugi ya mamaye gefen fuskata na dama. Ni da nake tsaye na ganni a zaune a can gefe kamar an yi wurgi da ni. Na dafe kunci na yi shiru ina shafawa.  

     Wai ashe wani mahaukacin mari ya sakar  min da wannan tafkeken tafin hannun na sa. 

      Toh amma ban yi mamaki ba dan na san babban laifin da na tafka masa amma kuma na yi matuqar yin mamakin yadda har Usman ya dauki hannu ya taba jikina alhali na sha yi masa laifin da ya links wannan a baya bai taba nuna alamar daukana ko marina ba.

      ” Me yake faruwa ne haka? Lafiya kuwa ? Ko dai mummunan mafarki nake yi ne?” Ni nake tambayar zuciyata. 

      Amma fa ba mafarki ba ne gaskiya ne, dan na hango Usman a fusace ya tunkaro ni ya daga hannu zai sake maimaita min gauron marin nan a karo na biyu.

      Wannan karon ba zan bari ba wancan ma ban yi tsammani ba shiyasa ya sami galaba ya ga fuska galala yayi abin da yayi. Dan haka na daka tsalle gefe na kudindine fuska. Na kwalla ihu ina fadin  “kada ka sake marina dan ba baiwa aka aura maka ba.”

        Ban ji saukar mari ba sai dai na ji shiru hakan ya sa na dago da sauri dan in ga me ya tsayar da shi har yanzu bai qaraso ba. 

      Abinda na gani ya fi marin ciwo, abinda na gani ina addua ko a mafarki kada Allah Ya sake nuna min irin shi. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Tabbas na girgiza na firgita na ji na tsani kaina. Gara Usman ya kwana yana yi min irin wannan marin sau dari akan abinda ya faru a kan idona.

      Makwabciyata Mufidah Ansar marar aure, qatuwar budurwa, cikakkiyar Lauya sanye da kayan bacci yaloluwar riga fara iya guiwa bayan gajartar rigar an tsaga cinyar, dama ga ta shara shara ciki babu undies komai ga shatinsa nan a cike dam a tsatstsaye. 

       Ta damqe hannun mijina da ya daga zai mare ni. Ranta a bace ransa a bace sun jima su na kallon juna bata sake shi ba shi kuma mamaki ya hana shi ya fisge.

       Su dukka huci suke tamkar kasa amma a wajensu ne yake hucin bacin rai, ni a wajena hucin damuquwa da juna ne. 

        “Innalilahi wa inna ilaihi rajuun haka na fada yayin da na taso a guje a fusace ina qoqarin raba wannan daquma.  

       Mufida na tunkara da zunmar in tunkude ta daga jikin mijina yayin da shi kuma ya sake kai min wani sindiqin mari a karo na biyu , mufidah na qoqarin tunkude shi ta riqe shi gam sai ga su sun hade girji da qirji cinya na gugar cinya. Kokawa ta hargitse a junansu shi a dole sai ya zo wajena ya yi min duka, ita kuma a matsayin mai cetona  suka cakude gaba daya suka dame suka harhade ana riqe hannu ana tunkude tunkude. Ina addua kada Allah Ya sake maimaita min abinda na gani. Wannan ceto bai amfane ni da komai ba sai masifa da ta sake jefani. Gara mari da dukan da zai yi min akan in ga mijina a kusa da wata matar, kusan ma irin ta kusa-kusa jiki da jiki.

        Na yi kukan kura na damqo Mufidah ina qoqarin cillar da ita gefe dan ta daina daqumar mijina, a tunanin ta kama ta na yi dan in sami mafaka a wajenta, ta zaci buya na yi a bayanta ina neman ceto.

       Dan haka sai ta ce “Maman Ahmad kar ki damu ba zan bari ya sake marinki ba, shiga cikin daki ki rufe.” 

      Na fada cikin daga murya “in shiga daki a ina ? Ki bar shi ya kashe ni ai mijina ne.”

       Nan fa mu uku muka cakude Mufidah na tsakiyarmu ina qoqarin banbare ta daga kusa da mijjna, Usman na zuro hannu yana kai min duka yayin da Mufidah take tare dukan ta na riqe hannunsa.

       Gashin kanta ya tuje sai wasu lallausan gashi har qasan qeyarta mai tsananin baqi da tsawo da yawa. Ina kallon idanuwan Usman sai da ya kalli gashin. Na sake zuciyowa wani qarfi ya zo min, na cije baki na yi galaba na jawo Mufida na tunkuda ta gefe hanyar waje.

       Ina huci na ce ki “tafi ki bar ni ya kashe ni kada ya bar ni da rai ai mijina ne.”

         A tunanin Mufidah haushin dukan da yake yi min ne ya sa nake ganin gara a bari ya kashe ni bata abinda ta yi min ya fi zafin marin da yake yi min ba.

       Na tunkude ta waje da kyar, na samu na saka mukulli na datse falon.

        Na bar ta anan tana ta bugawa tana fadin “Maman Ahmad kada ki yi haka qarfin mace da na namiji ba daya ba ne, zai iya illata ki ko ma ya kashe ki. Ki bude qofar nan.”

         Usman ne ya zaro belt din jikinsa ya danko qeyata ya ce ” wuce mu je daki yau na sai na lahira ya fi ki jin dadi, gobe ko giyar wake kika sha in an ce ki sake shiga hurumin aikina ba za ki shiga shiga ba, gashi yanzu kin jawo min masifar da zan rasa aikin da nake yi nake rufawa kaina asiri.”

       Muryar mufida ce take fadin “wallahi Usman idan ka illata matar nan sai na tsaya mata a kotu an bi mata haqqinta, jada ka dauka dan matarka ce zaka zalumce ta a bar ka. Mutumin banza wanda bai san darajar mace ba. Sai na nuna maka cewar mace ba abar wulaqanta ba ce. Ka sake ta ka bude qofar nan. 

      “Ni kuwa ihu nake ina kwakwazo ina fadin “ki bari ya kashe ni din ai mijina ne.”     

      Dan ni ba shi ne yake bani haushi ba ita ce.

        Usman ya fusata ya harari jikin qofar da take ya ce ” kada ki fasa tsaya mata a kotun ki sa a daure ni tunda ke kika aura min matar. Ki fita harkar gidana kuma ki bar jikin qofata.” 

      Na yi kukan kura na maqalqale wuyan Usman na maqure shi. 

     Ina cewa “ka fada min dalilin da ya sa ka bari ‘yar iskar matar can Mufidah ta dinga daqumarka. Cin amanar taka ta zo har cikin gidana har a gabana. Yau sai dai mu kashe juna wallahi akan in dinga ganin bacin rai ka na daqumar mata.”

       Ya fusata ya banbare ni dakyar da alama shima jikinsa ya gaya masa dan har idanuwansa sun firfito saboda maqure shi da na yi .    

        Ya tunkude ni na fadi a gefe ya daga belt zai zabga min sai ga yara sun fito da gudu su na ihu su na kuka dan haka ya fasa dukana. Ya kalle su suka kalle shi sai ya yi wuf ya shige cikin dakinsa ya saka mukulli ya datse kansa.

      Wasa farin girki ni kuma a lokacin ne nawa fadan ya tashi dan daga Usman har Mufidah ba su ci banza ba. Yau sai an yi gagarumin tashin hankalin da baa taba yi ba kowa ma ba zai yi barci ba wallahi har da sauran  makwabta. 

       Dukan qofarsa nake yi da qafa da hannu kamar zan balla ina hayagaga yara na biye da ni su na ihun kuka . Yayin da Mufida da sauran maqwabtana suke bakin qofa su na bugawa.  Hayaniya ta hargitse wani  baya jin abinda wani yake cewa. A tunaninsu har yanzu dukana yake zai kashe ni.

      Wayar Usman ce ke ta ruri a yashe a qasa a falo anan ta fadi garin dambe, dan haka a dole ya bude qofar ya fito neman wayarsa.

      Na tari gabansa ina ta baloqoqo akan sai ya fada min alaqarsa da Mufidah da har za ta riqe hannunsa su tsaya su na kallon-kallo. Ya yi tsaki ya dauki wayarsa. Ya ga lambar maqwabtanmu ne Dr.Isa da Dr. Musa. Su ka shaida masa su na bakin qofar falonmu ya bude.

     Zai bude na hana shi nan ma dambe ya barke dakyar ya ture ni ya murda ya bude  

       Mufida Ansar na fara hangowa tana a gaba-gaba dan naci ba zata bar mu ba. Sai dai wannan karon ta saka hijabi akan wannan shegiyar rigar da ake yiwa laqabi da taya ni kasuwanci.

      Nan da nan suka afko cikin gidan su da matansu Safiya da Umma suka rirriqe ni suka ja ni zuwa cikin daki.

        Cacar baki ta kaure tsakanin Mufidah da Usman, sai na zabura zan fito su Safiya su danne ni su mayar da ni kan gado su zaunar.      

     Sun kasa gane hatsari da gobarar da take yunqurin qona ni wato haduwar Usman da Mufidah. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun sun kasa ganewa basu san yadda nake ji ba ne. Fadan ya koma da turanci sai na ji kalamansu kamar su na cewa juna  I LOVE YOU , I MISS YOU. Ga ta da wata zazzaqar murya mai sautin sanyi musamman idan tana magana da turanci. 

        Na dora hannu aka na sulale na kwanta akan hado na rusa kuka ina fadin ” innalilahi wa inna ilaihi rajuun.  Ku bar ni in je falon nan ba za ku gane abinda nake nufi ba.” 

     Har wani qara danne suke, dama da haguna sun riqe ni qam ba zan iya fusgewa ba.

 

WRITTEN BY: JAMILA UMAR TANKO (JUT)

NOVEL NAME: KISHIN BAL-BAL BK 1,2&3

UPLOADER:     AIHAUSANOVELS 

  DOCUMENT SIZE:         26KB

DOCUMENT TYPE:              TXT

MODIFIED DATE:      1- SEPTEMBER -2022

CATEGORY:               LOVE   STORY

PRICE:                            ₦500 

Proceed To Download Kishin Bal-Bal Book 1,2&3 Hausa Novel Document.

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Domin Karanta Littafin Sai ku Danna Inda Aka Saka Read More

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

Copyright 

If you are the right owner of this novel and you want us to remove it from our site please mail Us at aihausanovels@gmail.com

Back to top button