Uncategorized

Gaskiyar Magana Akan Aure Hadiza Gabon da Malam Isah Ali Pantami

 Zan daina wasan kwaikwayo idan Sheikh Pantami zai aure ni – Hadiza Gabon

 Hadiza Aliyu Gabon, yar kasar Gabon kuma daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood, ta shiga shafukan sada zumunta inda ta nemi Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Pantami ya aure ta.
 Jarumar wacce ta zo Najeriya sama da shekaru 10 da suka gabata, kuma tun daga lokacin ta zama attajira ta hanyar wasan kwaikwayo da tallace-tallace na kamfanoni, ta wallafa cewa a shirye ta ke a kowane lokaci ta daina yin fim idan Sheikh Pantami zai aure ta saboda ta ci gaba da mafarkin kasancewarsa matar aure.
A cikin bidiyon da ta ɗora a kafafen sada zumunta, ta gabatar da cewa za ta zama uwar gida mai nagarta, mai tsananin addini da bin duk ƙa’idodin iyali da Pantami na iya dora mata.
 Sha’awarta ga ministan sadarwa ta samo asali ne tun lokacin da yake lacca a Jami’ar Saudi Arabia.  A cewarta, ba ta bayan kudinsa ne, domin tana jin dadi.  Abinda kawai take so shine ta zama matar aure kuma ta haifi managartan ‘ya’ya kuma Pantami shi ne mafarkinta.
 Hadiza Aliyu Gabon wacce ke zirga -zirga tsakanin Abuja, Kano da Kaduna don kasuwancin ta, mai son jama’a ce, mai karamci da kirki.  Yanzu tana zaune a gidanta da ke Millennium City Kaduna inda har ta gina masallaci ga Musulmai don amfani.

Also Read:

Dalilin da yasa naki Auren Adam A Zango – Ummi Rahab

Idan ba ku manta ba, a kwanakin baya jarumai mata na Kannywood sun dauki wata ta’ada ta fita ƙasashen waje yawan shaƙatawa kamar irin su London, Dubai, America da dai sauransu.

Jaruman da suka fi zuwa waɗannan ƙasashe sun haɗar da Hadiza Gabon, Fati Washa, Hafsat Barauniya wadda har yanzu zancen da muke maku bata kasarma, Rahama Sadau itama bata kasar yanzu haka ta ƙasar Indiya a ƙoƙarinta na fara yin fim din India da ake kira da Bollywood.

Su dai jaruman sukan dauki hotuna ne a wajen da suka sauka kamar daki, gurin hutawa, Hotel da kuma bakin ruwa.

Binciken da muka yi ya tabbatar mana da cewa duk masana’antar Kannywood babu waɗanda suka kai waɗanda jarumai huɗun fita ƙasashen waje.

Ko a yan watannin da suka wuce jaruma Hadiza Gabon ta wallafa wani hoton ta a shafin twitter, inda nan take wani saurayi ya ya yi mata tsokaci akan cewa wannan hoton sai da ku ka yi zinah sannan kuka yi shi duba da irin kayan da suka kafin a ɗauki hoton.

Nan take jarumar ta mayar masa da martani cewar sai da muka yi da mahaifinka sannan muka yi hoton.

Bayan ta mayar da martanin ne kuma sai ta dawo ta goge shi, sannan ta wallafa wani gajeren bayani na neman gafarar Ubangiji akan zagin saurayin da tayi bisa fusata ta da yayi na jifanta da wadannan miyagun kalamai da ya jefe shi da su.

Jim kaɗan da wallafa wannan jawabi nata sai mutane da dama su ka yi ta yi mata jinjina akan tuban da ta yi na gano kuskurenta akan zagin mutum ko da kana cikin fushi ne. 

To, acikin masu yi mata jinjina harda Malam Isah Ali Pantami wato ministan sadarwa, sai kwana nan kuma ka jiyo jarumar tana ambata cewa muddin zai iya aurenta, to itama a shirye ta ke.

Mene ne ra’ayinka kan wannan batu?

Back to top button