Hausa novels

Halysaah Page 120 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 120…Wajen karfe shidda da yan mintuna na yamma Ajay ya shigo dakin Hajja, har sannan Khaleesat na zaune dakin tana danna wayarta ko nan da can bata fita ba, inda Allah ya taimaketa Hajja na dakin all through ita ma ba fita take ba, wannan yasa Hadiyah da cousins dinta sai dai su shigo su harareta su fita babu me ce mata uffan sai kallon banza, Walid ma yayi shigowa yafi goma zuwa dakin amma duk ya shigo zai tarar da Hajja zaune sai dai yayi ma Khaleesat kallon kasa kasa ya fita daga dakin, su Aunty da Gimbiya Firdausi kuwa sun ma ki shigowa dakin tun zuwan Khaleesat gidan, duk da ba hira Khaleesat suke da Hajja ba amma she prefer it that way akan a bar ta da su Hadiyah ko su Aunty ko Walid don kam ba karamin taimako rashin fitan Hajja daga dakin yayi mata ba, a yanda ta lura duk yan matan gidan cike suke da ita kuma akwai magana a bakinsu amma ba dama saboda Hajja, jifa jifa Baby ke shigowa dakin da duk wani abu na dadi in dai ta ci to sai ta kawo ma Khaleesat tunda ta bata kyautan Handbag, in kuma ta shigo dakin sai ta cikata da surutu kafin ta fita, tun da Ajay ya shigo dakin Hajja ke bin sa da kallo tana jin ranta babu dadi, gashi sam baka gane inda ya dosa da mood dinsa, kullum a haka yake baza kace yau yana cikin farin ciki ba ko kuma akasin haka, baka gane walwalarsa da rashin walwalarsa, baka gane damuwarsa da akasin hakan, if you are lucky to see him laughing or vibing probably you met him sitted together with Jay back then, Khaleesat dai taki kallon inda yake sai danna wayarta take, yana kallon Hajja daga inda yake tsaye yace “Sai da safe Hajja, I am leaving” Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace “A tsaye zaka min sallaman kuma Ahmad?” Bai dai ce mata komai ba, after some seconds ya karasa cikin parlon ya zauna, tace “To abinci fa Junaid? Me zaka ci?” Yace “Ke komai abinci, to na koshi” Hajja tace “To ai shikenan, Allah ya tashe mu lafiya” Yace “Probably zan koma Maryland gobe in sha Allah” Hajja tace “Gobe kuma? Ai nayi tunanin kuna nan har weekend” Ajay yace “In zauna inyi me a England har weekend” Hajja tace “Daxu naji Hafsat na cewa za su je can Maryland din ita da Gimbiya Firdausi, ban san me za su je yi can din ba” Ajay dai kallon Hajja kawai yake jin abinda tace, Can ya mike yace “Alright, Good night” Hajja tace “To Allah ya tashe mu lafiya, amma dai ba sallaman kenan ba ko, ya kamata goben ku zo ku yi ma iyayenka sallama tunda basu san za ku tafi ba” Ajay yace “Ohk” Hajja ta kalli Khaleesat tace “Toh sai da safe Jiddah, a baki abincin ki tafi da shi ne?” Duk da yunwa Khaleesat ke ji don bata wani ci abincin daxu da Hajja ta zuba mata ba amma ta girgiza kai kawai tana ɗan murmushi tace “A’a na koshi Hajja, Nagode” Hajja tace “To Allah ya tashe mu” Tuni Ajay ya fita daga dakin Hajja, Khaleesat tayi ma Hajja sallama sannan ta bi bayansa tana tafiya a hankali cikin sanyin jiki, Hajja ta bi ta da kallo har ta fita, babu abinda Hajja tace mata akan yanda suka samesu ita da Jawwad daxu don tasan shi ya kamata tayi ma magana tunda ya fita hankali not her, sam bata ji Khaleesat ta kwanta mata a rai ba har yanxu amma kuma bazata iya walakanta ta ba… Tun da Khaleesat taji Hajja tace su Aunty za su je Maryland jikinta yayi sanyi sosai ba kadan ba, har cikin ranta tsoron Aunty take ita kam, ga ita ma Gimbiya Firdausin taga idan ta gaisheta bata amsa mata gaisuwarta, infact tsoron duk family din ma take ita, da kyar take jan kafa tana biye da Ajay har suka isa parlor, babu kowa a parlon har ma da gidan baki daya don Hajiya A’isha da Ummi da Mami sun tafi daya apartment din wajen Hajiya Shema’u Yayar Baban Hadiyah, Gimbiya Firdausi da Aunty kuwa sun fita zuwa gidan wata kawar Gimbiya Firdausi dake England ita ma, Hajiya Nafisah a safiyar yau ta koma Nigeria saboda wani uxurin ta, ita dai Khaleesat na biye da Ajay suka fita daga apartment din, ko juyawa bai yi ba balle yasan tana biye da shi ko akasin haka, ya bude gaban taxi din dake gaban apartment din ya shiga, a hankali ta bude back seat din motar ta shiga ita ma, driver ya ja motar suka bar wajen. Tun da suka shigo hotel room din Khaleesat ke zaune gefen gado tana danna wayarta, tana kallo ya shiga banɗaki ya dauro alwala ya fito don lokacin Magrib yayi, hakan yasa ta ajiye wayarta taje tayi alwalan ita ma ta fito, kamar yasan abinda zata yi bai tada sallah ba har ta fito, tana dauko pray mat zata shimfida a bayansa ya juya ya kalleta fuska daure yace “Fita a bayana” Kallonsa ta tsaya yi, cikin tawa yace “Ko baki ji abinda nace ba?” Juyawa tayi ta bar wajen, ya tada sallahn sa, ta turo baki ta tafi ta zauna gefen gado tana hararansa, yana idar da sallahn bayan kusan minti goma ya mike daga saman darduman alamar ya gama azkar ya fice daga dakin, sai a sannan ta mike ta tada nata sallan, ko da ta idar kayan baccinta ta dauka ta shiga bandaki tayi wanka ta canza kayan a ciki sannan ta fito taga bai dawo dakin ba har lkcn, a haka lokacin sallan isha’i yayi ta mike don yin sallan, har karfe goma Ajay bai shigo dakin ba gashi yunwa take ji, tana kwance edge din gado suna chatting da Sophie da yarinyar Hajiya Zaliha ya shigo dakin, ita dai bata daga kai ta kallesa ba har sai da ya wuce ta sannan ta bi sa da kallo taga ya canza kaya, which shows daga gida yake kenan, kashe wutan dakin taga yayi sannan yayi kwanciyarsa a inda yake kwantawa, ta kalli direction dinsa cikin duhun duk da ba ganinsa take yi ba, tura baki tayi tace “To ni bazan ci abinci ba?” Taji yayi mata banza, after some minutes kamar zata yi kuka tace “Ka ji….” Nan ma bai kulata ba, kawai ta ci gaba da danna wayarta, bayan kusan minti sha biyar ta kashe data din ta ajiye wayar ta hau kan gadon ta rarrafa can daya side dinsa tana kallon ƙasa duk da ba wani ganinsa take sosai ba, kamar zata yi kuka a hankali tace “Ni fa yunwa nake ji wallahi” Still dai bai kulata ba, ta ɗan duka closer to him tana kallonsa cikin duhun tace “Ka ji mana” Cikin kakkausar murya yace “I will give you a dirty slap idan ba ki dena damuna zan yi bacci ba, uban me ya hanaki amsan abincin a can gida” Shiru tayi don sai da ya bata tsoro da intonation din da yayi using, bata ma san sa da irin tone din ba, after a while ta koma inda take kwanciya a hankali ta kwanta ta rufe kanta da duvet tana goge hawayen da ya kawo idonta, after almost 30 mins ta gama juye juyenta bacci ya dauketa. Cikin bacci Khaleesat taji an sauke duvet din da ta rufe kanta da shi, firgita tayi sosai ba kadan ba ta fara kokarin mikewa zaune tana komawa baya tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un….” Tun da Walid yayi mata haka to tana jin an taɓa duvet dinta komin nauyin baccin da take sai ta firgita don scenario din ne ke dawo mata, kunna wutan dakin yayi yana kallonta, ta sunkuyar da kanta kamar zata yi kuka ta dau hularta tana cusa gashinta ciki a hankali tace “Tsoro na ji” Ya mata wani kallo yace “Tunda baki da gaskiya dama me yasa baza ki ji tsoro ba” Yana fadin haka ya juya ya bar wajen ta bi sa da kallo, Sleeping mask dinsa taga ya dauka, ta juya tana kallon paper bag dake ajiye bedside drawer kusa da ita saboda aroma din abinci da taji, wayarta ta jawo ta duba agogo taga karfe sha biyu saura few minutes, ta ajiye wayar ta bude paper bag din taga takeaway din abinci ne ya siyo mata da ruwa, turo baki tayi ta juya ta kalli direction dinsa taga har ya kwanta, sai kuma a hankali tace “Thank you” Dama bata sa ran zai amsa ba don kuwa banza yayi mata, ta dau abincinta ta fara ci, tana gama ci ta shiga bandaki don wanke bakinta, bayan ta fito ta tafi ta kashe wutan dakin sannan ta koma saman gado ta kwanta ta rufa da duvet. Washegari da safe Khaleesat ta gama rufe akwatinta ta mike tana kallon Ajay dake zaune dakin yana danna wayarsa fuskarsa daure, tashi yayi ya nufi kofa ya fita daga dakin, ta turo baki sannan ta dau handbag dinta ta bi bayansa, can gida suka tafi zai je yi ma wa enda Hajja tace sai yayi ma sallama kafin su tafi, ya sami Aunty da Gimbiya Firdausi da Hajiya A’isha zaune parlor, ya zauna kan kujera ya gaishesu gaba daya, Khaleesat ma ta zauna kasan Carpet ta gaishesu cikin sanyin murya, Ajay bai jira sae sun amsa gaisuwar ba yace “Za mu koma America yau” Gimbiya Firdausi da Hajiya A’isha ne kawai suka ce “Allah ya tsare” without giving much attention, Aunty kuwa kara wayarta tayi a kunne tana answering call, Ajay ya mike ya nufi sama, tuni Khaleesat ta tashi ta bi bayansa da sauri gashi taki yarda ta hada ido da su, duk suka bi ta da kallo don yau ma tsadadden Black Abaya ne jikinta da yayi mugun amsan fatar jikinta, tayi kyau sosai ba kadan ba kamar balarabiya, dakin Hajja Ajay ya tafi ita ma zai yi mata sallama, Hajja na kallonsu bayan sun gaisa tace “Flight din karfe nawa ne?” Ajay yace “Karfe daya in sha Allah” Hajja ta dau wayarta tana duba agogo taga karfe sha daya da rabi, tace “Lokacin ma ai ya kusa, toh Allah Ubangiji ya kai ku lafiya, amma kaje can apartment din kayi ma Hajiya Shema’u sallama, ita ma Asiya da Ummi suna can, duk ku sallame su” Ajay dai bai ce komai ba, Hajja ta juya tana kallon Khaleesat, ita kanta a ranta sai da tayi admitting kyan Halysaah, amma damuwarta jikokinta da suka samu matsala ta dalilinta shi yasa ma bata jin ta kwata kwata a ranta, Khaleesat ta sauke kanta kasa ganin kallonta Hajja take, Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace “Kun karya ne Jiddah?” Gyada mata kai Khaleesat tayi tace “Eh Hajja” Ajay ya mike, Hajja na kallonsa tace “To Allah ya kai ku lafiya Ahmad, we will speak on phone idan kun isa” Ajay yace “In sha Allah” Khaleesat ta yi mata sallama ita ma sannan ta mike ta bi bayan Ajay da har ya fita daga dakin, ji yake kamar ya gansa a Maryland yanxu. Apartment din da su Mami suke Ajay ya karasa don it’s just few houses away, Khaleesat dae na biye da shi har suka isa gidan, Hadiyah ce ta bude masu kofa bayan Ajay ya danna bell, daga sama har kasa take kallon Khaleesat tana kare ma kayan jikinta da jakar hannunta kallo, can ta koma gefe fuskarta babu walwala, kamar warce ake tilasta ma tace “Ina kwana Yaya” Ba tare da Ajay ya kalleta ba yace “Lafiya” Tuni ta juya ta bar bakin kofar ta koma cikin parlon tana cika tana batsewa, a karo na farko tun fitowarsu Ajay ya juya ya ɗan kalli Khaleesat da ta rakube jikin kofa kamar munafuka, juyawa yayi zai karasa parlon suka hada ido da Jay dake saukowa stairs dake opposite din kofar parlon, Ajay ya dauke idonsa ya karasa cikin parlon ya zauna ya gaida su Mami da Hajiya Shema’u, duk suka amsa masa, da fara’a Hajiya Shema’u tace “Fatan kun tashi lafiya?” Yace “Alhamdulillah” Khaleesat ta karaso ta zauna kan Carpet jikinta a sanyaye bayan da ta hada ido da Jay zai sauka downstairs amma ganinsu ya juya ya koma sama, cikin sanyin murya ta gaida Hajiya Shema’u da su Mami da Ummi, duk suka amsa a takaice, Hajiya Shema’u kadai ce ta bata attention, Hadiyah dai na zaune parlon fuskarta daure tana danna wayarta, Ummi kuwa sai satan kallon kayan jikin Khaleesat take, Ajay yace “Za mu koma America ne dama” Hajiya Shema’u tace “Allah sarki, nima gobe in sha Allahu zan koma Nigeria, kace sallama ku ka zo yi mana kenan” Ajay yace “Ehh haka ne” Hajiya Shema’u tace “To Allah ya kai ku lafiya” A takaice Ummi da Hajiya A’isha suka ce “Allah ya tsare” Ajay yace “Ameen” Khaleesat ta ɗan daga kanta ta kalli sama ko zata kara ganin Jay amma taga ba kowa wajen, Ajay ya mike yace “Jirgin nan da awa daya ne, za mu tafi airport…” Hajiya Shema’u tace “To Ahmad din ne zai kai ku Airport din? Ni duk yau ma ban gansa ba” Ajay yace “A’a nayi booking ride” Hajiya Shema’u ta kalli Hadiyah tace “Ke Hadiyah ina mijin naki?” Hadiyah na danna wayarta tace “Ya fita baya nan” Khaleesat ta daga kai a karo na farko ta kalli Hadiyah suka hada ido, wani matsiyacin kallo Hadiyah ta watsa mata akan idon Ajay, Khaleesat ta sake kallon sama sannan ta sunkuyar da kanta, Hajiya Shema’u na kallon Ajay tace “Ko kun yi sallama ne da ɗan uwan naka?” Ajay yace “Eh mun yi sallama” Hajiya Shema’u tace “Toh Allah Ubangiji ya sauke ku lafiya, Allah ya kara ɗankon zumunci” Ajay yace “Ameen mun gode” Ajay ya mike ya sake yi ma Mami sallama tace “Allah ya tsare” Sannan ya juya ya nufi kofa Ummi ta bi sa da harara ta taɓe baki, Khaleesat ma tayi masu sallama sannan ta mike ta bi bayan Ajay tana tafiya a sanyaye, Hajiya Shema’u ta bi su da fatan alkhairi tana sa masu albarka, sai kuma ta kalli Hadiyah tace “Ji shashashar yarinya, baza ki tashi ki raka su ba” Hadiyah ta kara hade rai sai kuma ta mike ta bi bayan Khaleesat, Khaleesat na isa kofa bayan ta saka takalminta sai da ta kara kallon upstairs tana jin hawaye na taruwa idonta kawai ta juya ta fita daga parlon, Hadiyah dake mata wani tsinannen harara ta kulle kofar parlon da karfi….. Har suka koma hotel Khaleesat taki yarda ta kalli inda Ajay yake, sai daure fuska take tana cika tana batsewa kamar warce ke jiran kiris ta fashe da kuka, bata san shi ma bata ishesa kallo ba don ko bin ta kanta bai yi ba balle ya kalli inda take yasan halin da take ciki, ya dau Charger dinsa da Hand luggage ya fice ya bar ta a dakin don Taxi din da zai kai su Airport din har ya iso, ta bi sa da wani harara sai kuma ta goge hawayen da ya fara taruwa idonta, daga karshe ta dau akwatinta da Handbag after making sure she is forgetting nothing in the hotel room sannan ita ma ta fita daga dakin…. Da daddare karfe takwas da rabi suka sauka Baltimore, nan ma dai ya bar ta da akwatin ta yayi gaba, bayan sun shiga mota she was expecting zai sa driver ya tsaya a restaurant ya siya mata abinci don babu abinda ta ci a jirgi saboda she was moody all through amma sai taga kawai sun wuce gida, shi ya rigata sauka motar ya dau jakarsa ya wuce cikin gida, nan ma ta bi sa da harara, driver ya dau trolley dinta ya kai mata parlor tana biye da shi, daukan akwatin tayi bayan ya ajiye mata ya fita ta wuce sama ta shiga dakin da take, bayan tayi wanka tayi sallah ta gama shafe shafenta ta saka kayan bacci ta daure gashinta ta saka hula tayi kwanciyarta tunani iri iri na yawo a ranta, a hankali ta goge hawayen da ya fara sauka idonta ta jawo wayarta ta kunna data, DM din Jay ta shiga tayi tagumi, it took her almost 2 minutes hawaye na zuba idonta kafin ta tura masa message, ganin baya online yasa ta kashe data ta ajiye wayar ta kwanta tana shesshekan kuka, har karfe daya saura Khaleesat bata yi bacci ba, ta mike zaune jin she needs to eat something, after a while ta sauka daga kan gadon tana tafiya a hankali ta nufi kofa ta bude ta fita ta sauka downstairs, wuta mara haske ne kunne a parlon, walking slowly ta nufi hanyar kitchen zata shiga ta ci karo da Ajay ya fito hannunsa rike da mug din tea, saurin komawa baya yayi amma sai da shayin yayi splashing har a hannunsa, ta fasa masa ihu don ita ma ya ɗan fallasan mata ta durkusa a wajen, he literally became confused and out of his mind at once, ko bin ta kan hannunsa bai yi ba ba yayi saurin ajiye cup din sauran shayin ya duka gabanta ya dago kanta yana kallonta yace “Are you okay?” Kuka ta fara yi tana yarfe hannu tace “Wayyo Allah” Ya dagota da sauri ya karasa cikin parlor da ita ya zaunar da ita saman kujera ya zauna dab da ita yana facing dinta har tana jiyo breathing dinsa yace “Did it spill on you?” Bai jira cewarta ba yayi saurin ciro wayarsa dake aljihun pajamas dinsa ya kunna flash yana haska kirjinta ganin nan take shafawa, rigar bacci ne dai dai gwiwa jikinta da yayi revealing almost half part of her chest, cire hannunta yayi daga saman kirjinta yana haskawa sosai yace “Where did it spill?” Yana tambayar ne at the same time yana kai yatsan sa saman boobs dinta da ya ga ya ɗan yi ja saboda farin fatar ta, ya shafa gun a hankali da thumb dinsa yana kallonta, lokaci daya ta zaro ido ta duka da sauri cikin rikicewa tace “A’ahh….” Sai a sannan yayi realizing what he just did after coming back to his sense, shi ma da sauri ya koma baya in a state of confusion har sai da wayarsa ya fadi a hannunsa, sai kuma ya mike daga kusa da ita duk ya daburce yace “Ke makauniya ce, why don’t you watch where you were going” Khaleesat dai taki dago kanta daga dukawan da tayi saboda shock din abinda yayi mata, within seconds ya juya ya bar wajen kawai ya wuce sama, sau biyu yana missing step a benen har dai ya haura sama, tafi minti biyar bata dago kanta ba duk da taji sa ya wuce sama, daga karshe ta dago a hankali tana kallon stairs din, har sannan she could feel his thumb gently rubbing the upper part of her boobs kamar lokacin yake yin hakan, hade rai tayi ta mike ta wuce sama ta shige daki, direct gaban madubi ta tafi ta tsaya, sai a sannan ma taji kunyar rigar jikin nata duk da ya wuce gwiwa amma saman rigar is too revealing, tana tafiya a hankali ta karasa gefen gado ta zauna ta kai hannunta dai dai inda shayin ya fallasar mata tana shafawa still feeling his finger there, gaba daya ji tayi ta dena jin yunwan saboda incident din nan, turo baki tayi ta kashe wutan dakin tayi kwanciyarta….*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*

Back to top button