Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 50 Hausa Novel

Kai tsayen bakin gadon ya nufa ya kai hannu ya yaye duvet da take lulluɓe ciki, a hankali ya sauƙe hannunshi a goshinta hakan ya sa ta ɗan buɗe ido ta kalleshi sai ta mayar ta rufe, ta sake buɗewa idanunshi a kan wuyanta zuwa kan kirjinta da har saman ke a bayyane, muryarta yaji tace “Ya Saraki!”Sai ta sake mayar da idanun ta rufe, ƙarasa yaye duvet ɗin gabaɗaya yayi ya kai zaune gefenta yana kai tafin hannunshi ya shafa wuyanta da shima ya ɗan yi dumi amma ba zafi ba.”Kuka kika yi? Me ya sameki?”Shiru tayi bata buɗe idanun ba shi kuma bai daina shafa wuyanta da ya ɗauki hankalinshi sossai ba, jin yana ta da mata da tsikar jiki yasa ta kai hannu ta riƙe hannun nashi cikin wani irin murya ta sake kiran sunan nashi “Ya Saraki!””Na’am Matar masu sarauta.”Yadda ya amsan sai da ta buɗe idanunta, sunan ya shige ta har inda bai kamata ya je ba.”Mu je ki gayamin dalilin wannan kuka”Ko motsi bata yi ba, ganin ta ƙi motsawa Ya sanya hannu ya ɗauke ta chadak sai jinta tayi cikin hannunshi bai sake cewa komai ba ya fice da ita zuwa ɗakinshi, a kan shimfidadden gadon shi ya yi mata masauki zai kalleta don tunda ya ɗauketan a bazata kallon fuskanshi take tana jin soyayyarshi na shiga jini da bargon ta tayi saurin rufe idanu, bai ce komai ba ya miƙe yaje ya watsa ruwa ya sanya kayan baccin shi ya rage wutan ɗakin kan ya zo ya hau gadon ya kwanta.Duk abinda yake tana jinshi, kwanciyarshi da janyota zuwa jikinshi duk lokaci ɗaya hannunshi zagaye da kwankwasonta ɗayan a haɓarta ya furta “uhmm faɗamin”Da kyar ta iya samo kalmar “Mene?”Ta furta “Abin da ya saka Matar Saraki kuka har ya ja mata ciwon kai”Shiru tayi for seconds tsantsin rigar jikinta da kamshin dake fita daga jikinta har gashinta ya shagaltar dashi a hankali yake ɗan bin jikin nata yana shafawa ba tare da ya sake magana ba. Chan tace “Wai da gaske ku nan tun yaro na ƙarami ake mishi mata? Da gaske sarki ba zai iya zama da mace ɗaya ba?”Shiru yayi, chan ya ce “Wa ya faɗa miki wannan magana?””Kawai na ji ne a wani labari…”Murmushi mara sauti yayi kishi ne ya sakata kuka kuma ya san tabbas faɗa mata aka yi don wulakanci daga zuwanta an tarbe ta da abin da zai sakata kuka a banza, kwafa yayi bai ce komi ba “Da gaske ne kenan?”Ya ji muryarta na ɗan rawa tayi tambayar.”Shhhh ki yi bacci, za mu yi maganan wani lokaci”Dole tayi shiru, hannunshi yake ɗan bubbugawa a bayanta kaman mai rarrashin ‘yar baby har tayi bacci ya sauƙe numfashi yana saƙe-sake mai dumbin yawa har bacci ya sure shi shima a haka.Washegari ko da ya tashi sallah ya san bata yi so bai tashe ta ba, ya gyara mata kwanciya kan ya miƙe ya shige toilet yayi alwala ya fice masallaci, daga nan ya tsaya suka gaisa da su Uncle sun jima suna magana da Saleem da duk yau suke zancen juyawa, sai da gari ma yayi haske sossai ya dawo bai sameta ɗakin ba amma ta gyare tsaf ta saka turare ya tsinci kanshi da murmushi kaɗan kan ya wuce yayi wanka bayan ya shirya yana ma shirin fita ne ya ji sallamar ta.Ya amsa yana mayar da idanu kanta sai ya lumshe su ya sake buɗewa, yarinyar tana fusgar hankalinshi fiye da yadda zai misalta sanye take da wani coffee doguwar riga mai shige da material amma yana da kauri an tattare kirjin ƙasan a sake wane umbrella suna haɗa idanu ta kawar da nata don bata iya jure kallon cikin idanunshi barin ma in yana binta da mataccen kallon nan da ya tsira, gaban kujeran dake dauke da table ta ajiye mishi tray ɗin da ta shirya abincin kaman ka kwace don kyaun da yayi a ido, doya ne dafaffe da sauce na manja kana ganin kifi nasha nasha a ciki da kuma dafaffen kwai cikin Miyar, sai dafaffen plantain da ta musu wani yanka mai kyau, da tea mai kauri cikin mug sai da ta ajiye ta ɗago lokacin ya matso dab da ita.”Good Morning!”Ta faɗa har lokacin bata wani fara’a don ba wani daaɗin zuciyarta take ji ba, hannunshi na dama ya miƙa mata alamun su yi musabaha sai ta sanya nata ciki a hankali, da sanyawar da sauya hannun nashi da yayi zuwa hagunshi da fusgarta zuwa kirjinshi da zagaye kwankwasonta da yayi da hannunshi na daman duk lokaci ɗaya, kirjinta da nashi suka haɗe ta zaro idanu tana kallon shi shima cikin idanunta ya zubawa idanu sama da seconds biyu kan ya furta “Good Morning Caramel Queen..!”Ya faɗa yana bin smooth and silky skin ɗinta da wani irin kallo, kanta ta mayar ƙasa.Ya zame hannunshi dake kwankwasonta ya kai kan fuskarta da ta sako ‘yar gashi kaɗan gaba ya ɗan shafa gashin da yatsa ɗaya yana mayar dasu gefe ya furta “Ya ciwon kan?”Ta kalleshi ta kawar “Alhamdulillah na ji sauƙi””Har yanzu fushin ne?”Tayi shiru, ya ɗago haɓarta ya hura mata iskar bakinshi ta lumshe idanu, tana jin tender nd soft palms ɗin shi na wasa da tafin hannunta.”Talk!”Ta sauke nannauyar numfashi tana jin salon shi na kasheta, zamewa tayi tana zare hannunta “Abincin ka na sanyi”Haka kawai he doesn’t like this silent treatment of hers.Zama yayi bai ce komai ba ta tura mishi abincin ya fara ci da bismillah ta juya ta fice, bayanta ya bi da kallo har ta rufo kofar ya sauke numfashi a lokaci daya yana tunanin wanda ya fada mata batun zarah shi da ko za’a shaƙe shi ma bai san kamannin zarahn a idanunshi ba, salon kishin ta kuma ya tafi dashi har yana dan murmushi wai ita tana fushi hmmmMisalin karfe sha ɗaya dukkansu suka fito don sallama da su Uncle Musa da zasu koma da Saleem, ita jannah na nan akwai wani taron Matasa da aka haɗawa Yariman na Matasa kuma Ciroman fombina wanda zallar al’ada suke son fitarwa a wannan gagarumin taron za’a yi shi a jibi sai gata sai ta wuce itama ta bar Abeeha da har sun fara batun neman transfer don Rayyan ya rantse ba gidan da zata je ta zauna kuma ba zata zauna hostel ba.Tun tahowarsu ya zuba mata idanu magana yake da Afeefah matsayin ɗan uwa da ‘yar uwa yana kuma bata ƙwarin gwiwar zaman cikin gidan amma tahowar Aisha ya ɗauki hankalinshi har bai san kuma me yake cewa ba, Afeefah ta juya ta kalli wacce yake kallo haka ta saki murmushi ta juyo tayi waving “Ya Saleem ya dai?”Cike da dariya shima ya ɗauke kai ya mayar kanta “An tafi da ni ne, kanwata za ki taya ni yaƙi”Dariya tayi lokacin Rayyan ya ƙaraso inda suke har lokacin Afeefah na murmushi yace “Me yayi muku daaɗi haka?”Idanunshi a kan matar tashi da murmushinta ya tafi dashi ainun.”Sirri tsakanin yaya da kanwa”Inji Saleem, ta ɗan waro ido ta kalli Saleem tace “Gwara ka kiyaye aka hana ka babu ruwan Afeefah””Da fa gaskiyarki, Yayanmu barka da fitowa”Ya juya yana miƙawa Rayyan hannu da kaman yanzu ne suka haɗu cikin ladabi.Murmushi Rayyan yayi yana girgiza kai wanda ya shagaltar da Afeefar a kallonshi don murmushi ne da bata taɓa gani yayi ba, murmushi na mishi kyau ainun barin ma fararen hakwaranshi da suka bayyana suka haske fuskar tashi.Gaisuwar da su Aisha ke musu ya sa ta dawo daga duniyar shagaltuwarta sai dai ganin kallon da zarahn ke yiwa Rayyan ya sa taji duk mood ɗinta ya chanza, shi kam Rayyan ko kallonsu bai yi ba ya amsa Uncle Musa ke yiwa Saleem magana akan su wuce kafin su yi missing flight dole duk suka yi wurin motar ya dubi Afeefah”kanwata za mu yi magana fa”Ta gyaɗa kai kawai suka yi sallama suka fice cikin motocin alfarma wanda da Rayyan suka tafi, su matan su uku suka yi sashenta suna ‘yar hira yayinda Zarah da Aisha suka nufi ɓangaren Ammi.Rayyan bai tashi shigowa gidan ba sai yamma sossai, a parlor ya zauna ta kawo mishi ruwa ya sha hankalinshi duk a na kanta a koyaushe dressing ɗinta na kashe shi don yanzu fitted atampha ne a jikinta tayi ɗaurin ture ka ga tsiya da ya zauna mata tana kokarin ɗage tray ɗin gabanshi tace “Abinci fa?””No sai anjima am not Hungry”Kai ta gyaɗa ta nufi kitchen shiganta ba jimawa tana ba kuyangin ta umurnin aikin da za su dan yi mata su yanke yanke na shirya mishi abincin daren bayan ta gama ta nufi fitowa daidai Gaabɗo ya shigo da wani paper bag ya zube a ƙasa”Ranka ya daɗe wannan saƙo ne daga Gimbiya zarah tace a baka”Da wani irin hanzari ya ɗago ya kalli kofan kitchen ɗin, bai taɓa jin tsoron wani ya ga ko yaji abinda babu daaɗi ba irin yanzu da yaji duk duniya tashin hankalinshi shine taji wannan zance.”Fita dashi, kar ka kara karɓan abu da sunan sako zuwa gareni matukar ba matata bace ko mahaifina””A gafarceni ran…””Fita nace!!”Da ɗan karfi yayi maganan da sauri Gaabɗo ya fice.Ya tashi shima gabaɗaya a parlorn ya wuce ɗakinshi a lokacin ita kuma ta fito hawayenta na zuba, Jannah da Abeeha dake daga chan jikin ƙofan ɗakinsu suka yi dariya.”Allah ya sa ta ji, don hakan ne kawai zai kawo musu kusanci idan tana kishin nan tana fusgar hankalinshi ne kanta”Jannah ta faɗa Abeeha tace”Amma kam za ki sakata kuka a banza Adda Jannah… Allah ka yafe mana baiwar Allah Zarah””Eh gwara tayi kukan ta nemi mafita wa zuciyarta, ita kuma zarah dama kar tayi tunanin samun matsuguni a ran Ya Rayyan don shi ba namijin da zai iya da soyayya bane muddin Afeefah ta mishi dabaibayi a zuciya”Hirarsu suka cigaba da yi cikin nishadi don sun tabbatar ko Afeefah bata nemi Rayyan ba shi a yanzu ba zai jure nisantarta ba.Ɗakinta ta koma ta zauna bakin gado babu abin da bata saƙa ba kuma ta hana kanta kuka, dole ta yi me ɗungurungun wai haihuwa da hanji! Dole taje ta ji shin yana sonta ko da gaske baya sonta wata zai aura…Kiran Sallar Magrib ya sa ta miƙe ta gabatar da sallah don ta yi wanka tun rana, kitchen ta nufa ta haɗa mishi macroni da gasashen chicken breast tana cikin yi aka kira isha taje ta gabatar kan ta dawo ta ƙarasa taje ta shirya mishi a dining a yanzu hijab ne jikinta har ƙasa, daidai yana shigowa take cewa Sa’ade “Ki tattare kitchen nan please ban yi shafa’i da wutiri ba bari na gabatar”Bata ma kula da Shigowar tashi ba don ciki ciki yayi sallama ta wuce ɗakinta ya bi bayanta da kallo hannayenshi zube cikin aljihu, a natse ya ƙarasa dining ɗin daidai Fitowar Abeeha da Jannah suka mishi sannu suma suka zauna suka shiga cin abincin, ganin ta jima ya sa ya dubi Abeeha”ƙira min Afeefah”Ta miƙe ta nufi ɗakin ta samu ta idar tana zaune ne kawai, jin yana kiranta ta miƙe ta nufi parlorn zuwa dining.”Zauna ki ci abinci”Ganin fuskarshi ba fara’a yasa ta zauna ta zuba abincin kaɗan tana ci kaman bata so, karamin kwalin da bai jiman nan ba Gaabɗo ya zo ya ajiye mishi ya tura mata.”Na gode”Ta faɗa tana jan paper bag ɗin ta buɗe ciki sai ta ga waya ne dall a cikin kwali Iphone 17 Air ce, bata nuna zumudi ko farin ciki sossai ba sai ma su Abeeha ne ke ta santin wayan ta sake ce mishi ta gode ya bi fuskarta da kallo.Bayan sun bar dining ɗin su sa’ade suka zo suka tattare wurin tsaff.Ɗakinta ta koma ta bar su Abeeha da wayan a parlor suna mata setting ta yi wanka, ta duba wani orange and Black nigty silk ne mai hannun shimi ya bi jikinta sossai don Black lace ɗin ya kara haske kayan, hijabi ta saka a kai ganin yadda ko motsi tayi komai na jikinta na motsawa cikin kayan musamman hammatan dake bayyana tudun na shanunta time ta kallah almost nine.Fitowa tayi Abeeha ta bata wayan don jannah ta gudu waya da mijinta a ɗaki, ɗakinshi ta nufa kai tsaye da sallama ta kutsa kai rike da wayan a hannunta don tana so su yi magana.A tsaye take bisa kanshi yana kishingide cikin tattausan Italian cushion a hankali yake ɗan taune lip ɗin shi kaifaffun idanunshi zube bisa kanta”am…am just fed up, ba na tunanin zan iya cigaba da zama a haka i’ve had enough na san ba ka aureni ba ne saboda kana so na, ka aure ni ne out of pity da kuma am… Mammi. Muddin na cigaba da zama a haka zan iya mutuwa a yanzu bana jin zan iya cigaba da kasancewa matsayin ma..matar k…””It’s pretty!”Ya furta chan ƙasa cikin deep voice ɗin shi da ya sa ta kame, duk maganar da take yi ba idanunta yake kallo ba lips ɗinta da take motsa su a hankali ya ƙurawa lumsassun idanunshi yana wani kashe su yana buɗewa…”W…whatt?””Ur lips… They are pretty”Ko kan ta farga ya yunkura ya fusgo hannunta guda ta tafi gabaɗaya kanshi tayi masauki a kan kafafunshi fuskarta ya sauƙa kan wuyanshi a tare suka ɗauke numfashi. A ɗan razane ta shiga mutsu-mutsun sauƙa ya sa hannunshi na hagun ya zagaye kwankwansonta yayi pinning ɗinta jikinshi, na daman ya sanya ya zare mata hijabin idanunshi na sauka kan jikinta, ya bi damtsen hannunta da yatsa biyu cikin wani salo har cikin tafin hannunta kar yayi baya ya riƙe wrist ɗin hannun ya ɗora saman heart ɗin shi da ke beating very very fast. A take nata ma ke ƙoƙarin sauya bugu numfashi na neman kwace mata idanunshi a saman fuskarta kaman zai tsagata da su ya furta “saƙon zuciya baki ne yake furta wa sai dai kuma wani lokacin yana iya fin ƙarfin harshe ya bar wa idanu nunawa, Lil angel saurari bugun zuciyata ki kalli tsakiyar kwayar idanuna na tabbatar sun isa sanar miki da cewa Ryan na ƙaunarki ba zai iya rayuwa babu ke ba, kuma yana tsananin buƙatar ki, you are like a Light in my darkness. You are not just my wife Afeefah you are my safe space, my solace…you are the key to my salvation…”Wani irin birkicewa ta nemi yi saboda nauyin zantukan nashi ga idanunshi masu kaifi da yake zagaye fuskanta da su yana wani lumshe su, maganar ma har cikin ɓargonta take ji saboda yadda muryarshi ke fita very deep nd husky.”A haka kike cewa in rabu da ke? Uhmm? Ki fahimta rashin ki a gareni masifa ne Afeefah”Ƙuri tayi da idanu kalamanshi suna samu matsuguni daram a cikin zuciyarta, sakinta yayi ta koma zaune kawai akan kafar tashi, kanta ta mayar ƙasa tana neman dulmiyewa tsabar yadda kalaman suke zuwa mata a bazata Rayyan ne fa gabanta shine yake fitar da waennan tsadaddun kalmomin daga cikin bakinshi?Anya ta ji da kyau? Ko dai yaudararta yake shirin yi ganin irin kallon da yake mata ba tare da ya sake furta uffan ba, shi ne zai so mace kamarta? Sake ɗago kai tayi ta kalleshi suka hada idanu. Sarai ya san kokonto take akan kalamanshi kuma hakan bai mishi daaɗi ba, ya kai hannunshi ya kama haɓarta ya ɗago fuskarta yana kallon cikin idanunta cikin karantar yanayinta bai furta komai ba.Idanunta ta mayar kasa zuciyarta na bugawa da tsananin karfi har tana jin kaman cikin ko wani lokaci zuciyarta zai iya yin bindiga ta mutu, amma shi ko a jikinshi kuma fuskar a kame yake magana idanunshi na yawo bisa jikinta yace”Idan kuma kin matsa da sai na rabu da ke, zan iya yin hakan ne kawai under 2 conditions Afeefah sai ki zabi wanda kike gani ya fi miki sauki ni kuma i promise zan rabu da ke!”A razane ta dago ta zuba mishi idanunta da har sun fara zubar da kwallah lips dinta dake rawa ya bi da kallo kan ya dauke idanu yana lumshe wa ya budeDa ma na sani baya so na tunda gashi zai iya rabuwa da ni amma me yasa nake jin zafi?Meyasa nake jin kaman karshen rayuwata ne ya zo? Abinda take ayyanawa kenan a ranta..Da kyar ta iya furta”Menene conditions din?”Tana ji gwara ta sani gwara ta hakura ta nemi daidai ita.”It’s either ki mayar da lokaci baya ki goge ranar da na fara sanin ki a rayuwarta don daga ranar ne zuciyata ta fara bugawa da Ƙaunarki ko kuma ki tsaga zuciyata ki sauya min da wata zuciyar don wannan ta jima tana sakar da jini mai dauke da kaunarki zuwa ko wani sashe na jiki da jijiyoyina….”Baki kawai ta saki hawayenta na zuba sossai da sossai, ya kai hannu ya janyota suka samu kusanci ainun, ya ɗago babbar yatsarshi ya shafa soft lips ɗinta dake ta rawa idanunshi na cikin nata yayi leaning a hankali ya ɗora bakinshi kan nata zuciyoyinsu na amsa baƙon yanayin nasu da karfin gaske…….

Back to top button