Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 41 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

    FORTY-ONE📍

           Aka dauko goro da sauran abubuwan aka matso dasu kusa lokacin masallacin ya cika makil da jama’a, gadan gadan aka shiga hidimomin daurin  aure kowa fuskarsa dauke da farin ciki zaa hada sunna, gyaran murya sheikh Abdallah yayi sannan ya fara da bismillah…….

        “A’uzubillahis-sami’ul aleem, minash-shaydanir rajeem, bismillahir rahmani raheem, allahumma…”

Kamar wanda aka mintsina sheikh jabbar ya taso ya dawo kusa da sheikh Abdallah, kasa yayi da murya yace;

     “Ya sheikh ya ake shirin daura aure ba maganar waliyyai”……

Dakatarwa yayi ya dago ya kalli sheikh jabbar, cikin dan rudani yace;

     “Subhanallah! Wallahi na sha’afa saboda labarin da suka bani sheikh, wayennan yara ne masu tinani kwarai”…….

        “Wani labari sheikh?”…..

     “Aure zasuyi saboda suna tsoron afkawa zina, kaga kuma a zamaninnan sai yara masu tsoron Allah ne zasuyi wannan tinanin shiyasa suka burgeni suka shiga zuciyata”…….

Tsit masallacin yayi saboda kowa so yake yaji dalilin dayasa aka dakatar da daurin auren……

Kallon khaleel sheikh Abdallah yayi yace;

      “Bawan Allah ina waliyyanku?”……

Kasa da kai khaleel yayi yace;

      “Babu su a kusa dake baa kasarnan muke ba amma sun san da maganar auren”…..

Murmushi yayi yace;

     “Yanada kyau a samu waliyyi koda kuda dayane”…

Karab fatima zainab tace;

      “Dole saida waliyyi zaa daura aure?”……

Kallonta yan gurin suka hauyi suna murmushi, su dayake larabawa masu nuna affection dinsu a fili sai sukayi tinanin san da take masa ne yasata kasa shiru……

      “Ba dole sai da waliyyi ake aure ba amma saboda yanayin rayuwa yanda komai ya zama sai a hankali yanada kyau a samu waliyy koda a cikin mahaifa ko yan uwa ko makusanta, da zasu zama shedu gudin bijirowar wani abu daga baya dukda ba fata ake ba”…….

      “Mudai sheikh ka taimaka kawai a daura mana auren wallahi bamu da kowa a kusa”…..

Cewar khaleel kamar zeyi kuka…….

Murmushi sheikh jabbar yayi ya dafa kafadar khaleel yace;

      “Gwara ku samo koda mutum daya ne habibee”…

Dan shiru khaleel yayi yana tinanin yanda zasuyi, kawai sai sameer ya fadomasa a rai, ya tina yanda sukayi da sameer akan zeyi supporting dinsa akan komai, yanzu this is the best time for that, murmushi yayi yace;

     “Toh sheikh, Insha Allah akwai wanda zezo daga Nigeria”……..

     “Masha Allah masha Allah”…..

Sheikh Abdallah ya fada yana kara yabawa da hankalin yaran…. Nan aka shiga sa musu albarka aka musu addu’a sosai……. 

Mikewa khaleel yayi yace ta tashi su tafi…….

Har sun kai bakin kofa sheikh Abdallah ya kirasu, dawowa sukayi suka sameshi, nuna inda aka ajye sadaki yayi yace khaleel ya tafi dashi tukun, girgiza kai khaleel yayi yace a barshi a gurinsa saboda gobe zasu dawo zuwa gobe, ajyewa akayi kamar yanda ya bukata sannan suka sake sallama dasu suka fita……… 

Kamar jira fatima zainab take su fita daga masallacin tace;

     “Yanzu shikenan ba zaa daura aurennan yau ba?”

Kashe mata ido daya khaleel yayi cikin tsokana yace;

      “Haka kika matsu a daura auren?”…..

Itama kashe masa ido tayi tana dariya tace;

     “Sosai ma”…..

    “Karki damu akwai wanda zan kira ya mana wakilci, zuwa gobe ze karaso Insha Allah”…

    “Ohk Allah ya kaimu ”……

Hannunta ya ruko suka fara tafiya yana fadin;

   “Kinga sai a daura aure musha amarcinmu sosai, kai can’t wait wallahi”…..

Ya fada yana dan matsa mata yatsunta cikin tausasawa…..

Kwace hannunta tayi ta rankwasheshi akai, fuska dauke da fara’a tace;

     “Koba amarci ba”…..

Dafe inda ta rankwasheshi yayi, yana kallonta kamar ze hadiyeta yace;

     “It’s painful but I love it”…

Dariya tayi tace;

     “Idan na fasa kan you’ll know that you love it”…

     “Serious I love it, honestly I love the new you wifey, I just love everything about the new you”….. 

Wani killer smile ta mishi da yaji kamar yayi melting a gurin yace;

      “If loving you was a job, I’d be the most deserving, dedicated, and qualified candidate. In fact, I’d even be willing to work for free! I love you countlessly!”….

Murmushin dayafi wanchan tayi tace;

    “If someone asked me to describe you in just two words, I’d say “Simply Amazing.”…..

Murza hannunta yayi yasa idonsa cikin nata yace;

     “You are a better part of me and my second half. Without you, I would probably be lost. You complete me, and right now, I could not wish for a better life partner.”…….

       “Hey you’re driving me crazy!”……

Ta fada tana fashewa da dariya”……

Dariyar yayi shima yace;

      “I don’t mind you being crazy but crazily in love with me hhh”…….

Jan hancinsa tayi tace;

    “My feet will walk with you anywhere you want.I promise!”……..

Hannunta yayi pecking yace;

     “Ba zan taba barin ki ba, saboda ke ce -rayuwata. Soyayyarmu tamkar babban lambu‘ ne ma’fi girma a duniya.’ Ina sonki sosai masoyiyyata.”

      “Ina sonka nima darling khal”……

Saida sukasha soyayyarsu sosai sannan suka koma gida, zubewa sukayi a parlor suka cigaba da soyewarsu kamar ba gobe……

      “Wifey kinga shaukin son ki ya mantar dani in kira sameer, let me call him now”…..

Khaleel ya fada yana dubanta cikin so da kauna…

     “Waye sameer?”….

    “Wanda ze wakilce mu”….

   “Okay, call him”

Sameer dake kwance abun duniya ya ishesa yaga kira da international number, dauka yayi da sallama…..

     “My guy how far?”…..

Ya tsinci muryar khaleel na fadin haka……

Tashi zaune yayi yana gyara zama yace;

      “Mutumina naga ka kirani da international number, yaushe kabar kasar?”…….

    “Ina dubai fah!”….

    “Dubai kuma? Ta samu ne?”….

   “Babban samuwa kuwa! Gani ga wifey muna shan soyayya!”….

Zabura sameer yayi ya mike da sauri, murya na rawa yace;

     “Me kace? Kaganta ne?”….

   “Yes naganta har mun bar kasar tare, anything?”..

Khaleel ya tambaya dan yaji alamun zaburar da sameer yayi……

     “No! it’s nothing, I was just happy ka ganta so easily, ni ina nan ina tayaka nemanta”…..

Sameer ya fada cikin kokarin kare kansa….

     “Kaidai bari, I need your help again, bansani ba ko zaka iya min?”…….

    “Anything for you my guy”….

     “Thank you, zaka iya zuwa ka samemu a dubai?”..

Wani mashahurin farin ciki ne ya lullube sameer da besan sanda yace;

      “Ba dole ba, ai dole in zo”……

Dan jimm khaleel yayi sai kuma yace;

    “Aurenmu zaa daura nida wifey and there’s the need of someone to be present, shine nake so kazo dan Allah”…….

Zaro ido sameer yayi kamar khaleel na ganinsa yace;

     “Aure kuma?”……

    “Yes sam”….

Ya tabbatar masa…

   “Meyasa bazaka bari a daura a naija ba?”….,

    “Saboda daddy bayasan in aureta yanzu and I really love her you know shiyasa muka gudo muyi aurenmu”……..

    “Ok nagane, bakada case zanzo goben Insha Allah, bari na duba available flight zan kiraka”…..

    “Yauwa thanks a lot”….

Ya fada yana kashe wayar…..

Gumi ne ya shiga karyowa sameer  tin bayan khaleel ya kashe waya, ya mike da sauri ya fara zarya a dakin kamar wani zararre, fadi yake “aure kuma! Aure! No! It’s impossible!”, sosai maganar auren ta daga masa hankali, yama zaace yana zaune khaleel yaci galaba a kansa bayan duk wahalar daya sha da kuma wanda yake kan sha, wallahi baze yiwu ba…… Haka yayita kai da kawowa har zuciyarsa ta kawo masa wani shawara da yake tinanin shine daidai, mafitar shine idan yaje ya zubawa khaleel poison a abinci ko a lemo ya kasheshi ya dauketa su tafi suyi aure, baze yiwu ace yana raye yaga khaleel ya aureta bashi ba……..

         Sosai abinda ya gani ya daga masa hankali amma a haka baka ce ba, sosai mamaki ya kamasa ganin yanda mutane suka zama abun tsoro a duniya, ace alhaji habibu of all people ne da wannan aika aikan? Mutumin dayake wa kallon uba bayan dad, ashe mugune haka? Toh amma wa suke magana akai haka? Dan ko waye tabbas meshi yana cikin hatsari, da kuma ze gane waye daya taimakeshi, sai a lokacin ya gane dalilin dayasa akayi kidnapping dinsa, wato sun gano flash dinsu na tare dashi shine sukesan ganin bayansa, toh amma meyasa Alhaji Ibrahim yasa a kasheshi? Ko bakinsu daya da alhaji habibu ne?….. Wani murmushin gefen baki Deen yayi yace;

      “Zakuci ubanku!!!”…….

    “Toh ko ina sameer yake?”….

Ya fada kamar shida wani ne a gurin, sun dade basu hadu da sameer ba tin bayan yace mishi yarinyar bata wajansa, yanzu ko dole ya nemo sameer dan ta hanyar sameer ne ze gane duk wani abu dayake san ganewa………

A system ya dauko number sameer ya sata a sabuwar wayarshi ya shiga kiransa……

Sameer da har lokacin be dena kaiwa da kawowa yaji wayarsa na ringing, ba bata lokaci ya daukota dan shi mutum ne me daga ko wata waya idan an kirasa, ga mamakinsa sai yaji muryar Deen, muryar da be taba tinanin ze jita nan kusa ba……..

      “Ina ka shiga ne sam?”….

Ya juyo muryar Deen for the second time bayan maganar farko da yayi be kulasa ba saboda mamakin daya shiga……

     “Kai zan tambaya boss, na kira wayarka harna gaji”…..

     “Yeah I lost my phone, ya ake ciki ne?,kai kaki barin naija ko?”………

     “Hmmm ai gashi zan bari dan dole yanzu, dubai zanje”…..

    “Me zakaje yi a dubai kuma?”….

   “Wani case zan kashe!”……

   “Ikon Allah! Ya labarin budurwar ka kuwa?”……

Deen ya tambaya dukda yasan baze samu information akanta a gurin sameer ba tinda yasan khaleel tabi suka gudu……

Nan da sameer yaji an tabo mishi inda ke mishi kaikayi, cikin kunar rai yace;

       “Akan haka zanje dubai ai, tana tare da dan iskan chan, kaji wai aure zasuyi shine sukeso na zamar musu waliyy?”…….

Gabadaya Deen yaji jikinsa ya fara rawa, wayar ma saita nemi ta zame daga hannunsa, ashe dagaske sun bar kasar? Wannan wata irin mahaukaciyar yarinya ce zataje a daura musu gantalellen aure da wanchan shashashan, inko hakane he needs to do something, kasa controlling kansa yayi cikin daga murya kamar ze fasa wayar yace;

       “A dubai ina suke sam? Are they living together? Idona idon yaran chan saina kasheshi wallahi! I must kill him!!”…….

Wani iri sameer yaji yanayin yanda Deen ya zuciya da abinda yake furtawa, ya maze yace;

      “Relax man! Meya hadaku haka? Nima so nake na kashe shi”…..

Cewar sameer yana jindadi ya samu partner din ganin bayan khaleel…

     “Ya shiga gona ta sam, ya shiga gonata, in ban kasheshi hankalina baze kwanta ba!!”….

      “I understand boss, bansan ina suke a dubai yanzu ba but karka damu zan kiraka inyi updating dinka duk yanda ake ciki”…….

       “Ka tabbatar ka kirani sam! Ka tabbatar ka kirani!”……

Deen ya fada yana kashe wayar har lokacin kuma yanajin wani daci a ransa, abu dayane ke damunsa akan zuwa dubai din da sukayi, yasan dole a guri daya suke maybe ma daki daya, wani abu ne yaji ya shake mishi wuya yaji bazai iya jira sam ya kirasa ba gwara yaje dubai din ya nemesu duk inda suke yaci ubansu duka daga ita har shi, sai ya tabbatar yayiwa khaleel jina jina sannan ze kyalesa, itako sai ya babballa kafar bin saurayi ya kuma sumar da ita, be damu ba koda zeyi jinyarta daga baya gwara ya samu yaci ubanta tukunna, in banda rashin zuciya daya fara samun shi yanzu wai har sawa yayi ake mata exam gudun kartayi losing semester amma wawuyar tana chan tare da wani gardi saboda ta rasa mafadi…. 

Abunka da masu hannu da shuni ya dauki wallet dinsa da tracker kawai ya tafi airport, zuwa yayi aka mishi visa a take ya siya ticket sai dubai…………..

           Cikin tashin hankali kamar jiya khaleel ya sake rushing dinta zuwa asibiti saboda wani matsanaicin ciwon mara data tashi dashi , allura aka sake mata kamar jiya aka daura mata drip khaleel na zaune sai sambatu yake yana fadin;

     “Wifey dan Allah karki mutu ki barni! Dan Allah karki mutu bamuyi aure ba, kika mutu nima mutuwa zanyi, ki taimakeni ki samu lafiya, ina sanki sosaiiiiiii my heart”………

Ganin sambatun nashi yayi yawa  yasa Doctor cewa ya yaje ya samo mata abinda zataci kafin ta farka…..

Fita yayi da sauri ya nufi hanyar restaurant din asibitin, yazo daidai harabar asibitin yaci karo da Abby dake dan tattakawa kamar jiya, da sauri ya karasa inda yake ya tsuguna har kasa yana gaishe shi……..

Amsa masa Abby yayi cikin faraa yace;

     “Yana ganka da sassafe kuma, na zata kun tafi tun jiya”…..

     “Eh mun tafi abby, jikinta ne ya sake tashi yau da safe shine na dawo da ita”……

Cikin tausayawa Abby yace;

     “Subhanallahi Allah ya bata lafiya”….

Cikin sanyin jiki khaleel yace;

     “Ameen Nagode Abby”….

    “Ina zakaje ne haka naga kanata sauri da’na?”……

Abby ya sake tambaya…..

A nitse khaleel yace;

     “Zanje restaurant in samo mata abinda zataci ne kafin ta tashi”…..

     “Okay, idan ka dawo ma shiga tare in duba ta”….

A ladapce khaleel yace;

     “Toh Abby, nagode”……

Sannan ya karasa restaurant din, abubuwa kala kala ya siyo mata dukda bashi da tabbacin zataci, akayi packing a wani katon box  sannan ya fito daga restaurant din……

Kamar yanda sukayi da Abby haka ya samesa suka jera suka nufi amenity ward din da aka kwantar da ita………..

Da sallama dauke a bakinsu suka shiga ward din khaleel na gaba Abby na biye dashi a baya, tana bacci har lokacin bata farka ba, addu’oi sosai Abby ya mata hakan kuma ba karamin dadi yasa khaleel yaji ba, sai yaji mutumin ya kwanta masa a rai sosai…….

 Bayan sun shafa addu’ar Abby ya kalli khaleel cikin son gano  wani abu daya daure masa kai yace;

     “Sannu da kokari my son, tin jiya kai kadai ka keta jinya”……

Da zuciya daya khaleel yace;

      “Bakomai Abby, in banyi ba wa zeyi? Bamuda kowa anan”

Murmushinsu na manya Abby yayi yace;

      “Bangane ba? Kana nufin kaida itane kawai anan?”…….

     “Eh mu biyu ne kawai”….

     “Allah sarki, amma meyasa kuke zaune tare tinda baa riga an daura aurenku ba”…

Sosa kai khaleel ya hau yi yana fadin;

       “Eh amma ankusa Abby, da jiyama an daura matsala aka samu”……

     “Matsala kuma? Wace iri? Shine kuma ba gayyata bayan nace a gayyaceni”…..

      “Ka gafarceni Abby rashin number wayarka yasa ban kira ka ba”….

   “Allah sarki ka samin number ka yau”….

    “Toh Abby”….

Gyara zama Abby yayi akan kujerar dayake yace;

      “Baka fadamin matsalar da aka samu ba da’na dan ni na dauke kamar dan dana haifa”……

Cikin sanyin murya khaleel yace;

     “Ance sai munzo da wani namu koda mutum dayane”……

Gyada kai Abby yayi cikin rashin fahimta yace;

     “Bangane ba? A ina zaa daura auren da?”….

    “Anan zaa daura Abby, already nayi magana da wani friend dina yau ze karaso”……

Cikin mamaki Abby ya kallesa jin yace friend dinsa bama mahaifinsa ko kanin mahaifinsa ko wnai dan uwa ba……..

Khaleel ganin Abby yayi shiru ya sashi gane katobarar dayayi yana nema ya tona musu asiri, cikin san gyara maganarsa yace;

      “Ina nufin dan uwana zezo”….

Murmushi me ma’ana Abby yayi yace;

     “Idan bazaka damu ba zamu iya fita muyi magana?”……

Dan jimm khaleel yayi yana tsoron maganar da mutumin ze masa amma haka kawai yakejin zuciyarsa ta aminta dashi, daga kai yayi yabi bayan Abby da har ya fara tafiya……

Garden din hospital din suka nufa suka samu guri suka zauna…….  

Dafa kafadar khaleel Abby yayi cikin muryarsa me cike da Kamala yace;

     “Tinda na ganka kashiga raina, bansan meyasa ba amma jinka nake kamar dan dana haifa”……

Cikin jindadi khaleel yace;

     “Nagode sosai Abby, nima Insha Allah zan maka biyayya kamar mahaifina”……. 

     “Masha Allah, Allah ya maka albarka da’na”….

           “Ameen Abby”…….

Gyaran murya abby yayi ya fuskanci khaleel yace;

      “Meyasa bazaa daura muku aure a chan gida ba?”……

Dan shiru khaleel yayi yana tinanin ya fadamasa gsky ko akasinta, saidai kuma yanda yakejin mutumin aransa babu abinda ze iya boyemasa…..

A hankali yace;

     “Cewa akayi bazan aureta ba shine muka gudo muyi aure”…….

Zaro ido abby yayi cikin jimami yace;

     “Kuka gudo kuma? Wayace bazaka aureta ba?”….

      “Mahaifina!”…..

Numfasawa Abby yayi sannan yace;

      “Kasan fa hausawa sunce abinda babba ya hango yaro ko ya hau tsani ba lallai ya hango ba, kasan dalilin dayasa mahaifinka kin yarda ka aureta?”….

Cikin bacin ran daya tasowa khaleel lokaci daya tuno yanda sukayi da daddy yace;

     “Cewa yayi bata da tarbiyya bayan a gidanmu ta tashi, tin tana karama kuma aka min alkawarin aure da ita sai yanzu yace kuma bazan aureta ba? Wallahi bazan yarda ba”……

Murmushi Abby yayi yace;

      “Yaro yaro ne, ka kwantar da hankalinka babu wanda yace bazaka aureta ba”……

Cikin farin ciki khaleel yace;

      “Yauwa nagode abby”……

Shiru ne ya biyo baya kowa da abinda yake tinani, shi abby a matsayinsa na babba yasan dole akwai abinda yasa mahaifinsa ya hanashi auren yarinyar musamman yanda ya bashi labari iyayensa ne suka mata tarbiyya, shi kuma khaleel tinani yake ko ya roki abby ya zama waliyyinsu da akace su kawo tinda shi babba ne sai anfi saurin yadda dashi akan sameer…….  

       “Abby ko zaka iyamin wani alfarma dan Allah?”…

Ya tambaya a darare……

     “Ina jinka da’na, in befi karfina ba meze hana in maka?”…..

    “Insha Allah befi karfinkaba Abby”….

    “Toh Allah yasa, ina jinka”….

Wani gauran ajiyar zuciya khaleel ya sauke sannan yace;

     “Dan Allah ka taimaka ka zama waliyyin mu a samu a daura auren mana aure yau”….

Murmushi me kayatarwa Abby yayi yace;

     “Au dama itace alfarmar da kakeso ka keta kame kame? Toh karka damu ka dauka andaura aurennan, bama iya ni ba zamuje duka da mutanena”…..

Khaleel besan sanda ya rungumesa ba yace;

      “Dan Allah dagaske Abby? Kai amma naji dadi wallahi”….

Daidai lokacin kuma wayar sameer tashigo mishi, sharewa yayi ganin da number Nigeria ya kirasa means har lokacin be tawo ba auren da zaa daura anjima kadan, yaga kawai gwara ya kyaleshi tinda ya samu wanda ya fishi, sai yayi blocking numbersa kawai for the mean time…..

      “Sosai ma kuwa! A wani masallaci zaa daura auren?”……

Cikin zumudi khaleel yace;

     “A Grand Bur Dubai Masjid zaa daura”…

Murmushi Abby yayi yace;

     “Ko shekaranjiya sheikh Abdallah yazo ya dubani, dayasan na sanka koshi ze iya maka wakilci, ka kwantar da hankalinka, ka dauka an daura aurenku angama!!”……

Back to top button