Health

Abubuwan Dake Jawo Rashin Kiba Da Rama Da Hanyoyin Magani

Abubuwan Dake Jawo Rashin Kiba Da Rama Da Hanyoyin Magani

Matsalar ramewa Mara misali matsala ce Wanda wasu daga cikin mutane suke fama da ita, Sakamakon ramewa da suke yi daga asalin yanayin kibar da suke da ita tun asali.

Kamar yadda masana suka bayyana cewa wannan matsalar tana faruwane sakamakon wasu dalilai Kamar haka:

Kamar yadda masana suka bayyana cewa wannan matsalar tana faruwane sakamakon wasu dalilai Kamar haka:

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

Kodai sakamakon wata rashin lafıya da ta samesu. Ko kuma sakamakon wasu kwayoyin cutuka da suke fama dasu a cikin jikinsu wadanda suke haifar musu da wannan rama, ko dai na wani lokaci, ko kuma Wanda zai dade sosai.

Masana sun bayyana cewa wasu lokuta hakan yakan faru sakamakon abinci da suke ci Wanda ba cikakke ba. Ko kuma sakamakon wata matsala ko cuta, Wanda aka gada daga iyaye.

Karanta>>> Tsumin Matan Aure Na Musamman Domin Inganta Zaman Aure

Amma abu mai muhimmaci a irin wannan yanayi, ko kuma dangane da lafıyar dan Adam, da kuma samun ingantacciyar lafıyar gangan jiki, wato shine cin abinci Wanda yake mai tsafta, da kuma ya zama cikakken abinci Wanda yake dauke da Vitamin, da kuma sauran sinadarai dake gina gangan jikin, domin samun lafıya mai inganci, da kuma hana wannan gangan jikin daga samun irin wannan rama, ta hanyar hana wasu kwayoyin cuta yin tasiri ga lafıyar wannan jiki.

Amma a wasu lokuta idan an sami irin wadannan matsalolin na rashin cin abinci mai inganci, Wanda yake cikakken kuma mai gina jiki, to zamu iya wai wayawa wajen wasu itatuwa, da kuma ganyayyaki, wanda zasu taimaka wajen dawo da martabar wannan gangan jiki Wanda ya sami rama.

Karanta>>> Tsumin Matan Aure Na Musamman Domin Inganta Zaman Aure

Ta hanyar da zasu Kara ma garkuwar jiki karfı sosai, da kuma kara sakawa mutum shaawar cin abinci, bayan haka kuma sai ya rika samun abinci mai kyau, kuma mai cikakken sinadari yana ci, domin ta hanyar Hakane wannan gangar jikin zata farfado Sai Kaga jiki ya ginu yakara girma.

Daga cikin itatuwa wadanda suke Kara kiba akwai, Hulba ana tafasa kofin ruwa tare da gram 3 na garin Hulba Sai Ka kasa shi gida uku a rana daya, kullum haka zaka/kiyi domin samun kiba Wanda tadace, domin magance wannan ramar. Ko a rika shanta tare da Zuma Mara hadi.

Karanta>>>  Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illa, Kuma Da Kanki Zaki Hadashi.

Amma a tabbata ansami mai inganci, ko a samo yayan Sai adaka kawai.

Ana amfani da yansun tare da tean: Za’a samo Tean kwara hudu, kuma bushashe Sai a hada da garin yansun Sai a zuba acikin ruwa kofi daya sai adora akan wuta Mara karfı sosai, har Sai yayi dumi, sannan a sauke Sai a cinye wannan yayan Tean din, sannan a shanye ruwan, zaayi hakan kafın a karya ko kuma kafin cin abinci.

Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata

Cin ayaba Shima yana taimakawa wajen Kara kiba

Ana samo wani magani daake cemasa Hubbul_aziz Sai adiba kadan adaka Sai azuba acikin ruwa zaa barshi tsawon dare, sannan da asuba Sai a tace azuba Zuma asha.

Ana amfani da Simsim: Ana so mutumin da bashi da kiba rama yayi masa yawa to Sai ya sami ridi ya rika cin akalla Kamar kofi guda a kowacce rana idan yanaso ya kara kiba.

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

Waken soya: Shima waken soya ana samo shi mutum Wanda yakeso, takeso tayi kiba Sai Ta dinga shan kofi daya na waken soya a kowacce rana, amma Za’ayi Hakane bayan anci abinci Wanda yake da ganye, ko ganyan kansa, masana sukace to wannan ma yana Kara kiba da yanayin mai karfi.

Bayan haka sukace cin Jan dankali Wanda zai kai adadin rabin kilo yana Kara kiba, saboda yana Kara ma jiki daukar yanayi dumi mai karfi ta Hakane yake Kara kiba.

Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi

Ana amfani da wani magani da ake kira Kuzbara, Zaka sha cokali daya na garin kuzbara amma bayan kaci abinci itama wannan hanya tana Kara kiba, ko kuma ka rika zuba wa ga abinci Wanda yake da nauin ganye, karika ci da shi. Ko kuma a rika hadawa da Zuma ana sha.

Bayan haka bakin inabi da Hulba Shima yana Kara kiba idan aka mai maita sau uku ko sama da hakan. Ana zuba inabi a ruwan Kamar Lita bayan wasu awoyi Sai atace, Sai a zuba Hulba cokali biyu, sai yakara wasu awoyi sannan a tace arika sha, kuma ana cin wannan yayan inabin insha Allah Shima yana Kara kiba.

Karanta>>> Maganin Kowacce Irin Cuta Da Izinin Allah.

Albasa, tafarnuwa suna taimakawa wajen Kara shaawar cin abinci musamman idan ana hadawa da daya daga cikin su wajen dafa abinci, to zasu Kara amfani ga lafıyar jiki, kuma sukara bude ciki ta hanyar Kara sanya shaawar cin abinci.

Ana samun Sazabu arika hadawa anacinsa da waina ko kuma gurasa Shima masana sukace yana Kara kiba.

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

Ziitir, tare da man zaitun da waina ko asha gurasa ko kuma a rika hadawa acikin abinci masana sukace wannan yakan zama abinci cikakken.

 

Arkusus :Karamin cokali na irkusus tare da kofi daya na ruwa mai sanyi zaa sha sau daya a rana Shima yana Kara kiba da iznin Allah.

Ana sanya kammun a cikin abinci domin Shima yana Kara ma abinci amfani da kuma kasancewar ciakakken abinci.

Ganyan kwa kwa ana dafa kadan, ko azuba a ruwa Wanda aka tafasa Sai arufe minti 15 Sai arika sha ana cin abinci Kamar yadda ake shan ruwa idan ana cin abinci, akalla zaa sha daya bisa uku na kofi 1/3 a kowanne abinci da zaa ci.

Kirfa da Zuma idan ana sha suma suna Kara kiba.

Karanta>>>  Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illa, Kuma Da Kanki Zaki Hadashi.

Back to top button