Uncategorized

Tubali Book 1 Chapter 3 hausa novel complete

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

Kallo mai cike da tarin takaici ya watsa mata, rikitattun idanunshi cikin nata kwayar idanun kasan cewar suna fuskantar juna.

Wani irin azabebben zogi lips ɗinshi sukeyi sabida yadda ta bugi gemunshi da goshinta, har hakan yasa lips ɗin suka haɗe da kyawawan haƙorinsa.

Zut-zut haka yakeji suna zogi.

Da raɗaɗi, wani irin tafasa zuciyarshi takeyi tare da harbawa, files ɗin campany’nsa da yake da matuƙar mahimmanci da suke watse a ƙasa ya zubawa idanu.

Wani irin mugun kallo ya kuma watsa mata duk a cikin abinda baifi 5 second ba.

Idonshi ya kai bisa hannunta dake shaƙe da kwalar rigarsa ta gefe.

Hannunshi na dama yasa ya damƙo hannunta da azaban ƙarfi, kana ya yarfashi.

Wanda sanadin fizge hannun nata da yayi kuma wayarshi, kirar iphone 12 pro max dake cikin al’jihun rigarsa ya faɗo ƙasa.

Kana  ita kuwa Jannart wani irin masifeffen karkarwa jikinta keyi.

Yayinda kuma gaba ɗaya hankalinta kecan baya.

Sabida masifar tsoron Yah Junaid da ta tabbatar muddin ya ganta sai ya kusan kasheta.

Haka yasa gaba ɗaya ma hankalinta baya kanshi, bare taga ta’adin da ta aikata mishi.

Tangal-tangal tayi lokacin daya yarfa hannun nata, da sauri ta dafe ginin gefenta tare da gyara tsayuwarta, cikin rashin sa’a ta sauƙe ƙafarta ta hagu kan glasss ɗin fuskar wayar tashi, da tsinin takalminta mai masifar ƙarfi.

Saurin yin ƙasa da kansa yayi, sakamakon jin ƙaran sautin fashewar glass din wayarsa, wanda take dauke da screen mai tsada. 

Idonshi ya rumtse da ƙarfi.

Yana mai jin tamkar ya shaƙe wuyanta sai tayi sanyi.

Sam Ba ɗaruruwan kudin wayar yake tunawa ba, muhimman abubuwansa dake cikin wayar yake tunawa wanda yasan tabbas zai iya rasa wani abun.

Ita kuwa Jannart da sauri ta sunkuyo jin ta taka wani abu kuma tsantsi ya ɗebi ƙafarta.

Da sauri ta janye ƙafar tata cikin wani akasin kuma, ta sauƙe tsinin takalmin nata, kan tattausan ƙafarsa dake cikin tattausan takalmin fata,

dai-dai kan farcen babbar yatsarshi ta kafa tsinin takalmin tare da sake iya nauyi ta.

“Auchhhhhh!!”. Ya sake wani irin sauti tare da rumtse idanunshi da ƙarfi, hade kuma da taune lips ɗin shi na kasa dake ta zogi tun buge shi da tayi.

Ƙara rumtse idanunshi yayi sabida wani irin,

masifeffen azaba da yaji tun daga tsakiyar kanshi har cikin ƙoƙon ranshi, kana ya iso kan babbar yatsar tashi.

Da sauri ta kuma janye ƙafarta, tare dayin baya kaɗan tana mai wai-wayen bayanta, alamun sam hankalinta baya gabanta sai baya.

Wani irin kallo ya zubawa tarin ɓarnar da tayi mishi,a lokaci ɗaya ta lalata mishi abubuwa da yawa, har lfyarshi bai tsiraba

Ta nuƙurƙusashi tamkar wanda yayi karo da tirela.

Wani irin nannauyan numfashin ta sauƙe ganin Salman ne ke biye da ita a bayan yana ce mata ke ɗin.

Da sauri Salman ya iso garesu.

Ganin yadda suke tsaye cirko-cirko.

Rayyern ya kalla cikin nitsuwa,

tare da fahimtar karo sukayi, cikin sauri yace.

“Innalillahi karo kukayi, bawan Allah kayi haƙuri.”

Ya ƙare mgnar yana sunkuyawa files din ya fara tattarewa, yana mai cewa.

“Subahanallahi, wayarka duk ta dare, Jannart garin ya akayi haka”.

Ita dai Jannart sai numfashin tsoro take sauƙewa, ta gaza cewa komai sabida ganin wani irin mugun masifeffen kallon da yake watsa mata, sai yanzu idonta ya kai ga ta’adin da tayi mishi.

Da sauri tayi ƙasa da kanta dan bata da jarumtar da zata iya jurar kallon nan daga kwayar fitinennun idanunshi.

Yatsun ƙafarshi ta tsurawa ido ganin yadda suke tsuma alamun tsananin azaba, ga kuma jini da take tsastsafowa.

Dib-dab-dib-dab haka taji zuciyarta na bugawa a 170. 

Salman kuwa cikin yanayin damuwa ya miƙowa Dr Rayyern Mai-nasara Takardun da wayar cikin yanayin jin ba daɗi yace.

“Dan Allah da Manzonsa kayi haƙuri bawan Allah”.

Idonshi ya rumtse da ƙarfi tare da miƙa hannunsa ya amshi takardun da wayar.

Sabida Salman ya gama dashi, tunda yace.

“Dan Allah da Manzonsa yayi haƙuri, to ya zame masa wajibi kuma dole yayi haƙuri sabida wannan shine mafi ƙololuwar al’farmar da mutun zai nema a wurin musulmi yayi mishi, wannan shine kalaman da Abban sa ke cemasa a mafi akasarin lokuta.

Amman badon haka ba yaso ya yarfawa wannan birkitacciyar yarinyar mari ɗaya rak, taji salon yadda tafin shi yake, so yayi ya yarfa mata mari da hannun hagunshi wanda yasan tabbas sai ta saki fitsari sabida ya lura bata iya bada haƙuri ba, kuma bata da nitsuwa.

Wani irin juyowa yayi ya watsa mata wani irin kallo da fuska a murtuƙe,

“Mchewwwww “. Yaja mata wani irin tsaki tare da yin kwaffa kana ya juya yayi gaba ba tare da yayiwa  Salman mgn ba.

Cikin kaɗuwa Salman yace.

“Jannart ya akayi haka, kinga asarar da kikayi mishi kuwa, nasan tabbas duk yadda akayi kece da laifin karon tunda kin hango mala’ikan ɗaukan ranki, kina gudu kina rawan jiki kina wai-waye kinzo kin mishi ta’adi.

Kin kuma san kuɗin wayar nan da kika fasa mishi sarai amman ko a jikinki. 

Sannan kin tsaya kinyi shiru, wannan wanne irin tsorone kijeyiwa Junaid?”

Ajiyan zuciya mai nauyi ta sauƙe, tare da lumshe idanunta a hankali cikin nutsuwarta da ta fara dawowa tace.

“Allah ya bashi haƙuri, wlh Salman na rasa ta ina zan fara bashi haƙuri ne,  kagafa wani irin kallon da yakemin tamkar zai shaƙeni ya kasheni, tsoronshi naji.

Sannan kuma duk tsorona kada Yah Junaid ya ganni, wlh in ya ganni a nan kuma bance zanzo nanba bisa aikina sai ya kusan kasheni, duk allurarsa ta sojoji a kaina zai direta.”

Cikin takaici Salman yace.

“Shike nan ai mun rasa damar farko, dan yanzu dai da wuya in Dr.Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara bai wuceba tun tuni, matsalar ba sanin fuskarsa akayi ba bare ace da mun ganshi zamu ganeshi.

Dama dole bincike zamuyi da numbers din motocinsa, da aka bamu zamu ganeshi mubi bayanshi muga gidansu. Kinga har lau dai tsoron Junaid yana hanaki nasara.

Har nima ta shafeni.”

Cikin takaici tace.

“Toh ya zanyi?”.

Kwaɓe fuskarsa yayi tare da juyawa yayi baya.

Itama kuwa juyawa tayi tabi bayanshi.

Riyyam-nsra kuwa, ɓat RAYYERN da Usman PA suka ɓacewa ganinsa.

Gaba ɗaya ya gama zagaye wurin babu su ba dalilin su.

Wani irin masifeffen kuka yakeji tun daga can ƙasan maƙoshi sa yana taso mishi.

Saboda lokaci daya yaga samu ya kuma ga rashi.

Kana layinshi bazaiyi aiki a nanba bare ya kira Mammy ya sanar mata halin da yake ciki.

Hakan yasa yake jin wani irin ƙuncin rai.

Gefe ya koma ya zauna bisa kujera, tare da maida kanshi ya jingine yana mai jin wasu irin zafafan hawaye na tsastsafo mishi.

Da sauri Salman ya nunawa Jannart Riyyam-nsra tare da cewa.

“Ikon Allah Jannart ga mutuminki”.

Juyowa sukayi suna kallonshi.

Shidinma kuwa Idanunshi da sukayi ja ya buɗe yana kallonsu.

A hankali Jannart tace.

“Kai ba shi bane, sai dai ko ƙaninshi”.

Da sauri Riyyam-nsra ya miƙe tsaye tare da rataya jakarshi bisa kafaɗa.

“Assalamu alaikum”.

Yace yana miƙawa Salman hannu.

“Wa alaikassalam”.

Yace tare da bashi hannu.

Sukayi musabiha, cikin sanyi Jannart tace.

“Ayyah dan Allah ka cewa yayanka yayi haƙuri, ban sani bane”.

Cikin fahimtar cewa. Rayyern suka gani suke cewa yayanshi, ya ɗanyi murmushi cikin hikima yace.

“Ta ina kuka haɗu ina yake.

 Ni ya ɓace min ne nasan kuma shima ni yake nema yanzu”.

Da sauri Salman yace.

“Ikon Allah ta nan yayi, to amman ba zuwa za’ayi a ɗaukeku ba”.

Da sauri ya nufi inda Salman ya nuna mishi yana mai cewa.

“Dan Allah kuzo ku nuna min inda yayin”.

Cikin nitsuwarta tace.

“Wani aiki mukazo yi nan Airport ɗin kai dai kawai kayi nan ɗin zaka ganshi.”

Salman ne ya ɗan harareta irin hararar da har yau bata gano manufarsaba,

Bayan Riyyam-nsra yabi tare da cewa.

“Na nawa kuma aikin yau dai ai mun rasa damar sai dai mubi mataki na gaba, kuma dan Allah fa yace so muje mu nuna mishi.”

Dole tabi bayansu.

Gaba ɗaya harabar wurin Airport parking din babushi babu alamarsa.

Kana sun dudduba gefe-gefen duk bashi, cike da gajiya da son komawa gida Jannart tace.

“Kai to ka tare taxi mana ya kaika gida”.

Dafa motarsu yayi tare da kwaɓe fuskarsa kana yace.

“Ai baƙone ni, mu baƙine daga Ethiopia, wani aikine Hamma na yazo yi, shine mukazo tare”.

“Toh ka kirashi a waya mana”.

Cewar Salman.

Dafe kai yayi tare da cewa.

“Toh ai dole sai na sai layin nan ƙasar taku nasa.

Shiru sukayi baki ɗayansu,

Can dai Jannart tace.

“Toh yanzu ya zakayi”.

Cikin danne tarin damuwarsa yace.

“Ku taimaka ku kaini na sayi layi.

Sannan sai in nemi masauƙi”.

Haka kuwa akayi Salman ya amince bayan sun kaishi, ya sayi sim card layin Mtn, yayi register.

Tuni lokacin biyar ta gota,

A hankali suka fito bakin shagon.

Cikin kula da alamun kallon akwai inda Salman ya sanshi yace.

“Toh ƙanina yanzu ina zakaje ne?”.

Jingina kansa yayi da jikin motar kasan cewar, CRV ce tanada tudu.

Idonsa ya lumshe tare da fara wassafo dajar shigar dake jikin Rayyern.

Kama daga Suit ɗinsa agogon hannunsa takalmansa zoben yatsarsa, uwa uba wayarsa.

Da kuma irin takardun da yaga yana ciccikewa da matsayin inda suka zauna.

Cikin sauƙe numfashi ya ɗago kansa tare da gamsuwa da tunaninsa yace.

“Ku taimaka ku kaini hotel mai kyau, wanda yake anguwar manyan mutane.

 In na isa na samu layi na ya hau zanyi mishi text ta Email ɗinsa”.

Da sauri Jannart tace.

“Toh ni dai Salman ka medani kafin ka kaishi.”

Murmushi Salman yayi tare da cewa.

“Toh ai sai mun wuce ta inda yake so ɗin ba yace unguwar manya ba, mu kaishi hotels ɗin Nasarawa GRA kawai”.

Juyowa tayi ta kalleshi kana tace.

“Uhum kafa san abubuwan wuraren tsada garesu ko, sannan kai kana ma da kuɗin ƙasar nanne?.”

Murmushi Riyyam-nsra yayi tare da cewa.

“Yess ina dasu, nayi canji tun a ƙasata, kuma in ma bazasu isaba ai zasu amshi transfer ko?.”

Kai ta gyaɗa mishi tana kallon tarin kamanninsa da wanda tayi karo dashi.

Bayan sun shiga motar ne.

Baba Ado yaja.

Salman na gaba kusa da Baba Ado shi kuma yana gefenta.

Cikin hausarsa da bata isasshen inganci yace.

“Hotel mai kyaufa”.

Gyara zama Salman yayi tare da cewa.

“Kada ka damu. *Nasarawa GRA* itace unguwar da ta tara kaf manyan masu kudi na Kano,babu wani babban mai kudi ko ɗan siyasa na Kano da ya isa yake ji da kansa dama  sauran jahohi da basu da gida a. Nasarawa GRA hatta Government House ma anan yake. 

 Sannan a cikin GRA din akwai manyan layuka da sunayensu 

*Lamiɗo Creasend* da kuma *Ahmadu Bello way*  da kuma sauran ƙana nan layuka.

Kana akwai manyan Hotel’s din da suke Nassara GRA akwai *Tahir Guest Palace*

 da kuma *Ni’ima Hotel* da *Green Park*  da *Liyafa Hotel* duk wadannan suna cikin Nasarawa GRA ne, kuma manya ne sosai ana ji da su suna da tsada da kuma kyau da inganci, zaka samu duk abinda kakeso a ciki.

Yanzu sai ka zaɓi wanne zan kaika, kaga dare ya fara yi mana.”

Numfashin ya ɗan sauke cikin jin daɗi da gamsuwa da bayanin unguwar da suka shigo ɗin, daga shiga unguwar kasan ta manya ce.

“Muje Taheer Guest palace hotel”.

Riyyam-nsra ya faɗi yana kallon gefen titin garin.

“To Alhamdulillah gashi ma mun kusa.

”Salman yace yana mai karya kwanan shiga layin da hotel ɗin yake.

Suna shiga bayan yayi parking, Suka sallameshi suka tafi.

Salman na cewa.

“To sai zuwa gobe zan kiraka in sha Allah inji ko ka gane ya’yan naka. Tunda na amshi number taka ta ƙasarmu”.

Toh yace tare dayi musu godiya.

Suna fita Suka nufi ma’aikatar su ta Arewa 24. Tafiya ce mai ɗan tazara tsakani.

Hakane yasa Baba Ado yake gudu.

Mintuna kaɗan suka isa.

Suna isa suka samu su Sunday a tsaye ƙiƙam to babu salla bare salati sai tsaron Jannart in wata tayi a biyasu makudan kud’in, da su kansu har yau basu gano manufar tsaron da ake bata, fiye da shi kanshi Alhaji Idi Sale Dakata’n ba,  ko kanshi bai bawa wannan tsaron ba haka babban ɗan sa dasu Abdul, to ko dan ita macece shiyasa.

Cikin hikima Baba Ado yayi parking jikin motarsu.

Kana suka fita suka shiga cikin ma’aikatan jim kaɗan Jannart ta fito.

Suna ganin ta fito suka mara mata baya.

Tana shiga mota Baba Ado yaja.

Kana yaja suma sauran suka bishi a baya ganin. Yaja ɗin.

               *Dr Rayyern*

Wani Irin karkarwa ƙafarsa keyi, sosai yatsar ke fidda jini.

A haka ya tsaida ɗan taxi ya shiga, ba tare da yace komaiba, mai taxi ɗin yaja.

Bayan sun fita Airport ɗin sun miƙa hanyar cikin gari.

Kanshi ya jingina da jikin kujerar, wani irin masifeffen zafi yakeji zufa na tsastsafo mishi tako ina, sabida zogin da yatsarsa keyi, ga lips ɗinsa dake raɗaɗi kana ga zuciyarsa dake tafarfasa.

Sosai mai taxi ɗin ya dai-dai ta motar tasa bisa titi, a hankali yace.

“Sir ina muka nufa?”.

Shiru yayi tamkar bai jishi ba sabida zogin fashewan farcenshi da yatsarsa su suka buwayeshi.

Sai da ya kuma tambaya kana cikin taune lips ɗinsa yace.

“Nassarawa GRA”.

Toh yace kana yaci gaba da driving.

Tabbas da AC cikin motar amman bai gamsar dashi haka yasa yaketa haɗa zufa.

Suna shiga cikin tsakiyar anguwar Driver’n ya kuma juyowa ya ɗan kalleshi a hankali yace.

“Sir ta ina zamu ɓullo?”.

A takaice yace.

“Ahmadu Bello way”.

To ya Kuma cewa kana sukaci gaba da tafi kan kyakkyawan titin mai faɗi da wadatan tsabta.

Tafiya yakeyi a hankali.

Yanayi yana ɗan kallon tabka-tabkan gidajen dake shumfud’e na gani na faɗa tamkar abirnin India.

“Kayi hannun dama”. Dr Rayyern Mai-nasara ya faɗa mishi a hankali.

To yace tare da ratsa wa damanshi.

Wow yace lokacin da suka fito kan ɗan madaidacin titin, da wani irin tamfatsetsen gida mai tsananin kyau na al’farma yake forkon layin.

“Yayi tsaya a nan”. 

ya kuma tsinkayo muryar Dr.Rayyern.

Juyowa yayi ya kalleshi kana ya juyo ya kalli tamfatsetsen gidan, na al’farmar da in ya kintata nanne gidansu.

Cikin ransa yake tasbihi ga Allah.

Tare da juyowa ya kalli shi kana a mutunce yace.

“Mai gida in shigar da kai ciki mana, naga tun kan ka shiga yatsarka na zubda jini”.

Wani irin  taɓe fuskarsa yayi,a rayuwarsa babu abinda ya tsana sama da haka, mutun ya shiga harkar sa, sam shi a tsarinsa babu ruwansa da shiga sabgar da bata shafeshi ba, sai dai kuma yana matuƙar son tausayawa sabida shi mai tausayine.

Cikin dakekkiyar murya yace.

“No ba matsala.

Bani da canji ko zaka bani Account number ɗinka inyi maka transfer’n in ba matsala?”.

Da sauri mai taxi yace.

“Okay Sir”.

Kana ya fara karanto mishi ac no ɗin.

Wata ƙaramar waya ya zaro a al’jihun rigarsa ta ɗaya gefen.

Ya ɗan lallatsa jim kaɗan ya medata al’jihun.

Cikin tsananin jin daɗi mai taxi ya kalli text ɗin Alert daya shigo masa na dubu ashirin. 

Cikin jin daɗi yace.

“Ngd matuƙa Allah ya ƙara buɗi ya jiƙan iyaye”.

“Amin”. 

Yace kana ya sako ƙafarsa waje, a hankali ya takata.

“Shehyytt”. Ya ɗan fidda sautin sabida ƙafar tayi tsami, tuni yatsar ta kumbura.

Bayan ya fito ne kuma mai taxi ɗin yaja motar ya tafi.

Shi kuwa Rayyern  a hankali tare da d’an ɗingisa ƙafar tasa ya nufi bakin kekyawan gate ɗin.

Kan yatsarsa manuniya yasa ya ɗan ƙonƙosa jikin ƙofar.

Da sauri wani kekyawan buzu dake zaune bakin ƙofar ya miƙe tsaye, tare da zuwa ya ɗan tura wani abu, kana ya leƙa da ido ɗaya.

Da sauri ya meda abin ya rufe tare da sakin murmushi cikin tsananin jin daɗi ya ja ƙofar ya buɗe yana mai cewa.

“Masha Allah, Dr. ya dawo”.

Da sauri wani kekyawan matashi dake fitowa daga can cikin gidan cikin ya nufi baki gate ɗin cike da farin ciki.

 Yana cewa.

“Alhamdulillah, Abba! Abba!!! Mamy ga Hamma Rayyern ya iso”.

Ya ƙare mgnar yana mai rungume Dr Rayyern da ya shigo.

Yayinda wasu mutanen suka taso da sauri suka iso garesu.

“Dakta Barka da isowa lfy”.

Shine abinda suke haɗa baki wurin faɗa da alamun shaƙuwa da so.

Duk da alamun akwai driver’ a ciki da kuma mai bawa fulawa ruwa sai kuma mai wankinsu da guga,

Sai Baba Mauɗo wannan buzun da alamun mai gadinsu ne, shi.

Wani ɗan guntun murmushi yayi tare dasa hannunshi ya shafa kan wannan kekyawan matashi daya amshi takardun hannunshi yace.

“I miss you so much my Ramadan”.

Kana ya bawa Baba Mauɗo hannu cikin kulawa da girmamawa tare dasu Ari sukayi musabaha.

Anutse yayi gaba Ramadan na biye dashi a baya.

Yayinda Su kuma suka koma wurin aikinsu, suna me farin cikin dawowar Dakta wanda yayi kusan mako huɗu baya nan.

Suna ratsa farfajiyar gidan da a ƙalla zai ɗauki motoci 7 zuwa 9 kuma ko wacce bazata matsi ko gogi ƴar uwarta ba.

Gaba ɗaya gidan zagaye yake da dogayen bishiyoyin na mijin gwanda, sai sirran Ayaba dake ƙasansu a jere da ƴan guntayen dabino.

Kana daga can baya kuma wani ɗan ma dai-dai-cin Garden ne mai masifar kyau, wanda yake cike da itatuwa da tsirrai masu sanyi da ƙamshi.

Kana daga farfajiyar gidan akwai wani baranda mai kyau da faɗi, wanda yake da steps.

Ata ƙasanshi gefen bishiyoyin an jera fararen kujerun silver hakama a ciki.

Kana tura ƙofar zaka riski wani hamshaƙin falo mai ɗan karen girma, Dan fadi da girmawa kuwa AC ma biyu ne aciki.

Ta gefen hagun falon gab da bakin ƙofar shigowa kuwa, wani ɗan madaidacin Bathroom ne.

Sai kuma gefen hagu, wani corridor ne mai fadi.

Kana shiga wurin zaka ga steps ɗin hawa sama masu faɗi.

Can gefen Bathroom din kuma ta gaba, wani kekkyawan Dinning area ne mai dauke da table mai kujeru takwas, sai wani Fridge mai suffar show glass Wanda ke cike maƙil da kayan sha.

Sai gefenshi kaɗan washing hand baby ne.

Kana ta kanshi ƙofar kitchine ne mai girma, wanda yake ƙawace da Kitchen cabinets and drawers masu masifar kyau, komai na ciki blue color and white ne.

Daga cikin kitchen din kuma ƙofar store ne.

Daga cikin store kuma akwai ƙofar baya, inda wasu igiyoyin shanya ke jere da kuma inda suke ajiye kamarsu dankali,  doya, al’basa, da dai ire irensu.

Daga Kitchine din kuwa akwai wata ƙofar da zata ratsa ta cikin wani corridor, mai ɗauke da ɗan madaidacin falo mai 3 Bedroom,s and bathrooms. Sai ɗan Dinning area ƙarami.

Can gefen dama kuwa inda benen yake, kana hawa sama kan steps din, kana iya hango cikin falon ƙasa.

Tafiya kaɗan zakayi ka riski wani babban falo mai masifar kyau da tsaruwa.

Can gefe kuma wani kekkyawan Dinning table ne shirye cikin Dinning area mai sarƙafe da labule mai zirin-zirin igiyoyin dake sarƙafe da duwatsu masu daraja sheƙin Diamond.

Kana sai wani Fridge shima kamar show glass kana gefenshi kuma Show glass ɗinne mai shirye da cups, plates, spoons, mug’s da dai sauransu.

Sai Kitchen dake gefe da store kamar na falon ƙasa. 

Kana sai Bedroom guda biyu, wanda basa kusa da juna dan a tsakanin su Dinning area da kitchen da store suke.

Akwai wata baranda mai kyau ta bayan ɗaya Bedroom ɗin inda nanne ɗakin Dr.Rayyern ɗayan kuma na Ramadan.

Ƙasan benen kuma akwai wata ƙofar wanda kana shiga zaka samu wani side ne kuma irin na saman sak, koman su iri ɗaya.

Sai can gefen kitchin ɗin falon ƙasan kuma akwai wani kofa wanda room and parlour ne mai kyau da Bathroom a ciki.

Daga gefe kuma can akwai ɗaki ɗaya inda masu aiki zata iya zama, amman bbu mai aikin a gidan.

Can waje kuma akwai BQ, Boys Quaters.

Gefen BQ ɗin kuma wani part ne mai kyau matsakaici a rufe yake su kansu Dr Rayyern da Ramadan Basu san menene a cikin wannan Part ɗin ba.

 

Tsarin gidan dai masha ALLAH.

Bisa wannan babban baranda mai steps biyar zuwa shida suka hau. Kana suka buɗe kofar babban falon.

Ramadan na mai kiran Abba! Abba!! Yana buɗe kofar suka hango Abba da Mamy, suna sauƙowa daga steps ɗin Dinning area, Wanda ta nan zasu fito side ɗinsu.

Wani kyakkyawan mutum ne mai matsakaicin shekaru, mai jini a jiki da tarin cikar haiba da kamala.

Ganin Rayyern dinne kuma yasa shi sakin wani irin yalwataccen murmushi, tare da buɗe hannayenshi dake cikin gariyar jikinsa.

Da sauri Dr Rayyern ya ƙarasa gabansa.

Rungumeshi yayi tsam a jikinsa tare da sauƙe ajiyan zuciya.

Mamy kuwa gefe ta zauna bisa kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, cikin haiba da tarin son ɗan nata tace.

“Babana wato Abba kawai kayi missing ko”.

Da sauri ya saki Abba yana murmushi mai cike da farin cikin ganinsu yace.

“Na isa Mamy, bakiji me bahaushe yace ba.”

Da sauri tace.

“Me yace”.

Ta ƙare mgnar tana yiwa Abba kallon tsokana.

Matsowa yayi kusa da ita, hannunta ya kamo ya ɗaura tsakiyar kanshi tare da yin ƙasa da murya yace.

“Uwa mafi uba koda uban sarki ne”.

Dariya mai cike da so tayi mishi.

Abba kuwa gefenta ya zauna tare da tsareshi da ido.

Ƙeyarshi ya ɗan sosa cikin sanyi yace.

“Abba bani ne na faɗa bafa, Malam bahaushe ne ya faɗa”.

Ramadan ne yayi murmushi yana mai jin daɗin, yaga Hamman nashi yana gaban iyayensu, dan nanne kaɗai zakaga fara’arsa ka kuma ji yayi doguwar mgn Especially in da Abba ne.

A hankali ya zauna gaban Abban nasu, tare da miƙar da ƙafarsa dake masifar mishi zogi.

Ita kuwa Mamy Dinning area ta nufa.

Plate ta ɗauƙa cikin show glass din, kana ta buɗe Fridge.

Chocolates da sweet ta cika cikin plate ɗin.

Kana ɗayan kuma tasa  Apple da inibi.  sai kuma goran ruwa da cup a ɗaya ta shiryasu, bisa tray’n kana ta nufo falon.

Da sauri Ramadan ya matso kusa dashi, tare da zubawa ƙafarsa ido cikin mmki yace.

“Innalillahi Hamma Rayyern meya samu ƙafarka?”

A hankali ya miƙar da ƙafar tare da motsa ta.

Da sauri Mamy ta ƙasaro, Abba kuwa sunkuyowa yayi ya kama ƙafar cikin tashin hankali, ganin yadda yatsar ta haye ta kumbura ga jini har yanzu zuba yakeyi.

“Rayyern, meya sameka? Meya faru?”.

Yayi tambayar a rikice.

Kanshi ya ɗan sunkuyar ya kalli ƙafar tasa, kana a hankali yace.

“Wata mahaukaciya ce ta takani”.

Yayi mgnar cikin salonsa na rashin iya ƙarya.

“Wacece ita a ina kuka haɗu?”.

Abba ya kuma tambaya.

“Ban santaba, just kawai dai I know mental problem ce, kuma a Airport muka hadu.” 

Ya bashi amsa, adan takai ce yana mai cije labb’ansa, wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar kafar tanayi mishi zafi sosae. 

Ramadan kuwa da sauri ya miƙe, ɗakinsa ya haura da sassarfa, dan ƙaramin akwatin taimakon gaggawa na likitoci ya ɗauko.

Yana sauƙowa ya zauna daɓas a gaban Dr.Rayyern ɗin,  kamo ƙafar yayi tare da fara bashi taimakon gaggawa dan jinin ya tsaya.

Cikin mmki Ramadan yace.

“Sorry Hamma har nail dinka ya fashe, amma Mahaukaciya a airport how? then why akabarta ta shiga airport din?” 

“Uhmmm” yace dan azaban zafin da yakeji.

Da sauri suka ɗago kansu baki ɗayansu.

Shi Dr.Rayyern TV dake like jikin ginin ya zubawa idanu.

Tamkar zai mannasu jikin fuskar kekyawan Dattijon nan Malam Mai-nasara da aka hasko a tashar Sunnah TV.

Ahankali ya janye ƙafarsa daga riƙon da Ramadan yayi mishi.

Tare da  juyawa ya maida hankalinshi ga TV, yayinda shima Ramadan hakan yayi.

Abba da Mamy kuwa idanu suka zubawa Rayyern ɗin.

Wani irin kallo Abba yakeyi mishi mai cike da ma’anoni.

Cikin haɗe fuska yace.

“Kai Ramadan tashi ka kashe tv’n nan”.

Juyawa sukayi baki ɗayansu suna kallonshi.

Fuskarshi dake haɗe ne yasa Rayyern yin ƙasa da kanshi, cikin sassayan sauti murya can ƙasa yace.

“Please Abba kayi haƙuri wa’azinshi nada daɗi”.

Cikin tsawa yace.

“Ramadan kashe min TV nan”.

Da sauri Ramadan ya miƙe jiki na rawa ya kashe TV’n.

Shi kuwa Rayyern cikin wani irin rauni da biyayya, ga mahaifin nashi da bin umarnin shi da neman izininshi yace.

“Abba kayi haƙuri”.

Fuska a haɗe yace.

“Ramadan zokayi mishi aikin daya dace.

To yace kana yazo ya wonke mishi yatsar yayi mishi dreesing ɗin wurin da duk abinda ya kamata.

Yana gamawa magriba nayi.

Dole suka miƙe sukayi al’wala kana suka nufi masallaci.

Jannart kuwa. 

A hankali ta kutsa kanta cikin falon nasu.

Tazo tsakiyar falon kekan tayi kiciɓis da…!

TUBALI

PAGE 6

NA

AISHA ALIYI GARKUWA

Da Yah Junaid, wani irin masifeffen tsorone ya rufeta wanda yasa ta fara ja da baya.

“Dan ubanki sai yanzu kika dawo? Ina kikaje kika tsaya? Tukun nama ƙarfe nawa ne ƙa’idar tashi aikinki?”

Ƙara matsota yayi tare da buga mata tsawa.

“Shegiya ƴar iska badake nake mgn bane kina jina kinyi shiruba”.

Cikin rawan murya tace.

“Uh uhm dama gidan Baba Kabir nake”.

Ta ƙare mgnar tana komawa gefen Mom da yanzu ta iso.

Cikin haɗe fuska tace.

“Yarinyar nanfa ba isasshen lfy ne da itaba”.

Juya kai yayi ya watsa mata wani irin masifeffen kallo tare da cewa.

“Toh uwar shisshigi”.

A hatsale Mom tace.

“Toh  ubana, anyi Shisshigin aikin banza”.

Ta ƙare mgnar da kama hannun Jannart sukayi ciki.

Shi kuwa kwaffa yayi tare da bin bayan Abdul  da yazo ya wuce su, bai ce musu ko ƙalaba.

Riyyam-nsra ne kwance bisa tattausan gadon ɗakin hotel ɗin daya kama.

Tuni yasa sim card ɗin sa na Mtn har ya zauna ras a wayar.

Kana yasa katin daya saya tun wurin sayan layin.

Mgn yakeyi da Mammy.

Yana mata bayanin haɗuwarsa da mutumin nan da suke kama.

Harma da haɗuwarsu da su Salman, kana ya ƙara da cewa.

“Mammy al’ummar Nigeria suna da kirki, suna da mutunci da mutunta baƙo, naga karamcinsu tun a cikin jirgi.

Mammy ina son su ina son ƙasar.”

Cikin sauƙe numfashi tace.

“Yesssss! Riyyam akwai masu kirki, da amana da kawaici.

Amman kuma akwai maha’inta azzalumai macuta,  ka kula da kanka kayi taka tsantsan.”

Cikin gamsuwa yace.

“Toh Mammy in sha Allah zan kula”.

Daga nan ta bawa Zayton sukayi ta hira yana mai gaya mata yadda ƙasar take.

Zaune suke a falon gidan Dr Lukman.

Cikin tawagarsu ta gamayyar kamfanonin jihar da kuma likitoci.

Dr Lukman keyi musu bayanin cewa.

“Dr Rayyern Mai-nasara ya dawo a yammacin yau, kuma Alhamdulillah dama akwai taron da gwamnatin jiha zatayi damu likitoci a gobe da safe, shine babban dalilin dawowarsa.

Toh muna tashi a taron zanyi ƙoƙarin tahowa dashi campany’n Alhaji Idi Sale Dakata, muyi taron jan ra’ayin nashi a can”.

Cikin gamsuwa sukace eh hakan yayi.

Kana  sukaci gaba da tattaunawar.

Ab’angaren Dr Rayyern Mai-nasara kuwa, kusan atare suka shigo cikin gidan shida Abba da kuma Ramadan, wanda yanzunne dawowansu daga masallaci, domin koda suka yi sallah’n magriba basu fito daga cikin masallacin ba, har saida aka sallame salla’n Isha.

Kaitsaye cikin babban falon gidan suka nufa, Yayinda zuciyar kowannensu ke cike da sanyi da kuma salama, musamman ga yanda iska mai dadi ke kad’awa tana ratsa kowani hudan gashi na jikin d’an Adam mai rai. 

Haka suka shigo falon Abba na gaba, sai Rayyern dake take masa baya, wanda yayi na k’arshen shigowa kuwa shine Ramadan, wanda yake d’an shafa screen d’in wayar dake rike a hannunsa. 

Ganin shigowarsu ne kuma yasa Mamy dake, tsaye agaban had’add’en dining table d’insu wanda aka k’awatasa da wasu fitinannun royal chairs, ta saki sassanyar murmushin dake bayyana tsananin k’aunarta ga ahalin nata, murya asake tace.

“Masha Allah! Our dinner is ready.” 

Jin hakan da sukayi dinne kuma yasa kasu sakin murmushi, tare da wuce wa dining area din kai tsaye. 

Ramadan kuwa kulolin da Mamy ta miƙo kishi ya amsa dasu plate and spoos da  gorunan ruwa mai sanyi.

Kana ya juya ya fita, dan kaiwa su Baba Mauɗo nasu abincin cikin kamala da mutuntaka ya kai musu kana ya dawo.

Shikuwa Rayyern da tun fitowarsu daga masallaci, yake tasbihi acikin zuciyarsa, kaitsaye gaban had’add’en fridge’n mai kaman show glass d’in dake dining area din ya nufa, yana isa kuwa ya bud’e murfin fridge’n, tare da d’ansa kansa ya zaro babban ledan chocolate na diary milk , wanda ya d’au sanyi sosai.

Maida murfin fridge’n yayi ya rufe, tare da juyowa ya zauna akan d’aya daga cikin kujerun dining table d’in, wanda aka cika saman babban table d’in, da kayan cima kala kala, more especially fruits.  

Ahankali ya b’are ledan, tare da kai chocolate d’in bakinsa.

Fitinannun idanunsa masu d’auke da long eye lashes ya lumshe, adaidai lokacin da yaji d’and’ano da kuma zak’in chocolate din ya mamaye harshen sa, wanda hakan yasa shi sake tura chocolate din abakinsa, tare  da soma taunawa ahankali, yana maijin wani irin sanyi aransa, Tabbas aduk sanda yake cin abunda yakeso, yakanji wani irin gamsuwa na musamman, musamman madai duk wani abu mai zak’i, kwarai yanason zak’i sosai da sosai. 

Abba da Mamy dake zaune kuwa idanunsu kawai suka zuba masa, musamman ma Abba da bayajin dad’in, yawan shan zak’in da Rayyern d’in keyi, always shan zak’i sai kace karamin yaro. 

Shikuwa Rayyern da har yanzu idanunsa ke lumshe, hakanan yaji ajikinsa cewa akwai k’wayoyin idanun dake kansa, wanda hakan yasa ahankali yad’an ware oily eyes d’insa, masu matuk’ar kyau da daukar hankali.

Karab sukayi ido hudu da Abba, hakanne kuwa yasa shi d’an gyara zamansa, tare kuma da yin k’asa da kansa, saboda acikin 2 second din ya fahimci wani irin kallo Abban, nasa keyi masa.

Zare chocolate din dake bakinnasa yayi, tare da ajiyewa agefe. 

Ganin hakanne kuma yasa Mamy da Ramadan yin murmushi, shikuwa Abba plate d’in dake dauke da crispy microwave Patatoe chips, and salad, da kuma onion sauce ya turowa Rayyern d’in gabansa. 

Tare da cewa.

“Maza kacinye wannan.”

Plate din da Abban nasa ya turo masa ya kalla, tare da d’an zaro idanunsa, kana lokaci guda kuma ya sanja mood dinsa izuwa shagwab’a,  akasalance cikin kuma muryarsa da bakowa kejinta ba yace.

“Abba duka wannan zan ci?.”

“Eh duka kuma yanzu nakeson kaci.”  Abba ya fad’a cikin tsare gida. 

Ahankali ya saukar da idanunsa k’asa, saboda yanda yaji tone din Abban nasu, yasan abun is seriously.

D’aukan plate d’in abincin yayi tare da fork ahankali, yakai abincin bakinsa bayan yayi bismillah. 

Bai kuwa wani ci abincin sosai ba, ya d’ago kansa ya kalli Mamy dake cin abincinta itama.

Cikin muryarsa dake bayyana rashin sabonsa dayin magana mai yawa yace.

“Please Mamy na k’oshi da abincin nan ki bani tea.” 

D’agowa Abba yayi ya kalleshi, still kuma cikin tsare gida yace.

“A’a fa yau sai kacinye abincin nan tas, saboda haka babu wani tea din da za’a baka.”

Maraitattun idanunsa yad’an lumshe, cikin kuma yanayin dake bayyana tsananin biyayyarsa ga mahaifinnasa yace.

“To Abba amma dan Allah abani tea sai in had’a, na tabbata abincin zaifi shiga…”

Yanayin yanda ya k’are maganar yana karyar da wuyansa gefe ne, yasa Abban sakin murmushi, cike da k’aunar d’an nasa yace.

“Shikenan to na yarda ka had’a da tea d’in.” 

Jin haka yasa Mamy tashi ta soma kokarin had’a masa tea, kamar yanda ya buk’ata. 

Shikuwa Murmushin jin dad’i yayi, saboda dama shi yafison ko yaya idan zaici abinci, ya zamana yana mixing abincin da abu mai zak’i, gashi kuma dama shi.

 Sam baya da yawan cin abinci, sometimes idan yaci chocolate d’insa ya d’aura da bootle water, yakanji sa dai-dai. 

Had’a masa tea d’in acikin mug Mamy tayi ta mik’o masa, koda ya karb’a bai wuce 3 sipping yayi ba, ya d’ago kansa ahankali ya kalleta.

Cikin yanayi da salon maganarsa yace.

“Ayyah Mamyna sugar baiji ba dai, please ki karamin.” 

Idanu Mamy tad’an zaro cikin yanayin mamaki tace. 

“Rayyern Shugar 3spoon amma kace baiyi maka ba, kai dai kam shan zak’i ya zama maka jiki.” 

Ta kare maganar tana mai k’ara masa Shugar one spoon acikin tea d’in.

Murmushi kawai yayi, batare  daya kuma cewa komai ba, ya maida kansa ya cigaba da sipping tea din, sai time to time yake daukan patatoe daya yakai bakinsa, nan ma kuma gudun kada Abba yayi masa fad’a ne.

Saida yasha kusan rabin tea d’in, kafin ya d’ago da kansa ahankali ya kalli Ramadan dake cin abinci.

“Ramadan ya hospital d’in, ina fatan komai yana tafiya dai-dai ko?.”

Ramadan kuwa Jin abunda Hamman nashi ya tambaya ne, yasa shi dakatawa da cin abincin, tare da cewa.

“Alhamdulillah Hamma Rayyern komai yana tafiya yanda ya kamata, bayan wannan tafiyar taka ma Ya Sulaiman yana zuwa, tare mukeyin duk wasu abubuwan da suka dace.” 

Idanunsa ya d’an lumshe ahankali tare da jinjina kansa, Tabbas dama yasan koda bayanan, Sulaiman da Ramadan zasu gudanar da komai yanda ya kamata kana ga sauran Doctor’s ɗin, kasancewar dukansu Doctors ne way’anda suka san aikinsu, kuma kowannensu da irin k’warewarsa. 

Hiran hospital d’in da kuma irin manya manyan ayyukan da sukayi, alokacin da  bayanan Ramadan d’in ya shiga yi masa.

 Yayinda shi kuwa ahankali yake d’an jinjina kansa, alaman gamsuwa, saboda zuwa yanzu bakinsa ya dan fara gajiya da motsawa. 

Abba da tun d’azun ya kafesu da idanu baya ko k’yaftawa, murmushi ne kawai ke bayyane akan fuskarsa.

 Yayinda yake yiwa yaran nasa, wani irin kallo mai d’auke da tsananin k’auna had’i da soyayya, Tabbas yanaji aransa cewa yaransa GARKUWA ne, sannan koda bayan ransa da izinin Ubangiji,

Zasu ƙarasa ginin TUBALI’n da aka fara ginasa zasu karasa ida ginasa da yardar Allah, akullum a kuma koda yaushe yana alfahari dasu, Tabbas ako ina zaiyi al’faharin cewa.

 Yay’an nasa jajirtattune kuma masu k’wazo, Lallai watarana Tabbas zasu cimmawa abunda suke so yana jin gamsuwa mai tarin yawa na riƙo da amarsu da Allah ya bashi da basu gamsasshiyar tarbiya.

Jin da yayi hirar tasu ta tsaya ne kuma, yasashi Kallon Rayyern tare da cewa.

“Rayyan ya tafiyar taka? Ina fata ansamu abunda akeso ko!?.”

Kai Rayyern d’in ya jinjina tare da bud’e bakinsa anutse yace.

“Alhamdulillah Abba, duk wani abu da muke nema na samu, dama kayan amfanin companies dinmu ne naje sayawo, to kuma ba abunda ban samu ba, nayi ordering Insha Allah kuma soon zasu sauk’a nan Nigeria.” 

Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwa, kana yace. 

“To kaida kaje US kuma sai gaka a ethiopia’n harda karb’an wani kambun karramawa.” 

Murmushin daya bayyana fararen haƙoransa  yayi, cikin kuma sakewa da mahaifinnasa yace.

“To Abba ai acikin Airport na hadu da yarannasu harna  taimaka musu, shine fahimtar likitane Ni yasa dole aka wuce dani k’asarsu,

Jin dadin ceton ahlin masu muƙamin ƙasar ne yasa sukamin wannan karramawar.” 

“Masha Allah Allah Ubangiji yaci gaba da taimakawa.” 

Abba da Mamy suka had’a baki wajen fad’ar hakan.

Ramadan kuwa daya kammala cin abincinsa, mik’ewa tsaye yayi tare da d’aukan wayarsa dake kan table d’in, cikin kuma yanayin nuna kulawa ga Hamman nasa yace.

“Yauwa Hamma Rayyern bari na amso maka maganin rage zogin ciwo acikin pharmacy d’inmu.” 

Kai kawai Rayyern din ya jinjina, Yayinda shi kuma Ramadan yasa kai ya fice daga cikin falon.

Koda ya fito daga cikin gidan nasu direct Mai-Nasara’s Pharmacy Nig LTD ya nufa,  kasancewar kuma pharmacy din bashi da wani nisa da gidansu, hakan yasa bai wani b’ata lokaci ba ya dawo. 

Shida kansa ya d’auko bottle water marar sanyi, tare da b’are maganin ya bawa Hamman nasa yasha. 

Bayan Rayyern din yasha maganin ne kuma, ya mik’e tsaye ahankali tare da kallon su Abban nasa, aladabce yace . 

“Abba ni zanje na kwanta, dan inajin gajiya sosai ajikina.”

Kai Abba ya jinjina masa tare da cewa.

“To Allah ya tashemu lafiya.”

Da “Ameen.” Ya amsa kafun yayiwa Mamy da Ramadan saida safe, kana kaitsaye ya nufi sashinsa, da k’ofar shiga cikinta ke Cikin babban falon a nitse yake tattaki bisa steps ɗin haurawa saman.

Ahankali ya murd’a handle d’in had’add’Iyar k’ofar, tare da tura kansa ciki.

Wani irin sassanyan k’amshin room freshener daya shak’ane kuma yasashi lumshe idanunsa, wanda suke d’auke da wani yanayi na musamman.

Tabbas shi mutum ne maitsanin son k’amshi, wannan yasa aduk sanda yaji k’amshi sai zuciyarsa tayi sanyi. 

Ahankali ya bud’e idanun nasa, tare da soma bin kekyawan falon da kyawunsa ya zarce tunanin mutum da kallo.

Duk da kuwa cewar babu yawan tarkace acikin falon, amma yanayin tsarin falon da kuma kayan dake cikinsa, na millions din kud’i ne ya ƙawatashi. 

Domin kuwa acikin falon wasu irin had’add’un Roma complete sofa’s ne masu masifar kyau da tsada, wanda sukayiwa tsakiyar falon k’awanya, Yayinda aka cika samansu da wasu irin trow pillows new design, babban abu mafi d’aukar hankali ajikin sofas din kuwa shine, yanda  aka k’awata su da wani irin abu mai kaman royal glasses, da kuma ado na musamman, kasantuwar design din Golding ash ne kuma, yasa har wani d’auke ido adon sofas d’in keyi. 

Yayinda  daga k’asan sofas din kuwa aka shumfud’e wani had’add’en Ash colour Austin  carpet, mai tsananin taushi da laushi, domin kuwa saboda tsabar laushin carpet d’in, har k’afan mutum kan iya nutsewa idan ya taka. 

Yayinda aka d’aura wani had’add’en glass Roma table akan tsakiyar carpet d’in, wanda kuma shine ya k’ara k’awata kyau da had’uwar falon, musamman wasu beautiful roses masu kalan gold da aka d’aura asamansa. 

Acan b’angaren dama kuwa, wani irin makeken tv plasma ne black na companyn Samsung mai matuk’ar kyau da tsada, saboda tsabar girman TV din kuwa, ba a iya mannashi a bango ba, kan wani had’add’en Royal tv stand aka ajiyesa, daga gefe da gefensa kuwa aka zuba wasu glass roses masu kyau da tsada, wanda da zaran dare ya rufa suda kansu, suke bada deference colours na light.

Still kuma had’add’un dark and golding ash colour, plain curtains d’in dake sak’ale jikin kowacce door da kuma windows d’in dake cikin falonne, suka k’ara bayyana had’uwar falon, domin kuwa curtains ne masu shegen tsada da aminci, wanda aka k’awata su da had’add’en decoration na d’aukar hankali, Tabbas ko daga iya curtains d’in dake cikin falon ka tsaya, kasan an kashe matuk’ar kud’i, balle kuma aje ga kwalliyar wallpaper din, da akayiwa gaba d’aya jikin bangon falon da ako ina zai amsa sunansa falo. 

Har lau kuma acikin falon nasa tafiya kad’an zakayi, ka iske wani had’add’en  dining area’n da aka k’awatasa da decoration na classic curtains masu kalan grey, sai zazzafan Angel dining table mai d’auke da 6chairs, grey da kuma gray colours, Tabbas ko a iya wajen falon Rayyern ya amsa suna, ya kuma cika hamshak’in falon dake dauke da tsadaddun furnitures. 

Daga gefen dining area din kuwa wata koface, wanda da’alama kuma nanne kitchine d’insa. 

Sai kuma wasu kofofi guda biyu dake cikin falon, 2 bedrooms wanda kitchen and dining area ke tsakiyarsu. 

Sassanyar ajiyar zuciya ya sauk’e a dai-dai lokacin da ya gama, k’arewa had’add’en falonnasa kallo, komai nead babu wani alama ma dake nuna cewar, yakai 4 to 5 weeks  baya cikin dakin, kasancewar duk kwanan duniya Ramadan na shigowa yana gyara duk abunda ya d’anyi kura. 

Rigar suit d’in dake jikinsa ya zare ahankali, tare da ajiyeta akan sofa, ahankali cikin takun dake bayyana gajiyarsa ya nufi d’aya, daga cikin 2 door d’innan da suke d’an nesa da juna.

Sauk’e hannunsa akan k’ofar dake b’angaren dama’nsa yayi, wacce takasance itace bedroom d’insa. 

Koda ya tura kansa acikin dakin kuwa, wani daddad’an kamshi da kuma sanyin AC ne ya bugeshi, still ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa, musamman da yaga yanda aka k’awata, original royal bed d’insa da soft bedsheet mai kyau.

Kamar dai yanda yaga falon nasa nead, haka ma komai dake cikin dakin, babu wani abu na kushewa acikin bedroom d’in, saboda nan ma wasu royal furnitures ne aciki masu masifar kyau, tamkar dai agidan sarauta haka d’akin nasa yake, saboda komai kama daga kan bed, drawer, dressing mirror, gothic chairs duk masu kalan gold ne, sai kuma curtains din cikin dakin da suka kasance milk colour.

D’an sunkuyawa yayi ahankali ya zare takalman dake k’afarsa, batare kuma daya jira komai ba, ya soma kokarin zare long sleeve din dake jikinsa, bayan ya cire rigar ne kuma, ya k’arasa gaban wani medium glass wardrobe, wanda acikinsu ne yake ajiye duk wasu abubuwan buk’atansa marassa nauyi, kama daga kan towel, bathrobe, short neakers, dadai sauransu.

Wani nead bathrobe ya d’auko tare da warwarewa ya zura ajikinsa, saida ya gama daure igiyoyin bathrobe din kuma, kafun ya zare wandon suit din dake jikinsa.

Kaitsaye bathroom d’insa ya wuce, Lallai ko acikin bathroom dinansa nasha kallo, domin kuwa hatta wajen da mutum zai tsaya yayi wanka na glass ne, daga cikin gurin kuma kana iya ganin komai na cikin toilet d’in, ga wani had’add’en jakuzzie mai daukar hankali wanda cikinsa, ke cike da tsabtataccen ruwa. 

A yanayin yanda yakejin kansa a matuk’ar gajiye ne kuma, yasa bai wani bata lokaci wajen yin wankan nasa ba, bayan ya kammala wankanne kuma ya dauro alwala, kasancewar haka ya sabarwa kansa, baya tab’a kwanciya babu alwala. 

Ahankali ya murda handle din bathroom din ya fito, hannunsa rik’e da wani towel, Yayinda gargasan jikinsa kuwa ke jik’e da ruwa, sunyi wani irin kwanciya lub, wanda kuma hakan shiya sake bayyana hasken fatarsa. 

Cikin yanayin nutsuwar daya zamar masa sabo, ya tsane duk jikinsa, tare da karasawa gaban dressing mirror ya shafa mai ajikinsa, bayan ya kammala shafa maid’inne kuma, yabi jikinsa da wani men body spray mai kamshin gaske.

Yana kammala duk wani abu da zaiyi kuwa, ya k’arasa gaban wardrobe dinsa, tare da ciro wani  sabon towel ya daura akan waist d’insa, yayi hakanne kuma saboda sometimes yafi jin dadin bacci, idan babu wani kaya mai nauyi ajikinsa, kamar dai towel yanajin dadin bacci da towel sosai. 

Numfashi ya fesar adai-dai lokacin da yayi amfani da wani remote, wajen yin off na hasken wutan dake cikin dakin.

Anutse ya haura saman tattausan gadonsa, tare dakai hannunsa ya kunna two bedside lamp din dake gefen gadon. 

Ai kuwa yana ajiye kansa akan pillow, yaji sautin kiran waya na tashi daga gefensa,  hannunsa yasa yadan dafe kansa akasalance, saboda Allah Yasani kwata kwata at this time bayason damuwa. Idan ya gaji bacci kawai yake so yayi, domin da hakanne kawai zaiji he’s okay.

Kallonsa ya mayar ga inda Ramadan ya ajiye masa wayoyin nasa uku, wato samsung da kuma iphone d’insa wacce, mental problem dinnan ta dazu ta kwankwatsa masa da tsinin takalmin ta, wanda dududu yasan kudin takalmin nata bai wuce 10 to 12k ba, amma gashi tazo tayi masa asaran dubu daruruwa sai kuma yar karamar woyar. 

Jawo wayoyinnasa yayi ahankali tare da ture iPhone d’in gefe, ya dauk’i Samsung S21 ultra din da take ta ringing, ganin sunan Sulaiman na yawo akan screen d’in wayarne kuma, yasa shi picking call d’in. 

Koda ya amsa sallamar da Sulaiman din keyi masa kuwa shiru yayi, sai shi Sulaeman d’inne, daga can

 b’angaren yace.

“Ya akayi nak’ikk’ira d’ayan layinka akashe, sai yanzu na samu wannan? Ykk fatan dai kana lapia, sarkin rainin hankali shine harda wani cemin ba yau zaka dawo ba, kai dai kam Rayyern naga randa zaka daina miskilanci.” 

Idanunsa ya d’an lumshe, tare da sauke ajiyar zuciya, kana agajarce yace.

“What’s up ai gani nadawo ko?.”

Kai Sulaiman ya girgiza domin kuwa idan da sabo ya saba da halin Rayyern Mai-nasara. 

“Nothing nakiraka na sanar dakai kada ka manta, gobe ne fa taron likitoti da za’ayi hope zaka je ai?.”

Sulaiman ya fad’a da kulawa.

“Insha Allah.” Still ya fada yana me gyara kwanciyarsa. 

“Okay to saida safe kurman dole, mitsss mutun baya gajiya ma da shirun.”  

Sulaiman ya fad’a yana me katse kiran. 

Rayyern kuwa ahankali ya zare wayar daga kan kunnensa, tare da fesar da wani irin numfashi.

“Ashyhhhhh”. wanda kuma yayi hakanne saboda zogi da yakejin yatsar k’afarsa nayi masa, duk da kuwa yasha magani,  amma dai har yanzu yakanji k’afar nad’anyi masa zogi.

Labb’an bakinsa ya cije da d’an k’arfi tare da rumtse idanunsa, lokaci daya ya soma tuna yanda yarinyar tayi masa babban b’arna, kuma wai dan saboda tsabar raini, ko hakuri ta kasa basa dan girman kai, sai wuki-wuki da ta soma yi masa da mayun idanunta. 

“Mchewww.” Yayi tsuka abayyane tare da cewa. 

“Da wani dan bakinta kaman na tsuntsu, dama irin wayannan ƴan yaran. Sam ba kai daya garesu ba.” 

Yakai karshen maganan yana sake gyara kwanciyarsa, tare da sakin kowanni irin tunani ya kama ambaton sunan Allah Acikin ransa, da haka bacci ya d’auke sa, yau ko samun daman duba system d’inshi baiyi ba. 

        Taheer Quest Palace.

Riyyam-Nsra ne kwance akan makeken bed din dake cikin d’akin hotel d’in daya kama.

12:30 am kenan amma har yanzu wayarsa kirar iphone 11pro ne ke rik’e ahannunsa, Yayinda yayi kwanciyar nan irinta rub da ciki, gaba d’aya hankali, tunani da kuma nutsuwarsa ya badasu ne ga wayar tasa, Inda yake ta receiving DM da kuma comments na mutane, akan videos d’in daya sake d’azu na shigowarsa Nigeria, inda mutane da yawa kanyi masa message akan cewar, suna matuk’ar son su had’u dashi, ciki kuwa harda y’an mata masu tambayarsa awanni masauk’i yake, domin acewarsu zasu kawo masa ziyara, burin mutane da yawa shine su had’u dashi suyi videos, wasu kuwa zallan kyawunsa ne yake rud’arsu, wanda hakan yasa suke bayyana maitarsu afili, ko kunyar kai da addininsu basaji, amatsayinsu na musulmai, kuma yaya mata, wanda kowa yasani Mace nada matuk’ar daraja, amma Ina wasu matan kam haka suke watsar da kansu kamar shara a bola. 

Shikuwa Riyyam nsra ayau ya sake tabbatarwa da kansa cewar, mutanen Nigeria nada matuk’ar mutumci da kuma iya karrama bak’o, sannan da yawansu suna nuna masa k’auna k’warai. 

 

Bayan ya gama amsa DM na mutane ne kuma yayi posting videos d’insa, wanda yayi musu shida Rayyern, Yayinda a k’asan videos d’in yayi godiya da irin karamcin da Rayyern d’in yayi masa,  wayyo Allah ai kuwa kaman jira mutane suke, suna gama watching na videon ya fara samun new comments and DM, wanda shi kansu bazai iya amsasu duka ba, Yayinda mafi yawancin mata kuma suka sake haukacewa, nanfa kowacce ta fito ta fara maganganu kala-kala, harda masu tambayarsa wai dan Allah ko zai had’asu da kyakkyawan yayanshi. 

Shidai ya gani amma baiyi reply ba.

Bakin shi ya dan zumbura gaba tare da cewa.

“Wayyo wannan Hamma Rayyern ɗin ya kashemin kasuwa fa, ji duk an shareni sai mgnarsa ake,”.

Ya kare mgnar da murmushi

Ana Cikin hakanne kuma saiga k’iran Nasir Ahmad ya shigo cikin wayar tasa.

Koda ya d’aga hira suka sha inda Nasir Ahmad ya dinga yi masa fadan cewa bai Kirasa ba, da kuma mai yasa zai sauka a hotel, saboda da ace yakirasa da bazai taba bari ya sauka a hotel ba.

Hakuri Riyyam din ya basa, daga nan kuma suka ci gaba da hirarsu, ananne Nasir din ke tambayan a Riyyam hotel din daya sauk’a,  bayan ya fad’a masa cewa a Taheer ya sauk’a ne kuma sukayi sallama, inda Nasir din ya shaida masa cewar, Gobe Insha Allah zaizo nan Taheer Guest Palace din, ya d’aukesa su tafi gidansu…!

Uhummmmm, akwaifa abu a wanga littafin, fatana dai Allah ya bamu aron rai da lfy, mu gama lfy, amman kam ku shirya karatu da murmushi a fuskokinku🤝🏻🥰

                                 By

                    *GARKUWAR FULANI*

Back to top button