Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 3 Hausa Novel

Tayi dariya itama ta cigaba da cin abincin.Bayan ya hadiye na bakinsa yace ‘Ina ga ai ya kamata in an jima muje mu debo su Afaf ko? Tun da suka ji an kawoki suke ta zumudi.’Ta kalleshi tana wasa da cokalinta a kan abincin saboda ta riga ta koshi, tace ‘Babe ai na zata za a barsu sai mun dan huta, kaga shekaran jiya fa na tare. Ko gajiyar biki ma ai ban gama hucewa ba.’‘Haba, ai sai ku huta tare, kin san suma fa they missed home don tunda mahaifiyarsu ta rasu rabonsu da gida.’’Allah sarki, ni kaina ina dokin dawowarsu nan but babe please ka bari koda zuwa next week ne na dan gama kwance kayana.’ ta fada da muryar magiya da lallashi.Ya ture farantin gabansa ya sake cika kofinsa na zobo, ya dan gatsina fuska yace ‘Ok, amma dai ba zasu ji dadi ba. Dazu muka gama waya da su suna ta dokin dawowa wajenki.’Ya mike ya nufi wajen TV yayinda itama ta mike ta fara tattara kwanukan tana cewa ‘Allah sarki, in sha Allah next week da ni zamu je mu daukosu kaga daga nan ma sai mu biya gaba daya mu gaida Mommy mu gaida su Hajiya sai mu dawo gida.’’Umm!’ ya amsa yana canza channel din TV.Ta cigaba da kwashe kwanukan tunani kala-kala yana yawo a kwakwalwarta; ta yi zaton yana dokin kasancewa da ita, ta yanda zai bari su dan kara fahimtar juna kuma su more amarcinsu kafin ya dauko yaran amma shi yana maganar yau. Babu kananan yara a gidansu amma kusan kullum suna tare da yaran Yaya Mama, ta san yara ba zasu bari ta mori amarcinta ba tunda su rayuwarsu suna bukatar kulawa ne kullum. Musamman tunda ga Shukra mai shekaru uku kacal. Sati dayan ma da tace a kara kawai dai daurewa tayi don ita da a tunaninta ta sami kamar wata uku a gidan kafin ya kawo mata yara tunda a can ma inda suke ana kula dasu. To amma bata da wani zabi, zuwa next week din sai ta bishi suje su dauko yaran.…….Ana fara kiran magriba yayi alwala ya dauki mukullin motarsa, ya sameta a kitchen tana tsugene a tsakiyar kitchen din tana tuka tuwon shinkafa. Motsinsa ya sa ta saurara da tukin tuwon ta juyo, ta dubeshi tace ‘Fita zaka yi? Ko masallaci zaka je?’’Eh, daga masallacin zan wuce na dubo yara sai kuma na wuce wajen Hajiya.’Ta dan langabe kai ‘Babe ai da ka dawo, nima sai na shirya muje na gaida Hajiyan.’’No ki bari next week zamu je tare.’ Ya amsa yana duba wayarsa. Ta saki tukin tuwon ta mike ta nufeshi da niyyar ya rungumeshi, sai dai ya dan kauce don haka ta gefe ta rungumoshi. Jikinta ya dan yi sanyi ta sumbaci kumatunsa tace ‘A dawo lafiya Babe, I will wait for you idan ka dawo sai muyi dinner tare. Ka gaida su Hajiya.’ ‘Ok.’ ya amsa sannan ya fice. ………A parlor ya sami Daddy, bayan sun gaisa suka dan taba hira. Daddy yace ‘Wai ka debo yaranka kuwa?’ ‘Ban debo su ba, tace a bari sai zuwa next week idan ta gama hutawa.’ Yana wani kau da kai.‘To babu laifi; Amma fa idan ka daukosu to ka saka ido, ka san mata yanzu basa son riko. Idan baka yi wasa ba haka za a mayar maka da yara kamar almajirai a gidanka.’ ‘In sha Allah zan kula, duk da ma na kula kamar bata da muguntar.’’A’a, basu fa da tabbas, kai dai ka sa ido. Kuma ka dinga bincikar duk motsinsu.’ Ya fada yana nuna shi da yatsa. Suka dan sake hira sannan ya shiga wajen Hajiya inda ya samesu ita da Yaya Jidda suna hira; da yake ita gidanta kusa da gidan ne wataran ma sai an yi sallar Magriba take zuwa. Bayan sun gaisa suka cigaba da hirarsu gaba daya. Jimawa kadan Yaya Jidda tace ‘Musty ina amarya? Tsohuwar sirikar taka ta baka yaran ko har yanzun ba zata bayar ba?’Ya gyara zama yace ‘Haba, sai kace ita ta haifa min su ai dole ta bani su.’Hajiya tace ‘Sai yaushe zaka dauko su?’ ‘Tace wai a bari ta huta zuwa next week, don ni da yau ma na so a daukosu. Yanzu ma idan na fita zan je na kai musu biscuits din da na saya musu.’ Yaya Jidda tace ‘Wai wacece tace a bari ta huta? Khadijan?’ Yace ‘Eh, tace wai a bari ta huta ta gama ware kayanta kafin a kawo su.’’Kai Musty! Yanzu kai har ka bata dama su da gidan ubansu sai ta ga dama za a kawosu, to me tayi ya gajiyar da ita har take bukatar hutu.’ ‘To nima dai haka na gani, amma dai zan ga yanda zamu yi.’ Ya fada yana kauda kai.Hajiya tace ‘To ka dai dinga kula sosai don kada ta dinga cutar da su, ka sa ido sosai don yanzu mata ba tausayi ne da su ba.’Yaya Jidda tace ‘Musamman gashi tun yanzu ta fara iyayi da kafa dokoki, a jira ta huta kafin a kawosu gidan ubansu.’Haka suka gama hirarrakinsu suna jaddada masa ya sa ido sosai kada Khadija ta cutar da yaransa; yayi musu sallama ya wuce gidan iyayen Ma’u wajen yara. Sai da ya tsaya a hanya ya saya musu yoghurt da gasasshiyar kaza sannan ya wuce. Yana shiga bayan sun gaisa da Mama ta turo masa yaran suka sameshi a guest room. Suka karbi kajin da yoghurt suka kaiwa Mama; wadda ta riga ta saba idan ya kawowa yaran abu to ba zai bata ba sai dai ya bawa yaran a hannunsu su su kai mata; sannan suka dawo wajensa suna ta murna don su sun shirya kayansu tsaf yau zasu tafi wajen Anti Khadija.Hakan yayi masa dadi don dama hakan yaso. Nan da nan suka sheka cikin gida suka fara fitowa da kayansu, Anti Nihla kanwar Ma’u ta taya su duk suka fito da akwatunansu. Mama ta fito ta sameshi, bayan ta zauna tace ‘Ga mutanena nan tunda suka ji uwarsu ta tare sun kasa zaune sun kasa tsaye fa, ni da mukayi da su sai an kwana biyu amma ka ga suna ganinka sun fara fito da kaya. Kayan nasu ma fa wasu suna wajen wanki.’’Wallahi kuwa, ai babu komai daga baya sai na zo na karbar musu sauran, kuma ma ai zasu dinga zuwa in Sha Allah.’ Ya bata amsa.Haka aka gama fitar da kayan aka zuba masa a mota ya kwashe su suka kama hanya, suna ta murna zasu je wajen Anti Khadija. ……. Tunda ta gama tuwo tayi Sallah sai ta yi wanka ta shirya cikin bum short dinta da wata figalalliyar riga, ta sha turare sai kamshi takeyi ga gidan ma tayi fes da ko ina ta kunna turaren wuta kamshi sai tashi yake a hankali. Tana kwance a kan three-seater tana danna waya ta jiyo motarsa ya bude gate yana shigowa, ta tashi zaune ta dan gyaggyara tana jiran ya shigo ta taro shi daga bakin kofa. Mintuna kadan ta fara jiyo motsinsu a kofar shigowa parlor, ya zura mukullin yana kokarin budewa yana cewa ‘Afaf rike hannun Shukra na bude kofar.’ Ta dan yamutsa fuska tana kokarin ta gane shi da su waye; tas ta jiyo muryarsu gaba daya. Ta dan rikice kadan tana mamakin dalilin da yasa ya taho da su bayan ya amince sai next week.Ta jiyoshi yana zare mukullin daga jikin kofar; ta kalli jikinta yanda take kusan tsirara. Ta yi wuf ta zaga bayan kujera daidai lokacin da yake sako kai cikin parlor din, ta dauki jilbab dinta wanda yake ajiye a saman kujera ta saka. Tana karasa saka jilbab din suka shigo da gudu bayan ya shigo, suka hada baki gaba daya ‘Anti Khadija, Anti Khadija.’ Suka karasa da gudu suka rungumeta suna murna.Haka ta yashe baki tana amsa gaisuwarsu, ta dauki Shukra tana cewa ‘Shukra baby, ya Mama? Kin barota tana kuka ko?’Cikin muryarta ta gwaranci tace ‘Ba kuka take ba, ta ce ma na gaisheki.’’Ina amsawa.’Ta ajiyeta ta kama hannun Habib tace ‘Ya Habib, welcome.’ Ta kalli Mustapha suka hada ido, yayi sauri yace ‘Sun ki barina na taho sai da suka biyo ni, ga kayansu nan sai ku shigar.’’Uhm, bari mu gani.’ Ta amsa murya kasa-kasa. Ta dauki babban akwatin nasu ta ja ta nufi dakin yaran tana cewa ‘Afaf dauko wannan jakar mu iai daki.’

Back to top button