Halysaah Page 82 By Khaleesat Haydar
Safiyyah na zaune gefen gado a dakin Khaleesat tayi tagumi tana kallon Khaleesat da ta gama shiryawa ta dau Charger dinta ta saka a backpack dinta kar ta manta shi, a hankali Safiyyah tace “Shikenan yanxu dai tafiya za ku yi ku bar ni a kasar nan” Khaleesat tace “Toh ba kince Ya Musty yace next week za ku taho ba, nan da few days ne next week din fa” Safiyyah ta taɓe baki ta mike tace “Ai shikenan, kafin nan da next week din ai kadaici ya min illa Khaleesat, babu ke babu Housemate, ga Ajay ma ya tafi, i have nobody remaining in this country kenan ai” Khaleesat ta kashe komai na dakinta sannan ta dau karamin mayafinta suka fita, tun daxu Jay ke jiransu a waje patiently, bayan sun sauko downstairs Safiyyah tace “Ya kai luggages din mota ne gaba daya?” Khaleesat na kashe duk wani abu dake kunne na wuta a parlon tace “Tun daxu ya fita da su ai” Safiyyah ta wani kyabe baki tace “Sae wani rawan jiki kike za ki tafi Nigeria kamar irin nima ba zan zo ba din nan” Dariya Khaleesat tayi tace “Ban gane rawan jiki ba, don Allah mu fita tun daxu fa yake garage yana jiranmu” Safiyyah tace “Da Ajay ne da ya cika mu da bala’i yanxu mun gigice, ai Housemate akwai patient” A haka suka fito daga apartment din suka gansa zaune a mota yana danna wayarsa, yafi minti talatin da biyar a motar yana jiransu, ya bude motar ya sauko yana kallonsu har suka karaso inda yake sannan yace “Done with preparation?” Khaleesat ta gyada masa kai, yace “Ohk let me order a ride, dama ina son ku bata duk lokacin da za ku bata ne so that we won’t keep the Uber driver waiting” Safiyyah tace “To mu shiga motar mu ɗan yi hirar bankwana kafin nima in zo Nigeria din Yaya Jay” Murmushi Jay yayi ya bude masu back seat, Safiyyah ta shige, ita dai Khaleesat na tsaye bata shiga ba, ya kalleta yace “Baza ki shiga ba?” Ba tare da ta kallesa ba tayi Murmushi ta girgiza masa kai, hakan yasa shi ma bai shiga motar ba ya gama order din ride din da wayarsa sannan ya jingina da motar yana kallon Safiyyah yace “So what is ur plan when back in Nigeria?” Safiyyah ta gyara zama tace “Ni dai da za a bar ni a gidanmu ina son in je masarautan ku ziyara, dama ban taɓa shiga ko wani Emirate ba a Nigeria” Jay yayi dariya yace “Really?” Tace “Wallahi, kuma gashi bamu da yan uwa kwata kwata a Bauchi, Khaleesat ce dai kanwar Babanta ke can amma ita ma bata taɓa zuwa ba tace min, sai dai ko in yi karya ince Gombe zan je biki, don akwai Cousin sister dita an kusa bikinta kawai dai bama shiri da ita ne kuma ban yi niyyar zuwa bikin ba, amma tunda naji ance Bauchi da Gombe neighbouring state ne kawai sai in fake da bikinta inje Masarautan ku in gaida Mai martaba in de baza a koreni ba” Tana washe baki ta kare maganar, Jay dai murmushi kawai yake, Khaleesat dama juya masu baya tayi don ta gaji da halin Safiyyah, Jay ya kalli Khaleesat yace “Kuna da yan uwa a Bauchi dama?” Khaleesat tace “A’a ni ban taɓa gaya mata haka ba, we have nobody in Bauchi…” Safiyyah tace “Kai haba, na zata kince Aunty Murja a Azare take” Babu yabo babu fallasa Khaleesat tace “Ni ban ce maki haka ba Sophie” Safiyyah tace “To ni muna da yan uwa a Gombe, ga er uwata nan ma zata yi aure a can” Jay yace “In dai zaki je bikin that won’t be an issue in Sha Allah, I will bring you down to the Emirate” Tace “Har Mai martaba zan samu gani?” Yana Murmushi yace “In sha Allah zan kai ki har gabansa” Ya ɗan kalli Khaleesat da ta kagu Uber din ya zo ko Safiyyah zata hakura da surutun haka, yace “Ina makullin apartment din?” Khaleesat ta mika masa ya amsa yace “Let me check the electrical appliances ko akwai wanda ku ka manta baku kashe ba” Daga haka ya nufi cikin apartment din, Khaleesat ta leka motar tana kallon Safiyyah tace “Does it even make sense to you ki ce zaki je masarautan su ziyara?” Safiyyah tace “Ban gane ba? Wani mugun waje nace zan je? Ai ba wani abu bane a ciki kema in zaki ki shirya kawai mu je sai mu fake da bikin Karima, balle ni nasan denying kika yi kawai amma kin taɓa ce min Aunty Murjan ku a Bauchi take, haba ai kamar Excursion ne wannan za mu je ba wani abu ba, ke duk abun wayewa kun yi hannun riga da shi, har Yankari Game reserve ni dai zan je wallahi idan naje masarautar tasu, su ma kuma za su ji dadi idan naje, har Ajay zai yi mamaki yaji dadi kuma, Ni dai it’s a privilege for me” Khaleesat bata sake ce mata komai ba ta koma can Edge din motar ta tsaya tana kara mamakinta ita dai duk wani harkar kareranci ta iya, Jay na fitowa sai ga Uber da yayi order ya iso. Har Airport Safiyyah ta masu rakiya, sai da Jay ya jira ta samu Lyft da zai maida ta gida sannan ya bata 1000 dollar, da farko kin amsa tayi yace “Common Safiyyah, na taɓa baki kudi ne? I won’t be happy idan baki amsa wannan ba” Tana ɗan murmushi ta amsa kudin sannan ta masa godiya tace “Allah ya kai ku lafiya nima in sha Allahu ina nan zuwa ranan litinin ko bai bar ni ba zan gudu da izinin Allah” Jay yayi dariya yace “A’a gwara dai ki jira ya bar ki Safiyyah kar ki gudu” Safiyyah ta juya ta kalli Khaleesat dake kallonta don har ta fara missing kawartata, rungumeta Safiyyah tayi tace “Safe trip kawata, Allah ya kiyaye hanya” Murmushi kawai Khaleesat tayi cikin sanyin murya tace “Ameen, Thank you so much Sophie” Safiyyah tayi kasa da murya tace “Kuma saura ki kunyata ni ki ki sakin jiki da shi idan kun shiga jirgin, ko abinci aka baku ki tabbatar kun ci tare haka masoya suke yi idan za su yi tafiya tare, don nasan dai kusa da kusa ya siya maku ticket din, kin dai gane me nake nufi” Khaleesat ta turata ta bar wajen tana murmushi, a haka suka shiga cikin airport din Safiyyah kuma ta koma gida. Just handbag kawai Khaleesat ke rike da shi da za su shiga jirgi don hatta backpack dinta Jay sai da ya amsa ya rike mata, bai bari ta dau komai ba, jiran 30 mins kawai suka yi Departure lounge before boarding, su ne kuma farkon boarding din jirgin kasantuwar ticket dinsu Business Class ticket ne, kamar yanda Safiyyah tayi guessing seat dinsu kusa da kusa ne, ita dai Khaleesat tun incident din jiya da safe har yanxu ta kasa sakin jikinta wani irin kunyarsa take ji, ko kallonsa bata iya yi ko yana mata magana, bayan duk an gama boarding jirgin ta bude handbag dinta ta ciro wayarta zata ajiye ma Aunty Farida message tace za su taso, don tace mata ta gaya mata idan za su taso din, bayan ta tura message din ta daga kai ta ɗan kalli Jay taga kallonta yake kamar ya samu TV, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, yayi kasa da murya yace “You need help with the seat belt?” Ta girgiza masa kai ba tare da ta kallesa ba tayi fastening seat belt dinta don tashi jirgin zai yi…. Suna ɗagawa sararin samaniya Khaleesat ta ɓige da bacci don dama surutu da zantukan Safiyyah bai bari tayi bacci da wuri daren jiya ba, sai da suka kai karfe uku da rabi na asuba Safiyyah na labari yaki ci yaƙi cinyewa, suna idar da sallahn asuba kuma wai yunwa take ji su je kitchen suyi girki, haka ta hanata ɗan baccin safen da take yi ma, da rana kuma Jay ya fita da su shopping din tsaraban da Khaleesat zata kai gida, yayi ma har Safiyyah ma shopping din, kudi sosai ya kashe masu a wajen, daga nan kuma suka tafi gidan abinci me tsada suka yi lunch, sai kusan yamma suka dawo gida, suna dawowa kuma sai shirin tafiya Airport, Jay na ganin Khaleesat ta fara bacci ya mike ya karasa kusa da ita ya kwantar mata da seat dinta gently ta yanda zata zama comfortable tayi baccinta, ta bude ido a hankali tana kallonsa, murmushi ya sakar mata yana kallonta, ta mayar da idonta ta lumshe ya koma seat dinsa after making sure she is comfortable, haka ya dinga watching dinta tana bacci kamar an basa gadinta, ko da Khaleesat ta farka after few hours taga ya rufa mata blanket din da Airline din suka yi providing ma business class passengers, ta kara gyara kwanciya ta ci gaba da baccinta, after some Hours ya tasheta daga baccin ta ci abinci, ta marairaice masa tace “I am not hungry” Daga haka ta koma ta kwanta shi dai kallonta kawai yake…. Karfe shidda da yan mintuna na asuba suka sauka airport din Abuja, a cikin Airport din suka jira next flight dinsu to Kano which is 7 am flight, tun basu karaso Nigeria ba suna ƙasar da suka yi Transit ya sa a siya masu ticket din kan su karaso, Khaleesat dake ta kallonta ta jira har ya gama wayar da yake wanda da alama da Maminsa yake magana, yana daga kai ya kalleta a hankali tace “Gidan da Ya Junaid ya taɓa sa aka kaini a nan Abuja is she his late mother’s sister?” Jay yace “Ammi?” Khaleesat ta gyada masa kai, Jay yace “No, she is his mother’s Childhood frnd, since after his mother’s demise she was always there for him, har hutu Mai martaba yana bari yaje yayi wajenta when he was little, a Bauchi take da mai gidanta before suka yi relocating to Abuja years back, so she is just like a mother figure to him, yana kuma bata value sosai” Sosai jikin Khaleesat yayi sanyi, ta tuna irin yanda Ammi ta ja ta a jiki kamar ta taɓa saninta lokacin da ta sauka gidan, ta kalli Jay a hankali tace “She is very kind” Jay yayi murmushi yace “Sure she is, Ajay doesn’t joke with her matter, ko abu zai yi idan ta hanasa ya hanu, in kuma tace ga yanda zai yi to hakan zai yi, although yana son Grandma dinmu ma amma kuma ita baya jin maganar ta” Khaleesat tace “To kana da number din Inteesar din Ammin?” Jay yace “A’a bani da numberta, sai dai Ajay” Khaleesat tace “Pls ka amso min wajensa, da ace Flight dinmu zuwa Kano ba na yanzu bane da naje gidan in gaisheta” Jay yayi murmushi yace “Da nasan za ki je ai da nace ayi mana booking ticket din yamma, da sai in kai ki gidan ku gaisa” Khaleesat ta langwabar da kai tana kallonsa, yace “Ko ayi cancelling ticket din kawai?” Ta zaro ido, sai kuma tayi murmushi ta girgiza masa kai tace “A’a, ba haka nake nufi ba” Yace “To ya kike son ayi ur Royal Majesty?” Er dariya tayi tace “In ka amsar min number wajensa sai in kira Inteesar daga nan sai ta ba Ammi wayar mu gaisa” Jay yace “Ohk zan ce ya turo min number idan muka isa Kano in sha Allah” Khaleesat tace “Yana Kanon ne ko yana Bauchi?” Jay yace “Yana Bauchi, bai tsaya Kano ba” Khaleesat ta langwabe kai tace “Da ma ya auri Inteesar kawai because of her Mother, since she sees him as a son, and he takes her as a Mom, kuma Inteesar din ba ruwanta i like her so much, she will be of a good wife to him, she is so gentle, and she is beautiful” Jay yayi dariya yace “Ko?” Khaleesat tace “Allah…” Jay yace “Toh ko za ki basa shawara?” Khaleesat ta wara ido tace “Kai dai da yake brother dinka ka basa shawaran, zai samu peace of mind sosai idan ya auri Inteesar” Jay na murmushi yayi kasa da murya yace “Kamar yanda zan samu peace of mind idan na auri Halysaah?” Rufe fuskarta tayi da sauri tana murmushi, shikenan kuma yayi cutting conversation din don bata sake yarda ta ci gaba da hirar ba, he wish she will continue don yana jin dadin conversing da ita barin idan ta saki jiki, har wani natsuwa yake ji a ransa, don dai ta ci gaba da magana yace “Yanxu dai baza ki bi kawar ki ku zo masarautar mu ba?” Khaleesat tayi dariyar da bata yi niyya ba tace “Are you taking Sophie serious?” Jay yace “To ai ita da gaske take, she was so serious saying it” Khaleesat tace “Uhm, nasan ma baza a bari taje bikin da take cewa a Gombe ba balle har taje Bauchi, her father is very strict” Jay yace “Amma gaya min gaskiya, kuna da yan uwa a Bauchi kamar yanda tace?” Khaleesat ta ɗaga manyan idanuwanta ta kallesa, murmushi tayi ta girgiza masa kai alamar a’a, yace “Ban yarda ba, tunda har Safiyyah ta fada haka ne, so why are you hiding it?” Khaleesat tayi shiru, after some seconds tace “Stepsister din Dad dina ce a can amma a kauye suke, Nenne ce ta rike ta don tun tana karama Baabarta ta rasu” Jay yace “Ina kenan a Bauchi?” Khaleesat tace “Nima ban sani ba wallahi” Yace “Baki taɓa zuwa ba kenan?” Khaleesat tace “Ban taɓa zuwa ba, amma Aunty Farida da su Ummanmu suna zuwa idan ya kama, step mothers dina ma duk suna zuwa” Jay yace “Amma ita ta Bauchin bata zuwa Kano?” Khaleesat tayi shiru, sai kuma a hankali tace “Tana da yarinya with Cerebral palsy, and she is almost 14 years, saboda yarinyar yasa bata zuwa ko ina tunda bazata iya tafiya da ita ba saboda condition dinta, kuma ba me kular mata da ita kamar yanda ita zata yi” Jay yace “Allah Sarki, Allah ya basu ikon cin jarabawa” Khaleesat tace “Ameen” Bayan few more minutes suka yi boarding jirgin da zai yi take off zuwa garin Kano wanda shi ne jirgin farko da zai tashi zuwa Kano a ranan, duk da farin cikin da Khaleesat take zata je gida taga Ummanta da Aunty Farida da Siblings dinta har ma da Babanta, amma deep down her she is so afraid don bata kuma san me zata tarar wannan karan ba ko kuma me zai faru zuwanta kano, da ta tuna tashin hankalin da ta tarar zuwanta na karshe tare da Ajay sai taji faduwan gabanta na tsananta, bayan jirgin ya tashi Jay dake lura da ita don kusa suka zauna yace “Halysaah” Juyawa tayi ta kallesa, yayi kasa da murya yace “What happen?” Tayi murmushin karfin hali ta girgiza masa kai, yace “No Halysaah, tell me why you became tensed all of a sudden…” Sauke idonta tayi jikinta yayi sanyi, ganin yana jiran amsarta ta kallesa a hankali tace “Kawai naji gabana yana faduwa ne, I don’t know what I will meet home this time around” Calmly Jay yace “Babu abinda zaki tarar sai alkhairi in Sha Allah, stay positive dear” Sosai taji hankalinta ya kwanta with just his words, tayi murmushi tace “Toh Nagode” hannunsa ya saka a nata shi ma yana murmushin yana kallonta, ta zame hannunta da sauri, ta wani kallesa, kashe mata ido yayi yace “Ashe idan kina bacci sleeping beauty kike komawa…” Zaro ido tayi jin abinda yace, yana murmushi ya ciro wayarsa ya shiga videos din da yayi mata ƙashi ƙashi tana bacci, buda baki tayi with shock tana kallon video din da yake playing, kamar zata yi kuka tace “Innalillahi, ni dai wallahi ka goge” Murya can kasa yace “Anki”
Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788
