Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 102 Complete Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Kasa ɗagowa yayi daga kan ƙabarinsa,
Marshal Omar ne ya É—aura da cewa”In sha Allah junaid na aljanna,muna yi mashi kyakkyawan fata,Allah yasa Æ™arshen wahalarshi kenan,”gaba daya basu ji daÉ—in irin yadda mutuwar junaid ta kasance ba,kamar wani mara gata,babu mahaifinshi akusa babu Æ´an uwanshi,
Ruƙo hannun Sgr major yayi,tare da janyoshi,jikinshi duk ya saki,daƙyar ya iya mikewa ya tsayar da kanshi akan ƙafafunshi,
Sojojin dake kewaye da wurin sunyi su 50,Layi sukayi wani na bin wani, kowa yazo wurin Æ™abarinsa sai ya tsaya ya tottafa mashi addu’a kafin ya wuce,Na bayan shi yazo shima yayi mashi addu’a a haka har suka kammala,ba tare da mutane sun samu damar tsayawa ganin abunda ke faruwa ba,dama kuma hanyar sam ba mutane sosae.
Basu bar ƙabarin junaid a fili ba,saboda gudun kada mutane su dinga tattake wurin batare da saninsu ba,ko su zauna abakin bishiyar,waya suka sa suka kewaye bishiyar,

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Sun jima a awurin cike da jimamin mutuwar junaid,kafin wani lokaci suka shige motocinsu suka tafi ba don sunso ba,Kuma duk da haka sai da Sgr ya sanya sojoji guda biyu suka tsaya a wurin,batare da uniform ajikinsu ba,

*RIJF BABY JUNAID*

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 5:30 na marece,
Slowly motocinsu suka shiga cikin gidan,Bayan sunyi parking ɗinsu Major ya buɗe masu mota,don atare suka zauna shi da Sgr a motar Omar,kowa jiki babu ƙwari haka suka fito daga cikin Motar,kaitsaye suka nufi ƙopar shiga falon,

A lokacin hosana na zaune saman Sofa,duk ta takure kanta,tun da tafarka daga bacci take ta faman yin sintiri acikin gidan tana jiran dawowar Omar don ta faÉ—a mashi abunda haroon yayi mata,

Jin motsin shigowarsu yasa tayi saurin miƙewa jiki na rawa ta tunkareshi zata rungumeshi,
Da hannu yayi mata alamar karta matso kusa dashi,fuskarshi babu annuri,har cikin ranta bata ji daÉ—in abunda yayi mata ba,har gaishe dasu tayi amma babu wanda ya kulata,acikinsu,
Upstairs suka wuce atare,kowa ya nufi part ɗinsa,komawa hosana tayi saman sofa ɗin tana kuka,abun ya ƙona mata rai,Yadda Omar ya dakatar da ita don karta ta6a shi,
Faɗawa yayi saman gadonshi yayin da idanuwanshi ke fuskantar Ceiling,Fuskar Junaid ya dinga ganin tana yi mashi gizau,ji yake tamkar abunda ya faru mafarkine ba gaskiya ba,saboda wani sashe na zuciyarshi na raya mashi cewa Junaid yana raye bai mutu ba,Yayin da wani sashen na zuciyar tashi ke gasgata mashi mutuwar junaid,runtse idanuwanshi yayi Allah kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi daurewa kawai yake yi,ya jima a haka idonshi na kallon sama,kafin daga bisani ya miƙe tare da faɗawa toilet bayan ya rage kayan jikinshi,

Kwance yayi tsulundum acikin jacuzzi (kwamin wanka)wanda ke kewaye da glass,da niyyar yin wanka ya shiga toilet ɗin,Amma sai kasala ta baibayeshi ko yatsan shi ya gaza ɗagawa,abubuwa sunyi mashi yawa,tunda yake a rayuwarshi bai ta6a fuskantar mummunar rana irin wannan ba,da ace mutuwa hutu ce agareshi da ba abunda zai hana ya roƙi Allah akan ya ɗauki ranshi ya huta,Yaci alwashin saiya ga bayan waɗanda suka kashe junaid,Alƙawari ne ya ɗaukarwa kanshi,Ko bacci bazai ƙara yi ba,in har bai ɗaukarwa junaid FANSA ba,kamar yadda Sgr yaci Alwashin ɗaukar fansa haka shima Omar ya ɗauka,

Also Download FARRAH Hausa Novel Complete Document By Maman Shuraim

Kasa jurewa yayi saboda kukan da hosana ke raira mashi ta la6e a ƙopar dakinshi batasan halin da yake ciki ba,
“Hosana,”ya ambaci sunanta,muryarshi a kasalance,
Cikin shessheÆ™ar kuka tace”Na’am,”
“Zonan,”
Hannu tasa ta tura ƙopar tare da shigewa ciki,Kwance ta same shi saman gadonshi,Ya baje daga shi sai short,kallo guda zakayiwa fuskarshi ka gane cewa yana acikin matsanancin tashin hankali,
har Saman gadon hosana ta hau ta zauna tana kallonshi,lokaci guda ta dakata da yin kukan nata,Ganin dry tears asaman fuskarshi,nan fa hankalinta ya tashi sosai,
“Ya omar,hawaye akan fuskarka?meke damunka ya Omar,Ban ta6a ganin hawayenka ba,Sae yau,”
A hankali ya bude idanuwanshi da sukayi jawur dasu yana kallonta yace”Hosana,ki taimaka mun kaina kamar zai fashe,Ina cikin matsananciyar damuwa,Zuciyata raÉ—aÉ—i take yi mun,pray for me hosana kona samu sauÆ™i acikin zuciyata,
Jikinta ba Æ™aramin sanyi yayi ba,hannayenta ta sanya tana kokarin janyo shi hakan yasa ya dan matso daura kanshi tayi saman laps É—inta,Addu’o’i ta shiga karantowa tana tottafa mashi asaman fuskarshi,shafa sumar kanshi ta shiga yi,tana cewa”Ya Allah ga bawanka nan,kai kaÉ—ai kasan meke damunshi,Ya Allah ka yaye mashi damuwarshi,Ka sanyaya mashi zuciyarshi,Alfarmar Annabi Muhammadu (S.A.W),
Ba ƙaramin daɗin maganarta yaji ba,sosai ya gyara kwanciyarshi sama sama bacci ya fara ƙoƙarin daukarshi,
Yana jiyo muryarta tana tambayarshi Ko zaici abinci ta kawo mashi,
DaÆ™yar ya iya amsa mata da cewa”A’a hosana,bana iya cin komai yanzu,”
“Shikenan ya Omar É—ina,kayi baccinka kawai,zanci gaba da yi maka addu’a,har ka farka,”
Shafa sumar kanshi taci gaba da yi,tamkar jinjiri haka ta dinga treating É—insa har bacci yayi awon gaba dashi,Yau hosana tayi mashi abunda bai ta6a tsammani ba,Ta bashi kyakkyawar kulawa kamar ba wannan mai ta6in hankalin ba,wani iko na Allah ta so sanar dashi damuwarta,amma tunda ta gane cewa baya a hayyacinshi,Sae kawai ta fasa sanar dashi.

*Tashin Hankali!”

Jin dirar motoci acikin gidan yasa shi yin firgit ya farka,tare da yunƙurawa ya miƙe zaune,Hosana ya gani kwance tana bacci,asaman gadon ya ɗauketa,
Jiki na rawa ya saukko daga saman gadon ya samu jallabiya ya zura ma jikinshi ya bude ƙopar dakinshi da sauri ya nufi downstairs,Tunkan ya ƙarasa ya jiyo Muryar Abbansu yana ƙwalama Junaid kira,ko sallama baiyi ba,Burinshi kawai yayi tozali da junaid,
“Hasbunallahu wani’e mal wakil”ya furta hakan tamkar zai fashe da kuka,
Yana cikin wannan yanayin sai ga Sgr shima ya fito daga part É—insa,jikinshi sanye da jallabiya shima,kallon juna suka yi kowa fuskarshi ayamutse take,
“Daga shigowarshi ko sallama baiyi ba sunan junaid kawai ya ambata,yanzu yaya zamuyi dashi’?omar ne yayi maganar tare da kallon Sgr dake tsaye a gefenshi,
“Yanzu ya dawo yana buÆ™atar ya huta,yakamata muyi Æ™oÆ™ari wurin ganin mun daidaita natsuwarmu,if not za’a samu matsala ne,”

Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document

Shigowa cikin falon suka karasa yi,Abbansu ne sai Mommynsu,tare dasu twins,fawan gaba É—aya matasan gidan sun dawo,hada kanal yousouf su irfan da sauransu,Banda gwaggon katsina suma sun shirya dawowa tare dasu Ammi,zasu zo daga baya,

Agajiye suke kowa ya samu wuri saman Sofa ya zauna,Abba kuwa jiki na rawa ya wuce upstairs,su Sgr najin takun takalminshi hankalinsu ya ƙara tashi,Yana tafiya yana ƙwalawa junaid kira,
“Junaid!Junaid!where are you?Ur dad is back,Nayi missing É—inka sosai….”

Bai Æ™arasa maganar ba,ganinsu Omar atsaye,cirko cirko,Æ™aÆ™aro murmushi suka yi gaba dayansu suka tunkareshi,Sgr ne ya fara yin hugging É—inshi,Daddy I really missed you,Ya gajiyar tafiya?ya Æ™arasa maganar tare da É—agowa daga jikinshi,Bai amsa mashi gaisuwar tashi ba,yace”Yaushe ka dawo Abuja?ko kun dawo ne’?
“A’a daddy,Wani uziri ne ya kawo ni,Amma zan koma kano É—inne,”wani kallo da yaga Abbansu na binshi dashi yasa ya É—an sha jinin jikinshi,
“Abba sannu da dawowa,”Omar ne yayi maganar,wurga idanuwanshi yayi akan fuskar Omar,aÉ—an ruÉ—e yace”kunyi rashin lafiya ne?meke faruwa ne?naga fuskokinku duk sun kumbura,fuskar Rafayet tayi jawur da ita,kaima haka….”
Da sauri Omar yace”Am…Abba..I know u are tired,kana buÆ™atar hutu,yakamata muje bedroom É—in ka Inyi maka tausa,”
Harara Abban ya É—an watsa mashi tare da cewa”a Æ™ule nake dakai Omar,ina ta nemanka jiya,ka tashi ka kashe mun waya hmmmm…”yana kai Æ™arshen maganar ya soma Æ™oÆ™arin wuce wa ciki,Saboda tsabar ruÉ—u Sgr baisan sa’adda ya tarboshi da hannunshi,Zuba ma hannun nashi ido Abbansu yayi,fuskarshi É—auke da mamaki yace”Rafayet,lafiyarka kuwa?cikina fa ka tarbe,”
Zame hannunshi yayi tare da É—an sosa Æ™eyarshi yace”Am sorry Daddy,pls u need a rest,mu sauka down ka huta mana,ka kwaso gajiya,inaso na baka abinci kaci ka huta,Omar zaiyi maka massage ka É—an ji daÉ—in jikinka,
Cike da mamaki Abbansu ke kallonshi,”Rafayet!yau kaine da kanka kake zancen zaka bani abinci a baki na naci?Omar kuma zai yi mun tausa,sae kace wani Æ™aramin yaro,”gyaÉ—a kanshi yayi tare da cewa”Naji toh,Amma saina fara zuwa É—akin Junaid,idan nadawo sai mu je É—akin nawa,”yana kai Æ™arshen maganar ya wuce tare da nufar É—akin Junaid yana Æ™wala masa kira,
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,A hankali Abba ya tura ƙopar ɗakin junaid ya shiga daga ciki,Wayaam yaga babu kowa aciki,Bai kawo komai aransa ba,saboda ƙarar saukar ruwa dayaji a toilet,hakan yasa shi tunanin ko ya shiga wanka ne,ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa ya fito daga ɗakin,da niyar idan ya huta zai dawo wurinshi,don yau atare yake son su kwana dashi,

Koda suka yi arba da Abbansu yana nufosu sai kowannansu ya shiga Æ´an kame kame,fargabarsu kada ace zai tambayesu ina Junaid ya ke,.
Tunkan ya Æ™araso wurinsu suka ji yace”Ashe ya shiga wanka ne,idan ya fito daga wankan pls ku sanar dashi cewa nadawo kuma inason ganinshi,a bedroom É—ina,”
Atare suka haÉ—a baki wurin cewa”Toh Abba”

Saukowa down sukayi atare da abban yana gaba suna a bayanshi,Sae faman sauke ajiyar zuciya suke yi,

Lokacin da suka sauko down,Su kanal Yousouf na ganinsu kowa ya miƙe fuskar nan ɗauke da farin ciki,Yayin da su kuma kowannansu ya dabarbarce,
DaÆ™yar suke gaisawa da Æ´an uwan nasu,kowa ya lura da yanayinsu shiru kawai su kayi,Su fawan sai tambayar Junaid suke yi,Yana ina?basu ganshi ba,amsa daya suke basu ta yana a cikin toilet yana wanka,Duk wanda yaje É—akin Junaid yaji sautin saukar ruwa daga cikin toilet,sai yayi tunanin cewa wanka yake yi,Ashe fanfo ne Aka bari a kunne ba’a kashe ba,
Daƙyar suka samu kowa ya haƙura da ganin junaid,Omar yace su wuce ɗakunansu kowa yaje ya huta,an kwaso gajiya,
“Nifa ban yarda dasu babban yaya ba,Shi da ya Omar akwai wani abu da suke 6oye mana Allah,”Acewar Jahan,
A yayin da suke shiga bedroom É—insu,
Ayaan yace”nikaina na lura da hakan,musamman faces É—insu,kamar sunsha kuka Allah,Gaskiya hankalina bazai kwanta ba,sai naga junaid,ni ban yarda wanka yake yi acikin toilet ba,”
Jahan yace”mu bari mu huta,Zuwa dare sai muje É—akin nashi,nasan lokacin idan ma wankan ne ya gama,”
Ƙarasa shiga cikin ɗakin sukayi,kowa ya shiga rage kayan jikinshi,Jahan ne ya fara shiga waka,Ayaan ya zauna gefen gadon yana jiranshi ya fito shima ya shiga wankan,
A can falo kuwa,Mommynsu ta tsare Sgr da Omar,Tasa su gaba tayi tana binsu da kallo one by one,dama bakowa Sgr yafi ji ba fa ce Mommynsu,tana da wuyar sha’ani,
“Mommy,”Sgr ne ya ambaci sunanta,
bata amsa mashi sunan nata daya kira ba,sai cewa tayi”you didn’t answer my question,It seems like you are hidding something for us!Rafayet where is junaid!kada kuyi mun Æ™arya nasan ba halinku ba ne,just ku faÉ—amun Gaskiyar abunda ya faru,”
Murya na rawa Omar yace“Am..mommy,Junaid fa yana a toilet yana wanka zai fito ne…m”daÆ™yar ya Æ™arasa maganar ganin irin kallon da take yi mashi,kallon tuhuma,kallon ban yarda dakai ba
“Wai taya za ku ce mun junaid yana wanka?Nifa ba Æ™aramar yarinya bace,balle kuce zakuyi mun wayau,tun daga kan fuskarku na gane cewa akwai wani abu daya faru dashi….”
Saussauta muryarta tayi,sannan taci gaba da magana”pls idan wani abu ne ya faru da Romeo É—ina ku sanar dani,i will accept it,”yadda tayi maganar yasa su kaji jikinsu ya Æ™ara mutuwa,
“Am listening to u guys,ku faÉ—amun meya faru dashi ya mutu ko”?
Gabansu ne ya faÉ—i rass!da sauri Sgr ya ruÆ™o hannunta muryarshi na kerma yace”Mommy dan Allah kiyi haÆ™uri,ki rufa mana asiri,I will explain to u mu shiga daga cikin bedroom É—in…”
“Rafayet,meyasa zaka sanar da ita”?Omar ne yayi maganar fuskarshi a yamutse,

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

“To ya kakeso nayi Omar,Mommy bazata ta6a yarda ba,kwara kawai mu faÉ—a mata gaskiyar abunda ya faru,Ka wuce wurin Daddy,ni zanji da Mommy,’
Ya ƙarasa maganar tare da jan hannunta,Suka wuce upstairs bedroom ɗinshi,
Ajiyar zuciya Omar ya sauke,Ya jima atsaye yana tunanin Yadda zasu ƙare da Abbansu,tsoranshi kada farat ɗaya zuciyarshi ta buga idan yaji cewa Anyi garkuwa da junaid kamar yadda suka tsara,
“Omar,lafiya kuwa,”firgit ya É—anyi tare da kai idanuwanshi wurinta,Azmee ta nufo shi,Ganinshi a tsaye kamar akwai damuwa atattare dashi,
Dakyar ya Æ™aÆ™aro murmushin yaÆ™e yace”bakomai,”
“Omar,dama inaso na tambayeka ne,Wai ina junaid ne?tun jiya da suka fita shi da jahad shiru har yau basu dawo ba,nashiga damuwa sosai akan rashin ganinsu,har cewa yayi idan suka je shan ice cream zaiyi min tsaraba,” ta Æ™arasa maganar tana kallonshi,
“Aunty Azmee,bazan iya 6oye maki ba,Junaid da jahad anyi kidnapping É—insu….”jin wannan maganar yasa Azmee ta dafe Æ™irjinta da Æ™arfi,idanuwanta suka firfito waje,hankalinta yayi mugun tashi,
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!”kusan sau biyar tana maimata kalmar,
siraran hawaye ne suka soma saukowa saman cheeks ɗinta,ji tayi tamkar bazata iya ɗaga ƙafafunta ba,saboda nauyin da sukayi mata,
“Junaid da jahad suna buÆ™atar addu’armu Azmee,”acewar Omar,
DaÆ™yar ta iya buÉ—e baki tace”Nashiga uku!Yanzu junaid da jahad aka É—auke mana….”
Katse ta Omar yayi’pls Aunty azmee,ki daina É—aga sautin muryarki,na faÉ—a maki ne don ki taimaka mana,Wurin kwantar da hankalin sauran mutanen gidan nan,Mun shiga damuwa sosai,saboda gudun halin da zasu shiga,musamman mahaifinmu….”
Cikin shessheÆ™ar kuka tace”Ya Allah ga bayinka nan!ka tsare manasu a duk inda suke,Ya Allah ka ku6utar dasu daga hannun azzaluman da suka yi garkuwa dasu,wannan wata irin masifa ce……”kuka ne yaci Æ™arfinta,da gudun gaske ta juya tare da tunkarar kitchen,zama tayi ta dingi kuka kamar ranta zai fita,gani take yi kamar zasu rasa su ne,Ta Æ™wallafa rai akan junaid,tana jinshi tamkar É—an cikinta saboda ta shayar dashi,baiwar Allah,
Jiki asanyaye Omar ya wuce bedroom É—in Abbansu,tsaye ya same shi har ya zura kayan bacci ajikinshi,ta cikin mirror ya hango Omar,juyowa yayi fuskar shi É—auke da murmushi yace”halan junaid ya fito daga wankan ne”?yayi tunanin abunda ya kawo shi ne,
“Abba,me kake buÆ™ata na kawo maka”ya tambaye shi ne don ya kawar mashi da tunanin Junaid aranshi
Murmushi Abba yayi tare da cewa”Sannu Azmee,Yau kaine ka kar6i aikinta kenan”?
Duk da halin daya ke ciki na fargaba sai da ya É—an murmusa,jin abunda abban yace,
“No,kawai inaso na baka kyakkyawar kulawa ne saboda nayi kewarka,ka fara faÉ—amun abunda kakeso sai in kawo maka,”
Murmushi Abba ya É—an yi kafin yace”shikenan,junaid nake son gani ka kawo mun shi,idan ma ya fara bacci ka É—auko mun shi,ina jiranka,”ya Æ™arasa maganar tare da samun wuri gefen gadonshi,yana kallon Omar da yayi mashi zuru da ido,
“Omar,lafiya ka zubamin ido kana kallona’?
“Babu komai Abba,bari na É—auko maka junaid É—in,”yayi maganar tare da juyawa yabar É—akin,Zaman jiran dawowarshi Abba yayi,sai faman sakin murmushi yake yi,harya Æ™osa Omar ya É—auko mashi Baby Junaid É—inshi,

A 6angaren Omar yana fita daga bedroom É—in abban nasu,kaitsaye kitchen ya wuce,Anan ya samu azmee zaune saman kujera tana ta matsar kwalla,
“haba Aunty azmee,meyasa zakiyi mun haka?Addu’a yakamata kiyi masu akan Allah ya bayyanar mana dasu,kukan da kike yi bazai amfane su ba,”
Zame hannuwanta tayi daga saman fuskarta,idanuwanta sunyi jawur dasu luhu luhu,
“Omar,ba zaka gane bane,dole inyi kukan rashin su junaid,ko ka manta shakuwar dake tsakanina dashi ne’?
Shiru omar yayi yana kallonta,Allah yaso bai sanar da ita gaskiyar abunda ya faru ba,da baisan abunda zai biyo baya ba daga gareta itama,
Lallashinta ya shiga yi har ya samu ta saukko,Tsayawa yayi ta shirya mashi dinner asaman tray,ya kar6a ya wuce É—akin Abbansu,ita kuma ta shiga É—aukar kayan abincin da ta shirya masu tana kaiwa dining,

Lokacin da Omar ya koma bedroom É—in Abbansu,yana shiga ciki Abbansu yaga tray a hannunshi sai ya É—aure fuskarshi tare da cewa”Nifa ba yunwa nace maka inaji ba,Junaid nace ka É—auko mun,”
Saman table omar ya ajiye tray din tare da samun wuri gefenshi ya zauna,ruƙo hannayenshi yayi tare da sassauta muryarshi
“Abba pls,kaci abincin ka Æ™oshi,idan ka kammala zamuyi magana dakai,”
Shiru yayi yana kallonshi kamar mai nazarin wani abu yace”Shikenan zuba mun abincin naci,Allah yasa naji alkhairi,”
Serving É—inshi Omar ya soma yi,sosai yaci abincin bayan ya gama da abincin,Omar ya tsiyaya mashi Lemu me sanyi a cup,yasha,
“Yanzu ina sauraronka,wata maganace zamuyi,”
“Abba ko zaka É—an kwanta ne?ina ga kamar hakan zaifi,muna magana inayi maka tausa,”
Abun ya daurewa Abbansu kai,gyara kwanciyarshi yayi saman gadon sannan yace”ina sauraronka toh,”
Hawa saman gadon Omar yayi,A hankali ya fara yi mashi massage É—in kafarsa,
A tsanake ya soma magana”Abba dama game da junaid ne,nasan ka yarda dani sosai,kuma zaka fahimce ni ne,
Tunda ya ambaci sunan Junaid,Abba ya miƙe daga zaune da sauri yana kallonshi
daurewa Omar yayi tare da cigaba da cewa”mun shiga matsananciyar damuwa Abba,idan ka lura da fuskokinmu duk sun sauya saboda tsabar tashin hankalin da muke ciki….”dakatar dashi Abba yayi ta hanyar É—aga mashi hannu,
“Ka fito fili ka faÉ—amun ainihin abunda ke faruwa Omar,sai 6oye 6oye kake yi mun,dama ni tuni sai da raina ya bani cewa wani abu ya faru da junaid,dan Allah ka sanar dani!ina É—ana yake”?hankalinshi atashe yayi maganar,

Karanta>>> Furar Danko Chapter 1 By Billyn Abdul

Cike da fargaba Omar ya É—aura da cewa”Abba,junaid yana cikin Æ™oshin lafiya,sai dai baya atare damu,Jiya bayan fitarsu shan ice cream tare da jahad,kidnappers su kayi garkuwa dasu,bana so ka tashi hankalinka Abba,Ni nayi maka alÆ™warin zan dawo maka da Æ´a’Æ´anka,cikin Æ™oshin lafiya batare da sun samu koda Æ™warzane ajikinsu ba…..”duk wannan surutan da Omar keyi baisan cewa Abbansu ya jima da sumewa ba,tunda ya ambaci sunan kidnappers sunyi garkuwa dasu,Bai Æ™ara sanin inda kanshi yake ba,
“Abba!”ya ambaci sunanshi,yayin da yake kallon fuskarshi,Hannu yasa tare da dafe goshinshi,Dama saida ranshi ya bashi cewar hakan zata iya faruwa,
Idanuwanshi ne suka cuccuko da kwalla,kamar ya fasa ihu haka yake ji,ta ko’ina babu sauÆ™i,dirshan ya zauna saman gadon fuskarshi a yamutse,ya zuba ma Abban nasu ido yana kallonshi,

Adai dai Lokacin Sgr ya shigo bedroom ɗin tare da Mommynsu,tasha kuka duk da irin juriyarta,daƙyar ya samu ya shawo kanta,shima ɗin don yayi mata alƙwarin cewa zai dawo mata da ɗanta har gida ba tare da komai ya same shi ba,jin motsin shigowarsu yasa Omar waigawa yana kallonsu,har suka ƙarasa shigowa wurin gadon,Gefen gadon Sgr ya zauna,Mommy ta tsaya daga tsaye tana kallon Abba dake a zaune ido rufe,
“Omar,ka faÉ—a mashi ne”!?É—aga mashi kai Omar yayi alamar eh,Ya kuma cewa”ko ya samu bacci ne”?
Girgiza kai yayi tare da cewa”a’a,taya zan faÉ—a mashi wannan tashin hankalin yayi bacci?Kaima ka sani,tun kafin ma na Æ™arasa sanar dashi ya sume a zaune,Na rasa abun yi ne shiyasa nayi zugum ina kallonshi,
MiÆ™ewa Sgr yayi da sauri ya fuce daga É—akin don ya É—auko masu ruwan da za’a yayyafa mashi,
“Mommy,dan Allah ku Æ™ara haÆ™uri akan 6atansu junaid,in sha Allah we will try our best don muga mun dawo dasu cikin gidan nan,”
Jinjina kai tayi “Na yarda daku Omar,Nidai burina ku dawo mun dasu cikin gidan nan,Na tambayi Son game da kidnappers É—in ya sanar dani cewa,Sau É—aya suka kira waya,Kunyi magana dasu kuma har sun baku Junaid kunyi magana dashi,Naso ace sun bar wata kafa da zatasa ayi tracking layinsu,Amma kashe yace mun Sun kira da hidden number ne,abunda nakeso naji shi ne,basu buÆ™aci adadin kuÉ—in da suke so ba?ni koma nawa ne zan bada a kar6ominsu,”
Jikin Omar ba ƙaramin sanyi yayi ba,gwanin ban tausayi haka yake kallonta,Aransa yana ayyana irin tashin hankalin da zata shiga idan taji cewa,Junaid ya mutu ta hanyar take shi da mota,
“Omar kayi shiru baka ce komai ba,”ta jifa mashi tambayar,tana kallonshi,
Girgiza mata kai yayi”A’a Mommy,basu buÆ™aci komai ba yanzu,Sun sanar damu cewa,Zasu tuntu6emu idan buÆ™atar hakan ya taso,kuma sunyi warning É—inmu,kada mu kuskura muyi gigin yin investigation akansu,if not zasu illatasu ne,shiyasa bamu yi wani yunÆ™uri ba ayanzu,Amma yanzu mu kanmu kiransu muke jira,muji nawa suke buÆ™ata sai a tura masu,”ba don yaso ba haka ya dinga shirga mata Æ™arya,kamar yayi kuka wai yau shine ke yin Æ™arya,duk da yayi ba’ason ranshi ba,Dole ce tasa su yin hakan,
Turo Æ™opar Sgr yayi hannunshi ruÆ™e da bottle water,Æ™arasawa yayi tare da buÉ—e murfi ya tarfa ruwan asaman tafin hannunshi,Sannan ya shafa fuskar Abban nasu,Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ware idanuwanshi akansu yana kallonsu É—aya bayan É—aya,a hankali ya furta”Ina junaid”?
Omar na Æ™oÆ™arin buÉ—e baki yayi mashi jawabi,Alexandra ta katse mashi hanzarinshi da cewa”Ku barni dashi,dare yayi sosai yakamata kuje ku kwanta ku huta,kafin gobe,”ta fadi hakan ne don tasan cewa ba karamin tashin hankali suma suke ciki ba da ganin yanayin su,
Saukowa daga saman gadon Omar yayi tare da ruÆ™o hannun Sgr yace”Mu tafi,”sallama su kayi mata tare da fucewa daga É—akin,
Hawa saman gadon tayi suna fuskantar juna,tallabo fuskarshi tayi da hannayenta biyu,suka zuba ma juna ido,na wani lokaci kafin tace”Hubby,ka natsu ka saurare ni,Nasan zaka fahimce ni,Kuma kai musulmi ne!kayi imani da Æ™addara mai kyau ko mara kyau haka ne”?kamar wani Æ™aramin yaro haka ta mayar dashi,
Nodding kai yayi mata alamar eh,
Murmushi ta É—an sakar mashi tare da cewa”haka nake son ji my hubby,”dakatawa ta É—an yi da yin jawabin tana kallonshi,saboda ta kasa furta mashi abunda take so ta faÉ—a,farin ruwa ta gani ya kwanta acikin idanuwanshi,la66ansa na kerma yace”Pls tell me the truth,Meya faru ne?kowa ya sauya mun,Dama ni sai da raina ya bani cewa wani abu ya faru da baby junaid É—ina,”jikinshi har ya fara kakarwa kamar wanda sanyi ya kama,

Karanta>>> Tabarmar Kashi Chapter 1 By Safiyya Huguma

Hawaye ne suka ciko tab a idonta,
“Am sorry to say,Junaid yana cikin Æ™oshin lafiya,Amma baya atare damu,Rafayet ya sanar dani cewa,since yesterday night around 8 suna kan hanyar dawowarsu gida,kidnappers suka É—aukesu gaba É—ayansu,”
Jin wannan maganar yasa hankalinshi yayi mugun tashi,wata irin zabura yayi yana Æ™oÆ™arin saukowa daga saman gadon,Da sauri ta ruÆ™o rigar jikinshi”dan Allah ka natsu ka saurare ne….”
Girgiza kai ya shiga yi yana faÉ—in”banga ta zama ba,Anyi garkuwa dasu junaid É—ina,Wlh bazata sa6u ba,duk inda junaid da jahad suke adawo mun dasu cikin daren nan in har anason zaman lafiya,wannan wani irin shashanci ne?har junaid ya kwana a hannun kidnappers tun jiya arasa wanda zai Æ™watosu daga hannunsu,Banga amfanin sojojin dana tara acikin gidan nan ba,Nikaina bani da amfani kenan!Kowa ma bai da amfani mun zama tamkar kwankwan ashana,tunda har bazamu iya ceto rayuwarsu ba,”idonshi ya rufe sai faman zazzaga masifa yakeyi,Ƙarasa saukowa yayi daga saman gadon,buguzun buguzun ya kama hanyar fita daga bedroom É—in nashi,da sauri Alex tabi bayanshi,tana ambaton sunanshi
Ko sauraronta baiyi ba,da alama ya zauce ne,
“Yau Æ™afata kafarsu junaid zamu dawo cikin gidan nan duk inda suke saina dawo dasu,abun ban haushi wai anyi garkuwa dasu junaid?sai kace Æ´a’Æ´an wani me siyar da kifi abakin titi,Ƴa’Æ´ana ne fa!Ni chief of army staff na Nigeria gaba É—aya,banga amfanin matsayin da nake dashi ba Allah,tunda har za’a iya yin kidnapping É—in ya’yana,wlh bazan yafewa kaina ba,in har bandawo da junaid cikin gidan nan ba,”ranshi amatukar 6ace yake yin maganar,jijiyoyin wuyanshi duk sun firfito waje,
“Pls hubby Calm down ur mind,Ina zaka je ne?acikin daren nan!indai akansu junaid ne,na tabbata zasu dawo ne”
Guntun tsoki yaja tare da cewa”baki da hankaline,da alama bakisan zafin haihuwa ba,Shiyasa kike faÉ—in hakan,”
“Ni fa na haifeshi,taya zaka ce mun bansan zafin haihuwa ba?Ya kake so nayi ne?ka Æ™i tsayawa nayi maka bayani,
Su Marshal na zaune asaman sofa,kowa da abunda yake saƙawa aranshi,kwatsam suka jiyo muryoyinsu,nan fa suka miƙe suna kallonsu,
Ganin Abbansu ya nufi hanyar fita daga falon ko takalma babu a ƙafarshi,da sauri suka sha gabanshi,
Rufe ido yayi atsiwace yace”Ku matsa ku bani wuri,wlh Omar ka bani mamaki,ko ince kun bani mamaki,How many hours su junaid na a hannun kidnappers amma baku iya Æ™watomun shi ba,babu wani mataki da kuka É—auka,to ni zanje in dawo da abuna,”yana magana huci na fitowa daga bakinshi,
Ruƙo shi Omar yayi tare da fashewa da matsanancin kuka,Girgiza mashi kai ya soma yi batare da ya furta mashi komai,jikin Abbansu ba ƙaramin sanyi yayi ba,Cos ya manta when last yaga hawaye a fuskar Omar,tabbas abun na ci masu rai sosai,Mayar da idanuwanshi yayi kan Sgr,Hawaye ya gani kwance Luf acikin idanuwanshi,wanda tunda yake arayuwarshi bai ta6a ganin ruwan hawaye a idon Sgr ba,tun ma da aka haifeshi har suna expecting ko baida cikakkiyar lafiya ne,
“Omar!kuka kake yi mun”?yayi maganar yayin da hawaye suka soma wanko fuskarshi,Kallon Sgr yayi tare da cewa”Kaima kukan zaka yi mun”?
Duƙar da kanshi yayi ƙasa,gaba ɗaya jikin kowannansu yayi sanyi,
“Abba,ka tausaya mana muna cikin matsananciyar damuwa na rashin Su junaid atare damu,Mun rasa yaya zamuyi,munyi tunanin zaka Æ™arfafa mana guiwa wurin ganin mun ceto rayuwarsu,Amma sam kaÆ™i tsayawa kaji abunda muke son mu sanar dakai balle har musa ran zaka fahimce mu….”ya Æ™arasa maganar tare da sanya tafin hannunshi yana share hawayen dake sauka a fuskarshi,
“Abba,saboda rashin su junaid,ko bacci ba muyi ba,Yadda muka ga dare haka muka ga rana,Ga rafayet nan saboda shi,Ya baro kano ya dawo Abuja tunda sanyin safiya,dukanmu nan babu wanda ya iya kora koda ruwa ne ta maÆ™oshinsa,duk don saboda 6atansu junaid….”dakatawa ya É—an yi da yin maganar yana kallon Abban nasu,da alama ya fara saukowa
“Kaine ka haifemu,kafi kowa sanin su wanene mu!me zamu iya da kuma wanda baza mu iya ba!Nasan ka yarda damu sosai,Idan har akwai wanda zai bada shaida akanmu kaine Abba!meyasa bazaka yi mana uziri ba?idan har bamu bi komai a hankali ba wurin ganin mun ceto rayuwarsu,Toh zamu rasa su ne gaba É—ayansu!”
Juyawa Abba yayi ya soma tafiya cikin falon,Saman sofa ya zauna,ganin haka yasa suma suka dawo saman Sofa É—in suka zauna suna fuskantarshi,Itama Mommy ta samu wuri daga gefen shi ta zauna,

Duk wannan abun dake faruwa akan idon ƙannensu,don tun lokacin da Abbansu ya fito yana sambatun nan,Kowannansu ya fito daga bedroom ɗinshi,Jikin kowannansu yayi mugun sanyi,jin cewa Anyi kidnapping ɗinsu Junaid,Abun ya ta6a masu zuciya sosai,

“Har tsawon wani lokaci,kuke so na baku ku dawo mun dasu junaid”?Acewar Abba,
Shiru sukayi gabansu na faÉ—uwa,Omar ne yayi Æ™oÆ™arin cewa”1 week”a hanzarce Sgr yace”Omar that’s impossible,ka manta yarda mu kayi dasu ne?Sunyi mana alÆ™awarin cewa in dae aka yi masu yadda suke so zasu sakosu,Amma ba a tare ba,saboda suna ganin za’a gano su adau mataki, akwai yiyuwar su fara sauko junaid shi kaÉ—ai acikin satin nan ko kuma su fara sakin Jahad,Ni ina ga kamar one month yayi,Kafin lokacin in sha Allah mun dawo dasu duka acikin gidan,
Girgiza kai Abbansu ya É—an yi tare da cewa”Har one month!su junaid basa atare damu?idan suka cutar dasu fa?
“Abba sunyi mana alÆ™awarin cewa in har zamu biyasu yadda suke so,bazasu cutar mana dasu ba,”
“Nawa suka buÆ™ata”yayi tambayar yana kallon faces É—insu,
“har yanzu dai su muke jira,sunce zasu kira su sanar damu,sannan sunce mu kwantar da hankalinmu,Bazasu ta6a cutar dasu ba,Zasu basu kyakkyawar kulawa,kuÉ—i kawai suke buÆ™ata ba wani abu ba,”Omar ne ya kora mashi jawabin
Cike da takaici Abba yace”just because of money,suka É—auke mun Æ´a’Æ´ana?Ae da sun sani sun nemi tallafi a wurinmu konawa ne zamu basu basai sun É—auke mun su ba,”
Miƙewa yayi sam babu kuzari ajikinshi,tafiya ya soma yi dakyar yake iya ɗaga ƙafarshi,har sai da yabar wurin Sofas ɗin,Sannan ya dakata da yin tafiyar,ya waiwayo tare da kallonsu,gaba ɗaya idanuwansu na akanshi,
Magana ya soma yi masu babu wasa a fuskarshi”Omar!”
“Na’am Abba”ya amsa mashi,
“Rafayet”shima ya amsa mashi”Na’am Daddy,”
“Na yarda daku sosai,abu biyu nake tsammani daga wurinku,Na fako ku dawo mun dasu junaid,Cikin Æ™oshin lafiya,Na biyu kuma ku kawo mun waÉ—annan gur6atattun mutanen da sukayi garkuwa dasu,Wallahi thumma tallahi idan har ku kasa yi mun waÉ—annan abubuwan dana lissafa maku,inaso ku sani Za ku rasa ni ne,NA HAR ABADA,daga yau zuwa 30 ga watan da zamu shiga,a kowace rana zan fara sa ran dawowarsu acikin gidan nan!kuma daga ranar ku fara Æ™irgen ranakun da su kayi mun saura acikin duniyar nan

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

*Tashin hankali!*
Mikewa Mommynsu tayi tare da kallonsu gwanin ban tausayi tace”Na yarda daku sosai,ku taimaki rayuwar mahaifinku,Zamu taya ku da Addu’a Har Allah yasa kuyi nasara akan kidnappers É—in nan,”tana kai Æ™arshen maganarta,tabi bayan abbansu,
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!”wannan shi ne abunda ke fitowa daga bakunansu,basu ta6a ganin tashin hankali irin na wannan ranar ba,A tsaye kowannansu ya kwana,har sun fara regretting É—in Æ™aryar da suka shirya ma Abbansu,

Acikin waÉ—annan kwanakin,Komai ya hargitse masu,safe da marece dare da rana,kullum cikin Zullumi suke,Suna cikin tashin hankali,Duk sunbi sun firgice,kallo guda zaka yi masu ga gane cewar basa a hayyacinsu,Don gaba É—ayansu daga Omar É—in har Sgr babu wanda baiyi rama ba ajikinsu,gidan ya zama tamkar maÆ™abarta,Babu wani sauran farin ciki daya rage masu,Saboda rashin junaid babu mai samun isasshen bacci acikinsu,Abinci ma har Azmee ta fara gajiya da girka masu saboda Asarar shi da akeyi,Yadda ta ajiye haka take zuwa ta same shi,duk rana ta Allah sai Abbansu ya tunasar dasu Adadin kwanakin daya rage masu na Æ™wato su junaid a wurin kidnappers,yayin da suke cikin wannan tashin hankalin,Abusufyan na can suma ba kwanciyar hankali wanda hakan ya É—auke hankalinshi gaba daya batare da ya fahimci halin da gidan suke ciki ba,Ciwon abu ya tashi gadan gadan,Kullum da daddare sai ta dinga kuka tana buge buge tana faÉ—in sunan sayyadi,hakan ba Æ™aramin ruÉ—ani ya sanyasu ba,har Sehrish ta fara zargin cewa,kodai yafara yi mata gizau ne?Anya ba wani abu ke faruwa ba?duk yadda taso Oummansu ta sanar da ita abunda take gani,Hakan ya faskara saboda bata da hankalin da zata iya fayyace mata komai,a Æ™arshe dole sehrish ta koma É—akinta da kwana,duk in haukan nata ya motsa da zarar ta fara raira mata karatun AlÆ™ur’ani sai ta samu natsuwa,a haka suke samu tayi bacci,

A 6angaren Su Hayaam kuwa,ba ƙaramin daɗi suka ji ba,lokacin da Abra ta dawo abuja,Batare da tasha wahala ba,bayan An sallami Hayaam daga Asibiti gidan Amani suka koma,Zasu zauna na ɗan wani lokaci kafin su wuce Maiduguri,duk wannan budurin da sukeyi basu son abunda ke faruwa acan gidansu na maiduguri ba,Sun manta da mahaifiyarsu da suka baro kwance ba lafiya rai hannun Allah,

A 6angaren Aunty babba kuwa ba Æ™aramin jiki taji ba,tun bayan da mai motar nan ya hankaÉ—e ta a Enugu,daÆ™yar aka samu wani bawan Allah ya É—auketa a motarshi suka kaita asibiti,Taci baÆ™ar wuya kamar bazata rayu ba,tsawon sati tana kwance a gadon asibiti batasan inda kanta yake ba,Komai ya Æ™are mata Æ™arÆ™af,mutumin daya kawota asibitin tun da ya biya kuÉ—in da za’a yi mata aiki a Æ™afarta da ta samu matsala,bai Æ™ara tako kafarshi yazo ba,Ga ciwo yaÆ™i ci yaÆ™i cinyewa,ta É—uri ruwa,tayi suntum da ita,daga baya ta ru6e sai uban wari dake fitowa daga jikin Æ™afar,Likitoci sunyi iya kar bakin Æ™oÆ™arinsu wurin ganin sunyi mata magani,amma abun ya ci tura,da suka gaji gashi babu wani danginta a kusa,kuma babu kuÉ—in da zasu cigaba da kula da ita,A Æ™arshe Suka sallame ta daga asibitin,Tashin hankali!ko ya rayuwar Laila zata kasance”?
Yau Two Weeks kenan da mutuwar Junaid,Wanda ya kasance Wata biyu cuf da sati É—aya da yin auren Sehrish Abusufyan da Rafayet salahuddeen,duk da muna sa ran kwanakin auren nasu zai Æ™ara tsayi saboda Sgr ya É—aga tafiyarshi ta komawa U.s,Zuwa Next One Month,dalilin É—aga tafiyar tashi saboda Investigation É—in da sukeyi na Æ™oÆ™arin gano waÉ—anda suka kashe Junaid,Ga kuma Abbansu daya zuba masu ido yana jiran su dawo mashi da Æ´a’Æ´anshi,bawan Allah ko bacci bai samu,duk ya rame ya fige,bai samun bacci da daddare saboda sallar daren da yake yi, haka zai zauna saman darduma yayi ta yi masu addu’a,Allah ya dawo mashi da Æ´a’Æ´anshi,ita kanta Mommynsu junaid tana cikin mawuyacin hali,cos ta fara zargin cewa ba Kidnapping É—insu akayi ba,there’s something behind da suka 6oye masu,har sun fara fidda rai da dawowarsu,A ranar Litinin sai ga JAHAD ta dawo gidan da Æ™afafunta,Murna a wurinsu kamar su haÉ—iyeta,duk da sun shiga damuwa ganin yadda ta rame ta fige,duk ta fita hayyacinta,Æ™ashin wuyanta duk ya firfito kamar zai fasa fatar wuyanta,Taji jiki sosai,Idanuwanta duk sun kumbura,duk yadda suka so jahad ta buÉ—e baki ta faÉ—a masu ina junaid yake,taÆ™i magana bakinta a rufe yake,sai dai kawai ta dinga binsu da ido,bakomai ya hanata yin magana ba,fa ce kukan dake cinta,muddin ta buÉ—e bakinta to zata fashe masu da kuka ne,kuma ta É—aukarwa Su ya Omar alÆ™awarin bazata tona masu asiri ba nace wa junaid ya mutu,har sai lokacin da suka shirya sanar dasu,tunda ta dawo gidan nan,Ta zama salihar Æ™arfi da yaji,magana saita zama dole sannan take yinta,ko É—akinsu batasan fitowa daga ciki,tun hosana na lalla6ata don ta faÉ—a mata abunda ke damunta,saboda kullum sai ta farka ta sameta tsakar dare tana sallah hawaye na gangarowa akan fuskarta,Har tagaji da tambayarta ta Æ™yaleta,

 

Karanta>>> Zurfin Ciki Book 1-4 Complete Novel Document

 

Kullum ne in zata kwanta da daddare sai ta É—aukko wannan zanen fuskar junaid da tayi a cikin drawing book É—inta,ta tasa shi gaba tayi ta kallo,Wani lokacin ta fashe da kuka wani lokacin kuma tayi murmushi,bakomai yafi tsaya mata araiba,kamar rana ta farko da ta fara haÉ—uwa dashi face to face,Yayi tsammanin Sehrish ce,ya ruÆ™o hannunta ya turata cikin motarshi,ya tasa ta gaba da wannan kyakkyawan murmushin nashi,jahad tayi kuka tamkar ranta zai fita,har ya bi jikinta,in har bata zubda kwallaba ita kanta bata jin daÉ—in jikinta,wani sa’in idan raÉ—aÉ—in yayi mata yawa Æ™ur’ani take É—auka ta zauna tayi ta karantawa har ta samu sauÆ™i acikin zuciyarta,Sau dayawa Omar yakan kirata a garden su zauna yayi ta lallashinta,yana yi mata nasiha,hakan yasa ta fara samun sauÆ™in raÉ—aÉ—in da zuciyarta keyi mata,har ta fara sakewa da kowa acikin gidan,hakan ba Æ™aramin daÉ—i yayi masu ba,Yanzu saura dawowar Junaid suke jira shima Masu garkuwar su sako shi,😥rashin sani yafi dare duhu

*Boss Bature*

Kano State,

Wuraren ƙarfe 8 na dare,Sehrish ta fito daga cikin toilet,chest ɗinta ɗaure da towel,ta canza sosai,duk da babu kwanciyar hankali atare da ita,Ciwon Oummansu ba ƙaramin ɗaga mata hankali yake yi ba,harta fara murnar zasu koma gida,sae kuma abu ya dawo gadan gadan haukan take yi,wardrobe ta nufa tare da buɗewa,ta dauko kayan baccinta riga da wando ta zurasu ajikinta,bayan ta kammala sanya kayan,gaban mirror ta koma ta zauna tana kallon fuskarta acikin madubin,ta ƙara kyau da haske,mayukan da take amfani dasu ba ƙaramin gyara suke yi ma jikinta ba,tunani ta shiga yi yau saura satittika suka rage aurenta ya mutu da Sgr,ta ɗan damu da rashinsa a kusa da ita,kusan kullum ne saita tura mashi text message a wayarshi,Sometimes yana maido mata da reply,harma ya tambayi ya lafiyar Oummansu,hakan ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba,
Kiran wayane ya shigo,nan take wayarta ta soma ruri,jiki na rawa ta miƙe daga saman kujerar ta nufi inda ta ajiye wayar asaman pillow,hannu tasa ta ɗauki wayar tare da duba sunan mai kiran nata,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta ganin sunan Mommy Azeema ya bayyana akan screen ɗin wayar,Cike da zumuɗi ta ɗaga kiran,
“Assalamu alaikum mommy”
On the other hand mommy Azeema tace”wa’alaikumus salam my Daughter hope kina lafiya,”
Shiru Sehrish tayi batare da ta bata amsa ba,ƙasa kasa ta soma shessheƙar kuka,
“Daughter,kuka kikeyi koh”?nan ma shiru bata amsa mata ba,
“Kinyi missing É—in mommynki ko?,
DaÆ™yar ta iya buÉ—e baki tace”Eh mommy,kin manta dani,ina cikin damuwa sosai,ta ko’ina ba sauÆ™i,dama kece kike kwantar mun da hankalina,gashi yanzu kona kira baki É—agawa,”
“Am sorry daughter,Nasan ban kyauta maki ba,Amma yanzu ki kwantar da hankalinki,In sha Allah this week zamu zo nan Abuja,Munyi waya da Abusufyan ya sanar dani cewa,Zaku dawo tare da Oummanku ko!
sehrish tace”Eh,”
“Naji daÉ—i sosai,Ban kira na tayaki murnar ganin Oummanku ba,Wlh na yi farin ciki sosai,har ina cewa gwaurancin Abusufyan ya Æ™are tunda sanyin idaniyarshi ta dawo,”
Murmushi sehrish ta saki,hajiya azeema taci gaba da cewa”Baki bani labarin rayuwarki da Sgr ba?ya ake ciki?ko har yanzu babu wani sauyi”?
Komawa sehrish tayi gefen gadon ta zauna,A tsanake ta labarta mata irin zaman da sukayi dashi,”
Hajiya azeema tace”Good,Koba komai ta wani 6angaren hankalinshi ya fara karkata akanki,Wannan ma mataki ne na nasara”
Dakatawa tayi da yin maganar tana sauke ajiyar zuciya,kasa kunne sehrish tayi tana jiran jin me zatace mata,
“Yaushe zaku dawo kano?kamata yayi ace kuna tare da juna,banji daÉ—in komawarshi Abuja ba,”
“Gobe muka shirya komawa gida,Amma ciwon oumman mu sai Æ™ara gaba yake yi,bansani ba ko tafiyar na nan,ko an fasa,Daddy nake jira ya dawo na tambayeshi,”

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

“Kisan yarda zakiyi Ku koma Abuja,if not duk wani shirin mu zai lalace ne,Ita kuma Oummanku,Allah ya bata lafiya,zamu tayaku da addu’a,Zan yi magana da daddy É—in naku gaskiya Æ™wara adawo da ita nan Abuja,zata fi samun caring,ga kuma su hosana da jahad,idan tana ganinku ku uku atare sai inga kamar zata iya dawowa hayyacinta in a short time,”
Sehrish ta Gamsu da bayaninta ita kanta tayi tunanin hakan,
“Nagode sosae Mommy,Allah yabarmun ke,Har na kosa mu hadu,don nayi missing É—inki sosai da sosai,”
dariya hajiya azeema tayi tare da cewa”don’t worry ur self in dai nice har sai kin gaji da gani na,Am coming back soon,Dani za’ayi yaÆ™in karshen nan,da makamaina zanzo,mu bazama a filin daga har sai mun cimma nasara,”cike da Zolaya tayi maganar,hakan ba Æ™aramin dariya ya ba sehrish ba,hada dafe cikinta,taji daÉ—in kiran da Hajiya azeema tayi mata,Ta sanyata farin ciki sosai,Sun jima suna waya kafin daga bisani suka yi sallama,

Wurgi tayi da wayar saman mattress,fuskarta É—auke da Æ™ayataccen murmushi,tana cikin NishaÉ—in nan ta soma jin faÉ—uwar gaba rass rass!tunani ta shiga yi ko mai yasa take jin faduwar gaba?kodai wani abu na faruwa ne,tana cikin wannan fargabar taji an kashe Æ™wan falo,da farko bata damu ba,tun da ba ita kaÉ—ai bace acikin gidan Akwai security guards zai iya yiwuwa ma Daddynsu ne ya dawo,dama ya sanar da ita cewa after isha’ prayer zai wuce gidansu Maman sadeeq,

Ƙwala mashi kira ta soma yi don taji idan shi ne ya dawo,
“Daddy!Daddy!Daddy Abusufyan”!shiru ba’a amsa mata ba,nan fa ta soma zargin kodai wani ne ya shigo masu,Amma ae akwai security a gidan,kasa jurewa tayi hakan yasa ta mike tsaye,ta tunkari Æ™opar É—akin a hank

Back to top button