Uncategorized

Abban Sojoji Chapter 36 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

          (Boss Lady)

cikin sauri Jahan ya miƙe fitowa daga ɗakin yayi ya sauko down kai tsaye freezer ɗin dake a babban falon nasu ya tunkara, buɗewa yayi tare da zura hannu ya ɗauki robar ruwa mai sanyi, sannan ya juya ya koma ɗakin nasu, bayan ya buɗe robar ruwan ya ɗebo ya yayyafa masa a fuskarsa, wata irin doguwar ajiyar zuciya Ayaan ya saki tare da buɗe idonsa da sukayi jawur dasu yana kallon jahan dake zuƙunne agabansa, ganin Ayaan ya farka yasa jahan faman sauke ajiyar zuciya, yayin da hawaye ke sintiri a fuskarsa yana kallon ɗan uwan nasa,

   Buɗe baki Ayaan yayi zaiyi magana, nan take wani irin yunƙurin amai yazo masa, a hanzarce ya zabura ya miƙe duk jikinsa ba ƙwari da gudun gaske ya faɗa toilet agaban basin ya tsaya yana faman kwarara aman, biyo sa jahan yayi cikin toilet ɗin tsayawa yayi kusa dashi ya sanya hannunsa yana ɗan bubbuga bayan Ayaan cikin muryar kuka yake cewa “Ayaan kayi haƙuri ina mai takaicin wannan ranar, naji natsani kaina Ayaan saboda nagaza ceton ka a hannun wancan fasiƙin, tabbas Haroon bai da Imani ko misƙala Zarratin kashe mu kawai yake son yi, ni ina kokwantan cewa Anya haroon JININ MU NE !!!!!!!!!!

dakyar Ayaan yasamu ya dakata da Aman hannunsa yasanya yana tarbo ruwan dake kwararowa daga jikin fanfon yana kuskure bakinsa, bayan ya kammala ya kashe Tap ɗin,

   Sannan ya ɗago da shanyayyun idanuwansa ya kalli jahan yace “Haroon bai da Imani, Ƙazamin banza mugu macuci kuma Azzalumi wlh Allah bazai ta6a ƙyalesa ba sai ya bi mana haƙƙin mu, Jahan ni sam bana jin kunyar videon tsiraicin mu ya fita, babban abunda nake jimawa shine Mutuncin mahaifin mu da kuma na Babban yayanmu, jahan dole mu nemi mafita akan wannan Baƙin Shaiɗanin………..’ ya ƙarasa maganar yana faman sakin Numfashi mai zafi, don tuni zazza6i yakama jikinsa,

  Jahan yace “yanzu dare yayi Ayaan,Gobe sai musan Abunyi amma gaskiya bazan ƙara bari haroon ya ƙara kusantar ɗaya daga cikin mu ba, ko nawa yakeso muyi ƙoƙari mu biyasa shine kawai !!!

  Sun jima suna jimamin abunda yafaru dasu kafin daga bisani suka sake sabon wanka don tsarkake jikinsu, bayan sun fito suka zura jallabiya ajikinsu, sai da Jahan ya canza musu bedsheet sannan suka kwanta, sun juma idonsu a buɗe kafin daga bisani bacci ya ɗauke su 😥

(Arayuwa kowa da irin tashi jarabtar, babu wanda Allah baya jarabta, kuma bawai don baya son mu bane a’a face don ya jaraba imanin mu)

**************Morning***********************

tun da sassafe sehrish ta farka daga baccin da ta koma na asuba, fuskar nan awashe yau zata fara shiga school, jiki na rawa ta faɗa toilet shaf-shaf tayi wanka ta fito jikinta ɗaure da farin towel,

  Uniform ɗinta ta curo daga cikin wardrobe duka ukun, ta jera su saman gadonta tana tunanin wanne zata sanya, duk kala ɗaya ne amma na farkon riga ce da mini skirt ɗan dai-dai guiwa shafa su tayi tare da girgiza kai tace “Ba wannan zansa, basu son cewa ni musulma bace, taya zansa wannan gajeran skirt ɗin cinyoyi awaje kamar ƴar christiana,” tayi maganar tana yatsina fuska, buɗe na biyun tayi riga ce tare da skirt pencil ba ƙaramin ɗame jikin mutun zaiyi ba,

 “Kamar dae wadda zata club,” ta faɗi tana ƴar dariya, na ƙarshen ta buɗe riga ce tare da dogon wando, duka uniform ɗin suna da Top wadda ake sanyawa daga sama bayan an zura rigar sai kuma guntun hijab wanda daƙyar ya dire kafaɗa,

“Kwarama wannan zasu fi dacewa dani,” ta faɗi  tare da hanzarin komawa gaban mirror sai da ta kammala shafe jikinta da body oil  tabi ta feshe shi da turare ko’ina yakama ƙamshi sannan ta koma gaban gadon tana zura uniform ɗinta, lokacin da ta kammala zura kayan duka ta kalli kanta a mirror sai da taji gabanta ya faɗi saboda yadda kayan suka hau jikinta su kayi mata wani irin kyau,

Rigar white colour ce wandon kuma Maroon colour launi ɗaya da Top ɗinta, jujjuyawa tayi agaban mirror ɗin sannan ta sakarwa kanta murmushi, sai da tagama shiriritar sannan ta ɗauko takalmanta,

   tsayawa tayi tana ƙoƙarin zura safa a ƙafarta, ta aza ƙafar asaman kujerar gaban mirror tana gyaggyara safar,  Azmee ta shigo ɗakin da sallama tana yin arba da sehrish ta soma washe baki tana cewa La!la! Irin wannan kyan haka, Masha Allah gaskiya uniform ɗin nan ba ƙaramin kyau su kayi maki ba Sehrish sai kace donke akayi su,”

  Murmushi kawai Sehrish ke saki tana ɗan kallonta a lokacin ta kammala sa safar da takalmin a ƙafar daman ta, saura ta hagun zata sanya mawa,

  “aunty azmee ina kwana fatan kun tashi lafiya,”  ta faɗi tana aza ɗayar ƙafar saman kujerar ,

  Azmee tace “Lafiya lou Alhamdulillah, naga sai faman shiri kike yi, maganar breakfast ba? 

  “Aunty azmee lokaci zai ƙure ne, idan nadawo zanci,” ta faɗi tana zura safa a ƙafar hagunta,

 Azmee tace “Kin ta6a ganin inda akaje ɗaukar karatu da yunwa? gaskiya bazaiyiyu ba, akwai sauran miyar jiya na ɗumamata saina haɗa maki da dankalin dana soya kici, bari na kawo maki”

  ta fadi tare da juyawa ta fuce cikin sauri bayan wasu mintina sai gata ta dawo hannunta ɗauke da plate, soyayyan dankalin ne aciki tare da jar miya, ajiye mata tayi asaman side drawer ɗinta, sannan ta koma ta ɗauko mata kayan tea don ta haɗa tasha,

   “Nagade sosai Aunty azmee da kulawarki,” sehrish ta faɗi a lokacin ta baro gaban mirror ɗin, wuri ta samu gefen gadon ta zauna tana cin breakfast ɗinta, yayin da azmee ta fuce tana cewa “ki hanzarta ki shirya kafin Junaid ya fito,”

  ta amsa mata da “Toh,” 

A can ciki kuwa tuni junaid ya farka saboda ya tashi da wuri ya sanya alerm a wayarsa, shaf shaf yayi wanka ya fito ya kimtsa cikin pakistani riga da wando farare amma anyi masu ado da stone launi daban daban ajikinsu, ba ƙaramin kyau yayi ba, bin jikinsa yayi ya feshe shi da Spice bomb, sannan ya gyara sumar kanshi, gaban mirror ya tsaya yana kallon kansa  yace “Nima kaina nasan cewa Ni kyakkyawa ne, Son kowa ƙin wadda ta rasa, Allah kaɗai yasan ƴan matan da suke crushing akaina,” ya faɗi yana tsumbula yatsansa na tsakiya a dimple ɗin fuskarsa daya Lotsa, 

  daga bisani ya ɗauki key ɗin motar shi tare da wayarsa ya fito daga ɗakin, cikin hanzari ya sauko down babu kowa saboda duk basu tashi daga bacci ba, wuri ya samu asaman Royal sofa ɗin dake a falon mai mazaunin mutun 3 ya zauna yana jiran fitowar sehrish, wayarsa ya shiga daddanawa, message ya tura mata cikin wayarta, na cewa yana jiranta ta fito, 

  a lokacin ta kammala kur6ar tea ɗin data haɗa, message ɗin junaid ya shigo mata karantawa tayi “Am waiting for u reesh,’ murmushi ta saki cikin sauri ta miƙe tare da ɗaukar guntun hijabin ta zura ajikinta, sannan ta ɗauki School bag ɗinta ta ɗan sagala hannun jakar a kafaɗarta,  sai da ta ɗauki wayarta sannan ta fito daga ɗakin, kai tsaye ta nufi falon tunkan ta ƙarasa junaid ke kallonta baki asake,

 Ganin hakan yasa ta sakin dariya, ƙarasa wa tayi wurinsa tare da tsaya agabansa ta ruƙe waist ɗinta tace “Nayi kyau,”?

 Cikin mamaki yace “Reesh irin wannan kyau haka? Anya karfa malaman makarantar su rikice? innalallahi,” ya faɗi tare da aza hannunsa akansa,

  ɗan bubbuga ƙafarta tayi tare da cewa “ka tashi mu tafi junaid har 8:30 fa tayi,” 

  Mamaki tayi ganin yarda yake kallonta hannunsa yakai tare da cafko wutsiyar gashinta da ta sauko har tsakiyar bayanta yace “Sehrish jibi fa? Babu wani dogon hijabin ne sai wannan? Taya zaki bar gashin nan haka bainan nasi? Kowa ya kalla? 

  Sai lokacin ma ta ankara sam ta manta bata sanya ribom ba ta ɗaure gashin, dafe kanta tayi tare da cewa “kash ! Wlh mantawa nayi ban ɗaure gashin ba, kuma fa in na sanya ribbom gyaran gashin da akayimun zai 6ace,”

  tashi junaid yayi tare da ruƙo hannunta yace “Mu shiga cikin ɗakin na ɗaure maki shi, nasan yarda zanyi batare dana 6ata maki gyaran gashin ba,”

  bin shi tayi suka wuce ɗakin nata, duk wannan abun dake faruwa akan Idon haroon sam basu ankara dashi ba, tun fitowar sehrish yake tsaye ruƙe da qugu daga shi sai gajeran wando fuskar nan a murtuke kamar ta shanu, jinjina kansa yayi tare da cewa “Wato ni waccen ƴar shilan zata raina ma wayau, in na ta6a jikinta taita ƙyamata amma gashi junaid har wani ruƙe hannunta yake yi, hada su shiga ɗaki ko uban mi zasu yi aciki,”? Ya tambayi kansa can kuma ya saki wani irin shu’umin murmushi yace “Wannan babbar dama ce agare ni ! Zanyi amfani da ita wurin gur6ata sunanta acikin gidan nan, Zan ƙala mata sharrin cewa ta koyama junaid lalata, kuma na kama su hannu dumu-dumu, ” fashe wa yayi da wannan mahaukaciyar dariyar tasa kafin ya juya ya nufi hanyar komawa dakinsa yana cewa “Yarinya kin gama yawo acikin gidan nan, sai kin gane baki da wayau !,” yana tafiya yana sambatu har ya shiga ɗakinsa,

  Junaid kuwa bayan sun shiga ɗakin sehrish ta cire hijabin nata agaban mirror suka tsaya, ribbom ɗinta dake ajiye saman mirror ta ɗauko tare da miƙa masa, hannu yasa ya kar6a sannan yashiga kiciniyar tattara gashin kanta donya ɗaure mata,

  Murmushi ta dunga saki saboda jinsa yadda junaid ke faman  nishi aranta tace”junaid ba ƙaramin rago bane, yanzu gashin kan nawa ma yagaza ɗaure wa, shi dai sai kace ba namiji ba, sam babu wannan karsashin na maza atattare dashi……

KARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA2022


Gurbin Ido… Na Huguma (Zafafa2022)

Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)

Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)

Babu So… By Billyn Abdul (Zafafa2022)

Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)

  Muryarshi ce ta katse ta da cewa “Gulma ta kike ko”? Cikin sauri tace “a’a ni na isa,”

  Murmushi kawai yayi, daƙyar yasa mu ya tattara sumar kan sehrish ya ruba ta biyu ya haɗa ya ɗaure,” sannan ta mayar da hijabin nata,

 “Gaskiya junaid ka iya dabara, gashi nan yanzu babu gashin bai leƙo ba,”

  ruƙo hannunta yayi tare da cewa “Mu tafi ko,” cikin sauri ta bishi suka fito da hanzari suka fuce,

  Buɗe mata motar yayi ta shige sannan shima ya zagaya yashiga ciki, yana a driver seat ita kuma tana a gefensa, tayar da motar yayi sannan suka fuce daga gidan, 

A natse yake yin driving ɗin sehrish na satar kallon shi tace acikin ranta “koya akai ya iya driving yanzu yadda yake shagwa6a66an nan karfa wata rana ya tunkari babban mota damu kwatsam ta rotse damu duk mu mutu…..’

 “Matsalar ɗan nigeria kenan,  duk wani bala’e shike fara kira ma kansa, yanzu ko menene na wannan tunanin”? Cikin mamaki tace “Acikin Zuciya fa nayi maganar” ta faɗi tana kallonsa

Junaid yace “Eh nasani, ae muddin zaki yi gulmata acikin zuciyarki to fa saina ji don haka ki kiyaye,” ya faɗi yayin da yake shan kwana dasu,

Shiru tayi tun daga lokacin bata sake maganarsa ba acikin zuciyarta amma fa tayi mamaki don ita tasan cewa acikin zuciyarta tayi maganar amma gashi yaji,”

 Tunkan su ƙarasa sehrish ke hangen katafariyar makarantar motoci sai shiga suke yi ciki suna sauke ɗalibai, tsayawa zayyana kyawun makarantar 6ata baki ne, gashi bani da isasshen lokacin yin wannan bayanin 😆

A parking space dinsu junaid ya sauke sehrish tare da cewa mun iso, atare suka fito gaban sehrish ne ya faɗi ganin tsala-tsalan ƴan mata young ladies irinta sun ɗau wanka, ƴa’ƴan masu kuɗi wayayyun gaske tun daga shigarsu zai tabbatar maka da cewa An sangarta su da yawa, saboda majority ɗin matan Mini skirt ne ajikinsa sai santala santalan cinyoyi awaye, kuma mafi yawancinsu babu hijab ajikinsu gyaran gashi ne kawai iri-iri, wasu kuma skirt ɗin nan ne ajikinsu waton pencil yabi shafe ɗin jikinsu, iya guiwar ƙafarsu ya tsaya,  

waro ido waje sehrish tayi tana cewa “kai!kai!!kai!!! Junaid mu koma gida, gaskiya bazan iya zama a school ɗin nan ba, wannan sunfi ƙarfi na Allah,” 

  Fashewa da dariya junaid yayi ganin yarda sehrish duk ta dabarbar ce, hannunta na kerma ta ruƙo rigarsa tana 6oyewa abayansa tana faman yi masa sambatun su koma gida, abu kamar wasa har hankalin wasu students ɗin suka dawo kansu ganin yadda Yarinyar ta ƙanƙame jikin dan uwan nata hada su hawaye a fuskarta,

 Shima kansa junaid sehrish ta rikita shi hankali atashe yake cewa “dan Allah sehrish ki daina, karki bani kunya mana kalli yarda hankalinsu yafara dawowa kan mu innalallahi, yanzu da ace school bus ce ta kawo ki bansan ya zaki ƙare ba,” 

  “Junaid nidai mu tafi gida, Allah bazan zauna anan ba” ta faɗi tana shesshekar kuka 😆

   dariya kamar zata kashe junaid ba shi kaɗae ba hada wasu daga cikin ɗaliban dake a wajen,

 Wasu gungun ƴan mata ne suka ƙaraso kusa dasu, ɗaya daga cikinsu tana cewa ” Wow friends kalli wani handsome guy nan ya burgeni sosai,” 

  Jin hakan yasa sehrish dakatawa da kukan tana ɗan kallonsu kai kana ganinsu kaga jarababbu,

  Murmushi ta gefenta ta saki tare da cewa “Kamar nasan shi a tiktok fa, zanso ko na tuna sunan shi daga gani cele ne shi sosai,” 

   Sai faman surutu suke yi suna yaba kyan junaid, 

  “Kai nifa bazan iya jure ba, sai nayi ma shi magana,” ɗaya daga cikinsu ta faɗi atare suka iso dab da su junaid da sehrish, su uku ne matan 

   junaid yace “Sannun ku fa,” suka amsa mashi da “Yawwa,” sannan ɗaya daga cikinsu tace “Kamar na sanka,”ta faɗi cikin rangwaɗa

Junaid yace ” Sunanki Parveena,” zaro ido su kayi jin yadda junaid ya faɗi sunan ɗaya daga cikinsu kai tsaye, Nuna ɗayar yayi ta tsakiyarsu yace “ke kuma Sunanki Amrish ta ƙarshen kuma sunanki Naja’at,” ya faɗi da murmushi a fuskarshi, su kuwa sai faman yarfa hannu suke yi suna kallon shi cikin mamaki jin yadda ya zayyana sunayen su gaba ɗaya, 

 Cikin mamaki wadda ya kira da Amrish tace “Dan Allah ya akai kasan sunayen mu”?

  Ta tambaya cike da zumuɗin son jin amsa,

  Duk wannan abun dake faruwa akan kunnan sehrish wadda ke ruƙe da rigar junaid taɗan la6e abayansa,

   Junaid yaci gaba da cewa “Ban son ku ba nima kawai abunda nasa ni  ke Amrish kece kullum kike isarmu da surutu a group, ke kuma parveena baki da aikin yi sai turo hotunan Chacolate iri-iri, Sannan ke kuma Naja’at kinfi kowa iya turo hoton abinci duk in zaki ci sai kin turo mana hotansa,” 

 Gaba ɗayansu suka saka ihu da sowa har suna haɗa baki wurin cewa “Wai dama kaine ! junaid romeo ko? 

 Murmushi junaid ya saki tare da cewa “Ni ne, bamu ta6a haduwa ba amma muna yin chat sosai ta whatsapp a group, na ruƙe fuskar kowannan ku da sunayen ku,”. 

  Ba ƙaramin farin ciki su kayi ba, Amrish ta nuna sehrish tare da cewa “wannan fa? sister ɗinka ce”?

Junaid yace “Eh, younger sis ɗina ce, new comer ce yau tafara zuwa,”

  Parveena tace “No wonder, that’s why naga tana hiding kanta abayanka, amma kamar batason mutane ko? Naga ko son kallon mu bata yi,”

   Junaid yace “No just kin gane shagwa6a6iya ce, Last born ɗin mu ce bata saba shiga cikin mutane ba kullum tana a gida, so aduk lokacin da aka fito da ita cikin mutane tana ɗan razana,”

  tunda ya soma jawabi sehrish ke kallon shi baki asake, jin irin ƙaryar daya zuƙa mata nafarko yace ƙanwarsa ce ita, kuma ya laƙwafa mata sharrin cewa tana shagwa6a bayan shine shagwa6a66e, jinjina kanta kawai takeyi,

  Amrish tace “Ayyah na tausaya mata but she’s so cute kuma ta fito daga babban gida yakama ace tana shiga mutane,”

     ta6e baki sehrish tayi tana ɗan kallonsu, 6an6aro hannunta junaid yayi daga jikin rigar shi, sannan ya miƙa ma Amrish yace “Gata nan dan Allah amana na baki ita, ki tafi da ita ba ta son komai ba da yake  ita ɗin rainon kakarmu ce, sai ahankali,” 😆

   Murmushi Amrish ta saki tare da kar6ar hannun Sehrish tace”aikuwa na gode sosai da wannan kyautar, kuma zan ruƙe amana,”

   Cikin raha sukayi sallama da Junaid yayin da suka shiga ciki da Sehrish duk ta zama tamkar mutun-mutumi , suna tafiya tana waiwayon junaid shima kansa sam yagaza tafiya kallonta kawai yake yi, sai yaji duk kewarta ta kama shi daker ya ɗaga mata hannu tare da yi mata bye-bye,’ 

  Sannan ya buɗe motarsa ya shige, yayi mata key sannan yaja ta da gudu yabar makarantar, sai da yayi nisa da driving ɗin sannan yayi parking ɗin motar agefen titi yana shesshekar kuka yana cewa “ko na minti ɗaya bana son rabuwa dake sehrish kewarki nake yi,” yayi maganar tare da curo handkerchief ɗinsa daga front pocker ɗin rigarsa yana faman share hawayensa, ya jima acikin motar duk kasala ta dabaibaye shi daker ya iya tayar da motar yaci gaba da driving ya miƙi hanyar komawa gida 😥

Parveena da Naja’at Class ɗinsu suka wuce, Amrish ce tayi ɗawainiya da Sehrish ta raka ta har Admin  ɗinsu wurin principal ɗin makarantar, maca ce hamshakiyar gaske tun da taji sunan sehrish tagane cewa daga Family ɗin Salahuddeen Hussein take, hakan yasa ta sake mata sosai har tana jan ta da fira, daga bisa ni taba ma Sehrish Sunan Class ɗin da zata zauna, Science department ne kuma an ci sa’a Class ɗinsu ɗaya da Amrish SS1 science C, Madaddalar ƴan iska ba  😂 

 (Nima Science C nayi a school ɗinmu wlh basa jin magana, dama anyi ittiƙafi babu wanda yakai ƴan C rashin jin magana)

  Hannunta na ruƙe dana Sehrish suka tunkari benen da zai sadaka da Upstairs ɗin makarantar, anan Classes ɗin suke akwai kuma na down, 

   sehrish dae sai bin ko’ina take da kallo makarantar ta haɗu kamar ba wurin ɗaukar karatu ba saboda tsaruwarta ga wuraren shaqatawa, 

   shiga Class ɗin sukayi mutun goma ne a cikinsa a ƙa’ida kowane class mutun 12 ne kacal acikinsa maza 6 mata 6, idan aka haɗa da Sehrish da Amrish 12 kenan student ɗin cikin sa, 

  gaba ɗaya Ido yadawo kan Sehrish kowa da irin kallon da yake yi mata, Mazan class din kuwa tuni sun soma sakin baki suna cewa “Wow so beautiful, so hot,  She looks so sexy,” 

  Gabanta ne ya faɗi kowa da irin abunda yake cewa, Matan kuwa wani irin kallo suke binta dashi irin kallon hadarin kajin nan,’ ƙara ƙanƙame school bag ɗinta tayi daga tsayen da take, 

  Amrish ce ta soma magana” Hello Class we ave a new comer today, She’s from awesome family, i hope zaku bata hankalin ku domin tayi mana Introducing kanta,” 

   ta ƙarasa maganar tare da kallon Sehrish tace “Pls introduce ur self,” 

   ɗan gyaran murya Sehrish tayi sannan ta soma cewa “am….Sehrish Salahuddeen Hussein by name, 17years old…. Alhamdulillah I love the Way i am,” 

  Wannan bayanin na sehrish yasa su gaba ɗayansu Clapping hands ɗinsu suna tafa mata, musamman ƙarshen maganarta ta ƙayatar dasu,

Sun mata kyakkyawar tarba duk da akwai waɗanda tunda ta shigo ma basu ɗago da kansu ba daga saman desk sun kife shi kamar masu bacci,

   Kowane seat mutun ɗaya ne,  Amrish ta sama ma Sehrish gurbi a Middle Roll na Class ɗin 0a Second seat Amrish kuma na’a First seat, sai da tafara neman alfarma wurin asalin mai seat ɗin na sehrish akan tabar mata, kuma cikin sa’a ta amince shine har tasamu gurbi abayanta, komai yazo mata cikin sauƙi kuma ba ƙaramin daɗi taji ba na haɗuwarta da AMRISH 💃

***********AUNTY BABBA***************

tun da sassafe suna kwance wayarta ta soma ringing a firgice ta farka jikinta na sanye da kayan bacci brown colour, leƙa fuskar Ishaq tayi taga koya buɗe ido samun shi tayi sai faman Sharar baccin sa yake, don haka a hankali ta lalla6a ta sauko daga saman gadon cikin sanɗa,

   Bayan ta sauko ta ɗauki wayarta data ajiye saman side drawer ɗin shi, sannan ta lalla6a ta shige cikin toilet ta duba mai kiran nata mutumin da tayi tsammani shi ta gani wato*BABA ALAMU* murmushi ta saki cikin sauri ta ɗaga kiran ta kara a kunnanta tun kafin tayi magana baba alamu yace “Na faso gari fa, tun jiya da daddare inata kiran layin ki baya shiga,”

   Aunty babba tace “wlh bansan ka kira ba, dayake nabar wayar acikin ɗakina sai da asuba na ɗauko ta, tun jiya nima nake jiran kiran naka mutumina,” 

 Dariya baba Alamu yayi sannan yace “Ae ke baki sani ba, jiya muna dira gari na kwaso rugwagwar motata na shigo unguwarku don in sanar maki kawai sai naga waɗannan Masu fuskar shanayen tsaitsaye ruƙe da bindiga ae ba arziƙi naja motata na koma,”

  Fashewa da dariya aunty babba tayi tace”Ae mijina ne yadawo jiya shiyasa kaga sojoji nan,” 

  Baba Alamu yace “Oh to ashe angon ne yadawo, yanzu dae ya za’ayi wurin fitar da yaran kinsan fa wlh shegen tsoran Soja nake, don kwanaki sun ta6a tarar mu a hanya suka sanya mu tsallen kwaɗi a tsakiyar titi da rana tsaka,”

   Aunty babba tace “Ae basu da Imani, musamman in suka ji su acikin kakin nan sai su dunga ɗaukar kansu tamkar wasu dodonni, yanzu abunda za’ayi kana ina ne?

Baba alamu yace “yanzu haka na fito da mota ta ina kan hanyar zuwa unguwarku amma fa bazan shigo ciki ba sai dai ki san yarda zakiyi a fito da yaran,

   Aunty babba tace “Shikenan ka jira ni, zaka ga kirana yanzun nan bada jimawa ba,”. 

   bayan ta kammala maganar ta kashe wayar sannan ta fito daga cikin toilet ɗin cikin sanɗa ta lalla6a ta fuce daga ɗakin,

   Kai tsaye ta nufi ɗakin hafsat ta shiga, tsayawa tayi tana kallonsu hussana da jahad dake ta faman sharar bacci baje saman gadon hafsat, yayin da ita kuma hafsat ɗin ke kwance saman doguwar kujerar ɗakin tana bacci, da alama dukansu daga tashin asuba suka koma bacci, 

   jinjina kanta tayi sannan ta ƙarasa dab da hafsat ta ɗansa hannu ta bubbuga ƙafarta, a dan firgice hafsat tafarka tana cewa “wanene,” 

  Murya ƙasa ƙasa aunty babba tace “ke ki taso inason magana dake,”

  Bin ta da kallo hafsat tayi tana yamutsa fuska Alamar bacci bai ishe ta ba, daker tasa hannunta ta janye bargon data lullu6e rabin jikinta da tashi sannan ta miƙe tsaye tabi bayan aunty babba, suka fito daga ƙopar ɗakin suna fuskarta junansu hafsat tace “Meya faru mommy naga kin tashe ni ina tsaka da bacci na? Aunty babba tace “Mutumin fa wanda zai kai su hussana da jahad gidan marayu ya ƙaraso….,”

   jin hakan yasa hafsat canza fuska tuni tace “Mommy yanzu dole sai kin raba ni da yaran nan? Wai me suka tsare maki ne? Dan Allah mommy kibarsu suyi rayuwarsu cikin salama, sun sha wahala fa baki tausayin su?

   tsoki Aunty babba ta buga tuni ta tamke fuska tace “Tausayin Uban me? menene alaƙata dasu? ke bana son zancen banza mun riga da mun gama magana dake don haka ! Ke nake so ki fidda yaran nan daga cikin gidan nan!! In yaso zan baki numbarsa in kin fitar dasu acikin motarki sai ki kira shi ki bashi su ya tafi dasu can Orphanage home ɗin,” 

   Murya asanyaye hafsat tace”shikenan mommy amma ina so ki sani haƙƙinsu ba zai ta6a barin mu ba! Sai Allah ya saka musu duk wani cin zalinsu da mu kayi,!!!!!!!!!!!!!!!! tana faɗin hakan ta juya tare da shigewa cikin ɗakin,

   wani irin matashin murmushi aunty babba tasa ki tare da cewa “Komai zaki ce ki ce, nidae in dae burina zai cika ba abunda bazan iya aikatawa ba ehen,” 

   acan ciki kuwa bayan hafsat ta shiga wuri tasamu gefen gadon ta zauna maimakon ta tashe su sai kawai tafashe da kuka mai cin rai

   Sautin kukanta ne ya farkar da jahad a firgice ta tashi zaune hankali atashe take cewa “Subhanallahi Aunty hafsat meya faru naga kina kuka? Meya same ki? jahad ta tambaya fuskarta cike da nuna alamun damuwa,

   Ci gaba da kukan hafsat tayi sam ta gaza cewa komai jikinta har wani jijjiga yake yi, jahad ta kuma cewa “dan Allah sister hafsat ki daina kuka, ban ta6a tunanin zanga wannan ranar ba, idan wani abu ke damunki, zan taya ki addu’a Allah ya yaye maki

   jin wannan maganar ta jahad yasa hafsat ƙara sautin kukan nata, ɗagowa tayi ta kalli jahad idanunta jawur suna fitar da zafafan hawaye tace”Jahad ba saboda kaina nake wannan kukan ba, face saboda ku ! Ina tausayinku, Nasaba daku zan iya cewa akanku nafara jin tausayin wani ɗan adam aduniyar nan !! 

   tun da jahad taji hakan gabanta ya faɗi Rasssss !! Duk da hafsat bata fito fili ta faɗa mata kai tsaye abunda yasa ta kuka ba, 

  miƙewa hafsat tayi tana faman sharar hawaye tace “Ki tashi hussana ku shirya inaso zan fita daku,” 

  Jiki a mace jahad tace “Toh,” cikin sauri hafsat ta fuce daga ɗakin,

   Jahad kuwa jikinta har kerma yakeyi saboda tsoran inda hafsat zata kaisu, daker tasamu hussana ta farka daga bacci sannan ta sanar da ita cewa ta tashi su shirya Sister hafsat zata fita dasu,

  Batare da sunyi wanka ba, tsaka tsami kawai su kayi acikin toilet sannan suka fito suka shirya, jahad ta zumbula doguwar riga Orange colour ta yafa mayafi launin fari akanta, ita kuma Hussana riga ce Square neck green colour, sai Skirt Ethnic maxi ta sanya ajikinta yana da dan faɗi ya bude da ƴar bazarsa, ba ƙaramin kyau su kayi mata ba, Mayafi tasamu launin skirt ɗin black colour  mai ɗigon fari² ajikinsa, tayi rolling ɗinsa tamkar yadda Jahad tayi,

Kallon hussana kawai jahad keyi kallon tausayi don ita ranta yana bata cewa lokacin barinsu gidan ne yayi, yanzu kuma zasu fuskanci wata ƙaddarar !!!

  lokacin da suka fito daga ɗakin hannunsu ruƙe dana juna,  Aunty babba na’a falon sai faman zagaye zagaye take yi, tana ganinsu ta nufo su cikin sauri gudun kada ishaq ya farka daga bacci ya fito yagansu,

   Tana ƙaraso wa inda suke tace “Ku biyo ni,” sannan ta juya ta miƙi hanyar fita daga falon, bin bayanta su jahad su kayi gabansu na faɗuwa, suna fitowa daga falon a harabar gidan tuni hafsat ta fito da motarta, buɗe musu motar aunty babba tayi tana cewa “Maza ku shiga ciki, ku jira hafsat yanzu zata zo, Allah ya kiyaye hanya,” ta faɗi tana faman tiƙar dariya sannan ta rufe musu motar, 

   Kusan minti goma sha biyar suna zaune jigum cikin motar gaba ɗayansu babu mai magana duk jikinsu yayi mugun sanyi ganin yarda Aunty babba ke faman yi musu dariya, tun daga haka suka gane cewa ba lafiya,” 😳😳😳

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Wannan na jiya ne da banyi ba, da Anjima zan saki next page insha Allah kuma shine, Ga masu son cigaba da karanta Littafin Abban Sojoji su tuntu6e ni ta wannan numbar (08103884440)

Back to top button