Uncategorized

Hotuna: Kalli Kyawawan hotunan Jarumai Ummu Rahab

 An haifi Ummi a jihar Kaduna a Najeriya . An haife ta a shekara ta 2004. Shahararriyar Jarumar Najeriya ce wadda ta kasance jarumar a cikin yara a masana’antar Kannywood. Ta taka rawar gani a fina-finai da dama. Ta fara wasan kwaikwayo tun tana ƙarama. Ummi Rahab yarinya ce kyakkyawa ga fara’a. Ta fara haskakawa ne bayan fitowa a wani fim mai suna “Kin Zamo Takwara” tare da Adam A Zango da Jamila Nagudu.

 Kyakyawar jarumar ta Kannywood daga karshe ta samu wani babban matsayi a masana’antar. Ta kasance yarinya mai farin jini hakan yasa ta samu nasarori da dama a rayuwarta. 

 A wata Hira da akayi da Ummi ta ce ta kasance mai sha’awar yin wasan kwaikwayo tun tana ƙarama.  Ta fito a fina-finai da dama. Sai dai ta samu matsala da ubangidanta a harkar Film wato Adam A. Zango. Wanda tasa ya cireta a Film dinsa mai suna Farin wata sha kallo, sai dai yanzu haka Ummi tana yin wani Film mai suna wuf wanda ya kunshi Lilin Baba wanda ta sanadinsa ne suka yi fada da Adam A. Zango.

Ga kyawawan hotunan da Ummi din ta saki a ƙasa. 👇👇

Please kindly share it to your friends and family thank you for visiting our site.

Back to top button