Hausa novels

Halysaah Page 149 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 149…Ajay ya sauke idonsa kamar zai juya ya koma, sai kuma bai yi hakan ba ya karasa cikin parlon ya zauna kan kujera ya gaida Hajja ba tare da ya hada ido da ita ba, Hajja dake kallonsa tace “Lafiya lau Ahmad, ya jikin?” Ajay yace “Alhamdulillah” Jay dai danna wayarsa kawai yake kansa a kasa, after some seconds ya mike yana kallon Hajja yace “Zan je in ci abinci….” Hajja ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace “To shikenan” Kofa ya nufa ya fice daga parlon, Hajja ta kalli Ajay tace “Ka shiga ka duba matar ka tana wancan dakin…..” Ajay dai bai ce komai ba, Hajja tace “Sarki na parlonsa warhaka ko?” Ajay yayi shiru, sai kuma yace “Ko suna masallaci, sai anyi isha’i yake dawowa cikin gida….” Tashi Hajja tayi ta fita daga parlonta, Ajay ya bi ta da kallo, sai kuma ya mike walking slowly ya nufi Bedroom din da Khaleesat take, he was so tensed amma haka ya dake yana tafiya toward the room…. Khaleesat na zaune daki tare da Yakumbo dake mata magana cikin ladabi da kwantar da murya, ita dai juya pepper soup din bowl din hannunta kawai take a hankali idonta a kasa, Yakumbo ta kara yin kasa da murya tace “Don haka ki saka a ranki wannan lamari da ya faru daga darajanki yayi a wannan masarauta me albarka, duk masu danganta ki da bazawara sun ji kunya ainun, na dade banga Hajja cikin wannan farin cikin da take ciki daga jiya zuwa yau ba a gidan nan, nasan har sarki sai da ya samu wannan labari me dadi, kuma babu inda labari bai je ba lungu da sakon masarautar nan na cewa ke Budurwa ce, to wannan ma kadai ya isa yasa ki yi farin ciki a ranki ki kwantar da hankalin ki, abinda zamanin kakanninmu har shela ake yi sannan sai an ajiye wannan zanin gado kowa ya shaida saboda tarihi, don haka nake rokanki ki dubi Allah ranki shi dade a matsayina na warce tayi uwa dake nake cewa kiyi hakuri kar ki kullace mijinki, in ma zaki nuna masa fushinki kar ya wuce na yan mintoci, shi ma ya shiga damuwa sosai baki ga yanda ya koma ba daga jiya zuwa yau duk ya fita hayyacinsa, ko abinci baya iya ci ga zazzabi me zafi da yake yi har sai da likita ya zo dubasa daxu da safe, amma hakan bai hanasa dinga tambayata halin da kike ciki ba, duk shiga idan nayi bangarensa wallahi sai ya tambayeki, ranki shi dade kin san yanda damuwa ke wahal da shi kuma bashi da me kwantar masa da hankali a yanxu sai ke a gidan nan, kema kar ki ce zaki juya masa baya don Allah” Khaleesat ta daga ido tana kallon Yakumbo, da sauri Yakumbo tace “Allah ya huci zuciyarki idan maganganu na sun bata maki rai Gimbiya, Allah ya baki hakuri, ayi min afuwa, a gafarce ni don Allah ba da wata manufa nayi ba wallahi” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, dai dai sanda aka bude kofar dakin, sosai gabanta ya fadi jin kamshin turarensa amma taki kallon hanyar kofar, Yakumbo na ganinsa ta hau jera masa gaisuwa cikin girmamawa har ya karaso cikin dakin, Khaleesat ta ajiye bowl din pepper soup din hannunta a hankali ba tare da ta yarda ta kalli direction dinsa ba ta kwanta ta juya ma kofar dakin baya tana jin hawaye masu zafi na sauka idonta, tuni Yakumbo ta mike ta fita ta bar masu dakin ta kullo kofa, Ajay na ta tsaya yana kallonta saboda rashin courage din karasawa kusa da ita, he is feeling so bad and guilty at the same time, bai ma san ta inda zai fara ba, bayan few minutes ya dake ya fara tafiya a hankali har ya isa kusa da gadon ya duka on his knee yana kallonta, bai samu kwarin gwiwan tabata ba don bai san yanda zata yi reacting ba, ya lumshe ido cikin sanyin murya yace “Jeeddah…. i am truly sorry! i am sorry I made you pass through all this, don Allah kiyi hakuri” Kasa ci gaba yayi har sannan idonsa a lumshe yana jin wani abu game da ita a ransa wanda yake ta dannewa yana ignoring for a year now, ita dai shesshekan kuka take hawaye na zuba idonta ta ki cewa komai don wani haushinsa ne cike zuciyarta at the same time maganganun da Yakumbo ta dinga yi mata for more than 15 minutes a dakin na mata yawo a kai, bude idonsa yayi a hankali moment din da ya amshi pride dinta na dawo masa kai and how he felt at that moment, har yanxu ganin abun yake kamar a mafarki it was something he never saw coming, tambayoyi ne iri iri a ransa suka samu waje suka zauna da yake bukatar amsar su, bai taba jin ya kagu ya samu amsan wani abu da ya sha masa kai ba kamar tambayoyin nan da suka yi occupying every part of his heart, he was so desperate about getting the answers, kuma ba a kasar nan yake son jin amsoshin ba, may be Maldives amma kuma visa din kasar might take a long process, Sai kuma Zanzibar ya zo masa rai, within 48 to 72 hours za a iya samun Visa din Tanzania, bai san sanda ya zauna gefen gadon ba ya dagota not minding how she will react kawai ya rungumeta sosai jikinsa ya daura lips dinsa kan gashinta ya lumshe ido cikin breaking voice yace “I’m….. I am sorry Jeeddah, I am very much sorry, it wasn’t intentional” Knocking din kofar dakin aka yi, hakan yasa Ajay ya kwantar da ita ya mike daga kusa da ita ya koma baya yana kallon kofar, ta kara juya masa baya har sannan hawaye bai daina zuba idonta ba. Mai martaba na zaune Parlonsa yayi shiru yana kallon Hajja at the same time yana sauraronta with full attention, Hajja tace “Don haka wannan magana da na kawo maka yafi zaman meeting din da aka tara yan gidan nan za ayi, akan me zaka zuba ido zumunci ya dauko hanyar lalacewa haka a gidan nan babu wani effort din gyarasa? Kai ya ma lalace, a halin da ake ciki yanxu dai komai ya tabarbare mana a masarautar nan, Farko ka dau budurwar wannan ka aura ma wannan saboda wasu dalilai naka, yanxu kuma ka dau title din wannan ka mayar ma wannan, who does that pls? me yasa baka tsayawa kayi tunanin abinda zai je ya dawo Yusuf?” Cikin nutsuwa Mai martaba yace “Duk abinda nayi Hajja idan aka tsaya aka duba daga karshe sai aga hakan shi ne mafi alkhairi for everyone, take for example title din da na kwace hannun Junaid, Ahmad Junaid is never fit to be a king in the future, ba shi da criteria din zama sarki wataran a masarautar nan, he is tough and aggressive most time, worst of all baya behaving irin na ‘ya yan sarakuna, wani dan sarki ne kika taba jin bashi da aiki sai dambe da mutane tun daga cikin gida har zuwa mutanen gari? Always throwing fist now and then, beside na lura title din ma baya gabansa, baya ba title din value kamar dai tilasta shi aka yi yake rike da shi, misali na gaba…. wannan yarinya da na aura ma Ahmad Junaid, with the way things are going now in this house da ace Jawwad aka aura ma yarinyar nan zata yi rayuwa ne cikin matsi da takura a gidan nan baza kuma ta taba jin dadin zaman aure ba, and Jawwad can not prevent that duba da mutanen dake zagaye da shi, Hadiyah ma kadai bazata bari yarinyar ta zauna lafiya ba, ko yanxu da ba mijinta take aure ba ki duba abubuwan da suka faru of recent, sannan Fulani Aseeyah ta kawo min wasu complain marasu dadi akan Hadiyah, wanda har da shi za a kawo a zaman meeting da za ayi….” Hajja ta katse Mai martaba tace “A’a kar wanda ya sa min jikata a bakin duniya Yusufa, kar ma a fara sako zancen Hadiyah a meeting din nan, duk ina da labarin mugayen abubuwan da Aseeyah ke yi mata a gidan nan, in taje bangarenta ta koreta, har da shi yasa na taho Bauchi bayan Dethroning din Junaid da kai da kinsmen dinka ku ka yi without even letting me know, idan Aseeyah ta mance wacece Hadiyah gwara a ankarar da ita tun wuri, tunda ita bata da mutunci bata da tsoron Allah” Sarki ya girgiza kai cikin nutsuwa yace “Amma Hajja baza a zuba ma Hadiyah ido a gidan nan tana abinda taga dama marasu kyau ba, nima ta min laifi biyu a yan kwanakin nan, na farko tayi ma matar Junaid sharri wanda hakan da ba karamin tarnishing din Image din masarautar nan zai yi ba banda Allah ya taimaka akwai shaida da yayi disclaiming allegations dinta, na biyu kuma ta min karya, ni kuma kinsan babu abinda na tsana irin a min karya, amma duk nayi overlooking hakan, Hadiyah ‘ya ce a wajena nima, bazan zuba ido tana wasu abubuwan da bai dace ba in ki daukan mataki akan haka, duk korafin da Aseeyah ta kawo a kanta abu ne da zata iya aikatawa Hajja….” Hajja ta tabe baki tace “To kuma in zaka mata gyara ko zaka mata fada lallai ne sai an tara duk yan gidan nan da kullum burinsu su ga wani abu mara dadi ya taso ta yanda za su yi barbadi da shi su koma gefe suna mana dariya? Ina laifin in ma zama za ayi akan Hadiyah ayi sa just between us cikin rufin asiri?” Mai martaba ya gyada kai yace “To in sha Allah Hajja” Hajja tace “Meeting din ma gaba daya a soke shi kowa ta koma gidanta, dama ai akan Dethroning din Ahmad Junaid ne za ayi meeting din kuma nice na bukaci ayi zaman, don haka kowa tayi tafiyarta zuwa gobe anyi canceling meeting din kawai, matar Junaid na kwance ba lafiya kuma duk sun san musabbabin rashin lafiyar nata amma babu er iskar da ta shigo takanas da sunan dubata saboda bakin ciki da hassada, hatta Gimbiya Firdausi bata shigo dubata ba amma suna zaune suna jiran ayi meeting su nadi abinda za su nada su tafi da shi, to daga yau duk wata magana da bata shafi Welfare din Masarautar nan ba gwara mu yi iya mu kawai” Sarki dai yayi shiru bai ce komai ba, Hajja ta gyara zama tace “Sannan shin Yusufa ina son sanin ko yanda Jawwad da Junaid basa ga maciji a gidan nan abun farin ciki ne a wajenka da ka kasa daukan mataki a kan haka ka zuba masu ido?” Sarki ya daga kai ya kalli Hajja, sai kuma calmly yace “I know nothing about that Hajja, considering the fact that Junaid basu dade da dawowa kasar ba, kuma normally muke karatu tare da su duk bayan sallahn asuba i didn’t notice that, sam ban kula da haka ba tunda shi dama Junaid ba shigowa fada yake ba unlike Jawwad that is together with me mostly” Hajja tace “To yau watanni kusan shidda kenan daga Junaid din har Jawwad babu me cewa dan uwansa ci kanka, duk kuma akan wannan abun da kayi, ni na zata komai ya wuce a wajensu sai da na zo jiya naga ana nan jiya e yau….” Mai martaba ya duba agogo jin an fara kiran sallan isha’i, Hajja tace “Idan ka dawo masallaci zan dawo mu ci gaba da magana, before then ka gaya ma Fulani ta sanar ma Gimbiya Firdausi ita kuma ta gaya ma kowa babu wannan meeting din da suke zaman jira” Mai martaba dai bai ce komai ba har Hajja ta fita daga parlon, jinginar da kansa yayi da kujera abinda Hajja ta fada masa ya tsaya masa a rai sosai, bai taba noticing Jawwad da Junaid basa magana ba, don after every subhi prayer as usual yanda aka saba duk ana gaisawa kafin a fara karatu kuma suna yin hakan a gabansa, kila kawai hadasu zai yi tare su tafi Ethiopia zuwa wajen dangin Mahaifiyar Junaid, it’s been 3 years now rabon Junaid da zuwa can din dama (To Alhamdulillahi za aje Ethiopia wajensu Rukky bjw, Moon, Mom twins, parrot, Jiddah, Summy, Yuguda, Aunty Zahrah, da dai sauran dangin uwar Ajay da suka yi bake bake a Halysaah conversation…)” Tun da Mai martaba ya sanar ma Aunty batun janye meeting tasan kawai yayi convincing din Hajja ta hakura an bar ma Jay title din Yariman kenan, ita sai a yanxu ne ma ta fahimci ashe tafi tsanar Jay akan Ajay ganewa ne kawai bata yi ba, ta yaya Sarki zai dinga fifitasa akan ko wani yaro a masarautar nan, bakin ciki take ji kamar ya kasheta duk da assurance din da Hajiya Nafisa ta gama bata ta waya yanxu akan ta zuba ido taga abinda zai faru next, ta sauke wani ajiyar zuciya ta mike ta tafi bangaren Walid taga ko ya ci abincin da ta kai masa daxu don kullum sai ta lallabasa yake cin abinci, kamar kullum yana zaune a yanda yake a dakinsa tun bayan da incident din nan ya faru tsakaninsa da Ajay, ga abincin a ajiye dakin ya ki ci, Aunty tace “Hannun bai dena zugin bane Walid?” Yaki ce mata komai, fuskar nan nasa a murtuke kamar kullum, Aunty tace “Wai Walid ta yaya zaka samu lafiya kana kin cin abinci? maganin ma sai an tilasta ka kullum sai nayi fama akan ka ci abinci ka sha magani, da wanne kake son inji? Da bakin cikin abinda ya dameni a gidan nan ko kuma da bakin cikin halin da kake ciki?” Ya fara huci yana daga kirji yace “Yanxu shikenan kema kin zuba ido a gidan nan an maida ni dan iska mara galihu, dubi abinda Junaid yayi min amma har yau ba a dau wani kwakkwaran mataki a kansa ba sai sauke sa a Yarima, title din da bai damu da shi da rashinsa ba, is that enough punishment for him bayan nakasa ni da ya so yi, ga hannuna ya karya min, kuguna ko zama bana iyawa sosai har yanxu, To duk ba ma wannan ba Momy, maimakon da aka saukesa a nada ni Title dinsa in compensation sai a wani ba Jawwad sai kace ni din agola ne a gidan nan? Ko dai da ni kika zo gidan nan ne Momy? Jawwad fa aka ba matsayin Yarima maimakon ni da nake dan sarki na biyu, To wallahil azeem bazan kyale Junaid ba, wallahi sai na dau fansa tunda anki bi min hakkin abinda yayi min a gidan nan daga karshe agola ma aka mayar da ni, to ina me tabbatar maki Junaid bai doki banza ba don Allah sai na dau mummunan fansa akan sa Momy” Cike da takaici Aunty tace “Daukar fansa ya wuce ka dauka akan Jawwad da ya zame maka barrier din da yayi maka cikas na samun title din Yarima a masarautar nan? Ai Jawwad shi ne babban wanda zaka dau fansa a kansa ba Junaid ba, don mahaifinku ya fifitasa ya kuma fi daukansa da muhimmanci akan kai da Junaid din, kana gani fa duk wani abu shi sarki ke dorawa a kai a maimakon ku da ku ke ‘ya yan cikinsa, duk Jawwad yayi bake bake ya kwace matsayin ku kuna ji kuna gani a gidan nan, yanxu haka idan bamu yi hankali ba shkkn sarauta tayi nisa da mu har abada sai dai labari, gwara a sanda Junaid ke rike da title din kai kanka kana jiyo kamshin sa a kusa da kai, amma a yanxu kam kwata kwata ya mana nisa Walid, Hadiyah na haihuwan da namiji shikenan kuma, don haka ka dau duk fansan da zaka dauka kan Jawwad, in kana da halin kashesa ma ni ban ki ka kashesa ba zan baka goyon baya dari bisa dari, kawai dai ka bi a sannu ta yanda babu wanda Zai zarge ka, balle ma babu me zarginka tunda an san da Junaid Kake da matsala ba Jawwad ba” Walid dai sai kallon uwar tasa wake yana huci yana nazarin abinda ta fada. Gimbiyah Firdausi ma kallon Hajiya Habibah tace “To ke amma Habibah a ina kika icewar Hajja zata umarci Sarki ya mayar ma Junaid title dinsa har kike gaya mana jiya?” Hajiya Habibah tace “Wallahi daga majiya me karfi naji wannan batu Gimbiya, abun da mamaki cancelling meeting din da Sarki yayi at die minute, kuma Sarki bai taba canceling meeting ba barin yanda kowa ke zaune gidan nan bai koma ba saboda meeting din” Kilishi tace “Tunda muka ga haka kilan Hajja bata yi convincing dinsa na mayar ma Junaid title dinsa ba kenan, ko kuma ya kawo mata wasu hujjoji da suka gamsar da ita ya bar ma Jawwad din, ni hakan ma ya min wallahi dama kuma fatanmu kenan dai dai mu wayi gari wataran mu ga buzu a matsayin Yarima karami” Hajiya A’isha dai taki tofa nata duk da deep down she is very happy da aka bar ma Jawwad don inda taje a mata aiki an nuna mata probability din auren Junaid da Iklima is very low, amma na Jawwad is very high, ita ma Kilishi dadi ne ya kusa kasheta don plan dinsu zai fi tafiya dai dai akan Jawwad instead of Junaid, in sha Allahu sai sun kawo karshen Ummi da Mami a gidan nan. Ummi ce ta shigo parlon Hajja ta zauna tana kallonta tace “Hajja yanxu nake samun labari wai anyi canceling din meeting din da za ayi bayan isha’i?” Hajja tace “Eh ni nace ayi haka, don duk abinda za a fada a meeting din abu ne da ya shafemu ba wasu ba Ummi, na kuma gamsu da hujjojin da kika kawo da wanda Sarki ma ya kawo min na kan cewar a bar ma Jawwad crowned prince din, kuma abinda yayi Junaid shi yayi Jawwad, dalilin da yasa naki a ba Jawwad Yarima tun farko dama saboda uwarsa ce ba wani abu ba, ni kaina sai bayan da kika yi magana naga rashin dacewar a sake cewa za a amshi title din a mayar ma Junaid din kuma, Allah ya sa hakan da Sarki yayi shi ne mafi alkhairi garemu baki daya, shi kuma Junaid zai iya basa wani title din daban” Ummi ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya ranta fari kal don tun jiya take kokarin gamsar da uwar tata akan cewar a bar ma Jawwad title din kar abun ya dawo kamar wasan yara nan kuma for her selfish interest ta dinga yin hakan, amma jiya kwata kwata Hajja taki daukan hujjojinta ta dage lallai sai an maida ma Junaid title dinsa, daxu da safe kuma da Hajja suka zauna da sarki shi ma dai yayi convincing dinta da maganganun da yayi, shi ne har ta saduda da batun mayar ma Junaid title dinsa. Jay na zaune parlon Mai martaba kansa a kasa ta dalilin kiran da yayi masa, after some minutes Mai martaba yace “Jeka ka kira min Junaid ku dawo tare” Jay ya daga kai ya kalli Sarki, sai kuma ya sauke idonsa kasa, a hankali yace “To ranka shi dade” Mikewa yayi ya nufi kofa, Mai martaba ya bi sa da kallo har ya fita, Jay ya koma part dinsa ya zauna kan kujera ya dau waya yayi dialing number Hadiyah don bata bangaren, sai da ya katse ya sake kira sannan ta daga tace “I am coming” Daga haka ta katse wayar ba tare da ta jira taji me zai ce ba, bayan dan lokaci sai gata ta shigo parlon tana yatsine fuska tace “Abincin fa yana ajiye a kitchen kake kirana bayan kasan ina wajen Ummi ne, kuma har yanxu baka tura min kudin ba gashi gobe Shahuda zata zo ta rakani siyayyan tunda ita ta san designers Abaya” Without looking at her yace “Ki tafi ki gaya ma Junaid Mai martaba na kiransa” Hadiyah ta wani kallesa tace “Tabdi, wallahi bazan je ba, what is my business with him da zan je part dinsa, mutumin da ya gaggaura min mari kaki yi masa komai a kai, wallahi bazan je ba meye hadina da wani Junaid” Tana kai wa nan tayi tafiyarta dakinta, Jay ya bi ta da kallo, yana ta zaune bayan ya tuna Sarki na jiransa ya mike ya nufi kofa ya fita daga parlon.

Back to top button