KANA SON A AMSA MAKA ADDU’ARKA A LOKACIN ƘUNCI KUWA?.
–
“Duk wanda yake son ya samu biyan bukata a lokacin da ya shiga cikin tsanani, to dole sai ya yawaita biyayya ga Allah maɗaukakin sarki da kuma nuna gajiyawarsa zuwa ga Allah ɗin a lokacin da shi bawan yake cikin halin yalwa”
–
“Idan kana son a duk sanda wata matsala ta addabe ka sami sauƙinta a gurin Allah maɗaukakin sarki bayan ka riƙoshi, to lallai ka yawaita yin addu’a a lokacin da kake cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, hakan shine zaisa Allah yayi gaggawar amsa maka addu’arka a lokacin da kake cikin ƙunci”
–
“Manzon Allah ﷺ, yace: duk wanda yake son Allah ya amsa masa addu’arsa a lokacin kunci da damuwa, to lallai ya yawaita yin addu’a a lokacin da yake cikin aminci”
صحيح الجامع 6290
–