Uncategorized

Matar Makaho Part 9 Hausa Novel

MATAR MAKAHO

Chapter 9

Wai yarinyar tana d’auke da ciki shiyasa sukeso na rufa musu asiri na aure ta.

Sosai nayi mamaki kuma zuciya ta takasa Aminta akan zancen cikine kawai ba, tunda yaran masu kudi da yawa suna cikin shege Amma ba’a  bawa talakawa saini MAKAHO sam nakasa yarda.

Dana matsawa bappa da tambaya ma cemin yayi koh naki koh naso sati mai zuwa d’aurin aure 

Harga Allah banso auren ba sam,  don inaji a jikina ba batun ciki bane, imma cikin ne taya za’ayi  a d’aura aure da ciki a jikin budurwan kenan, koh an zubar?karshe fa akafi karfine kafun sati d’aya  ba wanda   baisan zancen auren mu ba saidai sam ba wanda yasan dalili kuma duk wanda yaji batun auren saiya digawa auren ayar tambaya

Amma ke sumayya menene dalilinki na aure na?

“Auren ka,   ina ma na sanka kajimin mutumi fa” ?ta fad’a cikin kuka sosai abin ya mata zafi watoh bayan auren kaskanci da akaso mata har b’atata akayi a wajen mijin don aga abinda yafi wanda suka sata😭muni

Sumayya nifa tambaya  kawai nayi kuma abinda nayita gujema kenan,  kika ga nake gudun fad’a  miki gaskiyar abinda na sani, ya karasa maganar da kara rungumarta jikinsa

“Shikenan yanzun koh inada cikin sai ka yarda ka zauna dani” ?

Indai har cikin babu a jikinki koda kin tabayene  zan zauna dake a hakan ma naji dadi ai, na samu mata

Kuka sumayya ta sake sakewa watoh duk zaman da suke da Al’ameen na kokonto ne  tayi ciki koh batayi ba kai wai meta tsarewa dangin mahaifintane, na mahaifiyarta kamma bata sansu ba bare 

Kiyi shuru sumayya mundin bakece kika gaji da zama dani ba ni bazan taba juya miki baya ba a duniya,  bayan khadija da ke sai goggo bayan ku banida mutanen da suke sona  tsakani da Allah, ke kuma kin nuna mini tsantsar hallaci a rayuwa, don wata koh da gaske tayi ciki aka aura matani bazatayi hakurin zama dani ba bare ta taso cikin kudi yanzun kuma tana fama da rashi harsai ta nemi na kanta

Da sauri sumayya ta rufe masa baki cikin kuka tace”karka kara fad’ar haka banaso nima a yanzun kaine kad’ai Garkuwa ta kaine bangon da zan jingina ya rikeni, insha Allah  kome zai wuce kamar ba’ayi ba.

Allah yasa toh yanzun ya maganar kamilar?

“Bazan koya mata ba gaskiya kartazo tana shigewa mijina don yanzun kai ba tsaranta bane”

Yanzun shikenan saboda ni saiki rasa makudan kudi haka?

“Wani makudan kudi kuma bayan jiya ma na samu mutum uku da zasu fara zuwa, shiyasa yau zamu fita dakai muje bank zan bude Account maganar kudin  koyar,  shiyasa zan bude Account transfer zasu mini ta bank kuma yaran manya ne sosai fa, inaga anya ma bazan bude shago ba”?

toh Allah ya bada sa’a,  Amma banda maganar shago kam banyarda ba matar aure da shago kamar wata inyamura.

“Ayya koh a shagunan kofar gida saina kama d’aya tunda bakin titi ne”

Sumayya ban Amince ba, yace yana tashi akanta hade da karban eirps in hannunta ya mayar kunnensa kawai ya kwanta

Ganin ya kwanta yasata tashi ta d’auko musu karyawa jejjerawa tayi, ganin bai sauko ba yasa a hankali tahau kan gadon  agadon bayansa ta kwanta luf ta lumshe idanunta “breakfast is ready”

Shuru taji bai amsa ba Amma dai yasa hannu ya tabata,hannun ta buge hade da cire masa abinda yasa a kunnen san ta makala a kunnenta  wakar umar m shareef ke tashi a ciki

Jin ta cire masa yasa sa mikewa da sauri ya Amshi abin a kunnenta, wakar dadi tamin don Allah ki maida mini, ya fad’a mata yana mai mika mata wayar hannun nasa jin wakar ta chanja

Hhh”waikai kam anya ka taba saka eirps a kunnenka kuwa”?ta karasa maganar da sauka akan gadon

Da sauri shima ya sauko had’e da cewa wallahi kamar kin sani inadai jin ana zancen sa Amma ni bantaba sawa ba ashe da dadi

“Hhh toh zauna kaci abinci sai na baka bluetooth harda wa’azi da karatun qur’ani zakaji a ciki ba waka kawai ba”

Menene bluetooth kuma, banda na waya?

“Baka san ana posted a waya ba? toh ai yakamata kasan bluetooth da mp”

Nasan mp mana,  bluetooth ne bansani ba saina tura abu a waya inaji anacewa kai bude bluetooth naka na tura maka waka koh vedio.

“Kayi kokari wannan kuma na yayi ne a kunne zaka makala ba tare da igiya kamar eirps ba ka gane”

Eh na gane..yace yana zama

Abincin sumayya ta zuba musu mika masa tayi bayan ta damka masa shukali a hannu, wai nikam me kika maidani ne? an gaya miki bazan iyya d’aukar shukalin bane?

“Waya sani koh abincin ma saina fara baka”

Kwafa yayi kawai ya fara ci

Suna tsaka da karyawa sukaji sallamar khadija amsa mata sumayya tayi hade da bata izinin shigowa

Khadija bataso shigaba ganin yayanta na d’akin,  Amma ba yanda ta iyya haka ta shigo, ina kwana Aunty?

“Lafiya khadija ya goggo”?

Tana lafiya ina kwana yaya, tana maganar tana kokarin zama 

Lafiya khadija…ya Amsa mata

” khadija matso  muci” sumayya tace wa khadija

Ah ah Aunty nagode, daman takarduna ne na kawo miki duka kamar yanda kika bukata.

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 1 HAUSA NOVEL”


“Lallai ma khadija bansan yaushe zanna baki abu kisa hannu ki karba ba tare da kin mini filako ba”tace tana mikawa khadija plate na abincin data zuba mata sabo

Ba musu khadija ta karba 

“Yayan khadija”

Na’am sumayya..

Inaso zamu fita da khadija, zanje na sama mata makaranta tunda yanzun muna first time bazamu sha wahalar samun aji ba, Amma yakace ka Amince koh yaya”

Sumayya bazance miki kume ba sai dai nace Allah ya biyaki, tabbas yau zaki cikamin d’aya daga cikin buru kana dana so cikawa amma kana naka Allah na nasa.

Aunty makaranta zaki sani😳??khadija ta tambaya cikin zare ido fuska a washe

“Insha Allah kanwata zaki shiga makaranta yau yau ma amma wani school kikeson shiga”?

Koh wanne ma aunty nagode kin gama min kome arayuwa tunda zaki sani a makaranta bani da wani zabi koh wanne ki sani.

Matsalata dake kenan khadija in mutum yace kaza sai kice kaza, yanzun ni in baki fad’amin makarantar da kike soba ina zansan makarantan da ya dace ki shiga”

Nidai aunty na baki zabi 

“Shikenan bari yayanki ya zaba miki”

Da sauri Al’ameen yace, nikam ba ruwana tsakanin ku nida ba idone dani ba ina nasan makarantu inba na gw’annati tada ba

“Shikenan yanzun Art kikeso koh science”?

Aunty science nakeso.

“Shikenan sai muje GSSSJ ina ga makarantar tafi inganci a harkan science”

Kai Aunty tsadane fa da school in kuma ga kudin registration mai yawa gashi wai sai anye Attitude test kafun abawa mutum gurbin karatu.

Khadija kenan indai kin yarda da kanki Attitude test bazai baki tsoro ba maganan tsadan registration, kuma ai kyaunsa yasa kudin yayi yawa,  duk da makarantar goverment ne”?

Gaskiya ne sumayya kinsan koh lokacin mu ba makarantar da ta kaita inganci kyau da doka kuma sai wane da wane ne a ciki a kaf Taraba  daga goverment har private Amma yanzun xamani ya chanja saidai a sata a lissafin goverment school mafi inganci

“Yauwa bara na tashi in shirya kaima sai muje dakai yayan khadija zan bude account a bank da voter’s card naka”

Nikam gaskiya ba inda zani tunda khadija tazo da National ID card nata sai a bude miki babban Account kawai.

“Kace kawai bazaka ba shikenan”sumayya tace tana mikewa,kaya ta fitar zata saka ganin haka yasa khadija fita a d’akin ta bata waje

Nifa kawai zuwanne banji shiyasa nace kije da khadija

“Toh zamuje daga nan saina wuce bank in,  nama manta ban fad’a maka ba nayi posted na vedio n make-up da lalle harda photos yanzun haka next week za’ayi bikin yar kanwar Deputy Govnor an bani kwangilan musu lalle da make-up kawaye kawai da Amarya”

Duk sunzo gidan nan?Al’ameen ya tambaya da mamaki

“Ah ah a online fa muka gama kome har balance na fad’a musu yanzun ma jiran Amaryar take na tura mata account numbar na”

Wow Allah abin godiya Amma dai sunan ki da suka ganine yasaka su baki aikin hala?

“Wani irin suna kuma?toh ni ban ma saka sunana ba wani sunan na saka”

Wani suna kenan?

“Basai kaji ba” tace tana yafa gyalenda ta d’auko sai jaka da takalmi data rike a hannu zata fita a d’akin sai kuma ta sake juyowa ta kallesa jin tambayar da ya mata

Sumayya baki bani bluetooth in ba?

“Ikon Allah”tace hade da nufar cikin kayanta,  Allah yasa ma tayi charge insa, makala masa tayi a kunne ta saita da wayanta,” waka zan saka maka koh wa’azi”?

Waka….

Wakar ta kunna masa”ga wajen da zaka taba ta gefe in zaka danna next koh back koh stop koh play”tana fad’a tana kama hannunsa tana nuna masa gun 

Eh na fahimta, saikin dawo

“Allah yasa zanbi kasuwa duka me zan saya maka”?

Kasuwa kuma sumayya?

“Eh mana koh bakason naje? na saima khadija uniform ne da kuma d’an cefene nakeso na mana na sati uku kafun a fara azumi”

Saikun dawo Allah ya kiyaye hanya 

“Ameen baka fad’a mini abinda zan sai maka ba”

Am waken Gembu(Red beans)nakeso inkin iyya dafawa yanda suke innan asa tarugun Gembu(yellow pepper) da ice fish, irin dafin.

“Hhhh eyeee  kaima har kasan hadin dadi haka bansani ba”

Allah inason abincin sosai…

“Shikenan zan saya maka sai mun dawo”

Allah yasa…

Ameen, sumayya tace tana fita a d’aki,  suka nufi kofar gidan da khadija

Sunje makarantan kuma Alhamdulilah khadija ta samu gurbin karatu a makarantar science bayan interview da aka mata don an riga anyi Attitude test tun bayan sati uku, sun bawa khadija class,  sumayya ta biya kudin kome atake aka mata registration aka bata su  textbook,  notebook , da  tarkacen kayan makaranta su rigan sanyi rigan house socks vaji da sauran abubuwa

Bayan sun bar makarantar yau kam duk wanda yaga khadija koh ba’a fad’a masa ba yasan tana cikin farin ciki sosai  bank sukaje sumayya tasa aka budewa khadija Account .

Kasuwa suka wuce tasai ma khadija uniform jaka da takalmi don sune kawai ba’a basu ba, a kasuwar ta baiwa tailor ya d’inka musu kala ukune jibi khadija zatazo ta karba Turare ta saima khadija da mayuka masu kyau sai Dutsen guga karami na wuta.

Cefene tayi mai yawa sosai ta sai harda su drinks,  doya, dankalin hausa,  harda na turawa,  vegetables,  kai abubuwa sosai sumayya ta saiya saida kudin hannunta ya kare na machine kawai ya rage musu da d’an abinda baza’a rasa ba

Bayan sun dawo gida da sallama, suka shiga gabaki d’aya dan dazon yan gidan suka bisu da ido ga kaya niki niki kamar masu kaura suka wuce suka shiga kofar ga yara na rirrike da laidodi

Wa’alaikumus sallam,  sannun ku da hanya Al’ameen yace yana cire hannunsa daga cikin kwanukan da yake wankewa

“Yauwa yayan khadija” sumayya tace tana bin kofar da kallo ganin kayansu daya wanke ga randa a cike da ruwa Alamu dai jido yayi

Yaran na sauke kayan sumayya 10 10 ta basu da murna suka karba kowa na jin dadi suka fita

Sallah khadija da sumayya sukayi kafun suka baje cefenen suna dubawa, khadija kam ganin yanda sumayya ta loda mata kayan sayayyanta a gabanta kuka kawai ta sake tana rungumar sumayya,yanzun aunty duka wannan nawane? yaya kaga kayan kuwa wai duka nawaπŸ˜…, tana fad’a tana kamo hannun yayanta ta d’aura akan damin kayayyakin abin ma abin dariya da tausayi

Shima karan kansa Al’ameen yayi  mamakin kayan, sumayya abubuwan nan basuyi yawa ba kinje kin kashe kudi da yawa haka sumayya kina ga ba aiki nake fita ba bazaki tattala kudinki ba sai kina fashaka haka.

“Allah zai kawo kuma maganar baka aiki bazai hana nayi walwala ba kaima insha Allah kafun d’aya ga azumi zaka daina zaman gidan nan”

Allah yasa Amma dai sumayya kayan yayi yawa

Babu wani yawa yar fa makaranta ce sai da guga da wanki da gyara, kema khadija duk safiya kina zuwa kafun ki tafi makaranta kizo ki karya,ki karbi kudin tara dana keke kinsan sunce sai 2 ake tashi kuma ana dukan letti

Toh Aunty amma zanna karyawa a gida saina zo na karbi na kudin.

“Shikenan monday zaki fara zuwa jibi,  kije ki karbi uniform in ki gobe ki goge,  gata sai school”πŸ˜ƒ

Hhh hakane Aunty in tafi da kayan naje na nunawa  goggo kona barshi Anan?

“Ai yanzun kayanki ne ki tafi dashi”

Toh aunty tace tana rungumar kayanta ta fita

Khadija na tsananin farin ciki yau wanda rabon dana gansa har na manta, Al’ameen ya fad’a yana lalubar hannun  sumayya ya kama

“Insha Allah zaka yita ganin sa yanzun harka gaji”

Allah yasa,  kema Allah  ya biyaki

“Ameen,  na sai maka waken Amma na gaji gaskiya bazan iyya dafawa yanzun ba kasan sa da wahalar nuna”

Shikenan sumayya Allah ya kaimu goben

“Ameen”, tace tana d’aukar wayanta dake neman agaji”Assalamu Alaikum”

Shuru tad’anyi sai kuma yaji tace “toh bara na tura miki ta WhatsApp”

“Ok shikenan”, tace tana aje wayan

“Kasan waya kira”?

Ah ah …

“Yar kanwar deputy ne waina tura account number”

Toh Allah ya bada sa’a

Ameen, bara na tura musu

Tashi Al’ameen kam yayi yaje ya cigaba da wanke wanken sa

 sumayya kam Account numbar ta tura musu koh minutes 10 ba’ayi ba taji Alert kudine ya shigo account in khadija dayake da layinta aka bude account in…..

Khadija kam na fita a gidan yayanta da kaya niki niki sai sauri take kamar zata fad’i damuwarta kawai taga ta isa gida ta nunawa goggo abin Alkhari data samu, bata hankalta ba tazo tsallaka titi koh ganin gabanta batayi, ji kawai tayi jama’a na illalilahi keeee kalli gabanki

Ai jiii kawai kake kiiiiiiiiiiiii kauuuuuuuuu………….

Da karfi khadija ta watsar da kayan hannunta tsungunawa tayi jikinta na bari ta kama kai, gabaki d’aya ta gama sadakar wa yaukam sai Ta Allah

Cikin zafin nama da haushi mai motar ya fitoh da fad’a fad’a,kee wace irin wawuyace wai kina tafiya koh ganin gabanki bakyayi da yanzun na kadeki fa baki jawo mini matsala ba gashi yanzun kinsa na buge keke napep innan da sai dai me zan buge? nosense kawai stupid 

Khadija kam har yanzun bata dawo daidai ba ga kuma tsawar da ake buga mata, d’aga kanta tayi tana kallon mutumin don Allah kayi hakuri wallahi bangan ka bane

Da mamaki mutumin ke kallon ta sai kuma yayi murmushi,  ke bakece kanwar Al’ameen ba?

Eh…..eh..nice

Murmushi kawai yayi hade da dukawa a tsakar titin yana tattara mata kayanta,saiki taso ai inba so kike wani motar tabi ta kanki ba

Khadija kam cikin had’a fuska don sai yanzun takejin haushin zagin da ya mata, mikewa kawai tayi ta koma gefen titin 

Kizo ki shiga mota na kaiki gida?

Bazan hauba, kuma ka bani  kayana nikam.

Kinji haushine khadija?

Da mamaki take kallonsa toh a ina ya santa gashi itama tun d’azun sai tunanin inda tasan wannan fuskar take

Ke yar Kauye bar kallona 

Naki dainawa kuma miko mini kayana, ta karasa maganar da kai hannu zata karbi laidodinta

Da sauri ya kauce hade da cewa,  ke khadija  nifa yau gidan yayanki zaki kaini yau kusan wata biyu ina sintiri a sintali kowa na tambaya Al’ameen mijin sumayya sai ace ba’a gane saba yau ma Allah ne yasa zamu hadu shiyasa na biyo ta bakin kasuwa.

Aikuwa bazan nuna maka ba,  ba zagina kake ba

Yi hakuri haushi naji Shiyasa yanzun muje ki nuna mini gidan yayan naki 

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 2 HAUSA NOVEL”


Gaskiya ni yanzun gida zan koma ba gidan yaya ba sauri nake 

iyeee nace ki nunamin gidan da nafi wata biyu ina nema shine zaki wanice kina sauri

Kaga malam ni yanzun ma haka gidan na fitoh gaskiya bazan koma ba saidai nama kwatance

Toh shikenan yi mini, kuma ga kayanki karki shiga motar inkin ga dama

Oho maka dai, inka tsallaka titin nan  sai ka mike kaga lungun shan  kana shiga zakaga babban titi da yayi barade ka tambaye masu shagunan wajen,  gidan Adara za’a nuna maka saika aike yaro kofar MAKAHO 

Ok toh shikenan naji, yace yana komawa wajen mai keken biyansa yayi asaran da ya masa, ya shiga motarsa yaja 

Khadija kam da ido ta bisa ta kasa tuna inda tasan bawan Allah nan Amma tabbas akwai inda ta sansa.

**************

“Yayan khadija gaskiya nifa yau bazanyi girki ba wallahi na gaji wanka zanyi na kwanta “

Kidaiyi wanka amma banda kwanciya kinsan bakyau bacci bayan la’asar koh?

“Gaskiya ne amma dai zan d’an taba kafun goshin mangariba saika tashe ni”

In ance abu ba kyau sumayya ki gujesa don Allah kidai kwantan koh waya koh TV ki kallah Amma banda bacci kam.

“Toh shikenan akwai kudi a purse nawa anjima ka sayo mana abinci”

Ah ah zan dafa…

“Zaka dafa kuma yayan khadija, kaji mini kaudi”πŸ€•

Nine mai kaudi?😳

“Eh man in ba kaudi ba ina kai ina girki,  salon kaje ka kone koh ka yanke ba”

Amma dai wallahi sumayya kin gama raina mini wayo me kika maidani ne wai?

“Sorry toh me zaka iyya girkawa”

Oho…..

“Yi hakuri mana wasa fa nake maka”

Ba wani, ya karasa maganar yana zama a bakin dakalin

“Banace kayi hakuri ba,  habba danejo Am heedee Am buddi Am yafannam lee”ta karasa wakar da kamo hannunsa ta nufi kitchen in dashi

Kinga sakeni nafa fasa girkin bara kiji karma ki kama mini wani waka wai ma tsaya ke bafulatana ne daman?

“Bororoje ce ba bafulatana ba, kuma girki sai kayi ehen”

Ke wai ana girkin dole ne?

“Yau sai kayi ai duk wanda yayi niyar aikin lada sayya karasa”

Toh nace na fasa koh

“Nikuma nace sai kayi” ta karasa maganar da dokarasa akan kujeran kitchen in 

Kin zama yayi inta dosana sa saiya cije”wai kai kam menene haka kasan Allah yau saikayi girkin nan”

Zama yayi ba yanda ya iyya

“Me ka iyya girkawa”?

Me kikeso na girka miki?

“Iyeee lallai ma watoh am bani zabi kenan irin ga k’wareren nan”

Eh fad’a mini me zan girka miki?

“Waken gembun jiyan nan zaka girka”

Ah ah gaskiya banda shi don nidai ban iyya ba,  don ni ba d’an gembu bane.

“Hhhhh bakar magana koh”?

Kema Aishi kika fad’amin 

“Shikenan yanzun me ka iyya dafawa maganar gaskiya nafa gaji da tsayuwa kwanciya nake son nayi fa”

Doya na iyya soyawa da indomie, kwai, harda taliya dafa duka sai Tie

“Doya Da k’wai ka iyya soyawa ko daban daban”?

Soyayyen doya,kwai ma soyawa na iyya, da dafawa

“Ok sai ka soya mana doyan da salt daban saika soya kwai shima daban akwai yaji a roba ka hada mana da ruwan bunu”

Sannu hajiya,πŸ˜’ yace yana kokarin lalubar bojuwa(tukunya)

“Waye hajiyan kadaiji dashi”bojuwan sumayya ta wanke ta d’aura akan hot plate tasa masa mai Amma bata kunna ba Albasa ta yanka a ciki, doya ta d’auko da kwai tarugu Albasa lawashi maggi gishiri ta aje masa  a kusa dashi koh wanne a roba koh tire koh gwangwa ninsa ruwa ta iba a boket tasa kofi ta aje masa duka don ya huta da tashi koma ransa innan” ga kome a  zaune  Allah yasa yayi dadi”tace tana fita a kitchen in

Baiyi magana ba kawai wuka ya d’auka yafara feran doyan

Ruwa sumayya ta iba tayi wanka kaya tasa ta kwanta duk da Al’ameen ya hanata amma baccin tuni ya sace ta

Al’ameen na tsaka da feran doya yaji salaman yaro, amsa masa yayi

Wai ana sallama da MAKAHO

Inji wa?

Nima ban sansa ba yace dai in masa sallama dakai

Ok kaje kace masa ina zuwa

Toh, yace yana fita a kofar

Tashi Al’ameen yayi ya wanke hannun sa ya shiga d’akin, sumayya!ya kira sunanta jin shuru bata amsa ba sai numfashin ta dake sauka akai akai, girgiza kai kawai yayi ya d’auki sabon riga da wando da sumayya ta sai masa ya saka ya cire 3quiter dake jikinsa, waje ya fita yana mamakin waye yazo gunsa yau haka 

Waje ya fita yana tattaba jikin ginin kofar gidan don jin ina mai sallama dashin ya tsaya jin baiji  motsen saba ya sakasa, kara maimaita sallamar

Wa’alaikumu salam Al’ameen 

Laiiiiii wana kejin muryarsa kamar Ammar?

Baka mantani ba Al’ameen ka rike sunana baka manta ba.

Habba Ammar wanda ya maka hallaci irin wanda kamin ai ba mutumin da zaka manta dashi bane

Hakane Ya mai jikin?

Da sauki sosai Ammar, ya aiki ya gida?

Lafiya kasan yau kusan wata biyu da dawowa na ina zuwa unguwan nan ban gane kaba wallahi har Hospital in na koma sukace ai an mata tiyata ma har an sallame ku tuntuni

Eh kam satin mu d’aya aka sallame muma tuni.

Allah sarki yamai  jikin toh?

Da sauki fa sosai kamar ma ba’a taba yanka taba, na barka a tsaye muje bakin dakali

Ok toh in ba damuwa naga dakalin da rana kazo mu shiga cikin mota mana?

Tsakake Al’ameen yayi yana nazari kutt anya zai yarda ya shiga motar mutun da bai sansa ba(lokacin da ya taimake ka ka sansa ne) Am daman ina d’an aikine a gida nama manta na d’aura  tukunya 

Murmushi Ammar yayi watoh har yanzun Al’ameen bai yarda dashi ba kenan, toh ba kome nima bara na wuce naga yamma tayi sai na sake zuwa

Toh shikenan nagode da ziyara Ammar

Toh aje a cigaba da aiki mijin hajiya hhhhh

Hhh Ammar kenan, ya fad’a yana mikama Ammar hannu sukayi musabaha a karo na biyu 

Bayan tafiyar Ammar cikin gida Al’ameen ya wuce yana tunane tunane sai kuma yaji bai kyauta ba da Ammar nason cutar dashi da randa ya d’auke sa da sumayya ya cuce su, ta wani bangaren kuma sai yaji gwara masa hakan babu ruwansa da mutanen duniya sai mutunci yanzun bai yarda da kowa ba haka zalika tsoron shiga mota ne dashi tunda masu mota suka makantar dashi, kauda tunanin yayi  ya cigaba da aikinsa,  daya ya gama fere doyan ya zuba a roba wankewa yayi ya tsame a kwando ya zuba gishiri kunna hot plate in yayi ya kama Aiki.

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 3 HAUSA NOVEL”


Bayan kammala girkin Al’ameen juyewa yayi a kula ruwan shayi koma a flask wanka yayi yashiga d’akin, har lokacin sumayya bacci take, hawa yayi kan gadon  a hankali ya kamota d’agata yayi cak yayi waje da ita ajeta yayi a kan dakali 

Ido sumayya ta ware jinta a sama kafun ma ta gama nazartar inda take taji an ajeta a dakali”menene haka”?

Mangariba ake kira baccin ya isa haka, watoh bakiji bakisan baccin mangariba akwai matsala bako

“Baccin kwasheni yayi ai”

Sai kiyi Alwala nikam na tafi masallaci, bai saurare abinda zatace ba ya fita abinsa

Itama samayya Alwala tayi ta shiga d’aki…

Bayan sallan isha Al’ameen ne ya shigo kofar su,  kitchen ya wuce ya d’auko kulan da 🍽 ya shige d’aki

Sumayya dake kwance fuskarta sanye da glass ta d’aura system inta akan cikinta tana daddan nawa,d’ago kanta dake kan fillo tayi tana bin Al’ameen da kallo ganinsa d’auke da kula sosai tayi mamaki matuka, don ita harma ta manta da zancen zaiyi girki” ikon Allah wai da gaske kake kayi girki”?

Idanunki zai nuna miki, yana magana yana fita a d’akin bayan ya aje kulan hannun sa da plate da shukula, sai kuma gashi ya dawo dauke da flask da cups,  ajewa yayi a hankali akan cafet ya zuzzuba doyan da kwai sai yaji a gefen plate ya tsiyaye tie a kofuna 

Itakam sumayya sai ido kalala take kallonsa dashi”wai duk wannan kaika soya”?

Eh man bakin raina ni ba an gaya miki in mutum baida ido shikenan sai akace bazai iyya abinda masu ido keyi ba, ai harma yafi namasu ido muna iyyawa

“Ah ah kwadai kwatanta Amma badai yafi ba malam”

Au karya zan miki kenan?

“Bance ba,ina nawa doyan naga ka zuba plate d’aya”?

Eh namu ne yau tare zamuci a plate d’aya

Sumayya batayi magana ba sauka kawai tayi akan kujeran hannu kawai tasa ta fara cin doyan ” kai maggi yayi yawa”

Kiji tsorin Allah fa sumayya

“Toh da tsoron ka zanji”

Amma dai k’wan nan babu maggin da yaji inba sharri ba

“Nikam naji,  k’wan maggi ga Albasa doyan kuma bai soyu ba,  tie in kuma sugar baiji ba”πŸ˜•

Hannu yasa ya d’auke plate in gabanta da cup in tie in ya rike a hannunsa

“Yaya haka kuma”?

Ki miko mini kudi inje in sai miki abinci amma badai wannan zakici ba kowa ma ya hakura Almajiri zan kira na bawa, karasa maganar yayi yana shirin fita a d’akin 

Da sauri sumayya ta biyosa hade da kamo rigansa”dan Allah yayan khadija ka aje abincin mana waikai bakasan wasa bane?wasa fa nake maka”

Wasa koh?toh ni da gaske nake kuma sakar min riga karki yaga

“Habba don Allah yaga riga sai kace wata mai farashunan mayu”

Toh waya sani

“Yasan me”?

Sakarmin riga hajiya

“Ayya ka bani abincin mana wallahi wasa nake doya yayi d’adi haka tie ma k’wai innan inda kasan dafin Turai”

Mika mata plate in yayi shima ya koma ya zauna abinci suka cigaba daci

Bayan sun kammala ci yaukam ita ta d’auki kwanuka, bayan ta kaisu waje brush tayi shikam Aswakin sa  ya d’auka ya goge bakinsa d’akin suka koma kayan bacci sumayya ta saka rigane da wando cotton mai laushi da socks na sanyi a kafarta,  jin an fara yayyafi yasa Al’ameen fita waje ya tattare musu ruwa 

 shima kayan baccin sa da sumayya ta sai masa ya yasa

Sumayya gado tahau iyafis ta d’auka ta jona da wayan ta ta manna a kunne tana kallon film a ciki 

Shima bayan ya gama shiryawa d’akin ya rufe ya hau kan gadon, tattaba kan gadon yake har yaji ya tabota kwanciya yayi kusa da ita yasa hannu ya zame hular kanta 

Hannu tasa ta cire kunne d’ayan ta makala masa a kunne 

Kwanciya yayi akan filon da take gabaki d’aya ya nutsu yana sauraron abinda ke kunnensa, sai kuma yasa hannu ya taba sumayya hade da kiranta, sumayya!

“Na’am”

Uhmm Amma wannan indi’an film ne koh?

“Eh..ya akayi ka gane”?

Muryansu mana duk da Turanci suke magana amma dai sai kiji suna maganar sari koh bauta

“Gaskiya ne kasan sunan film in”?

Ah ah

“this is fate,  watoh kaddarar Rayuwa na Arewa 24”

Oh film in karam koh?

“Eh shine ma ke magana yanzun”

Ai da sauri ya zare abin kunnesa tare da sa hannu ya zare na sumayya, kinsan Allah bazaki kalli film innan ba

“Ikon Allah akam me bazan kalla ba”?

Nidai kawai bazaki kalla bane.

“Toh me kakeso na gani”?

Wani film banda wannan

“Uhmm nikam gaskiya shi nakeson kallo” tace hade da karban abinta ta mayar kunne

Da sauri ya fizgo abin gabaki d’aya ya had’a da system in yana  kokarin sauka akan gadon

Da sauri sumayya ta cakumosa baya hade da kokarin karban system in

Duk yanda taso kwatar abinta abin yaci tura duk inda tayi saiya zillar da hannunsa karshe ma hakura tayi takoma gefe tana maida numfashi

Tashi yayi jin ta kwanta,  zuwa yayi ya aje system in akan kujera, ya dawo ya kwanta abinsa 

Ganin ya aje yasa ta saurin mikewa zaune cikin azarbabi take kokarin sauka ta gefen kadon a hankali, tana sauka saboda matsen d’akin yasa dole saita biyo ta bangarensa kafun taje kan kujera, a hankali take tafiya

Shikam tun tashinta zaune da saukarta duk a kunnensa shuru kawai yayi yana son ganin gudun ruwanta

Tazo daidai dashi har zata gifta a bazata kawai taji ya fisgota baya ta fad’a kansa

Kokarin tashi take,  ya sake maidata, wai sumayya meyasa ne bakijin bari sam

“Me nayi kuma”? Ki

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 4 HAUSA NOVEL”


Yanzun ina zaki?

“Waje zan fita”

Me zakiyi a wajen?

“Fitsari mana koh an hana fitane in aka kulle kofa”

Jin amsar da ta basa ya saka hannu ya mannata da jikinsa sosai kamar zai maidata ciki

Karan shagwaba ta sake da karfi”wayyo”

Ke menene haka saikin tara mini jama’ane

“Toh ba kaine ka matseni ba”

Toh ai ke ince bakiji koh kad’an kannan naki taurine dashi fa

Eh naji kaina taurine dashi kuma ni ka sakeni fit………

Bai bari ta karasa ba kawai ya manna bakinsa da nata sosai yake kissing inta yana dad’a matsota garesa kamar zai maidata ciki 

A hankali tasa hannu ta kama kansa da karfi ta danke gashin kansa masu yawa sosai, hade da ajiyar zuciya

Washhh ashhh kawai Al’ameen yace bayan ya zame bakinsa a nata,  hannu yasa ya kamo hannunta data rike masa gashi ya d’aura a kirjinsa, da sauri ya maida bakinsa cikin nata

Sosai yau sumayya da Al’ameen suka farantawa junansu duk da tafiya tayi nisa sumayya ta copsa Shi kuma Al’ameen tsoro.

 *RANAN MONDAY* 

Yaune fa hajiya khadin Goggo zata makaranta jiya koh baccin kirki bata iyya ba, da sassafe ta tashi tayi wanke wanke shara kafun 6:00 har tayi wanka dumamen da goggo ta duma shi taci, uniform nata tasa fari kal wando da hijab harda riga duka farare ne socks ta saka fari ta d’aura bakin d’an kwali(kallabi)ta zura hijab,  sandal inta da Aunty ta tasai mata kala biyu d’aya πŸ‘Ÿ ne d’aya sandal,  πŸ‘Ÿin ta d’auka bakine shima don a dokar makarantar baki da fari suke so,  tasa a kafarta sai agogo shima baki turare ta fisa fuskar nan washe kamar gonan Auduga takema goggo sallama hade da d’aukar school back nata shima baki mai kyau, ta fita a gidan

Sumayya da Al’ameen ne a kitchen suna girkin karyawa kamar kullum yauma hakan take watoh ana aiki ana fad’a

Assalamu Alaikum

“Wa’alaikumus sallam, yan makaranta”

Kai Aunty ina kwana?

“Lafiya khadija harkin shirya gaskiya ne Allah yasa hakan ya d’aure banda littin”

Ameen Aunty, ina kwana yaya?

Lafiya khadija harkin shirya?

Eh yaya na shirya

D’aki sumayya ta shiga naira 200 ta d’auko sai drinks d’aya da goran faro d’aya ta fitoh “ungo khadija wannan kudi yayanki ne ya bada na baki koda zaki zo ya fita ashe da rabon zaku hadu ma kihau keke sauran d’arin saiki rike a hannunki  ga wannan kuma kisa  a school back naki kinji,  banda kawayen banza banda abota da maza kinga makaranta ne da Christian sukafi yawa sosai kuma benchi d’aya ake had’a maza da mata don haka babu ruwan ki da yaran Christian abinda ya kaiki shi zakiyi kinji ki maida hankalin ki akan abinda ya kaiki Allah ya tsare mana ke”

Hannu khadija tasa ta karbi kudin da drinks in hade dama sumayya godiya, yaya na tafi

Al’ameen kam ya rasa ma me zaice da sumayya sumayya Alkhari ce garesa matar rufin asiri, toh khadija saikin dawo kindaiji abinda Auntin ki tace miki koh?

Eh yaya..

Adawo lfy

Bayan fitar khadija sumayya kam kitchen ta koma taci gaba da aikin ta Al’ameen na tayata

Assalamu Alaikum

“Wa’alaikumu salam” sumayya ta amsa tana fita a cikin kitchen in da sauri jin muryar wance ke sallamar

Aiko itace da mamaki sumayya ta bita da kallo,   

 Al’ameen ma da sauri ya fitoh a kitchen in jin muryar me sallamar

“Lafiya” sumayya ta tambaye ta

Eh lafiya daman n…………….

Lafiya daman nazo akan maganar make-up inne,  naji shuru baki kirani ba inna kira ba’a picking call in.

“Ok toh ai na zaci koh kina da fahimta ne, ki gane me nake nufi”

Kamar ya sumayya ban gane ba?

“Ok toh kamila bara na miki gwari gwari, bazan koyar ba”

Akan me? bayan kince sai mijinki ya yarda kuma a gabanki yace ya Amince.

“Eh ya amince nima haka yace mini sai dai ni ban Amince dake ba har kizo gidana kina kare mini tanadi”

Kamar ya bangane ba me kike nufi?zanzo gidan ki in kare miki tanadi?ina ma gidan yake bare

“Hhhhh hayyeeee nanayeeee ashe gidan ba yanda yake akazo cin moriyan masu shi”

Ke sumayya nafiki rashin mutunci don naga baki dashi ya daga abin Arziki sai tsiya ya biyo baya matsalanka da matsiyaci kenan bai gaji arziki ba

“Ehhhhhh yariya tsiyama waje ya samu ki kalleni da kyau daga ni har mijina kinga Alamun yunwa a tare damu, kuma ki kallen sama da kasa koh uwar ubanki bataci arzikin da naci ba harta mutu ke uwarki data aure ubanki har yanzun bataci arzikin danake ciba.

A’uzu sumayya wani rin , zagine haka kar in sake jin kin tanka mata shige ki wuce d’aki, don Allah kamila kiyi hakuri

Kutt ni kike xagi? ai kamila super tayi da jakarta tayo kan sumayya da mugun sauri 

“Sumayya da gudu tayi kitchen tabarya ta rarumo ta rike”don uwarki kizo yau saina rusa miki kai shegeya harni zakima bariki kizo mini da yaudara da sunan koyan kwalliya”

Ai da sauri kamila taja birki, in ba tsoro ba ki aje abinda ke hannunki yau saina nuna miki true colour na. 

“Shegeya akan me zan aje nasan dame kikazo kizo kima mijina asara a banza “

Shammatar sumayya kamila tayi tana magana,  da sauri tayi kanta gadan gadan da kwalba a hannu

Ai ji kawai tayi Al’ameeen ya hankad’ata gefe, don duk abinda suke hankalinsa na kansu, keee kamila kin isa kizo har gida kice zaki bugarmin mata kimin asara akan me? Ke kin kini na samu mai zama dani shine zaki bugeta

Wayyyo nashiga uku na lalace wayyo hannu na innalilahih kun kasheni, kamila ke ihun nan tana rike da hannunta wanda Acid ya zube mata akai 

“Subahanallah daman abinda kike da niyar watsa mini kenan Algunguma shegeya, aikokin watsa min bashine yake nufin karewar auren mu ba tunda ba idone dashi ba bare yaga yanda na koma”

Sumayya meke faruwa ne haka meya sami hannun nata naji kina cewa zata zuba miki

Kamila kam ihu take kamar ranta zai fita

Ihun kamila shiya jawo da hankalin jama’ar gidan kofar su Al’ameen,  da sauri daga maza har mata yara da manya suka nufi kofar donjin ba’asi

“Ruwan Acid tayi niyar watsa mini Allah yasa ka shureta shine ya zube a hannunta hannun sai d’ayewa yake”

Subahanallah Al’ameen yace yana nufar inda kamila take, kee kamila tashi muje asibiti tashi tashi yau an bonu

Kaiii karka kuskura ka taba ta kaji na fad’a maka,  keee Kinsan su waye a gidan nan har kika iyya d’aukar Acid zaki zo ki zubawa mutum a cikin gidan Adara? kutumar  uba iro yace yana nufar kamila

Salame ce ta Lailayo Ashar ta maka, Ci ubanta dan uwarta(wa’iyyazu billah) koh dabban gidan Adara bama bari aci zalinsa bare mutum 

Ai kafun Al’ameen yace wani abu tuni iro ya fara wanke fuskar kamila da ruwan maruka ji kawai kake kauuu kauuuu kauuuu

Ihun kamila ke tashi yanda kasan ranta zai fita bugunta suke tana kokarin gudu wasu su kamo ta, Al’ameen karan kansa hankalin sa ya tashi  da kukan ta kamila keyi duk yanda yaso kwatarta abin yaci tura karshe ma salman turesa yayi saura kad’an ya fad’i sumayya ta taro sa

Jama’ar kofar gida su suka shigo gidan jin kukar mace kamar me, shigowa sukayi ganin abinda ke faruwa yasa su rugawa a guje suka kwace kamila

Ai kamila na ganin ta tsira da wani irin matsifeffen gudu ta falla waje kamar walkiya ga hannu duk ya d’aye fatar

Bayan gudun kamila suwaiba ce ta d’auki jakar kamilar, Kai Allah ya mini ga jaka mai azaban kyau maybe ma harda cash a ciki, takara sa maganar da fita a kofar 

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 5 HAUSA NOVEL”


Bayan fitar jama’a  a kofar Al’ameen rai a bace ya fara magana sumayya yanzun kin kyauta fisabilillahi daga abin arziki saiki kama zagin yarinya 

“Ok watoh laifina kake gani kenan na zagi budurwan ka koh”?

Waike sumayya meye haka duk wacece ummulkaba’isin wannan matsifar tun farko me yasa zaki zageta akan wani dalili yanzun mutuncin kine ashar koh zamanki a gidan nan ne kika koya, ni fad’a nake miki a matsayina na mijinki ba saurayin kamila ba, yana karasa maganar yayi d’aki ya barta tsayi kamar an dasa ta

Sai yanzun sumayya tayi data sanin biyewa kamila koh yaushe kamila tazo gidan saita had’ata fad’a da mijin ta ina bazai yuba, kitchen in ta shiga taci gaba da ayyukan ta, don batason basa hakuri yanzun ganin ransa ya baci sosai

Da misalin karfe 11:20 saiga yan koyan  make-up inta sunzo a waje suka zauna ta shinfid’a musu taburma suka fara training don yau kwanan su biyu da fara koyo

Jin d’uriyar jiniyar motar yan sanda sukaji ya tsaya a kofar gida, ba’a wani jima ba saiga matan yan sanda sun shigo gidan har kofar su sumayya

Sallama dai…

“Yauwa sannunku da zuwa lfy”?

Lafiya ba lau ba don duk wanda yagan mu baiga lfy ba, wacece sumayya?

“Ikon Allah nice wani abinne ya faru”?

In munje station zakiji dalili, shige muje d’ayar yar sandan tace tana kokarin kama hannun sumayya

Da sauri sumayya ta fizge hannunta tare dama police in kallon banza, babu inda zani wallahi akan me banyi kome ba Awani ce za’a tafi dani

Babu wanda zai tafimin da mata ba tare da sanin laifinta ba, Al’ameen da yafitoh d’aki da sauri yake fad’a musu haka

Kai ka iyye bakinka fa kasan a gabansu wa kake babu ruwan mu da makantar ka wallahi koya maka hankali zamuyi.

Sannu uwar sa koya masa hankali na rantse kika tabamin miji ubanki za’a taba,  station ne dai baza……

Bata karasa ba taji saukar mare tasss a fuska police in ta tsinketa dashi ai kafun ta sauke hannunta Al’ameen ya watsa mata rabonta itama duk da ba’a fuska ya saita ba amma ta maru kam 

Kutturu hukuma ka mara yau daga kai har matar taka sai munga gatan ku a jala yau innan, waya tayi wasu mazan yan sanda biyu suka shigo aka rufuwa Al’ameen da sumayya da karfin cin tuwo za’ayi waje dasu Al’ameen kam anfa kasa tafiya dashi sai kokuwa suke, yau sunga ikon Allah kama MAKAHO ya gagare su  sumayya kam an fita da ita waje bayan ta sanya hijab 

Ammar ne yayi packing mota da sauri ganin yanda jama’a suka cika kofar gidan ga sumayya an tisata a gaba cikin sassarfa ya karaso wajen yana tambayar ba’asi ganinsa da daula yasa police in saura ransa suka masa bayanin sunzo kama sumayya ne Al’ameen ya mari police

Cikin gidan Ammar ya shiga da mamaki yake kallon Al’ameen dake ta fama da police da sauri ya karaso wajen hannun Al’ameen ya kama ya rike hade da kiran sunan sa

Tsayawa da kokuwar yayi, Ammar kaine?

Eh wai meke faruwa ne,  meka musu?  

Wallahi ba musan me muka musu ba daga zuwa wai zasu tafi da sumayya na tambayi dalili wai sai munje office insu kajifa.

Gaskiya ne Al’ameen ba’a fad’awa mutum laifinsa sai a station kazo muje ba abinda zai faru mundin kaine da gaskiya 

Binsa Al’ameeen yayi police kam  sai hararan Al’ameen suke da kitsima irin dukan da zaisha a hannunsu in ya shiga cell

Alfarma Ammar ya nema a barsu sumayya su shiga motar sa inyaso sai police  shigo ciki

Bayan an isa station kenan officer ya had’asu da iyayen kamila a office insa sannan ya kalli sumayya, an kawo mana karanki  kinyi kokarin zubawa wata Acid  a fuska Allah ya kiyaye ta,  ya zube a hannu bayan haka baki barta ba kika mata duka yanzun haka tana kwance a police clinic don haka zamu rikeki anan don iyyayenta zasu kai kara kotu

Amma dai yallaboi kafun a kamata ai sai an tambaye ita sumayyar ba’asi itama aji tata jawabin sannan kamila ta kawo shaida ku kuma saiku kamata ku rufe,  Amma daga fad’a muku magana kuma sai ku rufe mutun ba bincike haka ake Hukunci?Ammar ne ke maganar yana nuna officer in

Toh kai kuma malam asuwa har zaka nuna mini abinda ya dace nayi koh kafini sanin doka ne?

Ban fika sani ba haka zalika bazan barka ka rufe baiwar Allah ba dalili ba akan me?

Kai malam dakata kasan a gaban wa kake kuwa? d’aya daga cikin police in yake Tambaya Ammar 

Koma waye ne shi,  nadai gama magana sumayya fad’a musu menene Ainahin abinda ya faru

Sumayya ba tsoro ta bayyana gaskiyar hakika nin abinda ya wanzu tsakaninsu da kamila

Kuna daiji koh asalima kamilar ce bata da gaskiya koh a hukunce wanda yazo ya sameka har cikin gidan ka kuma yajaka da fad’a kome akai masa shiya kai kansa, sannan a maganar nan ba ruwan sumayya haka zalika Al’ameen bada niya ya zubar da acid in a jikinta ba haka zalika itace take kokarin cutar masa da mata kunga kenan duka wannan abinda ya faru ba ruwan sumayya da Al’ameen duka, kuma jama’ar gidan ne suka mata basu ba ya karasa jawabin yana bin officer in da kallo

Kaima ai yanzun gashi ka yanke hukunci ba tare da bincike ba menene hujjar ka? nace wa kamila ce taje da acid in,  baban kamila ya tambayi Ammar

Ku tura d’aya daga cikin yaran ku officer aje a d’auko goran acid in Allah dai yasa sumayya baki taba bako?

“Eh yana nan ata gefen kitchen a kasa”

Ok aje a d’auko saiku saka a gwada yatsun hannun wanda aka gani  a kai wannnan ma ai hujjane koh?

Wai kai a matsayinka nawaye har zakana bamu order kai waye?

Hannu Ammar yasa a Aljuhu ya zaro ID card nasa ya nuna 

Ai da sauri duka police inda ke wajen suka kame tare da sara masa

A gaskiya station nan yana bukatar gyara tunda bakusan aikin kuba A matsayin ku na hukuma masu kare hakkin wa’inda aka zalunta shine zaku zamo masu tauye masu rauni ku aje hujja akan masu kudi, Ammar ya karasa maganar da tsantsan bacin rai 

Don Allah sir kayi Hakuri wallahi kuskure aka samu Shiyasa kuma duba da irin rauni dake jikin ita yarinyar da aka ma dukan shiyasa muka d’auki matakin gaggawa officern  ke magana cikin magiya

Mtwss Ammar yaja tsaki hade da rufesu da fad’a sosai, muje koh muhammad, yace yana kamo hannun Al’ameen

“Ina da magana yallaboi”

Wace magana kuma sumayya bayan an kashe case, Al’ameen ya karasa maganar da kamo hannun sumayya su tafi

Ah ah Al’ameen ka barta muji meke tafe da ita.

Ah ah Ammar mu tafi kawai yafi

Sumayya yi maganar ki, Ammar yace bai saurare Al’ameen ba

“Yauwa so nake Amana iyyaka da kamila Amata iyyaka da mijina Arubuta  a ajiye don ban yarda da ita ba wanda yayi niyar zubama acid wata rana zai dabama wuka”

Keee ki iyye bakin ki yar tamu yar daba’ce? da zata daba miki wuka wallahi karki kuskura ki kara jefin yarmu  da mummunan kazafi, 

Kallon d’an sandar Ammar yayi 

Da sauri yace an gama sir, ku kuma daga yau ku jama yarku kunne karta kuskura muji koh mu gani tsakanin ta da sumayya koh muhammad

Suna Fita a station in motar sa suka hau sumayya a baya Muhammad a gaba da Ammar

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 6 HAUSA NOVEL”


Don Allah kuyi hakuri da abinda ya faru sannan ke sumayya gaskiya banji dadin abinda ya faru ba yara irinsu kamila da basusan kwaba  babu Alkhari rigima dasu .

“Gaskiya ne Ammar ni karan kaina danasan wannan fad’ar zata kai ga haka daban fara ma tanka kamila ba”

Allah ya kiyaye na gaba

“Ameen”

Al’ameen kam kala baice ba shuru ya musu fuskar nan a hade don yau sumayya ta kular dashi tunda yake police basu taba kamasa ba yau ta janyo har station ya shigaπŸ˜† kad’an ya rage bai shiga cell ba

Suna isa kofar gidan Ammar yayi packing sumayya ce ta sauka tayi cikin gida abinta

Ammar kam maida kallonsa yayi akan Al’ameen dake kokarin sauka a motar, abokina kayi hakuri don Allah kasan halin mata kuma duk da bansan ainahin abinda yake tsakanin ku da kamila ba na fahimci kishine kawai ke damun sumayya,  kuma koh wace mace iyya abinda zata kwatanta kenan

Ba kome Ammar amma wallahi naji haushi sosai yau innan gashi sumayya  harda Ashar

Hakuri zakayi sai kuma ka mata fad’a a siyasa karkace zaka d’aga jijiyoyin wuya,  mata sha’aninsu sai su

Ba kome Ammar nagode da taimakon ka gareni ashe kai police ne?

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 7 HAUSA NOVEL”


Eh muhammad

Amma babba koh naga suna baka girma

Eh, wani aiki kake ne muhammad? kullum nazo a gida nake samun ka badai bara kake bako irin yanda wasu keyi?

Ah ah ammar ina sana’a bana bara 

Sana’ar me?

Mongoro, abakin titi

Amma meyasa kullum bana ganin ka a wajen sana’ar,  inna zo?

Shuru Al’ameen yayi yanajin kamar ya fad’i  gaskiya kamar karya fad’a, a hankali yace jarin nawane ya karye don mangoro yayi Araha yanzun ba ciniki shiyasa bana fita

Toh dame kake ciyar da iyalin kuma?

Had’a fuska Al’ameen yayi jin Ammar na masa tambaya kamar ya masa sata

Kayi hakuri muhammad ina ta tambayar ka Abinda bai maka dadi ba

Ah ah ba kome,  daman ita ke kwalliya da lalle tana mana cefene da sauran abin bukata.

Gaskiya hakan bai dace ba Al’ameen ace kana namiji mace ke d’awainiya dakai ya kamata ka samu ka dogara da kanka, zan baka jari kamar na 300k  sai ka kama shagon haya tunda azumi yazo kaga zama afi ciniki kayan narmari  cikin azumi ga kankana ga lemo ga sweet milo harda dabino saika had’a, kana saidawa kaga saika kula da matar ka,  ita kuma kudin da take samu saita  kashewa kanta da kanwar taka hakan zaifi maka mutunci a wajen mace koh bata maka gori ba, koh bata nuna wani abinba Amma dai inka kasance kaike ciyar da ita kimarka daban yake a idon ta

Ammar ni……

Da sauri Ammar  ya tare numfashin sa kaje kayi shawara da matar taka yanzun dai bana son jin kome bayan kwana biyu xan dawo inji Amsar ka eh koh Ah ah kawai nake bukata. 

Shikenan nagode, Al’ameen yace yana fita a motar 

Ta bangaren kamila kam da bacin rai iyayen ta suka shigo cikin clinic in tana kwance akan gado inda kasan wance tayi Accident haka ta koma gwanin tausayi sai kawarta dake gefe a zaune 

Amma dai ke kamila bakijin bari ba saida namiki tsakani da yaron nan ba shine tsabar rashin zuciya kika ibi kafa kika tafi gidansa harda zuwa watsama matar sa acid kamila?

Nifa mama wallahi bani bace itace ta d’auko zata watsa mini

Uban me ya kaiki gidan ta?

Koyan kwalliya naje

Kwalliyar ubanki?dabani na haifeki ba sai ki gayamin wannan zance na d’auka yarinyar da bata jiran kanta.

Habba Rabi da wanne zataji ne da ciwon da ke cinta koh da fad’anki? babanta ya fad’a 

Fita mamar kamila tayi,

Kamila tambayar baban ta tayi ya aka kare a station

Bai boye mata kome ba ya fad’a mata, tare da fita a d’akin

Kamila tun farko saida na fad’a miki karki fara abinda bazaki iyya ba matar Al’ameen ba wawuya bace kamar yanda kike zatoh mace mai shikara 26 koh 25 kema kinsan bazaki nuna mata tawaye ba shiyasa nace kibi abin ta bayan gida.

Wani banzan kallo kamila tama kawar ta, kinsan Allah sadika sai sumayya tayi dana sanin sanin muhammad saina dasa mata bakin cikin da yafi wanda nake ciki,  muhammad kuma nawa ne tunda nayi aure nasan dadin abin kinga yanzun na gane ba kyau koh ido ne jin dadin aure ba keda kanki kinsan Al’ameen  zaije duk inda ake so, 

Don haka yanzun ma jira nake naji sauki mai gabaki d’aya zan musu.

Me kike nufi?

Uhmm ba sun mini iyyaka da su ba toh Malamai zan shi………….

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 8 HAUSA NOVEL”


πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€

Back to top button