Mijin Marigayiya Page 4 Hausa Novel
Afaf ta kama jakar tana kokarin dagawa Abbansu yace ‘Ke ajiye jakar nan ba zaki iya dauka ba.’ Suna tsaye a dakin a gaban wardrobe tana tambayar Afaf ina jakar Abbansu ya shiga dakin dauke da jakar, yace ‘Ga ta nan, gani nayi ba zata iya daukowa ba na dauko mata.’Ta yi ‘yar dariya tace ‘Haba dai, Yaya Afaf ai ba raguwa bace, jakar ma da babu nauyi.’ Sukayi dariya gaba daya, ya ja yaran suka fice daga dakin suka barta ita kadai tana kokarin samarwa akwatin kayansu waje. Bayan ta ajiye akwatin a kusa da mudubi ta dan ja baya ta kare wa dakin kallo; komai tsaf yake tunda an share lokacin da ana kafi sai dai ba a shimfida zanin gado ba a kan babban gadon nasu. Bata san a ya suke kwana ba kafin a aurota amma dai tana jin a kan gadon suke kwana duka. Ta fito ta samesu a parlor sun baje suna kallo suna ta yiwa Abbanau surutu. Ta dubesu tace ‘Bari na ciro hijabin nan Afaf sai ki tayani mu gyara dakin.’ Abbansu yace ‘Wannan ce za tayi wani gyaran daki? Babu abinda ta iya fa.’Tayi ‘yar dariya tace ‘Bari ka gani.’Ta shige dakinta; tana shiga ta cire hijabin ta jefa kan gado, ta karasa gaban wardrobe ta bude tana duban babban rigar da zata saka.Wani malolo ya tokare mata makogoro saboda takaici; to ta ina zata soma? Haka kawai ya kwaso mata yara a wannan daren. Da ya gaya mata ma ai da tuni ta gyara dakin. Ta ja gajeren tsaki a Fili.Motsin shigowarsa ne ya katse mata tunanin, ya nufota yana cewa ‘Na zata a nan dakinki zasu kwana ai.’Ta dan goge idonta ta juyo tana cewa ‘No, gara kawai na gyara musu dakinsu tunda babu wata kura da yawa a dakin sai su kwanta a can.’ Ya dan tabe baki ‘Ok, ammma dai za ki dinga zuwa kina dubasu ko?’’Eh mana wannan ai dolene.’ Ta amsa tana dan juya jikinta.Ya juya ya fita ba tare da ya ko kalli jikin nata ba. Ta kalle jikinta ta dan murgude baki; yau dai kwalliyarta ta tashi a aikin banza kenan.Ta janyo babbar riga a wardrobe din ta saka, ta sa hula ta rufe gashinta sannan ta fito. Kai tsaye ta wuce kitchen ta dauki tsintsiya da parker, ta fito parlor din ta dubesu tace ‘Taso Afaf, maza mu gyara dakinku ku sami wajen kwanciya.’ Ta wuce ta barsu, a tunaninta yarinyar zata biyo bayanta. Sai dai har ta shiga dakin ta fara kokarin sharewa babu motsin tahowarta, ta dan dakata da sharar da takeyi ta kwala mata kira. A maimakon yarinyar ta amsa sai Abbansu yace ‘Abinci muke ci.’ Ba tare da ta amsa ba ta sunkuya ta cigaba da sharar, har ta dan yi nisa a sharar sai kuma ta tuna cewa yayi abinci suke ci fa; to wanne abincin? Tuwon da ta tuka da shinkafa gwangwani 1 da Rabi din ya tasa yaransa a gaba suke cinyewa? Bayan ta gaya masa zata jirashi ya dawo su ci abincin dare tare? Tuwon ma da gaba dayansa malmala uku ne ta tuka saboda ta san miyar ba zata isa su ci dumame ba. Har ta ajiye sharar ta nufo parlor din sai kuma ta tuna idan ta zo me zata yi a kai, don haka sai kawai ta cigaba da sharar ta tana fatan Allah ya sa su rage mata tuwon. Ta share dakin ta karkade ko ina sannan ta shimfida zanen gadon da ta dauko daga dakinta. Ta kalli dakin taga ko ina yayi tsaf, sannan ta dauko sharar da ta kwashe ta fito. Suna zaune a kan dining table suna ta cin tuwo shi da ‘yayansa, kafin tayi magana Abbansu ya dubeta yace ‘Yauwa dan karo mana tuwon nan Habib bai koshi ba, ga Shukra ma kamar zata kara.’Ta dan zaro ido tace ‘Wai kun ciye na flask din?’’To nawa yake, ai bashi da yawa.’ Kafin ta bada amsa Nasreen tace ‘Kuma miyar tayi dadi Anti.’ Ta yi murmushin yake tace ‘Shikenan dama na dafa, ko nima ban ci ba.’ Habib yace ‘Abba nifa ban koshi ba, dama bamu ci abincin dare ba lokacin da muka taho gashi mun manta bamu karbo kazar mu ba a wajen Mama.’Abbansu ya dubeta yace ‘Yanzu ya zakiyi da Habib? Yunwa yake ji.’ ‘Akwai ragowar bread sai mu raba ni da shi mu sha da tea, don gaskiya yanzu ba zan so dora tukunya ba.’ ba tare da ta saurari amsarsu ba ta wuce kitchen da sharar a hannunta.So take ta sami waje tayi kuka ko taji sanyi a ranta, don haka ba tare da ta kalli wajen ba ta jefa sharar ta juya sink ta fara wanke hannunta. Abbansu ta jiyo a bayanta yace ‘Khadeeja, daurewa fa zakiyi ki dafawa Habib Indomie don shi baya cin bread kuma kinga ai ba ya kwana da yunwa ba.’Ta kalleshi suka hada ido tace ‘Babe na gaji ne wallahi, nima ina son tuwon amma na hakura zan ci bread.’Ta dan saurara tana kallon yanda yake kara hade rai, sai kuma cinkin sanyin murya tace ‘Amma Afaf ta zo na kunna mata cooker ta dafa musu Indomie din.’Ya kalleta shekeke yace ‘Wai ke me kika dauki Afaf ne she’s only eleven babu abinda ta iya na aikin gida. Idan ta girma dai ta koya but ki daure kawai ki dafa masa.’ Ta juya ta bashi baya saboda hawaye ne yake Shirin kwace mata, ya juya ya fice ya bar mata kitchen din. Ta share hawayenta ta sauko da tukunya karama ta zuba Indomie din da ruwa da komai ta kunna wuta ta dora. Ta koma ta jingina da sink ta tsaya ta kafa tagumi; yanzu shikenan har ta gama amarcin, ko awa biyu yaran nan basu yi da zuwa ba amma sun gundireta, anya kuwa zata iya wannan rayuwar. Ko da yake dai yanzu suka zo ta san basu fahimceta ba itama kuma bata fahimcesu ba; amma dai zata dorasu a saiti kwanan nan. Tana cikin juye Indomie din suka shigo kitchen din suka wanke hannuwansu, sai dai abinda ya bata mamaki babu wanda ya dauko plate din da yaci abincin ya kawo kitchen din; duk a dining table din suka baro mata. Ta gama juye Indomie din ta mikawa Habib bayan ya gama wanke hannu.haka ta fito ta kwashe kwanukan daga dining su kuma suna zaune suna kallon TV. Ta hado shayi ta dauki guntun bread dinta ta wuce daki. Bayan ta gama shan shayin ta dauko kofin ta fito, tana isa gaban sink din zata ajiye kofin ta ga Indomie din da ta dafawa Habib ko rabi bai ci ba kuma ga dukkan alamu ya koshi kenan. ‘mtsewww’ ta ja tsaki a Fili.Ta wanke hannunta ta fito daga kitchen din. Har zata wuce daki Abbansu yace ‘Kizo ki shiryasu sun fara jin bacci kinga 10 har ta gota.’ Ta juyo ta dawo, ta dauki Shukra wadda ta riga ta fara gyangyadi Afaf, Habib da Nasreen suka bi bayanta. Sune suka nuna mata kayan baccinsu ta taimaka musu duk suka yi brush sannan suka shirya, ‘yan matan gaba daya suka haye gadon. Ta kalli gadon taga ma ba zai ishesu ba don haka ta koma dakinta ta dauko katifar da aka kawo mata saboda baki ta shimfidawa Habib a kasa. Ta gama tsaf zata kashe musu fitula Nasreen yace ‘Anti ba a kashe mana fitila sai mun yi barci.’Ta mayar da fitilar ta kunna musu sannan ta fice daga dakin, ta wuce Abbansu a parlor ta shige dakinta. Ta riga ta gaji sosai don haka itama kayan bacci kawai ta saka ta rufe dakin nata ta wuce dakinsa, ta kwanta ta rufe idonta. …….. Lokacin da Khadeeja ta fito daga dakinsa ya zata dakinsu Afaf zata koma don su kwana tare, amma sai ya ga ta shige dakinsa. Ya tashi ya shiga dakin yaran inda ya tarar dukansu sunyi bacci, don haka ya kashe musu fitilar ya fito daga dakin. Ya kashe fitilun falon ya shige daki.Tana kwance a kan gado kamar ma bacci takeyi, don haka ya kyaleta. Bayan ya gama shirinsa ya kwanta, ya mika hannu ya tabata, ta juyo ta bude ido tace ‘Babe, ka shigo?’’Um.’ Ya amsa a gajarce.Ta fara kokarin matsowa jikinsa, ya tashi zaune yana cewa ‘Kin baro yara su kadai, kin ga daga nan ma ai ba lallai ki jiyo motsinsu ba. Ni da na zata ma tare zaki kwana da Shukra a dakinki fa, she’s just 3 bata saba kwana ita kadai ba.’Ta dan matsa ta koma inda ta baro tana cewa ‘No, they will be fine fa, ba kaga a tsakiyar yayunta na sata ba kuma duk fa sun yi bacci. Ka ga na ma saka alarm wajen biyun dare zan je na dubasu sai kuma da asuba.’ ‘Uhm, amma dai da kin daure kin kwana da su din.’
