Zakuna Biyar Page 21 By Princess Teema
“Zayra’an, all what you said is true, mom ta cutar daku, ta zaɓi abin duniya a kanku, babban abin takaici ma shi ne yadda ta yarda ta sayar da kwakwalwar daddy, ta aminta aka kashesa aka cire brain ɗinsa, sannan ta yi poisoning Nirash, but realize something about Dr, she knows that she made a big mistake against you, dalilin da yasa kenan ta bada ranta ta ceceka dik dan ta wanke laifinta ka yafe mata, and Seraphina, she doesn’t deserve you to do that to her, dik rikicinku da Dr bata san wannan ba, and stop comparing mom and Dr, kasan Dr ba zata iya sayar da kwakwalwarka ba dik da ka kasance ɗan baiwa kaman daddy ko? And this innocent girl Seraphina, idan ka yi treating ɗinta ta wannan hanya shi ne ma zai sanya ta zama muguwa, yanzu bata san komai ba, yanzu take buƙatar ilimin rayuwa daga gareka, yanzu yakamata a koya mata komai, why would you banish her from your life? Why?”. Da kyar Champion ya kai karshen maganar saboda tashin hankalin da yake ciki, ALLAH ya ɗaura mashi kaunar Leo, idan ya tina lokacin da Lion ya zo da shi rike a hannunsa yana fafutukan mutuwa, bakinsa na kunfar poison sai ya ji tsikar jikinsa na tashi, a ranar haukace kawai basu yi ba, Lion ya sha alwashin sai ya shayar da mom guba kamar yadda ta shayar da wannan jaririn da bai san komai ba. Kuma har yau bai san in da mom ɗin tasu take ba, ya nemeta kamar hauka, tin a ranar da ya je gidanta a Washington, ya so kasheta, har ya daɓa mata wuƙa a gefen ciki guards ɗinta suka kama shi aka kaisa kotu daga nan aka kaisa gidan yari, tin daga wannan lokaci bai sake sanin in da take ba, shekarunsa 3 a gidan yari ya fito, tin da ya fito kuma nemanta yake yi. Amma allegedly mom ɗinsu ta yi surgery ne aka canza mata fuska dan ta kaucewa shiga hannun Lion, shiyasa yake ta nemanta bai ganta ba, ta yiwu tana kusa da shi bai sani ba, dan ance dik ta yi surgery ta canza halitta, ta koma ƴar yarinya mai ƙananan shekaru kamar 18 years. AKWAI CAKWAKIYA INA FAƊA MAKU, amma gaskiya mom ƴar duniya ce, tana can tana yaudarar samari bayan ya koma ƴar yarinya, da ciwo ace irin wannan uwar ce da su, gara ma su kasheta su huta.To shi Lion burinsa shi ne yakamata ta faɗa mashi su waye ta sadaukarwa da kwakwalwar daddynsa, dan ya yi alkawarin wlh sai ya karɓo brain ɗin mahaifinsa, gara mashi ya haƙa rami ya binne da ya barshi a jikin wanda aka yi mashi dashensa, to dalilin biyu yasa yake neman mom, ya kamata ta faɗa mashi su waye ta sadaukarwa, na biyu kuma ya shayar da ita gubar da ta shayar da Leo yana jariri! Dan haka dik abin da kuka ga Lion yana yi kada ku ga laifinsa, an kuresa ne, sun sa zuciyansa ya bushe ya ƙeƙashe, sun jefasa cikin manyan gangsters and terrorists ya yi rayuwa da su a prison, ya sha bakar wahala sosai, yanzu wutar fansa ce kawai take ruruwa a zuciyan bawan ALLAHN nan, shi kaɗai yasan wani irin raɗaɗi yake ji, sai ma idan ya tina cewa an dasawa wani banza can kwakwalwar daddynsa yana can yana morarta yana rayuwa, shin aikin alkhairi yake yi da kwakwalwar ko kuwa aikin sharri? Waɗan nan sune manyan ciwukan dake zuciyar Lion, amma kuma bai bari Leo yasan gaskiya ba, ya ɓoye mashi ta hanyar faɗa mashi basu da iyaye sun mutu, ya reni kaninsa cike da soyayya da kulawa, ya sadaukar da lokacin, dukiyansa da komai ɗinsa dan Leo ya zama mutum, babban abin takaicin kuma shi ne dikkansu da mahaifiyarsu suke tsananin kama, ko ɗaya basu yi kama da daddyn nasu ba, sai kaifin kwakwalwarsa kawai suka gado, shiyasa idan Lion ya ga fuskansa wani irin takaici ne yake kama shi, saboda in dai zai ga face ɗinsa to sai ya tina mom ɗinsu, shiyasa ko a cikin gida zaku gansa da face mask dan ma kada ya ga face ɗin nasa idan ya zo gifta mirror. —————————–🔥 “Aryan stop! Stop it i said! Dr and mom dik ɗaya ne, mata dik basu da imani, ita Dr ba ita ta zama sanadin mutuwar Big Bro ba? Ka manta lokacin da na kirata a waya, ban taɓa rokan mutum wani abu a rayuwata ba, amma a kanta na dinga rokonta da ta buɗe Big Bro ya gudu, ta sake shi akwai matsala, me ta ce mun?”……. Nisawa ya yi kafin ya ɗaura da cewa. “She said so kake shi ma ya zama irinka ne? Ba zai sake fita ba! Kamar zan yi hauka ina cikin Washington, I called you and I called Scorpion that time dik baku yi picking ba, ina ji ina gani Big Bro ya mutu mutuwar walaƙanci all because of her! Da ita aka haɗa baki, ita ta bawa wasu damar su shigo su kashesa, in ba haka ba meyasa zata ɗauke wayoyinsa, ta rufesa a ɗaki ta hana shi guduwa? Why?!!”. With harsh voice ya kai karshen maganar.Shiru su Aryan suka yi, dan basu da wani hanya na ƙoƙarin wanke zuciyar Lion kan mata ba azzalumai bane, saboda ta ko’ina macece ta jefasa cikin bakar wahala, ya ɗanɗani zafin dafin harbin mace, dan haka kome zasu ce ba zai taɓa yarda ba. Amma da yake Aryan soyayyar Seraphina ta rufe mashi ido, sai ya yi ƙoƙarin wanketa, yasan idan ya yi shiru har Lion ya gane yana zuwa wajenta to rabasu zai yi, shi kuma ya kai matakin da ba zai iya rabuwa da ita ba, dan haka dole ya tursasa zuciyar Lion ya yarda cewa ba dikka mata bane mugaye, kuma Seraphina bata cancanci hakan ba.Guru ne ya amsa da. “For sure Dr tana da sa hannu a kisan Big Bro, idan ba haka ba meyasa a lokacin da ka kirata kake ce mata ta buɗe mashi kofa ya gudu akwai matsala taki sauraranka? Meyasa ta rufesa a gida? Ai yana zuwa gidan bata taɓa rufesa ta hanasa fita ba sai wannan rana? Meyasa? Then ta kwashe wayoyinsa ta gudu da su, after mutuwansa ta gudu ta canza gida a lokacin da ka dawo daga Washington saboda tana tsoron haɗuwa da kai!”. Aryan ne ya amsa da. “Wlh bana jin Dr tasan za’a kashe Big Bro, kawai ina ga abin ya zo mata unexpected ne, and ku tina abu ɗaya mana, Dr bata da kowa, bata san kowa a US ba sai mu, and ta san su waye mu, ba zata taɓa yarda ta bi son zuciya ko zancen wasu a kanmu ba, zata ji tsoro, then dik wanda ya zauna da ita yasan macece mai rauni, meyasa idanunku ya rufe a tsanar mata kuke son ɓoye gaskiya ne? Zayra’an ai kafi kowa sanin halin Dr, amma saboda baka son mata shi ne zaka haɗasu kai masu kuɗin goro?”. Cikin fushi Lion ya ce. “Da sa hannunta, a wanan ranar kuɗi sun shiga account ɗinta daga wani account na daban wanda aka sanya mashi matakan tsaro, all IRON FIST members muna da information a kan dik wasu motsinsu kasan hakan, meyasa kake ƙoƙarin kareta bayan kafi kowa sanin cewa da sa hannunta?!!”. Cikin tsawa Lion ya faɗa tare da kara shake wuyan Aryan da karfi, zuciyarsa na tafarfasa haka ya buga Aryan da jikin bango da karfi, sun tina mashi da abin da ya wuce, sun ɗaga mashi hankali, ya shiga out of control.Da karfi Aryan ya ɓanɓare hannun Lion daga wuyansa, shi ma ya shake Lion ɗin yana faɗin. “Babu sa hannunta, kuma kaima kasan hakan, ni ba zan bi son zuciya in ki faɗar gaskiya ba, takan iya yiwuwa kuɗin da ya shiga account ɗinta na wani abin ne daban da wasu family suka tura mata! Baka yi tinanin hakan ba, sai ka tsani Seraphina, ƴarka, domin kawai mammynta tai maka laifi!!”. Ya kai karshen maganar tare da buga Lion da jikin bango shi ma.Guru ne ya ce. “Kun fara kenan, sai ALLAH ne kaɗai zai iya sassauta maku wannan ɗan banzan zuciya da fushin”. Ɗaga Aryan cak Lion ya yi ya buga shi da jikin wall glass na wajen restroom ɗinsu har sai da glass ɗin ta tarwatse watsa-watsa, cikin tsawa Lion ya ce. “Waye take da shi da zai tura mata kuɗi? All our family ni kaɗai nike tura masu kuɗi! Tana da ƴan uwa da ahali ne a nan? And ita da take ƴar kauye cikin daji a yaushe family ɗinta suka samu damar rike account mai tsaron da ba za’a iya bibiya ba? Ka daina rainawa kanka wayau Aryan!!”. Ya faɗa tare da dunkule hannu ya daki show glass na littafansu cikin fushi, take glass ɗin ya faɗi ƙasa ya tarwatse kaca-kaca. A daidai lokacin Aryan ya tashi tsaye, zuciyansa na tafarfasa ya nufi Lion gadan-gadan, glass table ɗinsu ya ɗauka ya makawa Lion a gadon baya yana faɗin. “Baka son gaskiya, saboda ka tsani mata shi ne a kansu baka taɓa kyautata masu zato, ba zaka yi tunanin kirki a kan wannan al’amari ba, ko bata da ƴan uwa za’a iya tura mata kuɗi”. Ya faɗa ne kawai amma shi kansa yasan ba haka bane, lallai kuɗin da aka tura account na Dr daga babban account mai tsaro ya fito, shi kansa Aryan ɗin yasan da kamshin gaskiya a batun Lion, amma soyayyar Seraphina yasa lallai sai ya wanketa a gaban Lion. Da karfi Lion ya juya ya shakesa, ya ɗagasa sama, sannan ya buga shi da ƙasa kafin ya ce. “Ba zan yi tinanin alkhairi ba in dai akan mata ne! I hate them and also you now, i don’t want to see your face!!”…….. Wani irin azaba Aryan ya ji, hakan yasa ya ɗan rintse idanu, da kyar ya iya miƙewa, cikin fushi ya sake ɗaukar flower decoration ɗinsu ya bugawa Lion a kai ta baya, nan Lion ya juyo suka fara gwabza faɗa tamkar mayunwatan zakuna. Shi dai guru rungumo hannayensa a kirji ya yi yana kallonsu, saboda yasan bafa zasu rabu ba, shi kaɗai bai isa ya rabasu faɗa ba, idan suna yi sai sun jigata dan kansu sun hakura, amma batun rabasu ma bata taso ba. Cikin ƙanƙanin lokacin suka wargaza ɗakin kaca-kaca, suka fashe dik wasu glass dake wajen, suka lalata komai, sun jiwa kansu ciwo sai jini suke zubarwa, Aryan yaki yarda da maganar Lion shi me Lion yaki yarda da maganarsa, kowa gani yake shi ne mai gaskiya.Yau sun jima suna faɗa saboda magana ce kan abin da ya shafi zuciya, sai da guru ya ga Lion ya ɓaɓɓako Tv ɗinsu daga jikin bango zai bugawa Aryan dake baje a kasa yana numfashi sama-sama ne ya yi saurin dakatar da shi ta hanyar dannawa da gudu ya rike Tv, suna cikin fushin nan zasu iya kashe junansu ne ma basu sani ba, kun san zuciya bata da hankali wani lokacin.Ƙoƙarin kwacewa Lion ya fara yi dan har yanzu zuciyansa tafarfasa yake yi, sanya karfi guru yai, suka fafata, da kyar ya kwaci Tv ɗin saboda Lion ɗin ma ya jigata babu karfi sosai a jikinsa, so ya samu damar kwacewa kafin ya yi ta mazan shigar da Lion cikin wajen balcony ya rufe glass door ɗin. Da gudu ya zo ya ɗauki Aryan cak ya saɓa a saman shoulder ɗinsa ya fita waje. Yana fita ya rufe kofar har da sanya key, a daidai lokacin Lion ya rugurguza glass door na wajen balconyn ya dawo cikin ɗakin, sai huci yake yi, kun san ance idan rai ta ɓaci sai hankali ya gushe to haka ne.Ɗayan room dake kusa da nasu guru ya kai Aryan, ya kwantar da shi saman gado tare da shiga cikin drugs room ɗinsu, cikin gaggawa ya ɗauki wata allura, jikinsa har yana rawa wajen fara ƙoƙarin haɗa alluran nan, yana jiyo Lion na ƙoƙarin ruguje door room ɗinsu, dama su biyun nan zuƙatansu na da wuyar sarrafuwa idan ta kwaɓe masu, shi ma Aryan ɗin dan Lion ya dakesa da laptop ɗinsu a kai ne yasa ya shiga wani irin yanayi tamkar ya suma, kun san duka a kai akwai wahalar iya jurewa, ban da haka da yana cikin hayyacinsa wlh ba zai hakura ba shi ma, zai ce sai dai a yarda shi ne mai gaskiya, to thank god ya shiga coma mood.Yana gama haɗa alluran ya fito da gudun gaske, kai tsaye room ɗinsu ya koma, yana zuwa daidai door Lion ya ruguje kofar zai fito. Cikin zafin nama guru ya shammacesa ya dankara mashi wannan allurar a gefen wuya, da sauri Lion ya dafe wajen tare da juyo da kallonsa a kan guru, ɗayan hannunsa yasa ya damki wuyar guru, ya shakesa da karfi, yana ƙoƙarin yin magana amma ya gagara, take idanunsa suka fara rufewa a hankali, ya fara ganin abubuwa bibbiyu, kan kace me wata yana ta fara rufe mashi gani. Jim kaɗan ya saki jikinsa gabaɗaya zai faɗi ƙasa tare da zame hannunsa daga wuyan guru. Jifa guru ya yi da kwankon alluran hannunsa, cikin zafin nama ya tare Lion ɗin, sannan ya zare alluran dake wuyan nasa ya jefar kafin ya gyara shi da kyau, ya ɗaukesa cak sai saman shoulder ɗinsa, ya fito da shi zuwa ɗayan ɗakin dake gefe ba wanda Aryan yake ciki ba, ɗakinsu da suke kwana su uku kam yau ma sun fashe komai kamar yadda in ta kwaɓe masu dama suke ruguje komai, sai sun huce ake sayan sabbin kaya, amma idan suka yi faɗa, oooooo kai kace abokan gaba ne ƴan duniya.Room da Aryan yake a ciki guru ya koma dan ya duba ba dai ya samu matsala a kan nasa bane. Yana shigowa room ɗin daidai Aryan na dirowa kasan bed ɗin, da alama ya dawo normal. Fuskan nan tasa tamkar wanda aka bawa bakar labarin cewa wuta zai shiga, yana wani irin huci ya ce. “Ina Zayra’an?”……. Hannu guru ya harɗe a saman kirji kafin ya ce. “Aryan kada ace idan rai ya ɓaci sai hankali ya gushe mana! Ka sani cewa Zayra’an ba zai taɓa saurarenka ba, ba zai yarda da abin da zaka faɗa ba, kuma kai da kanka kasan kan batun case na Dr Lion ya fika gaskiya, mun san bata da ƴan uwa a nan, sannan ƴan uwanta na can a daji suke, ta ina ta samu kuɗi daga irin wannan shahararren account da sai manyan gangster’s ko terrorists or manyan ƴan siyasa suke amfani da shi? Mun yi iya yinmu mun gagara bin diddigin mai wannan account ɗin, ka yi lissafi mana”. Hannu Aryan ya ɗaga mashi. “Is enough, koma dai menene Seraphina bata cancanci ya mata hakan ba”….. Kallon tuhuma guru ya wurga mashi kafin ya ce. “Aryan anya kuwa? Meyasa ka damu da Seraphina haka?”……. “Because she’s my daughter!”. Cikin tsawa ya faɗa. Gyara tsayuwa guru yai yare da ɗan karkata kansa, ya ɗan ɗaga mashi gera guda kafin ya ce. “After that kuma fa?”. Wani irin kallo Aryan ya wurga mashi kafin ya ce. “Get out of my room!!”. Cikin fushi ya faɗa. Kun san wani abu? A daidai wannan lokaci da suke ta faɗar su kuma Abba da Ammie suna can zaune suna shirin zuwa gidan makota tambayawa su Aryan auren yaransu, da Aryan, da Faryan and Harleen, Abba ya ce sun girma dik aurar da su zai yi, dan haka ya ga wasu ƴan mata uku a makwabta, ɗaya ma ƴar siyasa ce, yana ganin tana da kyawawan halaye, zata dace da Aryan, kun san su waye yake magana a kai? Su Aunty Luna Aunty’s ɗin Noor, su Abba ya gani, ya yaba da hankalinsu, kun ga shi ba’a auren soyayya a gidansa, dan haka gobe zai je nemanwa su Aryan aure, dama so yake su tsayar da magana da Ammie gobe ya kira Aryan maza su zo su shirya su tafi aje a kaisu ƴan’matan su gansu idan sun yi masu.Bafa idan ƴan matan sun yi wa su Aryan ɗin ba, a’a, idan dai su Aryan ɗin sun yi wa ƴan matan, shi Abba ba ruwansa da su Aryan basa so ko yaran basu yi masu ba, shi dai yardan ƴan matan kawai yake so, to jama’a wacece zata ga Champion namu na amana ta ce bata ciki? Ai kowacce makale mashi zata yi, akwai dai dirama, wai kaman Champion ɗin namu ne za’a kai mace ta gani ta zaɓa, lallai su Aunty Lusi anyi kasuwa mai tsadar gaske. Watau idan na hango cakwakiyar dake gaba a cikin littafin nan har wani ɗan juya mun kaina yake yi. Sanin cewa suna cikin fushi ne hasa guru ya juya ya fita, bai sake magana ba. Cikin fushi Aryan ya wuce toilet zuciyansa cike da tunanin Seraphina baiwar ALLAH kuma marainiyar ALLAH. Ni kam na ce daddy Aryan ko dai ko dai? Ka faɗi gaskiya fa!. —————————-🔥WS-HOSPITAL.Safiyar yau ta fara masu ne da yanayi na musamman, sun tashi cike da farincikin da basu san dalili ba saɓanin yadda suka yi barci jiya da takaicin sister Lazy. Shiryawa suka yi tsab cikin kayan aikinsu, suka fito zuwa wajen aiki, sun mance ma da batun sister Lazy na jiya, saboda su mutane ne da sam basa rike abu a ransu, da sun yi barci sun tashi zasu mance komai abinsu. Daidai zasu shiga side ɗinsu watau side C sai ga su Dr James a jere su ukun kamar yadda suka saba tafiya. Jikinsu na rawa suka sussunkuya suka gaishesu, dik in da zasu wuce sai an sunkuya an kaishesu saboda su ne manyan kwararrun likitocin. Ko kallon in da suke basu yi ba suka wuce suka shiga section D. Da kallon su sister Maya suka bisu har suka shige ciki, ajiyar zuciya sister Zinta ta sauke kafin ta ce. “Kwanaki biyun nan Dr James suna yawan zuwa section D, ko dai wani project suke yi ne? Kullum da safe sai sun shiga wajen, suna kuma ɗaukar awanni kafin su fito”. Maya ce ta amsa da. “A tinaninki menene a section D and section E?”………. Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. “I think akwai babban aiki a wajen, dan kinga su uku ne suke shiga wajen, project ne babba a wajen, musamman section E ɗin nan da yake killace a gefe guda, ga tsananin matakan tsaro har da kofofi masu amfani da lantarki a wajen, kai ina son sanin me a cikin wajen?”. Maya ce ta ce. “Idan kika koma aiki a karkashin office ɗinsa zaki iya sani fa, mu dai dage da aiki tukuru”……. “I wish hakan ya faru”. Sister Zinta ta amsa da hakan……. “Me ya tsayar daku a nan?”. Daga bayansu suka ji muryan sister Lazy. Da sauri suka wuce cikin section C ba tare da sun yi mata magana ba, ita kuwa fuuuuu ta zo ta wuce section D in da su Dr James suka shiga, tana wani hura hanci, ga hancin nata ya yi siriri sosai, ga shi dogo, ko ta hurasa baya huruwa, watau sister Lazy kyau ɗinta har yai yawa ya zama mata muni, kunganta kamar Aljana danginsu ifiritai, idanunta wlh in ta zarosu sai mutum ya ji hantar cikinsa ta kaɗa, manya-manyan ne idanun nata, gasu farare tas kamar audiga, sannan a waje suke, gashin idanunta tamkar an kara kuma a tsaitsaye suke, bata da lips in ji sauran nurses, saboda ƙanƙantar bakinta, yadda kuka san babyn roba dai haka take, ALLAH na tuba kyan yai yawa har ya mai data kamar aljana. Su kuwa su sister Maya komai nasu daidai ne gwanin birgewa, sai idanunsu suma kamar nata ne manya-manyan farare kal kamar audiga. Cikin section D sister Lazy ta shiga, a nan ne waɗan nan tarin mahaifa dake cikin kwalabe suke in baku manta ba, bata bi ta kan mahaifan ba ta wuce izuwa wani kofa dake fuskantar kofar shigowa. Tura kofar ta yi ya shiga. Ɗaki ne mai girma sosai a wajen, cike yake da gadajen tiyata da a kallah zasu kai gado 30 zuwa 50, ɗakin yana da girma sosai, tsayawa zayyana maku abin da ɗakin nan ya kunsa ba zai yiwu ba, kawai mu je ciki, dan abin babba ne. Kowani gado dake a cikin wannan ɗaki akwai mace guda ɗaya dake kwance a kansa, kuma ƴan mata ne da basu wuci 18 to 20 years ba, dikkansu kuma kamar barci suke yi ne ko suma, kai da alamar alluran barci aka yi masu, kowacce yarinya ka ɗaga ido ka kallah zaka san me ake nufi da kyan ɗan adam, wlh kamar su suka yi kansu, kyawawan gaske. Su Dr James suna tsaye a tsakiyar room ɗin, suna dudduba ƴan matan da kyau, sun canza kayan jikinsu izuwa surgical gown and gloves, alamar sun shirya aiki kenan. Dik macen dake kwance a kan wannan gadon gabanta a buɗe yake babu kaya, daga ta sama a rufe da patient gown, amma ƙasansu a buɗe. Dikkansu eggs retrieval za’ayi masu. Cikin kwarewa dikka Doctors ɗin suka ɗauki kayan aikin da zasu buƙata, kowannensu ya nufi gadajen dake layin farko a jere, gadajen line by line ne a jere, so suna bin komai daki-daki. Ita ma sister Lazy kayan aikinta ta ɗauko watau jota and pen ta nufi wajen bed ɗin da Dr James yake, su Dr Kamal ma kowannensu da PA ɗinsu kamar dai Dr James da sister Lazy.Ɗauko wani needle suction tube watau bututun ƙarfe su yi, kai bari mu bi Dr James mu ga yadda yake yi, ba sai mun bisu dikka ba, yadda yake yi haka kowannensu yake yi.siririn bututun ƙarfe ya ɗauka tare da ɗaukan wani siririn na’ura ya ɗaura a kan cikinta, take computer dake manne jikin gadon da yarinyar ke kwance ta kanta ya kawo wuta, kai tsaye cikin cikin yarinyar ne ya bayyana a kan screen na computer, ɗan zubawa computer waɗan nan dara-daran idanun nasa Dr James ya yi. Sai da ya ɗauki 3 mins yana kallon yanayin cikinta tare da ɗan junjuya naurar dake kan cikin nata yana duba lungu da saƙo kafin nan ya gyara kafafun yarinyar dake kwancen, ta gabanta kofar virginity ɗinta ya zura wannan bututun ƙarfe mai karfin da ya ɗauka, dik da yarinyar tana barci sai da ta ɗan tsuke fuska alamar akwai azaban zafi kenan, imagine, yarinya budurwa ka zura mata wannan siririn bututun ƙarfe a gabanta har izuwa cikin cikinta, dole akwai azaba mana.Yana zura karfen idanunsa a kan computer dake gabansa, yana kallon hanyar da yake bi ne, kada ya saɓa aiki, kai tsaye ovaries nata ya nufa da karfe, wlh yarinyar nan sai tsuke fuska take yi cikin barci, ga shi dai an mata alluran barci, amma har cikin ranta tana jin azaban aikin da ake mata.Kofar follicle ɗinta ya buɗe tare da zura needle suction tube ɗin ciki, tsotse ruwan dake cikin follicle ɗin nata ya fara yi, follicle ɗin kamar jaka haka yake, ruwa ne da kwan ke zama a cikinsa a cikin jakar, dan haka sai an tsotse ruwan idan ana son kwan. KAI JAMA’A KU CE ALLAHU AKBAR, billahil lazi dik wanda bai bi ALLAH ba ya yi asara duniya da lahira, kun san matakan dake akwai kafin ciki ya shiga mahaifar mace? Kun san irin halittar da UBANGIJI yai a cikin mace kuwa? Kai ku kara cewa ALLAHU AKBAR, UBANGIJINMU baya saɓa komai, dikkan likitocin duniya dik kwarewarsu basu isa su gano wani lamari na UBANGIJI da ya tsara a cikin mace ba, shi kansa kwan haihuwa UBANGIJI yai mashi follicle in da zai rayu ya ji daɗi na ɗan lokaci, a haka wasu zasu ce ALLAH bai da adalci? Kai na sake cewa ALLAHU AKBAR, ALLAH buwayi gagara misali!!Wannan ruwa na cikin follicle shi embryologists watau kwararrun likitocin mahaifanmu su Alhaji Dr James zasu zuƙe su shiga tube na gwaji zuwa laboratory inda zasu nemo kwan a karkashin microscope, to shi dai Dr James ya zuƙe. A taƙaice karamar tiyata yai mata, ya shiga ovaries ɗinta da wannan karfe ya ciro kwayayyen da ovaries ɗinta suka saki, kwayaye sun kai 10 a cikin wannan ruwa ya kwaso, sai da ya kwashe tas, sannan ya zaro bututun da gabaɗaya ya yi wanka da jininta. A cikin wani karamin kwalba ya zuba kwayayyen haihuwar da ruwan tata tare da sanya hannu ya ɗauko audiga bayan ya rufe kwalbar, a gaban nata ya sanya audigar dan tsotse jinin da ya biyo baya kasancewarta virgin. Daga haka ya ɗan haɗe mata kafafunta waje guda kafin ya matsa zuwa gado na gaba, ya gama da nata aikin, kwayayyen kuma suna barinsa a wajen gadon kowace da suka cire mata har sai sun kammala cire masu dikka, sannan su tattare kwayayye su wuce da su.Haka suka bi dikka yaran dake kan gadon suka masu wannan azabben tiyatan suka ciro kwayayyen haihuwarsu, abin mamakin kuma kowacce yarinya kwai sama da 10 suke cirowa daga jikinta, a ƙaida kuma mace tana sakin kwai guda ɗaya ne a wata, sai waɗan da ALLAH ya kaddara suna da rabon samun twins sai su saki kwai biyu, haka masu rabon samun ƴan uku, to amma ya aka yi waɗan nan yara suka bada kwai sama da 10 a lokaci guda? Abin da mamaki gaskiya.Amma ni bari in yi maku bayani yadda zaku fi ganewa. A jikin mace akwai ovaries, a hausa kamar ace ƙwanƙwason mace kenan, to ovaris side guda biyu ne ai, ciki ya raba kenan, ki duba a jikinki akwai wata ƙashi dake ta gefen ciki wajen kwankwaso ko? To ta jikinsa ovaries yake.A kowace wata, jikin mace yakan saki kwai ɗaya masu rabon twins biyu, daga cikin waɗannan ovaries ɗin kwan yake fitowa, shi kuma ake kira da ovulation, bari dai in kara maku yadda zaku gane, wata yana da kwanaki talatin ko? To ovulation watan sakin kwai yana faruwa ne kwanaki 14 kafin mace ta yi wani period ɗin, misali ace kina yin period 16 ga wata ace period ɗinki yana yin kwanaki 7 kafin ki kammala, idan an haɗa kinga mun samu kwanaki 23 a wata, to idan kin kammala jikinki zai huta na kwanaki 8 zuwa 9, sannan ki saki kwai a 2 ga watan da zamu sake shiga, kinga saura kwanaki 14 ki yi sabon period kenan, muna magana ne a kan idan 16 ga wata kike yin period ɗin, dan haka in 16 ga wata kike yi to 2 ga wata zaki dinga sakin kwai, fatan kun gane? To mu je zuwa, a sauƙaƙe kuma a gajerance nai maku. Yauwa mace na sakin kwai sau ɗaya a wata na ce ko? To amma kwararrun likitoci irinsu Dr James suna iya tsokanar ovaries ɗin, sukan yi amfani da hormonal medications dan ovaries su fitar da ƙwai da yawa lokaci guda ba kamar yadda mace ke fitar da ɗaya kawai a wata ba.And a ƙaida na kwan mace idan ya fito daga ovaries yana yin awanni 46 ne zuwa 48 idan ba’a sadu da mace ya haɗu da maniyyi ba sai ya lalace, shi yake zama period da muke yi a yau, idan ya lalace sai ya zama jini ya fita.To bayan su Dr James sun baiwa waɗan nan yara magungunan dake sanya ovaries sakin kwai dayawa irinsu gonadotropins fsh and lh, waɗan nan magunguna suna motsa ovaries su samar da ƙwai dayawa suna barin kwan ya yi 24h, ya girma kenan, sai su yi masu egg retrieval wanda suka yi masu a yanzu kenan suka ciro kwayayen.A likitance ana kiran hakan da egg harvesting, karin wani haske, idan eggs ɗin mace ya fito daga ovaries yakan bi wata ƙaramar hanya mai suna fallopian tube inda zai je wajen kusa da mahaifa ya tsaya, to a wannan lokacin idan mace ta sadu da namiji kafin 48h zata samu ciki, dan maniyin namiji zai haɗu da kwanta da nata maniyin sai su shiga mahaifa.To amma idan bai haɗu da maniyi ba, ma’ana ba’a sadu da ita a waɗan nan lokutan ba, to kwan yana mutuwa ne after 48 hours ɗin, idan ya mutu kuma jikin mace zai fitar da shi ta hanyar haila, idan mace ta samu ciki kuma ovaries ɗinta suna taukewa ne su daina sakin kwai, shiyasa take daina yin haila da ciki, kwayayen haihuwarta shi ne yake zama hailar dama, idan babu su to babu haila ai kun gani!. Wannan shi ne abin dake gudana a wannan sashi na SECTION D, mu je zuwa dan ganin me suke yi da waɗan nan kwayayye kuma.Tsab suka bi suna cirewa yaran nan kwayayyensu, virgin daga cikin yaran sun zubar da jini, wasu kuma a’a, bayan sun kammala suka tattare kwayayye suka komo da su cikin ainahin section D ɗin, suka rufe kofar da ya haɗa cikin section D da kuma in da waɗan nan ƴan mata suke. Kowannensu aikinsa ya kama, yanzu ma bari mu bi Dr James dan muga me zai gudana a wannan waje, tin da dik yadda ya yi hakan dikkansu suke yi. Dik kwayayen da suka zo da shi wajen wani jiga-jigan freezer dake cikin wajen suka nufa, a nan suka shisshirya kwalaben eggs ɗin, sannan suka fito da wasu kwalaben da already suke cikin freezer, da alama ma sun jima. A taƙaice dai freezing ɗin eggs ɗin zasu yi.Suka fito da waɗan da tin last month suka cirewa ƴan matan sannan suka cire kwan daga ruwan follicle a microsoft shi ne suka ajiye a cikin freezer, sai yau amfaninsu ya zo. Sister Lazy ana ta aiki ana satar kallon masoyi Dr James ɗin da ko sau ɗaya bai san tana yi ba, aikin dake gabansa kawai yake yi cikin natsuwa da taka tsantsar.Gaban wasu manya-manyan freezer dake can jefe nesa da in da wajen freezer na kwayayen macen suke suka tsaya, kun san section D yana da balain girma, gari guda. Wasu kwalaben suka ɗauko mai shake da sperm na maza dana mata. Suka isa gaban kwalaben dake ɗauke da mahaifan mata da suka shirya last time idan baku manta ba, sperm na maza dayawa ne a cikin kwalaben, dayawa sosai fa, kowani kwalbar dake ɗauke da maniyin akwai rubutun da suka yi a jikin kwalbar, a kallah kwalabe 50 haka suka fitar da su kamar yadda kwalaben kwayayyen matan ma yake 50.Hallau yanzu ma dai bari mu bibiyi Dr James dan ya fi kowa kwarewa a kan aiki. Amma kafin mu tafi ina da tambaya, ta ya suke samun maniyin maza masu yawa haka? Ku duba yawan kwalaben fa! Which means ba maniyin mutum ɗaya bane! To taya suke samunsu? Gara kwan mace suna iya tiyata su ciro bayan sun basu maganin da zai sanya su samu kwan dayawa, amma maniyin macen da maniyin ɗah namiji ta ya suke samosu? Gaskiya wannan ɓangaren akwai sarkakiya da ɗaure kai mai tarin yawa, yanzu dai muka fara shiga cikin labarin, koma dai menene zamu ji kuma zamu gani. Wani karin haske, idan sun ciro sperm na maza fa sai sun kaisa lab sun tacesa, su cire masu karfi a gefe, su ware marasa karfi a gefe, dikka kuma suna amfani da su, sai dai kowanne da amfaninsa ne, amma idan muka shiga cikin zaku gane me suke yi da sperm mai karfi da mara karfi bayan sun banbantasu.Dr James ne ya gyara hand gloves ɗin hannunsa, lokacin fertilization ya yi kenan, gaban wasu naurori ya tsaye, sannan ya ɗauki wata karamar na’ura mai kama da eyes care ya sanya a idanunsa, kamar glass haka na’urar take, wannan na’ura tana iya zuƙo komai ƙanƙantar halitta a wajen shiyasa suke sanyata, kamar microsoft take. Sperm masu karfi da aka rubuta baby boys a jikin kwalbar ya ɗauko, a gaban petri dish ya tsaya, kwan mace ya fara zubawa a cikin petri dish ɗin kafin ya tultula maniyin dake cikin kwalba guda ɗaya gabaɗaya, ya haɗesu waje guda kenan. Wai na ce kun san a cikin dubban maniyi kaɗan ne ALLAH yake hukuntawa suke ɗauke da halittar yaro ko baku sani ba? Shiyasa Dr James ya zuba maniyin dikka dan yasan akwai mai amfanin a ciki wanda dik iliminsu wanesu su iya zaƙulo shi, wannan ilimin mai sama ne kawai! ALLAH ne kawai yasa wannene mai halittar yaro.Bayan ya haɗasu sai ya sanyasu cikin incubator tare da saita yanayinta ya zamana kamar dai cikin mace, sannan ya barsu dan su haɗe da kansu dan ba’a isa a haɗesu lokaci guda ba, da kansu suke haɗuwa kamar yadda suke haɗuwa a cikin mace.Bayan ya yi wannan sai ya ɗauko sperm marasa karfi sosai ɗin wanda aka rubuta baby girls a jikin kwalbar, Intracytoplasmic sperm injection ya ɗauko tare da fasawa ya tsira a cikin kwalbar sperm ɗin ya haɗa da allura ta microscope, bayan ya haɗa sai ya zuba maniyin kai tsaye a cikin kwan macen, ya yi mashi yadda yai wa sperm mai karfi na farko, wannan allura da yai wa maniyi shi zai sanya sperm ɗin ya yi kwari har ya bada abin da akeso tin da ba’a cikin mace suke ba, dole sai ana kara mashi karfi!.Su Dr Kamal ma dik haka suka yi nasu, aiki tukuru fa suke yi cikin taka tsantsan sosai, suka shirya sannan suka barsu cikin incubator, zasu barshi ne ya yi kwanaki 3 zuwa biyar, a lokacin ne zai gama haɗewa da kwan yadda yakamata, sai ya zama zygote, a kwanaki na gaba daga sati biyu zuwa 4 daga zamansa zygote kenan, sai ya fara zama embryo, to idan ya fara zama embryo shi ne zasu dawo su canza mashi muhalli, dan idan ya zama embryo ya fara zama halitta, gudan tsoka kenan, kullum zasu zo su dinga dubasu dan su ga waɗanne ne suka fi karfi da lafiya suna ware kwalabensu jefe, masu raunin ma a gefe. To idan ya ƙara kwanaki kamar biyu nan ne ake cirosa daga in da suka sanya, a wannan gaɓa idan mace za’ayiwa dashensa sai ta zo ayi mata aiki, shi ne zaku ji ana cewa an yi wa mace dashen cikin ko an haɗa kwayayen haihuwar mace da namiji an dasawa wata macen ta ɗauki cikin ta haihu, ba aiki ne na wasa ba, sai an yi da taƙa tsantsan, ba dik kai ne ke iya wannan aiki ba, bugu da kari ana iya samun matsala sosai, dandai su Dr James mayun doctors ne, sun kware, na ce maku a duniya irinsu basu da yawa, sun kuma saba wannan aiki sosai, shiyasa a wuni ɗaya suna iya haɗa kwai da sperm sama da 50 idan suka tashi aiki, dan haka ku gansu ne kawai ku barsu. To su Dr James ba’a cikin mace suke dashen embryo ɗinsu ba, dan haka after 2 days suka dawo suka canzawa embryo ɗin wajen zama, suka yi dashensu a cikin waɗan nan mahaifa da suke sanyawa a cikin kwalabe masu kama da cikin mace, a ranar ma wuni suka yi suna dashensu, bayan sun kammala suka saita na’urar dake bawa cikin kwalbar yanayi daidai da cikin mace, suka shirya komai, sai da suka tabbatar komai na tafiya daidai sannan suka fito, Dr James ya wuce office ɗinsa tare da sister Lazy dake rike da takardun rahoton, dan ita aikinta a wajen shi ne suna aiki tana ɗaukar rahoton dik wani motsinsu, in sun kammala su duba rahoton dan su ga ko akwai wani matsala su yi gaggawar gyarawa.A lokacin su kuma su sister Maya suna wajen nasu aiki, ba su kaɗai bane suke aiki a SECTION C, akwai nurses dayawa, amma su kaɗai ne masu amfani a labarin namu shiyasa nike magana a kansu kawai. Wasu shirga-shirgan guards ne suka shigo da wasu sabbin chemical a cikin manyan-manyan glass box. A jikin kowani box da sunan chemical ɗin a rubuce. Mimmiƙewa dikka nurses dake wajen suka yi suna kallon box ɗin, taɓa sister Maya sister Zinta ta yi tare da cewa. “Yau kuma sabbin chemical muka samu, ya saɓa da waɗan da muka saba aiki da su, wannan kamar eesveratrol, nicotinamide mononucleotide, hyaluronic acid, retinoic acid and collagen peptides ne ai”….. Kai Maya ta jinjina game da cewa. “Su ne, sai mu hau shiryasu yadda yakamata ai”. Kai sister Zinta ta jinjina, daga nan suka umarci saura nurses ɗin da su zo su fara ɗauko ƙananan bottle suna zubawa a ciki suna rubuta sunan kowanne da kilonsa sannan su shirya a muhallinsa. Wai me ake yi da dikka waɗan nan chemicals ɗin ne? a ina suke samo sperm na maza? me suke yi da su? ina suke kai yawan uban sperm da kwayayen mace da dik wata sai sun cirewa mata ne? akwai sarkakiya da ɗaure kai a wannan ɓangare, na tabbata ba karamin ilimi zaku samu a wannan waje ba, bugu da kari zaku hankalta da abubuwa dayawa, sannan zaku gyara kurakuranku dayawa, zama nai sosai na shirya maku ingantaccen ilimi mai muhimmanci a wannan waje, i say it again, ban taɓa rubuta irin wannan labari ba, bana jin kuma har in gama rubutu a rayuwata zan sake yin littafi mai tarin iliminsa!!A office ɗinsa Dr James ya zauna tare da karɓar takardan rahoton, ba tare da ya kalleta ba ya ce. “Go and call Zinta for me”…….. Wani irin yawu ta haɗiye na takaici, yanzu ta gasgata cewa jiya shi ya kira Zinta kenan, ranta a matuƙar ɓace ta juya ta fito. Fuuu ta nufi section C, tana wani irin huci. Zata bar arear su Dr muryan Dr Kamal ya katseta da cewa. “Lazy call Maya for me”. Takaici yasa bata kallesa ba ma ta amsa da okey tare da wucewa, suna neman sanya mata karamar hauka.Cike da faɗa ta afko cikin section C, tana tafiya kamar zata faɗi ƙasa, wannan idan iskar mota ya zo tsab zai wuce da ita, ga wani kafurin high heel da ta kwama a kafa, sai ya sanya tana tafiyar ƴar tsana, tana wani cokala kafa, ni kam na ce ki dai tafi a hankali, a rage saurin kada a faɗi ƙasa, to naga kafafun ne sirara kamar na sauro, ga takalma yasa ta yi sama can ai kunga dole in faɗi haka.Tana sanyo kafafunta a cikin side ɗin sai da kowacce nurse ta natsu tsabar kowa yasan balainta, sai ƙoƙarin hura siririn hancin nan take yi abu ya ci tura yaki huruwa. Kai tsaye cikin chemical set ɗin ta shiga. Cikin gadara da bada umarni ta ce. “Ke Maya ki je Dr Kamal na kiranki, ke kuma Zinta ki biyo bayana”. Tana kai karshe ta juya fuuuu kamar wata kumfar teku ta wuce gaba.Tana fita nurses ɗin suka fara gulmarta, dan babu wanda yake sonta a hospital ɗin nan, miƙewa Maya ta yi, muryanta na rawa ta ce. “Sister Zinta a tinaninki meyasa Dr Kamal yake nemana?”….. Zinta da hankalinta ya gama tashi ne ta amsa da. “I don’t know what to say now gaskiya, kawai ki je da wuri, dan basa son ɓata lokaci su”. Tana kai karshe ta bi bayan sister Lazy da sauri, kirjinta sai bugawa yake yi da karfi-karfi, tana fatan alkhairi ne yasa wanna aljanar zata kirata, baiwar ALLAH bata san cewa Dr James ne yake kiranta ba.A tare da Maya suka fito, can a bakin side na office ɗinsu 3D (3 Doctors) ɗin nan suka hango Lazy a tsaye tana cika tana batsewa tana jiransu. Jikinsu dik a mace tamkar waɗan da kwai ya fashewa a ciki suka nufi in da take. Tin basu kariso ba ta juya ta wuce ciki fuuuu, bayanta suka bi, Sister Maya ta wuce office na Dr Kamal, ita kuma Zinta ta bi bayan sister Zinta zuwa office na Dr James. A tinaninku meyasa 3D suka buƙaci waɗan nan innocent nurses ɗin? Muje zuwa, Star Lady taku ta amana ina tare daku, sai mun warware komai a tare! Mu leƙa team DEATH OR LIFE (DOL) mu dawo mu ji meyasa 3D ɗin nan suke kiran ƴan matanmu.————————🔥DOL.🔥Har dare ya tsala suna wajen a zazzaune, idan wutar ya mutu su kara wasu kirare su hura hutan, babu alamar barci a tattare da su, domin a horon bar 2 an horasu da yunwa da rashin barci, sai su yi kwanaki uku basa barci, kazalika suna 24h babu abinci dik dan su saba, so yanzu ya zame masu jiki, yunwa da rashin barci ai abokin aikinsu ne. V tin tana dan ja baya, tana rike da hannun Romeo ɗinta suna hira har ta saki jiki ta kwanto jikinsa tare da miƙe kafafu suna hira, dik wani motsinta a kan idon Juraiz, har ga ALLAH yarinyar ta tafi da imaninsa. While Arya na ɗaki, ta gama iya dube-dubenta, daga karshe ta rufe laptop ɗin, ta ci abinci kaɗan sannan ta kwanta dan yin barci. Manassa na waje bakin kofa tana latsa waya.Bayan Agelina ta gama waya da Aunty Lisa sai ta dawo wajen ta zauna, matsawa kusa da ita Unays ya ya yi, cikin salo ya ce. “Hy, good evening”. Kallo ɗaya ta ɗan mashi tare da ɗauke kanta kafin ta amsa, dan ma dai yana gaba da ita ne da ba zata amsa ba. Ƙoƙarin janta da hira ya yi, amma ta basar da shi, saboda yaran GAT akwai jan aji wlh, V ce dai mai saukin kai.Takura mata Unays ya dinga yi da ƙoƙarin sai ta kula shi, ita kuwa tana amsa shi sama-sama, sai ya yi magana uku take amsa ɗaya, a gaskiya Unays karya ne mace ta ce bai haɗu ba, cikakken namiji ne, ga kyau, chocolate da shi, but Angelina bata nuna kamar ya haɗu mata ba.Sai da 12 ta buga ne, cike da bada umarni Zaynish ya ce. “Dik matan nan ku tashi ku tafi ɗaki”. Abin ku da shi musulmi ne, kuma yasan darajar mace. Ɗago ido Noor ya yi ya kallesa, sai ya ga Zaynish baya kallonsa, haka na nufin ba dan saboda Noor ɗin na baiwa flower ruwa shi da V ya yi maganar ba, hasalima shi bashi da matsala da soyayarsu, kawai dai yaga bai dace matan suna cikinsu a wannan lokacin bane.Ganin ba da wata manufa Zaysh ya yi maganar bane yasa Noor ce mata ta tashi su shiga ɗaki. Matsawa ta yi, sumbata ya bashi a kumatu kafin ta miƙe tsaye, miƙewa Angelina ma ta yi, suka nufi hanyar komawa tantinsu. Dab zasu shiga ciki V ta ji an rike hannunta ta baya, tana juyowa ya jawota jikinsa. Ajiyar zuciya ta sauke, wucewa ciki Angelina da Manassa dake zaune a wajen suka yi.Haɓar V Noor ya ɗago, cikin zafa ya haɗe bakinsu, hot kiss ya shiga bata, mayar mashi da martani ta fara yi, yasa hannu ya fara shafa tula-tulanta yana lumshe ido. Ita kuma ta kankameshi ta baya tana tura mashi tongue ɗinta. Sun ɗan ɗauki lokacin a haka kafin ya saketa tare da ce mata goodnight, ya faɗa still yana matsa tula-tulanta bai saki ba. Juyawa ta yi da sauri ta shige cikin tantin nasu, shi kuma ya juya ya koma wajen da suka hura wutan. Tin da ya zo wajen suke kallon juna da Zaysh kaman wasu munafukai, magana da ido suke yi.Kashewa Zaysh ido ɗaya ya yi kafin ya koma wajen zamansa ya zauna, harara Zaysh ya watsa mashi tare da ɗauke kansa, ya cigaba da dannar wayansa. Haka suka kasance har wayewan gari, basu rintsa ba. Da sassafe su Arya suka tashi, one by one suka fito waje, nan suka isko sojoji masu yi masu girki sun hura wuta. Wucewa Arya ta yi izuwa wajen koramar dan ta yi wanka, tana sanye da white bathrobe.Tana wucewa sai ga Angelina ta fito rike da waya a hannunta, daidai lokacin Leo ma ya fito sanye da sleeping dress ɗinsa, ya ɗaura towel fari a kansa, bai bi ta kan kowa ba ya wuce wajen karamar baya shi ma. Wucewa Angelina ta yi izuwa wajen da ta ga sojojinsu na zazzaune, tana sanye da kayan jiya bata canza ba. Daga ɗan nesa da sojojin ta tsaya tare da ɗaga wayarta ta kama ɗaukar su Unays hoto, dik suna zazzaune, basu sani ba, ta ga su Unays an mata kyau yau, sai kawai ta tsaya kashe masu hotuna tana murmushi. Daga bayanta ta ji an ce. “Aiki ya sameki kema, kin faɗa irin cutar V ko?”….. Ba tare da ta juya ba ta amsa da. “To ke Manassa wai ina ruwanki da mu ne? Ke dai ba kin ce Arya zaki biyewa ba? Babu namijin da ya kai ku yi soyayya da shi ko? Na tabbata watarana zaku faɗa tarko ne!”…… Brush ɗinta Manassa ta sanya a baki ba tare da ta sake cewa uppan ba ta wuce izuwa wajen wani dogon bishiya dake gefen su Unays ɗin tana goge bakinta.Harara Angelina ta bita da shi kafin ta cigaba da ɗaukarsu hoto. Ita kuwa Arya tana zuwa wajen koramar ta ware igiyar bathrobe ɗinta, ta zaresa ta ajiye a gefe, ya rage daga ita sai pant and bra da yake suna sakawa yanzu. Saboda santin da take ji ne yasa ta rufe idanu ta faɗa cikin ruwan dake kwance ƙasar koramar wai dan ma kada sanyi yasa ta fasa shiga. Ruwan a daidai kirjinta ya tsaya da ta tsugunna a ciki, kana iya hango tudun tula-tulanta a waje, ruwa ta fara ɗeba a tafukanta tana watsawa a fuskanta tana ɗan tsuke baki saboda sanyi, ga ruwan koramar daga sama yana zuba ta baya bayanta, sun kafa tantin wajen da zasu yi wanka fa, amma tsabar iskanci irin na Arya a nan take son yin wanka. Da yake ta rigada ta shiga sai ta fara jin daɗin ruwan, tsoma kanta a ciki ta yi tare da ɗagawa da sauri ruwan ya biyo gashinta ya hau wanke mata fuska. Cike da farinciki tasa hannu tana sharce ruwan face ɗin nata, slowly ta buɗe idanu kai tsaye sai a kan Leo dake tsaye yana ƙoƙarin kwance igiyar bathrobe na jikinsa. Ai bata san time ɗin da ta zunduma ihu ba, ya yi mugun bata tsoro, bata ji motsin mutum ba, bata ma kawo a ranta akwai wanda ya ga wannan koramar a cikin sojojinsu ba, ta zaci ita kaɗai ta ga abinta shiyasa ta zo shanawa a wajen taki zuwa toilet da suka kafa.Ko a jikinsa wai dan ta yi ihu, hasalima bai ɗago ya kalleta ba ya cigaba da kwance igiyar, ya buɗe rigar ga shi yana fuskantarta, daga shi sai shorts irin matsastsun nan da kana iya ganin shatin halittarsa, daga sama babu ko single ne, faffaɗar lion chest ɗinsa a waje, ko kaɗan bai damu ba, ita kuwa ta yi suman tsaye a cikin ruwan, ga shi ta kudurtawa ranta ba zata fita ba tin da ta rigasa zuwa, sai dai shi ya hakura ta gama. E kam akwai case, zan ga da ita da shi waye zai hakura ya barwa ɗaya wajen

