Uncategorized

Macijine Shi Page 7-8 Hausa Novel

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 7/8

https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share

________________Ihu jauro ya kurma mai ƙarfin gaske ya faɗi can gefe yana burbura tare da rikan “wayyo haroji jaurota zai cinyemin ka taimakeni  zan mutu wayyo maciji “ya ƙarasa   faɗa da kyar sakamakon wata danƙa mai ƙarfi da macijin nan yayiwa jauronsa har saida numfashinsa  ya ɗauke .

Haroji kuwa ya mugun tsorata ganin halin da jauro ke ciki,ga wannan ƙaton macijin daya kanannadeshi yana ƙoƙarin karya masa ƙasusuwa.

Cikin kiɗima ya rarumo wani ƙaton dutse yayi kan jauro da wannan macijin,yana zuwa baiyi wata wata ba ya ɗaga dutsen ya kwaɗawa macijin nan abayansa.

Aikuwa nan da nan bayan macijin ya fashe jini yayi tsartuwa har kan fuskar haroji,wani ihu haroji ya kwala ,sakamakon sauƙar jinin macijin nan akan fuskarsa ji yayi kamar an watsa masa ruwan batir,nan da nan gurin ya sale kamar wanda ya ƙone sai turiri gurin yake.

Jifa haroji yayi da dutsen hannunsa yana ihu yana faɗin”wayyo Allah idona bana gani wayyo kwayar idona ta zazzage na shiga ukuna “abinda yake daɗi kenan yana ihu da tsalle.

Shikuwa macijin nan silalewa yayi daga jikin jauro ya koma gefe guda tare da kwantar da kansa akasa ,dan kuwa sosai  haroji ya kwada masa dutsen nan,kuma da alama ya shige shi .

Gaba ɗayan abinda ke faruwa akan idanun fattu ,tana kwance tana kallon ikon Allah,tabbas zuwa yanzu ta gama yarda cewa macijin nan bashi da biyar cutar da ita ,saima taimakon ta da yake,shin wanene wanan macijin?meye alaƙarta da shi?me yake nema agurinta?anya ma MACIJINE wannan ?kodai aljanine yake zuwa mata asiffar macijin? Wadanna sune tarin tambayoyin da fattu ke yiwa kanta  tana daga kwancen wanda bata da amsarsu.

Saidai kuma gaba ɗaya hankalinta ya tashi ganin yadda macijin nan ya kwanta lamo kamar ya mutu.nan da nan tsoro ya mamaye zuciyarta ,cikin dauriya da jarumta ta yunƙura ta miƙe tsaye tana yamutse fuska,hannunta mai ciwon yana riƙe aɗaya mai lafiyar.

Gurin macijin ta nufa gabanta na ci gaba da faɗuwa,dan tsoro take kar ita kuma yayi mata wani abu.tana ƙara sawa ta durƙusa ahankali dai dai inda haroji ya buga masa wannan dutsen ,hannu ta sanya ahankali ,cikin karkarwa jiki ta  ɗan shafa gurin ciwon.ai tana ɗora hannunta agurin macijin nan yayi wata irin juyowa tare da fasa kai kamar zai sareta, cikin tsoro da fargaba ta cire hannunta tare da matsawa baya da sauri tana zare ido tana kallon macijin.

Shima yana juyowa yaga fattu ce ,sai ya tsaya yana kallon ta,tare da komawa yadda yake ,wato ya sassauta fusatar da yayi ,kawai ya tsaya yana kallon ta.

Itama kallonsa take cikin tsoro da bugawar zuciya,ahankali macijin ya fara tahowa ,har ya zo gareta ,runtse idanu tayi tana karanta addu’ar Allah ya tsareta.

Ga mamakinta kawai saitaji macijin ya hau kan cinyarta ya kanannaɗe jikinsa ya dora kansa a saman  gammon da yayi da jikinsa.

Ahankali ta buɗe idanunta tana kallonsa,shima ita yake kallo saidai idanunsa na zubar da hawaye kuma na jini .

Jikinta kawai rawa yake cike take da tsantsar tsoron abinda zai faru .juyawa tayi tana kallon haroji dake ta faman ihu yana yaɗuwa kasa.sannan ta kalli jauro wanda yake kwance ba alamun numfashi atare dashi,ga jauronsa nan tayi wani irin kumbura na ban mamaki sai jini ke zuba .

Tsorone ya ƙara kamata cikin azama ta yunƙura tare da mikewa tsaye,  ture macijin tayi daga jikinta ta kwasa da gudu tayi gida tana kuka .

Koda taje gidan, da sanɗa tayi saurin shiga ɗakinta tana kuka,zama tayi akan tabarmarta tare da kife kanta a tsakanin cinyoyinta tana kuka.damuwace fal cikin ranta,wai meke shirin faruwa ne da rayuwarta?wacece mahaifiyarta?waye wannan macijin da yake ɗaukan hukunci akan duk wanda yayi nufin cutar da ita?tanasan sanin wannan macijin waye shi,kokuma waye ya aikoshi gareta.tana cikin kukanta ne kawai taji abu yana hawa jikinta silililili!!! Afirgice ta ɗago kanta tana kallon macijin daya gama hawa jikin nata. kansa ya ɗora akan wuyanta yana  fidda wani irin huci ,shiru tayi tana sauraron yadda macijin ke huci,sanan jikinsa yayi wani irin zafi sosai.duk yadda akayi bashi da lafiya ,kuma dukan da haroji yayi masane solar hakan.

Tausayinsane taji yayi mugun kamata,ahankali cikin tsoro ta miƙa hannunta tare da riƙo saitin wuyansa ahankali ta janyoshi, ko motsi baiyi ba bare ya hanata abinda yake yi ɗin.

Akan tabarmar ta ɗorashi tare da ci gaba da kallonsa,cikin muryar kuka tace “bawan Allah kai waye?meke tafe dakai?waya aikoka zuwa gareni?meyasa kake ƙoƙarin daukar mataki akan duk wanda ya zalumceni?dan Allah karka cutar dani, bani da kowa sai baffana,dan Allah kayi tafiyarki ,idan mutanen garin na suka farga da kai zasu kasheka ,bazan so hakan ba dan Allah na roƙeka ka tafi”ta ƙarasa maganar tana haɗa hannunta cikin kuka.

Shidai macijin nan ko motsi baiyi ba sai huci da yake yi sosai,

Ahankali ta kalli gurin da yaji ciwo dazu sai taga gurin yana turiri kuma yayi wani fari fat.shiru tayi tana kallonshi ,yanzu ya zata yi masa ne?dan da alama fa yana jin jikine, data rasa abinyi kawai saita lulluba zanin sallarta ta fara karatun Alqur’ani mai girma.cikin abinda bai wuce sakwan biyar da fara karatunta ba  kawai macijin nan ya fara wata irin murmurɗewa yana sauya kala, da farko yayi jajur dashi,sai kuma yazo yayi baƙiƙirin sosai ,wani irin hayaƙi na fita daga jikinsa .

Duk abinda yake sam fattu bata kulaba ,dan ta ɗaga  kanta sama ne tana karatun ,kuma idanunta na zubda kwalla.

Shikuwa macijin nan burburwa ya ci gaba dayi yana murɗewa jikinsa na turiri tare da sauya kala.can kuma ya fara wani irin ƙara mai kama da gurnanin  zaki.cikin tsoro fattu ta dawo da kanta ƙasa tana kallon macijin , sakamakon wannan sautin ƙara da taji yanayi.sai lokacin hankalinta ya kai kanshi taga abinda ke faruwa.

Tsorone ya kamata ƙarara “innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”shikenan ta tabbata wannan ba maciji bane tabbas aljanine ,ko kuma aljanine  ya shiga jiki sa,na shiga uku ni fattu ya zanyi da rayuwata?meke shirin faruwa dani” ta faɗa cikin muryar tsoro da shiga ruɗu.

 Shikuwa macijin nan tana daina karatun saiya daina burburwar da wanann gurnanin,ahankali kuma jikinsa ya dawo yadda yake . Ya jima kwance lamo  kafin ya  fara motsi,kansa ya ɗago tare da fasa kan  yana kallon fattu,gaba ɗaya idanunsa sun koma baƙiƙirin dasu sannan wasu irin ƙananan layoyi suka bayyana kusan guda uku aƙasan kanshi, sai wani irin motsi suke kamar ya’yan tsutsa.

Karkarwa jikin fattu keyi kamar an saka mata shokin, lamarin ya matukar bata tsoro ,meye wannan ɗin haka suka bayyana jikin macijin nan? Me yasa daga fara karatun Alqur’ani gaba daya ya sauya kama?tabbas akwai wani boyayyen al’amari game da wannan halittar dake gabanta,kuma zata ci gaba da bibiyar macijin nan sannu kan hankali har saita gano menene tattare dashi.

Tana nan maƙale jikin katangar karanta kamar ƙadangaruwa dan tsabar tsoro da shiga shock ,idanunta ƙuri akan macijin ,wanda shima ita yake kallo ,kusan minti biyar suna haka ,taga macijin ya sulale ya bar ɗakin ta wannan hanyar tashi.

Rarraba idanu ta farayi tana dafe da ƙirjinta ,yau kam tana ganin ikon Allah kala kala ,anya kuwa bata janyowa kanta masifa ba?waima meye alaƙarta da wannan halittar ne?ko dai baffanta zata sanarwa halin da ake ciki ne?kai a’a ba yanzu ba tukunna ,ya kamata ta zama jaruma tayi wanann aikin koba komai zata taimaki rayuwar macijin,dan ta fahimci akwai boyayyen al’amari atareda shi.

Su haroji kuwa gaba ɗaya ya fice daga hayyacinsa sai ihu yake yana faɗuwa ƙasa ,ahaka ya nufi gidan lamiɗon garin ,wanda shine mahaifin jauro ,yana ihu yana tumami, har yaje gaban lamiɗo ya faɗi yana “wayyo idanuna ,wayyo fuskata lamiɗo ka taimaka min.

Ruɗewa lamiɗo yayi wanda yake tsaye jikin wata sanuwa yana bata ciyawa, lamiɗo bashi da imani ,azalumine sosai ,kuma mutanen garin suna matuƙar tsoronsa, dan haka yake mulki na zalumci agarina,ganin halinda haroji yake ciki”kai haroji menene hakan ?ina jauro?me yasameka?sune tambayoyin da lamiɗo ya jerowa haroji

Cikin azabar ciwo da fitar hankali haroji yace “jauro ya mutu maciji ya cinye masa jauronsa yana bakin rafi” 

Ai dajin wannan batu hankalin lamiɗo ya tashi ,nan da nan yayi kan haroji yana faɗin wane macijin ?me kake cewa ?jauro ya mutu?ƙaryane badai agarina ba ,ba wanda ya isa ya zo garina ya kashe min ɗana.”lamiɗo na gama faɗin haka ya kira mazan garin ,ya sanar dasu maza aje bakin rafi ataho da jauro.

Aikuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗauko shi kamar gawa .

Nan da nan lamiɗo ya nemi haroji ya sanar dasu abinda ya faru .

Nan ya sanar dasu iya abinda idanunsa suka gani,dan shima yana cikin mugun halin mutuwa ko rayuwa dan tuni gurin da jinin nan na macijin ya taɓa ajikinsa yayi wani irin kore shar yana zubar da wani yallow ɗin ruwa .

“Lamiɗo fattu ce ta Turo mana macijin nan ,shine ya kashe jauro”abinda haroji ya faɗa kenan ya sume.

Nan da nan mutanen gurin suka fara maganganu Suna faɗin da “da hansai ta faɗa tace mayyace yarinyar ,tunda har ta fara kashe mutane ba zasu yarda ba sai an hukunta itama.

Ran lamiɗo ya ɓaci sosai ,dan dama yana jin haushi yarinyar  da ubanta,ya shirya neman aurenta amma sam taƙi yarda wai karatu take,yanzu kuwa dama tasameshi da zai hukunta su ita da tsohon nata.dan haka cikin bada umarni yace lallai lallai aje ataho da fattu da ubanta .

Nan da nan fusatattun  maza suka nufi gidan malam bukar dan aiwatar da ƙudurin lamiɗo……..

Masu karatu meke shirin faruwa ne ?

Wane hukuncin lamiɗo zai zartar akansu fattu?

Mai zai far nan gaba?

Muje zuwa yaki ce dai anty mammy

Mrs babi💘💘💘

Share and comments fisabilillah.

More comments 

More typing.

Back to top button