Gargadar So Chapter 48 By M Shakur
Sosai Hawwa ke masifa aranta tana shiga cikin gidan, menene business din yaron nan da gidansu? She don’t understand sun masan wayeshi kuwa, tana shiga gidan Umma tagani a tsakar gida tana gyara hatsi tana ganin Hawwa ta dauke kai Hawwa tawuce dakinta batare datace mata ci kanki ba, dakin kamshi Ramla tasaka turaren wuta, kwanciya tayi akan gado ahankali, Ammi tashigo tace “mezakici nadafa miki Hawwa?”Ahankali tadaura kanta kan cinyan Ammi tai shiru batamasan me bakinta keso ba, Ammi tace “bari zanje kasuwa sainamiki farfesu” gyadama Ammi kai tayi tace “Ammi kidauki ATM card dina akwai kudi” dan gyadamata kai Ammi tayi Ramla na shigowa dakin, Ammi tace “Ramla zauna da yayarki kome takeso kimata, bari natasa Aminu gaba muje kasuwa tare muyi cefane zan taho da flask ma asaka ruwan zafi banso daga yanzu kuna zagawa da ruwan sanyi kinjina baida kyau ma mace” gyadamata kai Hawwa tayi Ammi tadauki jakan Hawwan tazare ATM dan bawani kudin kirki takedashi ba, tanaso tasaima yarinyar abubuwa da yawa tace “natafi” atare sukace “saita dawo” tafice tna fitowa waje taga Baba da Aminu na magana dasauri Baba yadakata yace “Zainabu ina zaki”? Anatse tace “wai kasuwa zani Malam nadanyo cefane Hawwa tace zatasha farfesu kasan har yanzu bata iyacin abinci sosai, Aminu tashi muje ka kaini” dasauri Baba yamike yana rage murya yace “inataso muzauna muyi magana Zainab, to mutanen sun samin miliyan hamsin din sadakin Hawwa a account an bani gwalagwalan kuma amman na adanasu, kece mahaifiyar Hawwa inaso na zauna dake da ita mubata sadakin daganan sai mu karbi abinda ba’a rasaba mu mata kayan daki kekuma kiyi naki shirin kinfini sani dai” gadamai kai Ammi tayi tace “ba matsala Malam yau zamuyi maganan da daddare In sha Allah, Aminu tashi muje” tashi Aminu yayi daidai su Khadija na zuwa sunma Hawwa girki Baba ya dakatar dasu yace “ban kuma ce naji wani ya sanar da Hawwa zancen nan ba”Wucewa Ammi sukayi kasuwan, sun sayi kan rago, dadan yan abubuwan datakeso tama Hawwa girki dasu sannan tasiyo mata babban flask na ruwan zafi suna dawowa taga Hawwa ma na bacci tashiga girki Umma sai bambami take yanda yaran ta ke dakin Hawwa wlh suka shareta wajajen 3 Ammi tagama girkin sosai Hawwa taci takoshi sai yau ta iya taci abinci.Around 9 Hawwa na zaune kan gado tana duba wayanta tareda Ramla da yawanci ke tayata replying chats na yan wajen aikinsu dan kowa yaji tayi accident, Ammi nakan dadduma ta idar da salla but still tanakan dadduma tana jan charbi Baba yayi sallama yashigo dakin, da sauri dukansu suka dago kansu Baba yashigo yanama Hawwa murmushi yace “kinji sauki yarinyana? Wannan dakuka natsu ahaka me kuke da waya? Kinji sauki” Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh Baba” kallon Ammi yayi dake shafe addu’a yace “kin idar Zainab”? Gyadamai kai Ammi tayi takalli Ramla tace “tashi Ramla je dakin Umma zamuyi magana da Hawwa” hakanan dan faduwa gaban Hawwa yayi wannan dahar suna kada Ramla waje maganan me zasu mata? Wani ciwo gareta aka fada a asibiti? Daidai lokacin Aminu yashigo dakin dawata yar jaka kaman ghana masgo amman bottega ne mai bala’in kyau Baba yanunamai gabansa yace “zoka ijiye anan” ijiyewa yayi Baba yace “zaka iya tafiya Aminu” sannan yayi gyaran murya yadauki kujeran dressing mirror yazo wajen katifan dab da Hawwa itama Ammi tazo dab da Hawwa tazauna kan katifar, Baba yakalli Ammi data gyadamai kai yayi gyaran murya yaciro wayansa yabude yace “Hawwa na aurar dake, ga sadakin ki nan” yanuna mata alert na wayanshi na 50M yace “miliyan hamsin da dirhamin gwal dari gasunan” ya jijjiga mata jakan gabanshi, bugawa kirjinta yafara tana kallon Ammi takasa magana badai Baba yaji haushin Ni’ima yace ya aura ma Baban Yaseer itaba, Baba na kallonta yace “Ba Baban Yaseer bane mijinki ba Hawwa, na aurar dake ga someone even better, wanda ya fisa, yaro mai kunya, yaro mai natsuwa, ga dattaku ga girmama na gaba dashi, sunan mijinki Ibrahim Khaleel” bugawa kirjin Hawwa yayi sosai Ibrahim Khaleel Ibrahim Khaleel waye kuma Ibrahim Khaleel? Kaman Baba yaji abinda take tambaya anatse yace “Mahaifin Noor! Wanda ya ceto rayuwanki yakaiki asibitinsa sannan yabiya masu motocin dakika bata garin hatsari” Wani irin zabura Hawwa tayi ta yunkuro daga jikin pillow data jingina dashi a bango tana kallon Baba maganganun da Khaleel yamata na dawo mata see you soon! Babu wacce nakeso da bazan iya samu ba, bakinta har rawa rawa yake tace “Pops Boy?” Dasauri Baba da Ammi suka kalleta basu gane metake cewa ba arude tace “Baba wannan mutumin daya kawo yarsa jiya da daddare asibiti? Ammi likitan daya kawomu gida? Shi wai kuke cewa kun auramin?” Dasauri duk sukace eh Baba yace “ai yagayamin kusan juna kece kika ceto Noor da aka sace” hannu Hawwa tadaura saman kirjinta dake bugawa kaman zai fito dasauri, Baba yace “Hawwa” cikeda fushi Hawwa tace “Baba kasan waye Khaleel kuwa? Kunsan wakuka auramin? Eh Baba” shiru daga Baba har Ammi sukayi suna kallonta, zuciya ba dadi tace “Baba auri saki Khaleel yakeyi fa, dan shaye shaye ne Baba wlh, dan giya ne Baba” tsayawa Ammi da Baba sukayi suna kallonta ganin basuce komiba yasa dasauri ta matso kusada Ammi dake kallonta tace “Ammi wlh dan shaye shaye ne babu abinda bayasha, banda haka ga auri saki ya maida mata kaman riguna yacire wannan yagaji yasaka sabuwa, Baba ni koshine namijin karshe aduniyan nan bazan aureshi ba na tsaneshi, bantaba haduwa da wanda na irinsa ba, ko kadan baimin ba, kucemai banyin auren, Baba bazan zauna dashi ba” kallon Ammi Baba yayi, Ammi ma takalli Baba hankali tashe Baba yace “Zainabu anya Hawwa ita kadaine?” Dasauri Hawwa tace “Baba nataba maka karya ne? Baba wlh Khaleel dan giya ne ga auri saki ni bazan taba yarda da auren nan ba gaskiya cus shi ba mijin aure bane” sosai Ammi ke kallonta saikuma ta kalli Baba tace “Malam gobe muje wajen malamin dakamin magana muma Hawwa ruqiya” turus Hawwa ta tsaya tana kallon Ammi jin maganan datayi wai basuji metake fada musu bane?Baba ya jinjina kai yace “ba shakka” saikuma yakalli Hawwa dake kallonsu yace “Hawwa bakiso kiyi aure ne kin fiso kiyita zaman gida kawayenki na cimiki mutunci akan mazajensu”? Dafekai Hawwa tayi ganin Baba da Ammi basu fahimcetaba sun dauko magana daban, kaman zata fashe da kuka tace “Baba baku fahimce ni ba, bawai auren ne banaso ba, wanda kuka auramin ne ba mijin aure ba, Baba bakuyi bincike akanshi ba” da dan masifa Baba yace “ke kinyi bincike akan shi ne?” Shiru Hawwa tayi saikuma ta girgiza kai alamun a’a, cikeda da dan masifa Baba yace “sau nawa duka duka kikaje gidansu aikin Noor da aka kiraku?” Ahankali tace “sau biyu” dadan masifa Baba yace “mutumin da sau biyu kika hadu dashi shine zaki dingamai kazafi haka kinsan menene dan giya kuwa?” Yakalli Ammi yace “Zainabu tsakaninki da Allah zaki fadi badan ni ba bakuma dan Hawwa ba, kifadi iyakan gaskiyan ki har zuciya Khaleel yamiki kama da dan giya?” Anatse Ammi ta girgizakai tace “Hawwa ko kadan Ibrahim baiyi kama da dan giya ba, muna ganin yara masu shaye shaye munsani, tundaga kan halayyansu, mu’amalan su, yanayin magana da yanayin bakinsu ana ganewa Khaleel ba dan giya bane” dafe goshi Hawwa tayi ranta yayi masifan baci, Baba yace “kikace yana auri saki Ibrahima yasanar dani tun yana yaro dan shekara ashirin da hudu mahaifiyarshi kemai aure, duk yasaki matan ciki harda mahaifiyar Noor, baitaba neman aure da kanshi ba sai akanki daya ganki yaji kuma yanaso, sabida yayi auri saki ada baya nufin zaiyi dake ke zakiyi abinda za’a sakeki ne? Ga mahaifiyarki anan zata koyardake yanda ake tattalin miji da sauransu”baki Hawwa tasaki idanunta na tsatso hawaye tana kallon Baba dake kare Khaleel kaman irin yayi shekara da shekaru dayasan shi yace “na natsu da natsuwar Ibrahima! Na yaba da hankalinsa da kyauta da sauransu, abinda na lura akan yaron shine yaro ne mai shagwaba wanda daga gani iyayensa sun sangartasa koda kin aureshi abarayin ne zaki iya samin matsala dashi sabida yasaba kome yakeso yana samu, wanda rayuwan nan babu wani bawa da baida aibu, inada nawa kinada naki mamanki nada nata bature yace nobody is perfect” Ammi tace “kwarai” Baba yakalleta sai kuma ya tausasa murya yace “Hawwa agabana aka cimiki mutunci aka zageki aka goranta miki sabida bakida aure kin zaci ina farin ciki da hakan?” Yayi shiru yanuna Ammi yace “an zageta, an zageni, an zagi tarbiyan damuka miki, aka goranta mini, aka kira diyata da tai kwantai, aka miki kazafi, kin dauka ina farinciki da hakan?” Jikin Hawwa sanyi yafara yi, anatse Baba yace “danabar dakin nan jiri ya debeni zan fadi Ibrahima yatareni” Baba yawani kalli saman dakin hawaye na gangaromai daga idanu kaman mai tuna abubuwa da dama yace “Ibrahima ya kamani, yarikeni ajikinsa kaman daman ya sanni daga wani waje, yakaini daki yabani kulawa da agaji na gaggawa, cikin tattausan lafazi yace Baba kadena damuwa zan auri Hawwa!” Sai kawai Baba yafashe da kuka sosai yace “ko yaran cikina basu tabamin hallaccin da Ibrahima yayimini ba, ya fitar dani kunya, yanunamin soyyaya haka yanunama yata, yakawo iyayensa aka daura aure, wani awaje ya sharemin hawaye sai kene yanzu Ina sanar dake namiki aure zaki watsamin kasa a idanu” Baba yafashe da kuka sosai Ammi ta taso ganin da gaske Baba kuka yake tace “Malam dan Allah kayakuri abin baikai ga hakaba ya isa ya isa” Hawwa Baba yanuna yace “Zainab yarinyar nan tasan yanda nake sonta kuwa? Ita kadai nake gani natuna Aisha matata ita kadai, amman maisa Hawwa ke wahalar dani tana bani ciwon kai” wlh at first Ammi tadauka Baba just lie lie cry yake but sosai Baba ke kuka, Hawwa tazo bakin gadon ahankali tadafa kafan Baba tace “Baba dan Allah kayakuri bahaka nake nufi ba dan Allah”Fashewa da kuka Baba yayi yace “Zainab kinsan shekara nawa rabona danai bacci? Wlh tunda Hawwa takai shekara ashirin da biyar batai aure ba daga ranan har zuwa ana gobe zatai hatsari bantaba kwana gari yawaye ban tashi inyi salla inama yarinyar nan addu’a tayi aure tasami miji nagani ba, bana bacci bana iya runtsawa tunanin Hawwa nake, sai ranan da aka daura mata aure shekaran jiya shine nai bacci sai asuba natashi da jiya dakuma yau in 4yrs ina abu daya sai ranaku ukun nan na iya bacci sabida na aurar da ita” dasauri Ammi itama tace “Malam meyayi zafi haka? Dan Allah kayakuri ya isa” takalli Hawwa dake kukan bakin ciki ganin abinda Baba keyi sabida dan iskan Khaleel tace “Hawwa I know concerns naki, tunda ba kisan kai Ibrahim yake ba, ko saida yara, ko fashi, ke kaddarama yana shaye shayen ke ba matarsa bace? Ai mata Allah yabasu power da suna iya gyara mazajensu from bad to good, banda haka bayan Baba yazo damaganan na jera kwana biyu a asibiti ina alwala nayi raka’a biyu nayi du’aul istikhara wlh naji na natsu da Khaleel and it’s a sign auren ku zaiyi albarka, Hawwa koma meke damunki dake hanaki aure fight it this time, karki bari shedan yayi nasara akanki, auren nan yanda aka daura an daura kenan har abada kibar zancen rabawa” baki Hawwa tabude zatai magana Baba yadaga mata hannu.


