Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 77 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

77

daga alƙalamin boss bature

قصة خائفة ومتعاطفة للسجناء💔

💋prisoners💋

gaba ɗaya taji an ɗauke ta, batasan ina aka dosa da ita ba saboda suman da tayi. tsawon mintuna, kafin taji saukar ruwa saman fuskarta wanda ya yi silar farfaɗowar ta, sambatu ta soma yi tana ambaton danish nifa danish ɗina nazo nema, wlh bada niyar leƙen asiri na fito ba, ni banga komai ba, dan allah a maidani cikin ƴan uwana, kada acutar dani, tsautsayi da ƙaddara ne suka fito dani, kuma bazan ƙara ba…….” kamar daga sama taji an ambaci sunanta da wata irin murya mai sanyin gaske daga ji mamallakinta ba ƙaramin mutun ba ne.

“unaiserh zaheer tajudden”! kai tsaye kiran ya daki dodon kunnanta, idanuwan ta dake a cike tab da ƙwalla sun mata nauyi ta buɗe tana kallon saman ceiling ɗin da ta ke fuskanta, fitilu ta gani guda ukku suna lilo, sune suka haskaka cikin ɗakin da take a kwance saman fata mai gashi gashi a jikinta, gaban ta na faɗuwa ta zabura ta miƙe zaune tana faman bin ko’ina na ɗakin da kallo a ƙoƙarinta nata ga wanene ke yi mata magana.

“ina a bayanki!” jin hakan yasa ta yunƙura ta miƙe tare da juyawa tana kallon shi, giant ne sanye cikin shigar su ta baƙaƙen kaya ya goya hannayen shi saman faffaɗan ƙirjin shi, waro ido waje ta yi kafin ta zabura ta watsa da gudu da niyyar ta nemi ƙofar da zata gudu, sai dai har ta gama kewaye ɗakin babu ƙopa, a jikin bango ta manne kamar zata shige mashi idonta akan shi yayin da yake tunkarota, ta dinga girgiza mashi kai muryarta a dabarbarce ta ke yi mashi magana

“wlh kada ka kuskura ka ta6a ni, idan ba haka ba zan ƙona ka da ayar allah, mugaye kawai ai ni bansan na fito daga inda aka killace mu ba, kuma ni danish na fito nema ba wani abu ba…..” a gigice ta ke yi mashi magana, gani ta ke kamar zai rikiɗa ya koma wannan halittar da unaizah ta bata labari, tuni hawaye sun wanke fuskar ta, har ta fara tunanin yadda zata koma idan ya kusance ta kamar dai yadda aka yiwa unaizah ta mutu.

duk haukan nan da ta ke yi bai tanka mata ba, yayi tsaye a gabanta kamar yana ƙare mata kallo ne.

“la’ila ha’illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” a saman jikin shi ta dinga tottofa mashi addu’ar da ta ke karantowa.

hakan yasa shi sakin dariya sautin ya karaɗe cikin ɗakin da su ke a ciki, a matuƙar ruɗe take kallon giant ɗin jin yana dariya, ita dai a iya saninta giant basa magana balle har suyi dariya, bakomai ya faɗo mata a cikin ranta ba fa ce giant ɗin da ya taimaki batul ya dawo da ita cikin su, nan take ranta ya fara raya mata cewa ko dai shine!? tun daga ƙasa har sama take kallon shi, muryarta na rawa tace “wah…nene kai”? a tsanake ya soma magana “ɗan adam ne ni, sai dai mun banbanta da juna saboda ni giant ne ba cikakken mutun ba” mamaki ne ƙarara akan fuskar angel.

“ki kwantar da hankalin ki, ni bamai cutarwa bane, mai taimako ne, kada ki yi tsammanin nima mugu ne kamar sauran,” wannan maganar da yayi ce tasa hankalin ta ya ɗan kwanta, har cikin ranta taji ta yarda dashi sai dai ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba, taya akai ya kawota nan, sannan yake yi mata magana? anya kuwa giant ne? ko dai ɗan leƙen asiri ne ya shigo masu kurkukun…….”

“ba ɗan leƙen asiri bane, nima ma’aikaci ne na gidan kurkukun ƙaddara kamar yarda na faɗa maki am a giant! ” ya ƙara jaddada mata maganar shi, aruɗe ta kalle shi jin ya bata amsar tambayar da ta ke acikin zancen zucinta.

“wanene kai? meyasa ka kawo ni nan? kuma meyasa kake magana bayan ni a iya sanina giant basa magana”

juya mata baya yayi taku ɗaya zuwa uku kafin ya dawo gare ta, rumfa yayi mata da faffaɗan ƙirjin shi duk tabi tasha jinin jikinta

“tambaya ta farko, sunana salsabeel! tambaya ta biyu na kawo ki ɗakin nan ne saboda in isar da saƙona! tambaya ta ƙarshe giant suna magana ba kurame bane, a tsakanin su da prisoners ne ke basa magana, idan kika natsu zan fayyace maki komai, ki bani haɗin kai saboda bani da isasshen lokacin da zan 6ata, mintuna talatin suka rage man kafin garkuwar sautin dana sanya ta karye,” jinjina kai angel tayi alamar gamsuwa da bayanin shi.

“da ace tuntuni mun haɗu da juna, da baku kai tsawon lokacin nan a gidan kurkukun nan ba, ” sakin jiki ta yi jin abunda yace, har ta buɗe baki zatayi magana ya dakatar da ita

“kada ki katse ni, idan na kammala magana daga bisani za ki iya jera min tambayoyin ki idan lokaci bai ƙure mana ba” jinjina mashi kai tayi alamar taji maganar shi.

“ni da mahaifiyata bamu da burin daya wuce mu kawo ƙarshen zuluncin da ake aikatawa agidan kurkukun nan, dukkan mu bada son ran mu muka kasance ma’aikata a cikin shi ba, mun miƙa wuya ne saboda fansar da mu ke so mu ɗauka da kuma kawo ƙarshen matsafan dake a cikinsa, mun jima da wannan ƙudurin acikin zuciyoyin mu sai dai ƙarfin mu bai kai mu iya ja da shuwagabannin dake mulkar kurkukun ƙaddara ba, saboda shaiɗanun mutane ne masu haɗarin gaske mai iya ja dasu sai allah ba dai mutun ba” angel ta natsu tana sauraron shi, ko motsi bata yi, har yanzu bata fahimci kan zancen shi ba, gashi ya hana ta tambaye shi.

cigaba da magana yayi “nasan har yanzu baki fahimci inda zancena ya dosa ba, ” dafe bangon da ta jingina dashi yayi da tafin hannun shi,

“tun kafin zuwan ki kurkukun nan munsan komai dangane da rayuwar ki! kaifin basirar ki da hankalin ki shiyasa muka kwaɗaitu da son zuwan ki tun da labari yazo gare mu na cewa kece ƙaddarar prison! ,” gaba ɗaya ya gama ruɗar da ita, duk tabi ta kakkame jikinta.

“ma’anar hakan shine ke kaɗaice zaki iya tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara! kamar yadda yazo mana a allon tsafin mu, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mana ba nida mahaifiyata tsohuwa tamira!!!!” ƙara zare idanuwan ta tayi akan mask ɗin da ya 6oye ainihin fuskarshi, al’ajabi ne ya kamata jin ya ambaci sunan tsohuwa tamira a matsayin mahafiyar shi!

“ƙaddara kala biyu ce, mai kyau da mara kyau, a hasashen matsafa idan suka killace ki a hannun su zaki zamar masu kyakkyawar ƙaddara, amma idan suka bar ki a cikin jama’a kina yawo shine zaki zamar masu ƙaddara mara kyau…….” kasa haƙura ta yi hakan yasa ta katse mashi maganar shi da cewa “taya akai na zama ƙaddarar su”? ta jefa mashi tambayar tana kallon shi da zararrun idanu.

“kin manta me na faɗa maki?” ko da ya ke halin ki ne iya tambaya kamar ƴar jarida shiyasa kika gaza haƙura har saida kika katse mini magana ta” muryarta a dabarbarce tace “bazan ƙara ba”

gyaɗa kai ya yi kafin ya ɗaura da cewa “rayuwarku tana a cikin haɗari mai munin gaske, musamman ɗan uwanki danish”! gabanta ne ya faɗi jin ya ambaci sunan abun ƙaunar ta.

“kasancewar shi garkuwar kurkukun ƙaddara, matsafa sun ƙwallafa rai akan shi, saboda shi ɗin tamkar wata nasara ce agare su, idan dashi baza a ta6a iya rushe ginin kurkukun ƙaddara ba, su kansu matsafan baza a iya cin nasara akan su ba, shiyasa suka bashi babban matsayi na prison shield! a halin yanzu da na ke yi maki magana, ɗan uwanki danish ba cikakken mutun bane, he’s a dangerous giant! sun riga da sun bashi horon zama giant duk wani zunubi da kika sani mai girma a duniyar nan na rashin imani da tausayi sun koya mashi, sun riga sun yi transforming ɗin shi into a giant, horo ne wanda ba mutane zalla suke basu shi ba harda baƙaƙen shaiɗanun aljanu, harshe na bazai iya furta maki abubuwan da su ka yi mashi ba da kuma wanda su ka sashi ya aikata kafin su tabbatar da komawar shi giant……..” bai ƙarasa maganar ba ganin ta sulale daga jikin bangon zuwa ƙasa, zuciyarta ba ƙaramin karaya tayi ba, idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla, bakomai take hangowa ba face fuskar danish ɗinta! yanzu shikenan sun canza shi zuwa giant, sun 6ata mashi rayuwar shi sun gur6ata mashi tunanin shi.

zuƙunnawa salsabeel yayi agabanta saman ƙafafuwan shi,

“Lokaci Yana tafiya, agurguje Zan faɗa maki yadda za ku Yi don ku gano ƙofar nan da zata fitar daku daga Cikin kurkukun nan, shine abu mafi muhimmanci agare ku!

Cikin shessheƙar kuka tace mashi “Idan dagaske ne Zaku iya taimaka mana mu fita zanji dadi sosai, sai dai Ni bazan Iya barin kurkukun nan ba tare da Danish ba, Dole in tafi dashi, in ba haka ba, Ni zan tsaya in yaso sauran ƴan uwan mu su ku6uta,” sosai ta fashe mashi da kuka.

“Ni kaina bazan bari ku tafi ba tare da Danish ba! Domin kuwa shi ba iya garkuwar kurkuku bane, Ku kanku garkuwa ne agare ku! Fita prison ba abu bane mai sauƙi, Shi kaɗai ne zai Iya taimaka maku don ku gudu cikin sauƙi, dalilin da yasa nace haka saboda ginin kurkukun nan a cikin ƙurmin Daji ya ke, Idan har Allah yasa kuka samu damar fita zaku faɗa cikin Daji ne mai hatsarin gaske mai ɗauke da mugayen namun dawa, Sannan tafiya ce wadda ƙafa bazata ta6a iya yin ta ba, amma in dai Garkuwa Yana a tare daku bazai bari wata dabba ta cutar daku ba, Koda kuwa Zaki ne ko Kura zai Iya rikiɗa ya koma irin suffar su don yayi faɗa dasu harma yayi nasara akan su…….” dakatawa ya ɗanyi da yin jawabin, Itama Angel tuni ta dakata da yin kukan tana kallon shi, Zuciyarta cike da mamaki haɗi da rudanin maganganun shi, Kuma daga gani ba ƙaramin mutun bane.

“Bana so ku ƙara Wata ɗaya a gidan kurkukun nan saboda muna gab da shiga watan da za’a gabatar da Black Night, taro ne na matsafan duniya da zasu halarta a gidan kurkukun nan daga ƙasashe daban daban zasu zo, ranar gwada rashin Imani, ranar zubda jinin prisoners, Idan muka bari ranar ta riske ku a cikin kurkukun nan, bana tunanin ɗaya daga Cikin ku zai Rayu! Dalilin da yasa suka daina zuwa ɗaukar ku saboda sun dakatar maku da Jinin al’adar ku na mata saboda tanadin da su ke yima wannan ranar, tsawon watannin da kuka ɗauka ba ku yi Jini ba, a ranar zasu yi maku sihirin da zaisa ya dawo maku gadan gadan don su gwada rashin imani akan ku……” Hankalin Angel ba ƙaramin tashi yayi ba, Idanuwanta azazzare ta ke kallon mask ɗin fuskar shi, tsigar jikin ta duk ta tashi haiƙam jin abunda yace,

“Lokaci Yana ƙure mini, Yanzu Zaki Iya yi mini duk wata tambaya dake a cikin zuciyar ki” Numfasawa tayi kafin ta soma jera mashi tambayoyi akan abubuwan da suka cunkushe mata kwakwalwar ta.

“Ka ce mini kai ɗan tsohuwa Tamira ne! Dama tana da ɗa? Da farko ta ta6a faɗin cewa da ace ta ta6a yin aure da tuni ta yi jika dani, daga bisani kuma ta gaya min cewa Itama prisoner ce kamar mu tun tana ƙarama aka kawota gidan kurkukun ƙaddarar harta girma ta yi aure harta haifi ya’ya da jikoki, kaina ya ɗaure, Kuma meyasa ku ke son ɗaukar Fansa? Sannan taya za’ai mu iya ganin ƙofar da zata fitar damu daga Cikin kurkukun, Bayan haka inaso insan ta yadda zamu taimaki ɗan uwanmu Danish Ya dawo Cikin hayyacin shi, menene dililin dayasa ake kira na da Ƙaddarar Kurkuku? Itama ƴar uwata Batul Akwai sunan da aka sanya mata a bayan rigarta Heart beat of prison, na jima inason sanin meyasa aka banbanta mana uniform ɗinmu dana sauran Ƴan uwanmu? Suwane ne keda gidan kurkukun nan? Waye ya sadaukar dani?” tun da ta fara jera mashi tambayoyi bai katse ta ba, har sai da takai ƙarshe tukunna ya soma magana a tsanake.

“Kamar yarda na faɗa maki da farko haka zan maimaita maki a yanzu, Ni ɗa ne ga tsohuwa Tamira! Ni kaɗai ne ɗa da ta haifa, wata’ƙil ta gaya maku hakan ne gudun kada asirinta ya toni a fahimci cewa Kamar tana son kusan wani abu dangane da rayuwar ta ne, wanda Yin hakan Babban matsala ce agare ta, Shiyasa ta ke yi maku ƙarya a kalamanta, Dalilin daya sa muke son ɗaukar fansa Saboda mahaifi na da su ka yi silar mutuwar shi, Babban malami ne wanda duniya tasan da zaman shi ana kiran shi da Habibullah, Yana ɗaya daga cikin manyan Malamai na duniya masu zagaye ƙasashe domin yin da’awa, Allah yayi mashi baiwar ilimi, ɗan ƙasar Nigeria ne, Tun da ya ke bai ta6a yin aure ba, a zamanin shi baida burin daya wuce Yayi koyi da manzo SAW wurin karkato da hankulan waɗanda basuyi imani da Allah ba don Ya Musuluntar dasu, Ita kuma mahaifiyata tsohuwa Tamira Ƴar Ƙasar America ce ba musulma bace bata da addini, Farkon haɗuwar su da mahaifiya ta yaje ƙasar Dubai domin gudanar da gasar Musabaƙa ta karatun alƙur’ani ta duniya da aka gayyace su tare da manyan malamai na sauran ƙasashen duniya A babban birnin Dubai wato Abu dhabi, A can Allah ya haɗasu itama lokacin taje ƙasar Gudanar da harkokin kasuwancin ta, kamar yarda ya bani labari tun da yake bai taba sanyawa ran shi zai so wata ƴa’ mace har takai su ga yin aure ba, sai gashi ƙaddara ta haɗa shi da auran Baturiya ƴar ƙasar america, bakomai ne yasa shi amincewa da tayin soyayyar da tayi mashi ba, face don ta nuna tana so ta musulunta in har ya amince zai aureta, kinji dalilin daya sa har ya aureta ba tare da sun samu matsala ba, kinsan su turawa da zarar yaro ya haura 18 years Yana da ƴancin da zai yi komi yake so, Iyayenta basu son auran sai dai ba yadda zasu yi dole suka haƙura tabi za6in ranta, Bayan sun dawo ƙasar Nigeria ne ta musulunta, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma dangin shi ba, tun da iyaye na suka yi aure basu ta6a haihuwa ba, Har saida auran su yakai shekara goma tukunna Allah ya ƙaddara samuwata, A lokacin sun manyan ta mahaifina Ya tsufa, Ita kuma Mahaifiya ta tana da shekara arba’in a duniya..” dakatawa ya ɗanyi da yin Maganar, Angel ta zuba mashi ido tana jiran yaci gaba da bata labari.

“Akwai wata baiwa da Allah yayiwa mahaifina, duk idan ya haɗu da mutun mai sihiri a jikin shi sai ya gane, To haka ce ta faru a tsakanin shi da ɗaya daga cikin shuwagabannin dake ruƙe da kurkukun ƙaddara, a lokacin an gayyace shi wani taro jihar Kano state za’a yaye ɗalibai da suka Haddace alƙur’ani mai girma, A filin taron Allah ya haɗa su dashi, tun da sukayi tozali da idon junansu hankalin shi yaƙi kwanciya, Saboda matsafa suna jin shakkar habibullah, tun bayan da aka kammala taron Mahaifina ya dawo gida yana ta tunanin wannan mutumin da su ka haɗu a wurin taro, Abun da ya ɗaure mashi kai Duk wurin shine babban Mutun da aka gayyata, basu ta6a haɗuwa dashi ba sai ranar, shigar mutuncin da ke a jikin shi ta bashi mamaki matuƙa, kuma sananne ne a idon jama’a, Bibiyar rayuwar shi mahafina yaci gaba da yi don ya gano me suke aikatawa saboda ya gane bakin sihiri yake da shi, duk inda yasan za’ayi taro na manyan mutane sai yaje don ya haɗu da wannan mutumin kuma cikin sa’a suke haɗuwa dashi harma su gaisa, A wata rana ne Bayan an yi wani taro na manyan mutane, mahaifina yabi bayan su a 6oye basu sani ba har yaga kaɗan daga cikin abunda suke aikatawa, Hankalin shi ya tashi matuƙa a daren ranar bai kwana a garin da akayi taron ba, Tsakar dare ya dawo Kaduna, babu wanda yasan da dawowar shi a wannan ranar sai dai muka gan shi ya shigo gida, ashe tun lokacin da yake yi masu leƙen asiri sun gan shi suka ƙyale shi don suga iya gudun ruwan shi, a lokacin da ba muyi tsammani ba Matsafan nan suka kawo mana hari, tsakar dare su ka yi mana zuwan bazata a cikin gidan mu, Gaba ɗaya suka tattara mu da mahaifiyata dani kaina da mahaifina, kinji silar kasancewar mu agidan kurkukun ƙaddara! Ɗakin da kuke rayuwa acikin shi anan suka kulle mu, mu duka ukun, tun kafin a sabunta ginin tun yana tsoho, Mahaifina yayi ƙoƙari wurin ganin ya nema mana hanyar da zamu ku6uta amma abun ya faskara saboda babu ƙopa a cikin ɗakin a datse yake tako Ina, Akan idon shi mugayen matsafan nan suka yi amfani da mahaifiyata da kuma ni kaina duk don su ƙuntata mashi, tsabar baƙin Cikin wannan abun yasa shi kamuwa da ciwon zuciya, mun fuskanci tashin hankali a hannun Giants dake tsaron kurkukun nan, Kamar yadda ake baku abinci sau ɗaya a rana haka suke bamu, Mahaifina bai cin Abincin shi ni yake ajiye mawa don kada inji yunwa, yana matuƙar sona, Nima ina ƙaunar shi, har roƙon mu yayi akan mu yafe mashi saboda shine silar jefa mu cikin halin da muka tsinci kan mu, da ace baiyi masu leƙen asiri ba da duk hakan bata faru ba, Ire iren waɗannan maganganun da yake yi mana ba ƙaramin karya mana zuciya yake yi ba, da kanshi ya faɗa mana cewa zaiyi mana hanyar da zamu gudu daga Cikin kurkukun Amma baya jin zai rayu, Yayi ƙoƙarin sama mana hanya koda ta bango ne mu bi mu wuce Sai dai hakan ya faskara, gashi komai muke yi idon su akan mu suna kallon mu, da zarar sunga ya fara ƙoƙarin yin ibada sai su shigo su kamamu suna azabtar damu nida mahaifiyata duk don ya dakata, Da zarar sun fara yake dainawa saboda baison su halakar damu, Bayan mun ɗan samu sassauci daga wurinsu ne yaci gaba da neman hanya a cikin ɗakin, Har Allah yasa ya gano wata tsohuwar Hanya da ruwa ke bi ya wuce ta cikin ta, Girman ƙofar mutun zai Iya bi da rarrafe ya wuce ta cikinta, koda ya gano hanyar bai bari sun fahimci hakan ba, Ya dinga bi a sannu wurin ganin ya tono ta saboda A garƙame take sun rufe ta da dakakken ƙarfe wanda Idan har ba Sihiri Mutun ke gare shi a jikin shi ba bazai Iya buɗe ta ba, Taya zai Iya buɗe murfin ƙarfen dake a jikinta bayan komai muke yi suna kallon mu? Zasu gane ne Asirin shi ya tonu, Silar hakan kuma zamu iya rasa rayukan mu, Abunda mahafina yayi a wurin da ya zauna yayi amfani da Baiwar ilimin addini da Allah ya bashi, addu’o’i ya dinga yi yana tottofe cikin ɗakin, Tsawon kwana biyu ya ɗauka bai motsa daga wurin ba, babu ci babu sha haka ya zauna yana kai kukan shi ga Ubangijin mu Allah subhanahu wata’ala, Silar wannan addu’o’in da mahaifina yayima wannan wurin yasa garkuwar sihirin da ke a zagaye da sashen ta karye, har yau har gobe matsafan basu Iya sanin meke wakana a ciki ba, Muddin Mutun ya shiga wurin baza su iya ganin shi a allon tsafin su ba, Mu kan mu sai daga baya muka fahimci cewa garkuwar sihirin da ke a wurin ta karye, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mana ba, sai dai kash muna shirin 6alle ƙofar don mu gudu ciwo ya turniƙe mahaifina ya faɗi ƙasa Yana ambaton kalmatusshahada, Dama yace mana da wuya ya rayu saboda cuwon zuciyar da matsafan suka dasa mashi ga ba magani, Munyi kuka tamkar ran mu zai fita, Yana a cikin mawuyacin hali yake roƙon mu akan mu tafi kada mu tsaya jiran shi, kada suzo su kamamu.

Bamu ji maganar shi ba, Muka ƙi tafiya saboda mun sanyawa ranmu cewa dole sai dashi zamu gudu, Muna tsaka da ƙoƙarin dawo dashi hayyacin shi don ya tashi mu tafi, Giants ɗin dake kawo mana abinci suka ritsa damu, Nan take kuma mahaifinmu Ya cika, Mu kuma suka tasa ƙeyar mu zuwa can cikin kurkukun, nasan dole an neme mu an kuma yi Addu’oi sosae saidae bawa baya wuce ƙadddarar sa, tun daga wannan lokacin Suka maida Mahaifiyata ma’aikaciyar su ni kuma suka bani horon zama Giant, horo mafi wuya a duniyar nan, Miƙa wuyan da mu ka yi gare su muka zama masu biyayya shiyasa suka yarda damu sosai musamman mahaifiyata tsohuwa tamira, Tabbas mun aikata babban kuskure na bin umarnin matsafa saboda son ɗaukar fansa duk da da farko da suka yi mana tayin aikin ko su kashe mu kin yarda mukai sai daga baya ita Mahaifiyar tawa ta amince saboda a tsarin su ba su yi ma mutun sihiri don ya amince zai yi masu aiki sun fi so da kan ka Amince kana a hayyacin ka, sai daga baya ne ake baka sihirin a koya ma abubuwa, lokacin ba irin ƙoƙarin da ban yi ba wurin nusar da ita kan illar hakan don kuwa sai mun yi ridda amman ta kafe dama kuma tubabba ce, ina ji ina gani mahaifiyata tabar addinin musulunci ta shiga Cikin matsafa sosai saboda taci galaba akan su, a lokacin ta roƙe su kan kar su wulaƙanta gawar Mahaifina su maida ta gida a samu ai masa sutura suka amince don dama ba zatai masu Amfani ba sai ma taja masu matsala, Amma ni an sha daga dani kan in amince naki, k’arshe dai soyayyar uwa ta kwashe ni da kuma nuna man da tayi in muka kawo k’arshen su hakan kaman jahadi ne mukai daga baya sai mu tuba mu rok’i Allah ya yafe mana, da haka na amince saidae ni har yanzu musulmi ne don zuciyata tak’i yarda in bar musulunci sai dai kuma bana sallah gaskiya, Saboda a gidan kurkukun ƙaddara ba’ayin sallah shine abu mafi muni da suka tsana shiyasa a duk lokacin da mutun yai niyyar yin sallah suke burkita mashi lissafin ƙwaƙwalwar shi, Ba don mun so muka kasance Ma’aikatan gidan kurkukun nan ba, kafin mutuwar mahaifina yayi mana addu’a mai ƙarfi akan Allah Kada ya basu nasara akan mu, Ya roƙi Allah da ya bamu ikon Tarwatsa matsafan da ke ruƙe da kurkukun ƙaddarar nan, Inaji araina cewa Addu’ar mahafina ce take bibiyar Rayuwata shiyasa har yau har gobe hankalina bai ta6a gushewa ba, ina sane da komai, duk wani zalunci da ake aikatawa bana ɗaya daga Cikin masu yi, ban ta6a kisa ba tun bayan da aka horar dani nazama Giant, silar hakan yasa har yau basu bani matsayi mai girma ba amman suna d’aga man sosae sakamakon mahaifiyata da tay mubaya’a gaba daya, Ina matuƙar tausayin rayuwar Danish! ni na fara rayuwa a gidan kurkukun nan na mallaki hankali na, shi kuma tun yana jinjirin shi bana tunanin ko cibi an yanke mashi a haka aka kawo shi nannaɗe cikin Towel, Matsafa sun girgiza da ganin irin kyan da Allah yayi mashi, wlh banji daɗin yadda suke sarrafa rayuwar shi ba, Yaron yana da kaifin basira fiye da tunanin ki, Allah yayi mashi baiwar da zaiyi wuya asamu mai irinta, Yana da saurin haddace abu, he’s a gifted sannan Yana da ƙarfi tunkafin su sanya mashi sihiri ajikin shi Danish Yaro ne mai ƙarfin gaske, ko ni nasha jaraba yin dambe dashi a gidan kurkukun nan tun yana da shekara sha biyar yake bamu wahala, Da biyu suke haɗa mu Faɗa dashi, don su jaraba ƙarfin shi, Abun da zai baki mamaki mu tsafi ne ajikin mu, shi kuma babu sihiri a haka yake cin uban mu……” Sosai Angel ta fashe da matsanancin kuka tausayin danish ya kamata, ashe tun yana jariri aka sadaukar dashi agidan kurkukun ƙaddara, maganar da Salsabeel ya gaya mata ta ƙara Sanya mata ƙaunar Danish acikin zuciyar ta, son shi ya ƙara ninkuwa, Ji take kamar tayi fiffike taje inda zata ganshi don ta rungume shi a jikin ta.

“Sauran tambayoyin da kikayi mini bazan iya amsa maki ba saboda babu isasshen lokaci, zasu iya riskar mu, Abu ɗaya da nake so kiyi mini alƙawari shine kiyi ƙoƙarin ganin kinbi duk wasu sharuɗɗa da zan faɗa maki don ku tsira daga Cikin kurkukun nan, Mun ɗaura buri akan ki Unaiserh, saboda ta hanyarki ne kaɗai zaki iya tona asirin matsafan da ke ruƙe da kurkukun ƙaddara! Muna so duniya tasan da zaman su, A san me ake aikatawa a gidan kurkukun, yin hakan da zakiyi shi zai janyo hankalin mutanan duniya daga nan za’a samu waɗanda zasu Iya kawo masu farmaki, Inaso ki ɗaurawa kan ki nauyin yin hakan ko dan saboda rayukan dake rayuwa acikin kurkukun nan cikin mawuyacin hali! Akwai ire iren ku da yawa wadanda basu ji ba basu gani ba, An kulle su an hanasu sakat, Kullum ne sai an rasa rayuka agidan kurkukun nan, kashe mutane suke yi tamkar kyankyasai, Idan har bamu kawo ƙarshen kurkukun nan ba to kuwa zasu cigaba da aikata 6arnar da babu ranar dainawa, Muna matuƙar jin tausayin yaran da ke rayuwa a kurkukun nan, Dan Allah Unaiserh ki taimaki rayuwar su! Ki daure ki jure wurin ganin kun tona asirin abun da ake aikata……” hannayenta Ya ruƙo a cikin nashi ya dinga yi mata magiya sautin muryar shi kamar zai fashe da kuka, Ga dukkan alamu sun gaji da ganin Zaluncin da ake aikatawa agidan kurkukun ƙaddara

Tun tana yin kuka har muryarta ta disashe da ƙyar ta samu ta tsagaita tana kallon shi tace “NAYI MAKA ALƘAWARI Idan Allah ya bani damar fita daga kurkukun nan zan tona asirin su harma mu bada gudunmawa wurin ganin an kawo ƙarshen su, Bi’iznillahi,

Ajiyar zuciya ya shiga saukewa kafin ya daidaita natsuwar shi yaci gaba da cewa “Silar sabunta ginin da aka yi ƙofar ta 6ace mana, amma muna hasashen tana a cikin ɗaya daga cikin waɗannan makewayin naku guda uku, akwai wata tukunyar fulawa da ke ajiye Cikin toilet ɗinku Mahafiyata ce ta ajiyeta saboda bayan an sabunta ginin shafen dake a ƙasan wurin bai zauna da kyau ba, kuma bakomai ya jawo hakan ba face silar zaman da mahaifina yayi awurin na tsawon kwana biyu yana ibada, to duk wani abu da ke da sihiri idan ya ta6a wurin bazai zauna ba sai ya nuna alama, gudun kada ta manta da ƙofar yasa ta ajiye wannan tukunyar fulawar, Idan kuna so shafen dake akan ƙopar Ya 6a66ako batare da kun sha wahala ba, Ku yi amfani da ruwan zafin da ake kawo maku a matsayin ruwan shan ku, da zarar kun yayyafa shi asaman wurin zai tsastsage daga nan ƙofar zata bayyana, amma fa sai kun yi takatsantsan, kada farin cikin ganin ƙopar yasa ku fasa ihu wanda zai janyo hankalin su………”

Wani irin Farin ciki ne ya lullu6e Angel, Bakinta yaƙi rufuwa

“Kada ku sanyawa ranku cewa dukkan ku zaku tsira, ba abune mai sauƙi ba, dole ku fuskanci tarin ƙalubale wurin ku6uta, musamman Makullin nan ɗaya da baya a cikin ku wato Danish dole ku dawo da shi saboda shi kaɗai ne zai Iya Cire murfin ƙarfen da ke a jikin ƙofar cikin sauƙi ba tare da kun sha wahala ba.

Cikin shessheƙar kuka tace”Taya zamu iya gano Danish har mu iya dawo dashi Cikin hayyacin shi”? bai amsa mata tambayar ta ba, ganin ya miƙe tsaye yasa itama ta miƙe tana kallon shi,

“Akwai ruwan zam zam da mahaifina yake yawo dashi cikin aljihun rigar shi, ya mallake shine a wurin wani hamshaƙin malamin addini wanda ake kira da Shaykh al-ikhlass ɗan ƙasar Madina, shi ya yi mashi kyautar jarkar ruwan zam zam ɗin duk mutumin da ya kur6i ruwan abakin shi ya haɗiya to zaiyi wuya Sihiri yayi tasiri a jikin shi, sannan waraka ne ga kowace irin lalura da izinin ubangiji, Dubarar da mahaifina yayi sai ya dinga ɗibar ruwan xam xam din yana ɗura shi cikin ƙananun robobi, duk in zai fita a cikin aljihun shi yake ɗauka ya tura, saboda tsaro baisan ko Allah zai haɗa shi da mai buƙatar taimakon wata lalura dake damun shi, shiyasa Yake yawo da robobin ruwan cikin aljihun shi, to aranar da matsafa suka farmake mu tsakar dare suka kawo mu kurkukun nan akwai kingin roba ɗaya da ta rage a cikin aljihun jallabiyar shi, Kafin ya rasu ya damƙa ma mahaifiyata ita mun 6oyeta wurin da babu wanda ya sani daga ita sai ni, Robar ruwan zam zam ɗin tana a cikin ɗakinta inda ku ke rayuwa, da zarar kun dafa jikin bangon ƙofar zata buɗe da kanta, Sai ku shiga ku ɗauko ta.

Ke za ki nemo Danish a gidan kurkukun nan saboda ke kaɗaice zaki iya sarrafa tunanin shi amma fa sai kinci baƙar wahala domin kuwa baisan wacece ke ba a yanzu, Har kashe ki zai Iya yi, komai zai iya aikata maki, duk runtsi duk wuya karki bari tsoron shi yasa ki kasa watsa mashi ruwan a cikin bakin shi, ki tabbatar ya haɗiye shi.

Sannan Giant basa jin Bugu, Wuƙa bata iya tsaga jikinsu, haka zalika harsashin bindiga bai iya tsaga fatar su, Mutane ne masu hatsarin gaske, ƙarfin shaiɗanun aljanun da ke a jikin su ya rinjayi halittar su ta ɗan adam, Giant’s heart ba irin zuciyar mutun bace, ta shaiɗanin aljani ce, Ko da ace kinyi nasarar sanya mashi ruwan abakin shi zai dawo hayyacin shi na ɗan lokaci ƙanƙani amma duk lokacin da Giant’s heart ɗin shi ta motsa zaku ci baƙar wahala, Shiyasa ni ke so ki dage dayi mashi addu’a saboda ku samu ya fitar daku daga Cikin kurkukun nan, In yaso daga baya idan kuka faɗa cikin mutane zan baki Address ɗin gidan mu da mahaifiyata ta rubutamin don in baki, idan ku ka duba zaku iya samun sauran robobin ruwan zamzam na mahaifina daya ajiye a ƙarƙashin gadon shi, da shi zaku dinga yin amfani wurin shawo kan Danish a duk lokacin da Giant’s heart ɗinshi ta motsa. Ki kula da rayuwar shi Angel Ki ɗauka cewa amanar Danish na baki, ki ruƙe mini shi hannu bibbiyu, kada ki kuskura ki bari yayi nesa dake, ku kasance atare domin mu samu muyi nasara agidan kurkukun nan, Danish yasan komai fiye da tunanin ki, mun riga shi zuwa kurkukun nan amma yafi mu sanin komai, shi kaɗai yasan hanyar da za’a iya ruguza su, Matsalar shi ɗaya mugun miskili ne kuma yana da taurin kai, zaku ci wahala kafin ku samu Ya baku haɗin kai……….” Yana kai ƙarshen maganar shi da sauri ya zura hannu cikin ajihun baƙin wandon dake ajikin shi ya zaro takardar dake a ninke ya miƙa mata, Address din gidanmu ne dake a Kaduna state, Daga yau ba zaki sake gani na ba, duk wani taimako daya dace inyi maku na riga nayi, yanzu saura ku ya rage ku fara naku, Zamu jira har zuwa lokacin da zaku dawo mana da kyakkyawan sakamako, Sai dai bamu da tabbacin zamu kai lokacin a raye nida mahaifiyata ko kuwa…..” bai ƙarasa Maganar ba Angel ta faɗa jikin shi ta rungume shi sosai ta fashe da kuka mai sautin gaske, Hannayen shi biyu ya ɗaura a saman bayanta ya ƙanƙame ta sosai tamkar ƴar cikin shi, Sun ɗauki tsawon lokaci rungume da juna, kafin daga bisani taji kanta ya fara sara mata, nan ta ke idanuwan ta suka lumshe bacci mai nauyi yai awon gaba da ita………

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button