Haihuwa Da Hanji Page 17 Hausa Novel
18hours Earlier Kanta a ƙasa tun da Sulaiman ya fita daga gidan tana tsaye ne jikin taga tana kallonsu tun Shigowarshi da ma isowar su saleem da tafiyanshi bayan ya ba Afeefar Abu a leda, bata taɓa sanin haka so yake ba sai da ta faɗa komar Sulaiman zuciyarta yayi mata wani irin nauyi, tsananin haushin Afeefah take ji kaman ta samu bindiga ta harbeta kowa ya huta, a yanzu ma bata san hawaye na zuba mata ba sai da ta ji an dafa ta.Ɗago kai tayi ta kalli Samha sai ta duƙar da kan again tana share hawayen fuskarta”Sameera me ke damun ki haka? Menene ya sameki kike kuka?””Babu Samha””A’a Sameerah ina fa lura da ke kwana biyun nan duk kin chanza kaman ba ke ba, kullum kina cikin damuwa ‘yar faɗan nan da kike biye ni muyi tayi duk yanzu bakya yi walwala ta kau daga fuskanki har mommy ɗazu maganan take yi, in baki faɗa min ba wa za ki faɗawa Sis?”Kuka kawai ta sakarwa samhar, sai da tayi mai isarta kan ta ɗago ta kalleta “Samha ko na faɗa ma ba ku da maganin damuwata””Ko Adu’a muka taya ki ai mun taimakeki bare kila akwai shawarar da zan iya baki, idan ba kya son kowa ya sani ne ma i promise ba zan faɗawa kowa ba”.”Samha na kamu da Soyayyar Dr. Sulaiman”Tsayuwa tayi tana tunanin waye Drn Sulaiman sai da yayi clicking a brain ɗinta kan ta yi saurin cewa “Wannan likitan dake zuwa duba Mayyar chan?”Kai ta gyaɗa a sanyaye “Samha kaman soyayya suke da ita””Amma Sulaiman ɗin bai santa bane ba ko? Ina nufin bai san wacece ita ba rufe shi take kokarin yi ta nuna mishi ita ‘yar gidan nan ce?”Samhar ta fada har yanzu tana mamaki, Afeefah ta kai Sulaiman ya ce yana so? “Da alama kam””Toh me kika yanke?”Ta ɗago jajayen idanunta tace “Dole su rabu idan na cigaba da kallonsu tare zuciyata zai iya bindiga Samha, dole ko in sakata ta rabu da shi ko kuma in san hanyar da zan bi gidansu su san wacece ita! Ko yana sonta ai ba shi zai aurar da kanshi ba ko?”Kai Samha ke gyaɗa wa “Wannan haka yake, shawarar nan yayi kuma ki sameta ki ja mata warning mai girma ta tsaya matsayin ta”A hakan suka yanke don har ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi da Afeefah da safe kuma tana tashi bacci wanka kawai tayi ta fito kaman an ce ta leƙa waje ta hanjeshi tsaye da ita, ko abinci bata ci ba ta zauna parlor tana jiran Afeefar ta dawo don ta lura abin nasu gaba yake, bata gama tunanin ba sai ga Samha da gudu ta ƙira su suka nufi ɗakin Afeefar…***Tana zaune kanta haɗe da ƙafafunta tana aikin zub da hawaye kawai ta ji an banko ƙofan ɗakin, suka tsaya suna ƙarewa ɗakin kallo kan Sadiqa ta nufi wayanta da ke zaune gefenta “Kutt! Yaushe kika yi waya? Na dai tabbatar ba da ita kika zo gidannan ba”Kayakinta Samha take dagawa tana cewa “Mommy yau dai kam Yaya da kike yabo ya watsa miki ƙasa a idanu duk wa zai saya mata su bargo har da su heather in ba Yaya ba? Dubi ƙwalamar dake ɗakin nan? Mommy anya ba asirce shi tayi ba?”Ita dai tana tsaye tana kallonsu duk da zuciyarta da ke dukan sakwara ta kame bata firgice ba, Sameera ta je ta fusgo ledojin da Sulaiman ya kawo mata tana zazzage kayakin ciki idanunta cike da kwallah.”Shikenan wallahi tambaɗe mana take shirin yi a gida, wani namijin ne zai na kashewa mace kuɗi haka ba tare da ta bashi komai ba?”Sadiqa ce tayi maganan tana ganin turaruka da dogayen riguna masu tsada da mahaifiyar Sulaiman ta bata.Sameera ta katse ta”Ko dai asiri ta yi musu ba yaya sadiqa in tambaɗe wa ne kenan har da Yayanmu kalli wayan nan kalar text messages dake ciki na tsantsar soyayya don tsabar rashin kunya da nuna cewa ta isa dashi ma kin ga sunan shi gatsau tayi saving saleemullahi”A fili ta fara karantowa mommy wasu inda yake tabbatar mata da zai iya jurar komai a kanta kuma zai jajirce har sai ya ga sun samu cikar burin su na kasancewa karkashin inuwa daya.”Ya isa haka sadiqa”Mommy ta faɗa jiri na kwasarta ta samu wuri ta zauna, har Dishi Dishi take gani saboda yadda kanta ya sara ashe salim zai iya tsallake maganar ta? Yanzu idan da basu lura da wuri ba tayi amfani da wannan dama ta kashe mata shi fa? Da gaske maita na tafiya da aljanu? Ai kuma duk inda Aljanu suke akwai asiri kenan dai tun farko ma asiri ta mishi ta sa ya kawo ta matsuguninsu? “Lallai saleem! Ni yaron nan zai nunawa ɗan yau ne shi? A kan mace? Macen ma Mayya marar galihu da tushe haɗe da asali mai kyau? Allah ya isa na a banza ya ɗauke shi? Ni saleem…?”Sai ta kama hawaye, hankalin Afeefah ne ya tashi ganin mommyn na mishi hawaye bata son masifar hawayenta ya taɓa shi ko ta wani ɓangare da sauri ta isa gaban mommyn ta zube a kan gwiwowinta”Don Allah Hajiya ki yi haƙuri kar ki mishi kuka, wallahi yana jin maganarki yana kuma tsoron fushinki, Ni ce mai kuskure ni ce na nemi ya sayamin kar ki yi fushi da shi domin fushinki bala’i ne a tare da shi…”Tauuuu sadiqa ta ɗauke ta da mari “Kin san hakan amma kike hure masa kunne ya saɓa mata? Kin san abin da ɓacin rai daga gareshi zai iya ja mata?”Samha da ta janyo jakar da saleem ɗin ya shigo ya ajiye mata ta zazzage komai na ciki tana cewa “Wallahi yarinyar nan so take ta raba mu da ɗan uwanmu Mommy, kalli uwar tsarabar da ya kawo mata a ɓoye ko ke bai kawo miki irin hakan ba bare mu… Farraku take shirin yi mana daga karshe ta sa ya kora mu daga gidan nan””ƙira min saleem sadiqa”Da wayan Afeefar ta ƙira shi, ringing ɗaya ya ɗaga a hankali ya kira sunanta sai ta duƙar da kai hawaye na gangaro mata jin muryarshi.”Yaya Salim Sadiqa ce Mommy ke son ganinka”Runtse ido yayi da ƙarfi gabanshi na faɗuwa, bai shirya ba! Bai shirya tashin hankali a yanzu ba ba yanzu ba da yake jin son Afeefah yayi mishi yawa a zuciya.Da sauri ya juyo kan motar dama bai yi nisa ba ya dawo wani irin parking yayi ya sauƙa ya nufi sashen Boys quaters ɗin yana Adu’ar Allah ya sa kar mommy tayi mata wani abu, sai kace-nace ya same su suke yi ana ta maida magana, Afeefar na tsugune kaman mai neman gafara tana kuka.Gaban mommyn ya je kusa da Afeefar shima ya duƙa kawai ba tare da ya furta kalma ko guda ba.”Saleem”Ta ƙira sunanshi ya amsa ba tare da ya kalleta ba “Ɗago saleem ka kalleni, ka ɗago ka tabbatar min da kai ke tura duk wani saƙo da na gani wayar yarinyar nan, da gaske kai ne kake son wannan marar cikakken asalin?”Ya runtse ido wani irin nauyin Afeefah yake ji kaman yayi yaya, baya so baya kaunar ta ke jin furucin ɓatanci daga ahalinshi zuwa gareta musamman mahaifiyarshi.”Mommy ni ne, Son ta nake kuma aurenta nake Son y….”Wani irin mari ta ɗauke shi da shi, karo na farko kenan da ta kai hannunta jikinshi don shi yaro ne mai tsananin biyayya a gareta.”Maimaita!”Ta daka mishi tsawa ya sake cewa “Mommy ina ƙaunarta, kuma aurenta nake buri”Wani marin ta sake dauke shi da shi, ba shi kaɗai ba har su sadiqa sun tsorata basu taɓa tunanin za ta iya kai hannunta jikinsu ba don ita Allah yayi ta da tsananin son yaranta, hawaye take yi ta sake cewa saleem ya maimaita “Mommy… Mommy da gaske zuciyata ta kamu da Soyayyar Afeefah da ba na tunanin ko wani hukunci za’a yi min zai sa ta fita daga ciki, mommy kila sai kin cire zuciyar gabaɗaya daga kirjina za ki daina jin harshena na furta kalmar ƙauna zuwa gareta…”Wani irin kuka Sameerah ta fashe da shi, a yanzu ta yarda ta yarda ba wani asiri don tabbas abin da take ji a kan Sulaiman shi ke azabtar da Saleem tunda har zai iya mayarwa mommy magana sau uku, Mommy ta sake ɗaga hannu zata mareshi sadiqa ta riƙe hannun tana hawaye “Mommy ba shi za ki daka ba ga Mayyar da ya kamata ki kassara chan, wallahi Afeefah sai kin bar gidan nan ba za ki tarwatsa mana gida ba”Afeefah dai ta rasa yanayin da take ciki, wani irin ƙauna da tausayin saleem ne suka sake mamaye zuciyarta ko tunanin inda za ta nufa in sun kore ta bata yi, damuwarta saleem idan suka raba su basu mishi adalci ba, shi ya cancanci bautar ta na aure har mutuwa.”Saleem!”Mommy ta kira shi karo na ba adadi muryarta har yanzu da wani irin mamaki, idanunshi da suka sauya ainun ya ɗago ya kalleta tamkar ba soja ba wani irin rauni ya bayyana karara a fuska da idanun nashi.”Saleem!!”Ya amsa a hankali “Saleem!! Sau nawa na kira ka?”A hankali yace “Uku””Wannan ba aikin hankali bane na asiri ne, amma ko da asirin ai ka san matsayi na a wurin ka ko? Ka san ni wacece ko?””Mommy ke mahaifiyata ce kina da darajar da babu wanda yake dashi a wurina duk faɗin duniyar nan. Kin isa da ni kuma na san za ki so farin cikina! Mommy a yanzu ba na jin ina da wani buri da zai haifar min da farin ciki kaman Afeefah, ban san sadda sonta yayi min wannan kamu ba don ba ya shawara kan ya shiga wallahi ina sonta! Ba zan iya rarrashin zuciyata ba don so bai san rarrashi ba…””Afeefah Allah ya isa tsakanina da ke! Allah ya isa”Mommy ta faɗa tana kuka. A lokacin hawayen da saleem ke danne wa suka gangaro ya ɗago ya kalli mommyn zai yi magana ta daka mishi tsawa a kan ya mata shiru “Aure kake so zan ɗaura maka aure da yar ɗan uwana Sabreena da take sonka tun bata san kanta ba, amma soyayya, magana ko zancen aure tsakaninka da wannan yarinya saleem har Abada, ko bayan raina ne Allah ya isa ban yafe ba! Wallahi wallahi sai na iya tsine maka ka sake shiga huldar yarinyar nan ko a hanya kuka haɗu ban yafe ba ka mata ko da sannu ne… In har ni na haif…haifeka Saleem sai dai in kana da wata uwar za ka iya”A razane yake kallonta, ta share fuskanta ta dubi Samha “Je ɗakina ki ɗaukomin akwatin da ya fi kowanne girma”Da sauri ta tafi, Sameera zuciyarta ne ke tsitsinkewa a yanzu tsoro ne ya rufeta, wlh tana iya jin irin abin da saleem da idanunshi ke runtse yake ji a yanzu, gabaɗaya jijiyoyin kanshi sun mimmiƙe girgiza kai take yi “Mommy don Allah ki dakata! Ki tsaya kar azabar yayi mana yawa… Ki barta don Allah ko bai aureta ba ta z…”Sadiqa ce ta kai mata duka “Kema asirce ki tayi don ƙaniyarki? Wallahi ta gama zaman gidan nan”A lokacin Samha ta shigo da wani cream trolley.Mommy ta karɓa ta jefa mata “Na tsani ganin ko inuwar ta ne, ku gaya mata ta tattari duk taeukucenta ba na son ganin ko ƙyallenta a gidan nan kar ma ta dawo cikin dare ta kama wani biya… Har Abada ko magana ta yi wa dana sai na tabbatar ta kare rayuwarta a gidan yari”Ko gwada roƙon su bata yi ba don ta san ko sama zai haɗu da kasa a yanzu mommy ba zata amince da hakurin ta ba, kuka mai sauti take yi jikin saleem ne ya fara rawa, ba zai cigaba da sauraron kukanta ba ba zai iya ganin tafiyar ta ba, zuciyarshi tamkar zai fashe saboda tsoro da fargaba in ta fita ina za ta je? Wa ta sani a duk faɗin Kaduna? A hankali ya miƙe jiri na kwasar shi a dafe da gini ya cigaba da tafiya har ya bar ɗakin zuwa lokacin da gaske yake hawaye, hukuncin Mommy tamkar zare mishi farin ciki tayi a wannan rayuwa, tamkar ta kulle shi ne a magarƙamar da ya fi kowani magarƙama duhu da azaba.Afeefah ta haɗa komai nata, wayar da saleem ya saya mata kawai ne ke riƙe hannun mommy kan suka tasa ta gaba har wajen gate, ta jima tsugune a wurin tana kuka kan ta miƙe ta share fuskarta ta ja akwatin ta fara tafiya.”Hasbunallahu wani’imal wakeel…! Innalillahi wainna ilaihi rajiun”Abin da take ta nanatawa kenan tana share hawaye ta yi tafiyan da bata san adadi ba har ta fito wani babban hanya dake dauke da ababen hawa fiye da cikin unguwar da ta bari, nan ma miƙawa kawai tayi ta cigaba da tafiya ko biyar babu a hannunta, ta fi awa biyu tana tafiya janye da trolley ɗin lokaci lokaci ta kan share hawaye masu zafi dake zuba mata, a daidai wani wurin ba da hannu ta tsaya ta ɗaga kai ta kalli garin, mutane ne ke ta hada hada kowa harkar gabanshi yake yi, daidai wutan ya nuna ja motoci suka tsatsaya wani daga gaba yayi kokarin kin bin doka sai hatsari ya faru a wurin tuni go slow ya wani irin haɗuwa.Tana tsaye har lokacin rike da akwatinta kamkam sam bata san me za ta yanke ba, bata san ya za tayi ba kaman an ce ta ɗaga kai sai idanunta da suka zama wasu iri tsabar kuka suka shige cikin nashi daidai yana sauƙe glass, kallon seconds biyar suka yi wa juna ya ɗauke kanshi ya mayar gaba yana tsaki, ita kam bata dauke kai ba sai take jin kaman ta je ta roƙe shi ya taimaka mata ko da ya haɗa ta da Sulaiman ne, amma kuma Sulaiman ai bai san wacece ita ba idan su ma suka kore ta fa? Innalillahi wainna ilaihi rajiun ta sake faɗa hawaye na silalo mata daidai ya sake kallonta idanunshi suka sauƙa kan hawayen a lokacin suka samu hanya ya ja motar ya bar wurin.Juyawa tayi ta cigaba da jan trolley ɗin dama ta sani bashi da kirkin saleem, babu mai kirkin saleem ma a duniyarta shi kaɗai ta sani mai kirki, daidai ta zo gaban galaxy mall da ta gani rubuce sama za ta wuce sai tayi karo da wata mata, baya baya matar tayi za ta faɗi Afeefar tayi hanzarin sake akwatin ta riƙe ta “Subhallah! Ki yi haƙuri”Ta faɗa cikin dasasshiyar muryarta, sai ta ga matar ta kasa tsayuwa numfashinta na ta kai komo ga ta dai cikin shiga na alfarma har da jaka a hannunta”Lafiya Aunty? Ko baki da lafiya ne?”Take ta tambayar cike da damuwa matar ta kasa magana.Hankalin Afeefah ya tashi, kar ta mutu yanzu ma a ce ita, ya zata yi? Ba Za Ta iya barin ta a nan ba a haka yadda take duk ta fice hayyacinta ta jike jagwaf da gumi Dukda sanyi ake. Wani tunani ne ya faɗo wa Afeefah ta yi hanzarin karbar jakar matar tana cewa “Aunty taimakon ki zan yi ba sata zan miki ba bani da ko biyar da ba zan taɓa jakanki ba”Buɗewa tayi ta samu ɗari biyar bata tsaya tunani ba ta tari abin hawa ta sanya matar a ciki itama ta shiga mai machine ɗin ne ya dauka mata akwatinta tana ce mishi “Asibitin dake kusa don Allah””Sannu, Sannu”Take ta maimaitawa matar gwanin tausayi sai taji tana yi wa Allah godiya da ya barta da lafiyanta ko ba komai ta tsira da shi, a haka suka isa wani private hospital ya shiga da su har ciki aka dauƙeta emergency zuwa lokacin bata numfashi.


