Hausa novels

Harijin Tsoho Page 21 Romantic Hausa Novel

Sun isa gurin dinner tara da rabi na dare,kamar yadda zahra ta tsammatace ta faru mata ne gasunan kamar ana gasar sarauniyar kyau.fitowar daddy daga mota sosai yaja hankalin mutane,musamman mata dan motar dayazo acikinta miliyan ɗari shidace da sabain,nanfa ya tsaya gaisawa da mutane dasuka masa barka da isowa,mata ko se kwarkwasa aketa masa da nufin anzo gaisheshi,zahra dake cikin motar ita abunma mamaki ya bata watakan uncle ɗinta haka yake da farinjini kenan ita take ta masa kallon nakasu ga rayuwarta. zagayowa yayi ya buɗe mata ƙofar.hannu ta miƙo masa ba musu ya kama kyakkyawan hannun nata dayasa jamaa da dama ƙosawa ta fito aga wacece mamallakiyar hannun.ƙafafunta ta ziro waje sannan ta taka ta sakko da ƙarfinta,wanda daddy yayi zaton faɗuwa zatayi yayi saurin kai jikinsa ayko ta lafe aƙijinsa ya rungumeta.mutanen dake gurin kansune yafara lissafi dan da sun ɗauka babantane amma wannan runguma tasa sun sauya tunaninsu.maida ƙofar daddy yayi ya rufe,ya matsa remote,sannan yasa hannu ya gyarawa zahra gyalen nata,sannan ya kama hannunta tana wani shigewa jikinshi suka bi bayan wanda sukazo yimusu iso.suna taka bakin hall ɗin mc ya fara gabatar da shigowarsu.”to jamaa atashi a girmama me girma honorable Alhaji sammani canji sanatanmu na gobe tare da Amaryarsa,bisa samun damar halartar wannan taro namu me albarka da yayi”ayko kowa miƙewa yayi harda ango da amaryar ana tafa masa hmmm zokuga step gurin zahra,ga dj yasa waƙar daddyn ta siyasa guri ko se tafi ake.daddy riƙe da kyakkyawar amaryarsa se ɗagawa mutane hannu yke ana sekayi honorable .gurin zama na musamman aka basu can kusa da abban zahran wanda jin daɗin ganinsu yasa yyi suman zaune,wai zahranshi ke tafe tare da hamshaƙin me kuɗi kuma fitaccen ɗan siyasa irin alhaji sammani wai amatsayin matarsa ta aure tilo,in be godewa Allah ba mezeyi.suna ƙarasowa ya miƙe suka rungume juna shida daddy,suna murnar ganin juna,yana sakin daddyn itama zahra ta shige jikinshi ya rungumeta tana faɗin “abbana nayi missing ɗinka”ta faɗi ashagwaɓe daddy na musu dariya.”muma munyi naki zahran abba,kina lafiya ko?”cewar abba.bayan ya saketa.lafewa tayi ajikin daddy ta manne kafaɗa tana dariya tace”ga tabbacin lafiya nake kuwa ka gani abbana”dariya sukayi su duka suka koma suka zauna masu hoto se haskasu sukeyi,zahra na lafe ajikin mijinta ta hana ƴanmata masu kawo farmaki rawar gaban hantsi shi kanshi daddyn hankalinshi nakan zahra yana mata hira akunnenta wacce yawanci yaba kyan da tayine ykeyi ita kuma tana shigewa jikinshi tana dariya.goma da rabi suka fito gurin badan antashiba sedan zahra dake hammar bacci da takeji.atare suka fito da abba,ga hadari ya haɗu wanda seka fito wajan hall ɗin kake ganinsa.dan har nfara yayyafi.sallama sukayi da Abba ya wuce motarshi suma suka shiga tasu daddy yaja suka bar gurin.ay kamar jira,ruwa ko ya kece a hanya kamar da bkin ƙwarya wanda ruwan haɗe yake da iska me ƙarfi da walƙiya ga tsawa anayi.dole tasa jamian kula da haɗɗura suka tsaya kan tituna suna bada umarnin motoci su tsaya ruwan ya lafa danko gabansu basa gani.dole daddy shima ya faka yasa double signal,zahra se rawar sanyi take dan ruwan yasaki sanyi sosai,bakinta har karkarwa yake.”ya akayi sarauniyar kyau,lafiya kuwa?cewar daddy yana ruƙo hannunta.dubanshi tayi ta taɓe baki kamar zatai kuka tace”sanyi nakeji kuma banason wannan walƙiyar tsoro take bani daddy.”ta faɗi a shagwaɓe.”da nace acanjo shiga ay cemin akayi wlh ahaka zaaje to ayga sanyinan da ruwa na miki hukunci”cewar daddy yana murmushi.Ayko kuka tasa nishi harda buga ƙafa ba shiri daddy ya ɗagota can daga kan kujerarta ya ɗorata kan cinyarshi yana mamakin rashin nauyinta dukda manyan ɗuwawukan da take dasu amma sam bata da nauyi.lafewa tayi ajikinshi ya rufeta da malum malum ɗinshi sannan yasa hannu ya kunna heater motar,cikin ƙanƙanin lokaci motar a ɗauki ɗumi.zahra lub aƙirjin mijinta tana shaƙar niimtaccen ƙamshinshi dama bacci takeji ayko tuni baccin yayi awon gaba da ita.daddy kallon fuskarta yayi yana murmushi so da ƙaunarta na ƙara wanzuwa a zuciyarshi ahankali yasa baki ya sumbaci ɗan ƙaramin bakinta ya ƙara rungumeta ajikin nashi.basu jima sosaiba ruwan ya lafa akacsaki hanya daddy yaja motar sukabar gurin,12 na dare suka iso gida,koda yayi parking be tashetaba ya fito ɗauke da ita ahannu ya rufe motar da ƙafa,ya matsa key ya shige gida da ƴar babynsa iya rigima a hannu.ɗakinta ya kaita ya kwantar da ita ta zare mata takalman ƙafarta sannan yaja mata ƙofar ya fice zuwa nashi ɗakin.

Back to top button