Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 21 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

    

Story 

     &  

       Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

Cikin natsuwa ya soma magana “tambaya biyu kawai Wacece ke? Kuma waya turo ki”? 

   Cikin rawar murya sehrish tace “Ni ba kowa bace ba, kuma babu wanda ya turon…….’. Interrupting ɗinta yayi da cewa “ki mun magana a hankali don bana fahimta sosai,” 

    Gyara muryarta tayi sannan taci gaba da cewa “Sunana Sehrish, kuma ni babu wanda ya turo ni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, aiki kawai nake don nasamu kuɗi……..’ buga wall ɗin da yayi yasata dakatawa a tsorace “Nace wa ya turo ki!!? 

        Hankali atashe tace “Allah shine shaidata, wlh ni babu wanda ya turoni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, ƴan uwana ne Basu lafiya an kwantar dasu asibiti ana buƙatar kuɗin aiki shine na nemi aiki gidan wata hajiya……………sehrish bata 6oye masa komai ba ta faɗa masa tass dalilin zuwanta da dalilin yin shigarta na maza batayi masa ƙarya ba ko kaɗan, ta ƙarasa masa labarin tana faman zubda hawaye tsoranta wane hukunci zaiyi mata don tasan watan Cin Ubanta ya tsaya, shiru su kayi na wani lokaci, kafin daga bisa ni Babban yayan yaja da baya ya juya

 bedroom ɗinsa ya shige kafin daga bisa ni, ya fito hannunsa ɗauke da wayarsa wuri yasamu ya zauna saman sofa ɗin sannan yaba sehrish damar ta matso kusa, sai da tafara tattara hularta da mayafin da yayi watsi dasu, ta ruƙesu a hannunta sannan jiki asanyaye ta matsa inda yake kamar wadda tayiwa sarki ƙarya, jikinta sai faman kerma yake,

   yace “su nan su? da sunan state  da sunan hospital da aka kwantar dasu? and the date!? 

    Murya na rawa tace   “Hosana Sayyad, da jahad sayyad an kwantar dasu a Fmc katsina……..”

Download>>> Sha’awar Shi Nake Complete Document

 duka ta faɗa masa hada date ɗin da aka kwantar dasu duka don bata manta ba,

     danna wayar yashiga yi kafin daga bisani ya danna calling, ta soma ringing, nan take aka ɗaga wayar suka soma magana, 

  Duk sehrish na tsaye tana kallonsa yadda yake speaking anatse,

    Bakowa ya kira ba face Babban Likita, dama already sai da yafara tura masa message na sunan yaran da bayanan dayake son sani sannan yakira, kuma anci sa’a On duty yake,’

   Tabbas yayi mamakin ganin kiran Surgeon general rafayet, kuma yayi mamakin jin sunan yaran da yakeson aduba mishi files ɗinsu, tabbas yasan yaran, waɗanda Omar ya taimaka daga wurin Police, ranshi ne ya bashi cewa may be Omar yasanar mishi game dasu ne that’s why yake neman Information akansu , without wasting time Babban likita ya binciko masa files ɗinsu Hosana Da jahad na rashin lafiyarsu duka bayanan ya masa snaping dinsa ya tura masa ta whatsapp ɗinsa,

 bayan sun kammala phone ɗin, Sgr ya shiga whatsapp ɗinsa ya duba, sai ga Files ɗin yaran na rashin lafiyarsu raɗau da sunansu ajiki Hosana Sayyad Da Jahad Sayyad, 

   Ajiyar zuciya yasaki yanzu ya shaida maganar Yarinyar duba time yayi dare yayi ga wani bacci daya ke ji gashi ko dinner ɗinsa bai cin ba, Ga yarinyar nan dake tsaye duk a tsorace don yana ganin yadda yatsun ƙafarta ke kerma,

    gyaran murya yayi sannan yace “You’re not guilty of anything, the mistake you made shine shiga na maza after knowing that it is forbidden in Islam for a girl to dress like a male,’ yayi maganar yana danna wayar hannunsa…

   Murya na rawa Sehrish tace “bazan ƙara ba……..’ 

   Jinjina kansa yayi kafin yace”As from now i don’t wanna see u wearing this dress again! u can go” ya bata Umarni ta tafi

    Wayyo Allah sam sehrish ta gaza rufe bakin ta don mamaki, kama hanyar fita tayi tana waiwayansa da kansa ya shiga saving dinner ɗinsa yana ci,

   Tsantsar farin ciki ne ya cika sehrish sam ta rasa inda zata tsoma ranta, ae tana fita daga part ɗinsa ta buga Wani uban tsalle na murna fuskar nan kamar wacce akayiwa Albishir da gidan Aljanna, watsa wa tayi da gudu gudu sauri sauri tana tattaka Stairs ɗin tana saukowa down a babban falon dama ba kowa nan fa tashiga rawar murna tana zagaye sofas ɗin dake a falon kamar wata yar baby, 

    Duk wannan abun da take yi akan idon Sgr domin kuwa ya biyo bayanta ashe yana daga can Upstairs yana kallonta, don bai cika yarda da mutane ba shiyasa yayi following back ɗinta don yaga reaction ɗin da zata yi bayan da ta fita daga part ɗinsa,

  abunda yayi tsammani ba shi ya gani ba,  zura hannayansa yayi cikin aljhun wandon baccinsa yana kallon Ikon Allah, 

   Sam sehrish bata son babban yaya yana kallonta ba, ita kaɗai tasan farin cikin da take ciki, ta jima tana mamakin yarda Sgr ya kasance mai matuƙar sauƙin kai har haka a tunaninta zai bata horo mai tsanani daga nan akore ta kuma daga gidan,

   Nace “*Sehrish ba ke kaɗai ba hatta Hafsat bature da sauran makaranta labarin rayuwarki sunyi tsammanin hakan tabbas Surgeon general Rafayet ya bamu mamaki, haƙiƙa shi ɗin na daban ne*”😍

Yanzu abunda ya rage wanda take yi ma fargaba shine sauran matasan gidan shin zasu amince a ranar da ta bayyana kanta a matsayin mace !? Uwa uba Abban su,kuma tuna wannan yasa jikinta yin sanyi, dakatawa tayi daga yin wasan da takeyi na zagaye gujerun babban falon, jiki a mace ta kama hanyar bedroom ɗinta, ranta ne ya bata cewa akwai mai kallonta, Cikin sauri ta juya ta kalli upstairs a time ɗin har sgr yabar wurin ya koma part ɗinsa

    Ganin wayam yasa ta sauke ajiyar zuciya,ba ɗakinta ta wuce ba ɗakin aunty azmee ta wuce don sam tagaza daina murna tafison ta sanar mata abunda yafaru yau ɗin nan da zafi zafinsa,

   Haryanzu hannunta na ruƙe da hularta da mayafin duka ta ƙanƙame su, tsayawa tayi a ƙopar ɗakin tana bubbugawa ,

Download>>> Rabon Kwado Book 1 Complete Document

Azmee dake zaune saman darduma tasha hijabi ajikinta ga qur’ani agabanta hannunta kuma na riƙe da Cazbaha sai faman gyangyaɗi take yi, jin bugun ƙopa yasata cewa “Wanene”

sehrish dake tsaye a bakon ƙopan tace”Nice aunty azmee”

  Murmushi azmee tayi tare da cewa “Ashe bakiyi bacci ba,” tayi maganar tare da tashi daga dardumar ta buɗe mata ƙopa,

  Shiga ciki sehrish tayi tana faman zabga murmushi,

  a ɗan ruɗe azmee ke kallonta bayan ta rufe ƙopan tace”Yau wata rana! Sehrish kece da Murmushi haka a fuskarki? Wane albishir ne akayi maki?Cos I forgot when last naga wannan annurin a face ɗinki” cikin mamaki azmee ke wannan maganar kafin ta mayar da idonta kan Hular sehrish dake ruƙe a hannunta ta kuma cewa “Ikon Allah yau kuma hularce da mayafin duka a hannu?

  Dariya kawai sehrish take yi daker ta tsagaita tace “Aunty azmeee abun mamaki! Abun farin ciki !”

   Cike da ɗoki azmee tace “menene shi?

    Nan sehrish ta shiga zayyana mata abunda ya faru tsakaninta da Babban yaya daga farko zuwa ƙarshe

 Baki washe azmee ta ɗaga hannunta sama tana cewa “Alhamdulillah ! Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata’ala naji daɗin wannan lamarin sehrish domin kuwa Babban yaya shine nafi ji dama, gashi kuma cikin sauƙi ya amince wayyo Allah murna bansan inda zan sa kaina ba don daɗi” cike da jin daɗi azmee ke magana fuskarta a washe

   Sehrish tace “Amma aunty azmee su fa sauran kina ganin zasu amince in suka sani”? Ni ina tsoran ta yarda zan fara fitowa a matsayin mace cikin gidan nan,” tayi maganar murya asanyaye tana kallon azmee

    Ƙarasawa azmee tayi ta dafa kafaɗarta sannan tace “Sehrish matsalarki tazo ƙarshe! tun da har babban yayansu ya amince ba ki da sauran damuwa, Abbansu ne kawai zamu jira muji ta bakinsa, yanzu abunda nake so dake kije kawai ki kwanta kiyi bacci zuwa gobe zamu ga yadda badaƙalar zata kaya idan matasan gidan nan suka ga tukur mai aikinsu a matsayin Mace lallai akwai tashin hankali, ” azmee tayi maganar da dariya a fuskarta, sehrish kuwa dafe saitin zuciyarta tayi tana zazzare ido tace “Allah sa su amince suma,”

   “Insha Allah” azmee tabata amasa afterwards suke yi sallama, sehrish ta koma bedroom ɗinta cike da zullumi haye wa tayi saman gadonta, ta janyo pillow ta rungume tana sakin murmushi tunawa da haɗuwarsu ta yau da babban yaya, Allah kenan a daren nan Haroon ya ƙuntata mata, har tayi addu’ar sai Allah ya nuna masa Iyakarsa akanta, to yanzu ga Iyakar tasa nan muddin sauran suka amince da ita kuwa, taci alwashin sai ta Ci mutuncin Haroon 😡👊 

A fili tasoma magana ” gajan haƙuri kenan Irin na ɗan adam, yanzu da na kashe kaina da shikenan nayiwa kaina, ashe Allah yana dab da kawomin sauƙi arayuwata,” ta faɗi tana faman murmushi wani irin nishaɗi take ji ayau , ta kuma cewa “Anya ma zan iya bacci kuwa? gashi ina fargabar mai zai faru gobe? kwara kawai nayi Bacci na goben tayi saurin yi, AYI TA, Ta ƘARE kawai🙅, In jalasa jalasa 😂 in Zahaba Zahaba shine kawai 😅😂😹😹😹

tana gama faɗan hakan bacci yayi awon gaba da ita, kai kana ganin yadda reesh ke bacci kasan tana cikin kwanciyar hankali,

 murmushi Hafsat Bature tayi tana kallonta wadda ke tsaye shigowarta kenan ta window tabiyo da suffar Farar Tantabara kasancewarta Aljanar sehrish, hannu tasa tajanyo bargo ta lullu6e sehrish dashi sannan ta 6ace 6aaat…………..😇

______________________________________

Kwance suke acikin store ɗin su biyu abunsu, kamar yadda Jahad ta saba yi musu dabara, na jera masu jarkoki su koma kamar single bed sai su kwanta suna facing ɗin junansu sam bacci yagaza ɗaukarsu zullumin su mai zai biyo ba? Wata alƙibla rayuwarsu zata fuskanta yanzu? 

  “Jahad idan Aunty hafsat ta zubar damu ina kuma zamu dosa”? Hosana ta tambaya tana kallon jahad wadda ta zuba mata ido,

   Cikin sanyin murya tace “Nima kaina bansani ba hosana, ina tsoran hakan,” ta faɗi zuciya a karye

  Hosana tace “Dama Allah ya ɗauke mu yakai mu duniyar sama ko? ko duniyar taurari inda ba mutane muyi rayuwarmu mu kaɗai tare da yaya Omar tunda kowa baison mu shi kaɗae ke son mu ko?  

  Wannan maganar ta hosana tasa jahad fashe wa da dariya daga kwancen da suke ta rinƙa 6a66aka dariya kaman kamar me,

  Hosana ta ɗan 6ata fuska don ita bada wasa tayi maganar ba,

  Daker jahad ta jinkirta da dariyar tace “Sorry hosana dole nayi dariya mana, wa kika ta6a ganin an ɗauke daga nan an kaisa sama ? 

Shiru tayi tana zumbura baki, jahad taci gaba da cewa “sannan kince tare da yaya Omar kaɗai zamu tafi saboda yana son mu, Shin kin manta da Sehrish ne”? Ita kuma fa? akwai wanda yayi mana wahala ne kamarta? sehrish tana son mu fiye da kowa na duniyar nan, saboda mu tashiga duk wani hali da take ciki ayanzu duk da bansan yaya rayuwarta take ba……………wani irin kuka ne yaci ƙarfin jahad har takasa ƙarasa maganar da take yi,

Nan take jikin hosana yayi mugun sanyi tunawa da Sehrish ƴar uwarsu mai tsananin son su da ƙaunarsu, tuni itama idonta sun cicciko da hawaye murya na rawa tace “Ya Allah hada sehrish za’a ɗauke mu akai mu duniyar Taurari…..’ 

   dakatawa da magana tayi ganin Jahad dake kuka ta fashe da dariya, wato tayi tazarce daga kukan da take Zuwa dariya ba don komai ba sai don jin abunda Hosana ke cewa, share hawayenta tashiga yi tana faɗin “Hosana wasan ya isa haka, muyi magana ta hankali, yanzu yaya za’ayi yaya Omar yasan halin da muke ciki kafin Hafsat da Momynta su sa azubar damu yakamata muyi tunanin hakan in ba haka ba zamu shiga wani mugun hannun ne ko mu ƙare rayuwarmu adaji…………..’ jinkirtawa tayi da maganar tana sauraron shawara daga wurin hosana,

Download>>> Yar Harka Complete Document

   “To ya zamuyi mu sanar mishi jahad? Bayan kullum waccen matar mai kama da samudawa mai kumatun alkubus tana tsare mu da ido duk in yazo tana hanamu kwakkwaran motsi,” 

  Shiru jahad tayi tabbas dole su nemi mafita in ba haka ba, zasu fuskanci tashin hankali

   Can tayi wani dogon tunani tace “Hosana mai zai hana, mu samu paper da biro sai mu rubuta mishi, in yazo sai ki lalla6a kisan yarda zakiyi ki tura masa a aljihunsa? Ko da rungumesa ne sai kiyi kamar yarda kikayi a asibitin nan kin tuna”?

  Murmushi hosana tasaki anzo inda keyi mata ƙaiƙayi kallon jahad tayi tace “Shawara mai kyau, amma taya zamu rubuta mishi to? Bamu da paper ba biro jahad,” 

    Shiru jahad tayi kafin tace “Akwai !!! Na tuna acikin wannan ɗakin da Momyn hafsat takaimu acikin wannan ƴar lokar naga Memo da biro,” 

   Cike da farin ciki hosana tace “dama ƙopa a buɗe take, yau ta manta bata rufe mu ba, jahad ki lalla6a ki ɗauko ki rubuta masa,” 

  Miƙewa jahad tayi tana faɗin “Zan fita dan Allah hosana karki biyo ni, nasan halin ki, in kika ja asirin mu ya tonu kashin mu ya bushe mu duka,” 

   Murmushi hosana tasaki tana cewa “sai dai in baki daɗe ba, kinsan ina jin tsoro fa nikaɗae anan,”

   “Karki damu yanzu zan dawo,”

“To shikenan,” hosana ta bata amsa,

Ficewa Jahad tayi cikin sanɗa take tafiya babu kowa wayam sai hasken daya gauraye ko’ina, 

Wuce wa ɗakin tayi a hankali ta tura ƙopa tashige cikin hanzari ta nufi drawer ta zaro gidan farko ajikinta, anan taga memo ɗin da biron data gani, 

   Fiddo su tayi jiki na rawa ta aza memon asaman drawer ɗin dayake ƙaramace, daga zukunne jahad ta soma bude papers ɗin sannan ta aza biro ta soma rubutu kamar haka 

     _ya Omar naji ma inaso na faɗa maka halin da muke ciki, wlh bamu jin daɗin zama agidan nan, saboda basu son mu, uban aiki suke samu har bugun mu suke yi, dan Allah ya omar in kaga wannan takardar ka taimaki rayuwarmu kamar yarda kayi niya ka tafi damu inda kake rayuwa_

    Kamar daga sama Jahad taji ance “Sannu da Ƙoƙari”!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!

  Jin wannan maganar a bayanta yasa jahad dakatawa da rubutun da take yi, hankali a matuƙar tashe idonta sun firfirto azare, jikinta ya soma wata irin kerma, Tuni Zufa ta soma gangarowa daga fuskarta da jikinta don bala’e hatta paper ɗin da take rubutun asamanta ta jiƙe sharkaf da gumin da take fitarwa 😳😳😳

     SHIN WACECE WANNAN ‼⁉❓❓❓

  

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Mgnr payment 300 ne amun magana direct  *08103884440*

Back to top button