Hausa novels

NIHAAD Chapter 61 By Khaleesat Haiydar Complete Novel

61

Nihad na shiga dakin hotel din ta zauna gefen gadon dakin a hankali, ya ajiye wayoyinsa ya kalleta yace “Will be right back” Ita dai bata ce masa komai ba ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita dakin, bin dakin da ba bakonta bane ta dinga yi da kallo, memories da bata son tunawa suka dinga dawo mata, lokaci daya tayi saurin kauda tunanin cause it’s making her sad, ta jinginar da kanta a hankali jikin gadon ta lumshe ido… Can dai ta gyara zamanta da sauri, ita dai tasan ba lokacin period dinta bane but she is feeling as if her period just came, beside sai tayi wata hudu ma bata yi period ba ita, tashi tayi ta tafi bandakin amma sai ta ga opposite dinsa, bayan few minutes ta fito ta dawo ta zauna gefen gado, wayarsa da ya ajiye side drawer ya fara ring, ta juya tana kallon wayar taga Nadeey a jikin screen din, ta dinga kallon wayar ko kiftawa babu, lokaci daya ta wani hade rai, sai kuma ta dau wayar tayi rejecting kiran, sake kira tayi nan ma ta kara rejecting, sun yi hakan sau uku, ganin bata sake kira ba ta mayar da wayar ta ajiye, wani sabon tsanarta kawai take ji a zuciyarta duk da dai bazata ce ga abinda ta taɓa mata ba, but she hate her with passion, dai dai nan aka bude kofar dakin ta daga kai tana kallonsa har ya shigo, ya ajiye ledan hannunsa ya cire agogon wrist dinsa sannan ya shiga bandaki, alwala yayi ya fito, ta bi sa da ido har ya sake fita daga dakin don an kira isha, mikewa tayi ta shiga bandakin ita ma tayi alwala ta fito tayi sallahn, tana idarwa ta jawo ledan da ya ajiye ta bude, gasasshiyar kaza ce sae kamshi take, ga fresh yoghurt me sanyi da kwalin lemo a wani ledan daban, babu bata lokaci ta fara aika kazar inda ya kamata, tana ci tana korawa da chilled drink din, sai da taji ya fita kanta tsabar cin da tayi masa sannan ta ajiye wanda ta rage ta shiga bandaki ta kuskure bakinta ta fito ta hau gado ta kwanta. Wajen karfe tara ya shigo dakin da karamin akwati wanda ke dauke da sabon abaya da ya siya mata guda biyu da duk wani abinda zata bukata gobe kafin su tafi Abuja, sae na shi kayan shima, ya ajiye akwatin yana kallonta don rufe ido tayi kamar me bacci, ya zauna gefenta ya kai fuskarsa nata, murya can kasa yace “Are you sleeping?” Bude ido tayi a hankali tana kallonsa, ya dagota ta zauna sannan ya jawo ledan kazar da ya ajiye yace “I bought…” Kallonta yayi da sauri ganin ɗan abinda ta rage a ledan, ta turo baki ta juya masa baya ta koma ta kwanta, ɗan murmushi yayi ya mike ya tafi bandaki bayan ya dau sabulun da ya siyo, babu yanda Nihad ta iya haka ya tilastata sai da ta sake yin wanka ita ma, tana fitowa bandakin ta ga kayan baccin da ya ajiye mata gefen gadon shi kuma yana zaune daya side din gadon sanye da wandon pajamas kawai, yana danna wayarsa with full attention, kana ganinsa kasan text yake rubutawa, bata sake kallon kayan da ya ajiye mata ba, ta jawo handbag dinta ta dau turarrukanta ta shafa sannan ta dau hijab dinta ta saka ta yi kwanciyarta ta juya masa baya… Ya gama rubutun text din da yake ya tura sannan yasa wayar a flight mode ya daga kai yana kallon Nihad, mikewa yayi ya kashe wutan dakin ya dawo inda take facing ya kwanta, da sauri ta mike zata bar wajen amma ya jawota jikinsa murya can kasa yace “Bayan kazata da kika cinye? Who told u it’s for free??” Ta marairaice tace “Ni kaina ciwo yake min, ina son inyi bacci” Yace “Ohk zaki yi bacci, but we need to talk now” Bata ce masa komai ba, a hankali yace “Are you ready?” Duk da ba ganin fuskar juna suke ba sai saukan numfashinsa da take ji a fuskarta ta daga kai tana kallonsa cikin duhun, kwantar da ita yayi a faffadan kirjinsa yayi wrapping dinta da hannunsa, bata san sanda ta lumshe ido ba tana numfashi a hankali, yayi kasa da murya yace “Few months ago, i saw u in Bristol… ke da wani gaye, me ya kawo ki?” Nihad ta bude idonta da sauri, tayi shiru tana nazarin abinda yace, gaye kuma?? wani gayen? Ita dai tasan duk yawonta da tayi a baya bata yi da maza sai dai su Husnah, then wani guy din yake magana akai? Ya katse mata tunaninta yace “Answer me” a hankali tace “I can’t remember” Yace “You just have to remember….. He is tall and dark” Tayi kokarin tuna guy din amma hakan ya faskara, ta girgiza masa kai cikin sanyi tace “Na manta, i am always coming here together with Husnah and her clique… I don’t know the guy are talking about, or probably suna ciki zanje in samesu ne” Yace “I see, amma me ke kai ku hotels? All the hotels in kano babu wanda baki taɓa zuwa ba” Ta ɗan yi shiru, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, yace “Ina jin ki” Ta rufe idonta don kawai sai taji kunyar tambayar nasa, how did he know tana zuwa hotels bayan ita dai bai taɓa kai ta ba, yaushe ma har ta tsaya suka yi shiri da shi balle ya kai ta hotels, Habibu ne me kai ta hotel wani lokacin har ya jirata ko kuma yaje ya dawo, she felt so ashame of his question, cike da karfin hali ce “Ba komai, kawai dai wani lokaci Naf tana kama daki sai mu je can saboda constant Power, and ita tana son waje me Ac, after that babu wani abinda ke kai mu hotel” Yace “Kema saboda constant Power din da Ac kike bin su bayan na gidan ku?” Tayi shiru kamar baxata ce komai ba, sai kuma tace “Ai dai ba wajen maza mu ke zuwa ba….” Yace “Babu warce bata zuwa wajen maza a kawayen naki, kema kuma kin sani” Tace “Ehh, but that’s their life, ni nasan ba wajen maza nake zuwa ba Allah ma ya sani….” Yace “The Codeine, Prophylactics….” Ta runtse ido da sauri gabanta na faduwa, lokaci daya taji kunya ya rufeta, girgiza masa kai tayi tace “Na Husnah ne, kuma ban san ta sa a jakana ba ranan, they are not mine i promise u….” Yace “Alcohol???” Ta bude ido a hankali, he could feel how her heart is beating so fast a kirjinsa, tayi karfin halin cewa “They lured me into taking it, amma bana sha wallahi, kuma ban taɓa sha ba, Allah shine shaidata” Muryarta na rawa ta kare maganar, yayi shirun kusan minti daya, sai kuma yace “What did u know about that Video?” Ta girgiza masa kai cikin sanyin murya tace “I know nothing about it” Yace “Amma kinsan inda aka yi Video din ae” Tace “I saw it just once, so i can’t even remember how it is…” Yace “Ohk, idan mun koma Abuja you will still have to see it for the second time because u need to figure out where d video was done” lokaci daya hawaye ya cika idonta tace “Ni bana son in sake gani, na bar ma Allah komai, koma waye yayi min na bar shi da Allah” Yace “No zaki sake gani, sannan zaki duba da kyau kiga a ina ne aka yi video din” Bata kuma ce masa komai ba, yaji saukan hawayenta a kirjinsa, lumshe ido yayi, ta dinga shessheka a hankali a jikinsa…. abubuwan da take ta ignoring a zuciyarta daxu su yake tambayarta yanzu and she have no choice then to give him answers to his question, she wish mutum na iya gyara past dinsa, she wish zata iya amending past mistakes dinta na rayuwa, but it’s just too late, Bai hanata ba ya bar ta tayi kukanta for few minutes kafin ya fara cire mata Hijab din dake jikinta a hankali, da sauri ta dago don she is wearing just undies, ta rike hijab din taki bari ya cire, murya can kasa yace “Take ur hands off it” sae da ya sake maimaita instruction din nasa sannan ta sake Hijab din a hankali, ya cire ya ajiye gefe, and he made sure he left her with nothing, ta dinga nonnoke masa tana son stopping dinsa amma ta kasa, daga karshe she realized her body is just too weak for her to stop him, and her body is welcoming duk abinda yake mata, ta gane cewar she is liking it, Romance irin wanda ke nuni da akwai tsananin so na gaske between the couples ya shiga yi mata as if his life depends on it, ba kowa ke samun matsayin kalan romance din ba sai wanda ake so har cikin zuciya, ai ko ta sakar masa jiki gaba daya ba tare da ta ma san ta yi hakan ba, he made sure she savor every bit of it, duk sai da ya birkita mata lissafi ya rikitata kamar yanda shi ma ya rikice telling her all what his mouth can, kyauta kam sae wanda ya manta ne bai mata ba a wannan moment din, kiris ya rage bai bata kanon gaba daya ba a kora su Chamo Zaria, and that night will always be a memorable night for them both, a night that will be worth remembering…..
Har kusan karfe daya yana aikin lallashin shagwabar da take ta zuba masa tana kara narke masa a jiki, daga karshe ya samu dai tayi bacci, mikewa zaune yayi bayan ya kwantar da ita ya kunna wutan dakin yana kallonta feeling so blessed, a karo na farko yaji kamar babu wani sauran damuwar dake tare da shi a rayuwa, he felt so relieve kamar ya sauke wani burden daga kansa, yaji ya kara samun kwarin gwiwan yanda zai tunkari sauran challenges dinsa babu fargaba, they all slept like a baby throughout the night suna makale da juna. Da safe Nihad ta kasa hada ido da shi tana zaune far end of the bed bayan ta gama shiryawa, wani mugun kunyarsa taji take ji, she just don’t know what came over her yesterday night duk da dai farkon lamarin ta wahala sosai amma daga baya sai ya zama opposite of it, idan ta tuna yanda ta dinga masa expressing feelings dinta sai taji kamar ta nutse, Khalil na lura da ita, ya dai gama shirinsa ya dawo kusa da ita ya zauna yana kallonta with smile all over his face, still taki bari su hada ido sai ma sunkuyar da kanta da tayi, she wish kasa zai bude mata ta shige, yayi kasa da murya yace “Ko mu bari sai gobe?” Ta daga manyan fararen idanuwanta tana kallonsa, they stared at each other for almost 30 seconds babu ko kiftawa, ko wanne da tunaninsa a zuciya, kuma babu wanda ya dauke idonsa a cikinsu, a hankali ya hade goshinsa da nata breathing slowly, yayi pressing nose dinsa to her’s, bata ankara ba sai jin bakinsa tayi a nata, nan kuma labari ya canza, ashe jiya da daddare bata ga komai ba, don kuwa this time around sai da yaga she can’t take it anymore duk tayi laushi sai hawaye take masa sannan ya hakura ya kyaleta, ya rungumeta sosai ya ja masu duvet yana lallashinta, daga ita har shi a haka bacci ya daukesu, sai kusan Azahar Khalil ya farka, ya zaro ido yana duba agogo a wayarsa don flight din karfe sha daya yayi masu Booking, shikenan kuma sai dai wani flight din don yasan sunyi missing wannan, ya kwantar da ita a hankali ya sauka daga kan gadon ya shiga bandaki… Still that same day ya sake masu Booking wani flight din karfe shidda na yamma. Nihad ta daga kai tana kallonsa bayan ya shigo dakin wajen karfe hudu da rabi, ya karaso ya zauna gefenta ya ajiye ledan hannunsa yace “Baza ki sake cin abinci ba?” Girgiza masa kai tayi tana avoiding eye contact da shi, ya dau ledan da ya ajiye ya mika mata yana kallonta, kallon ledan ta dinga yi babu ko kiftawa, can ta sa hannu ta karba ta ciro abinda ke ciki, kwalin latest iphone ta gani wanda bai jima da fitowa ba, ta daga kai da sauri ta kallesa cike da mamaki, ya sakar mata murmushi me narkar da zuciya, ta ma rasa me zata yi, amsar kwalin yayi ya bude yayi emptying dinsa, ya daura mata sabuwar wayar a cinyarta, lumshe ido tayi, kana ganinta kasan she is so happy, kawai sai gani yayi ta rungumesa tightly, murya can kasa tace “Thank you so much” ya kai bakinsa kunnenta as if whispering yace “I… I.. love u” Lokaci daya hawaye ya cika idonta amma bata iya ta ce masa komai, they remained like that for almost 5 minutes, can ya saketa ya mike yace “Let not miss our flight again” Yana fadin haka ya fara tattara kayansu dake dakin cikin trolley, cikin minti kadan ya gama ya dau wayarsa yace “Bolt will be here in few minutes” Ya dau sabon wayar ya saka mata a jakarta, kwalin kuma ya saka a trolley, sannan ya mika mata hannunsa, ta daga kai ta kallesa sai kuma ta mika masa nata hannun ya dagota suka nufi kofa…. Karfe bakwai da rabi suka sauka airport din Abuja, nan da nan Mood din Nihad ya canza, bata sake shiga tashin hankali ba sai da ta ga unguwan da suka shigo, shi dai yana rike da hannunta a cikin motar, lokaci daya hawaye ya kawo idonta amma bata bari ya gani ba, me bolt din ya tsaya dai dai kofar gidansu Khalil, Khalil ya bude motar ya sauka, ita ma ta fito daga motar, Mai bolt din ya sauke masu trolley dinsu, Khalil ya dauka yana rike da hannunta suka shiga gidan, basu tadda kowa babban parlon gidan ba har suka iso bangaren Mami, ba mood din Nihad kadai ya canza ba har shi mood dinsa ya sauya, ga wani faduwa da gabansa yake, wani shakkar Maminsa yake ji a ransa, ya shiga parlon Nihad na biye da shi, har zuwa second parlor din Mami, ya ajiye trolly din hannunsa ya karasa bedroom din, Nihad ta rakube jikin kujera feeling so sad, a hankali yayi sallama kofar dakin amma bai shiga ba, Mami ta bude kofar jin sallama, ta tsaya tana kallonsa, ya sunkuyar da kansa gabansa na faduwa, da ladabi yace “Ina yini Mami” a takaice tace “Lafiya lau” Daga haka ta juya ta koma bedroom dinta, duk Nihad na kallonsu, ita ma jikinta yayi sanyi lokaci daya, ya ɗan tsaya for few seconds a bakin kofar kafin ya karasa cikin dakin ya kulle mata kofar a hankali, saman kujera ya ganta zaune ya karasa har gabanta ya durkusa yace “I know i wronged you Mami amma don Allah kiyi hakuri ki yafe min, kar fushinki ya shafeni” Mami tace “I don’t have any problem with ur stupid act Khalil, kuma bana ma son zance…. Don haka spare me!!!” Ya kasa dago kansa, bayan wani lokaci yace “Kiyi hakuri don Allah Mami” Tace “Baka ji abinda nace maka bane?” Yayi shiru bai ce komai ba, can ya mike a hankali ya juya ya fita daga dakin, yana fitowa parlor ya kalli Nihad dake kallonsa yace “Ki shiga ciki ki gaida Mami” Bata ce komai ba ta mike tana tafiya a hankali ta isa kofar dakin tayi sallama, Sai da Mami ta amsa mata sannan ta shiga ciki, dai dai inda Khalil ya durkusa ta duka kanta a kasa tace “Mami ina yini?” Mami tace “Lafiya lau, ya kika baro mutan gidan?” Nihad tace “Lafiya lau” Mami tace “Toh madallah, sannunku da zuwa” Nihad bata kuma cewa komai ba, Mami ma haka, tana ta durkushe kasan, Mami tace “Kinyi sallah ne?” Ta girgiza kai ba tare da ta dago ba, Mami tace “Ki je kiyi” Mikewa tayi ta juya ta fita daga dakin, bata ga Khalil a parlon ba, a sanyaye ta shiga bandakin dake parlon ta dauro alwala…. Tana idar da sallah ta mike zata dauke sallayar Mimi ta shigo parlon, Mimi ta wara ido ta nufeta da sauri ta rungumeta cike da farin cikin ganinta tace “Welcome Nihad” Nihad ta mata murmushi tace “Nagode”
Khalil na fita parlon Mami dakinsa ya tafi yayi alwala yayi sallan Magrib sannan yayi wanka ya shirya ya dau makullin motarsa ya fita daga gidan zuwa gidansu Nadeeyah… Yana ta zaune compound bayan yayi Knocking ya gaya ma mai aikin gidan tayi masa sallama da Nadeeyah, don dama in yaje gidan a waje suka fi zama, amma for almost 30 minutes bata fito ba gashi ya kira wayarta a kashe, mikewa yayi daga karshe ya sake komawa kofar parlon gidan ya bude a hankali yayi sallama ya shiga, babu kowa parlon ya zauna saman kujera, yana jiran fitowar mai aikin, bai jima zaune parlon ba sai ga Hajiya Safeenah zata kitchen, da mamaki take kallonsa, suka gaisa sannan ta tafi dakin Nadeeyah, bayan almost 5 minutes sai ga Nadeeyah ta fito, Ta karaso cikin parlon kanta a kasa, ta zauna saman kujera bayan ta gyara mayafin jikinta tana wasa da zoben hannunta, bata dai ce masa komai ba, yayi kasa da murya yace “I am sorry Nadeeyah, this is all i can say to you” Lokaci daya hawaye ya cika idonta ta girgiza masa kai tace “It’s ohk” Dafe kansa yayi ya ma rasa ta ina zae fara, infact he is just lost of words, can ya dago kai cikin karfin hali yace “Kin dai san ina sonki ko Nadeeyah??” Ita dai bata ce komai ba sae hawayen dake sauka idonta, yayi kasa da murya yace “Toh kiyi hakuri let accept things the way God ordain it, i never bargained for all that has happened, Allah ne ya kaddaro min duk wannan abun, albarkacin son da kike min kiyi hakuri ki taya ni mu rungumi kaddarata tare Nadeeyah, in sha Allah kuma baxan mance halaccinki gareni ba wannan alkawari ne na maki, i am begging you kiyi hakuri don Allah Nadeeyah” Hawaye kawai ke sauka Idonta ta kasa cewa komai, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, Nadeeyah have sacrificed a lot because of him, tayi masa halaccin da ba ko wace budurwa zata iya yi ma saurayinta ba, he knows she doesn’t deserve this, mikewa yayi ya dawo kusa da ita ya zauna, cike da damuwa yace “Plss ki daina kukan nan haka Nadeeyah, u are making me feel guilty, nasan ban kyauta da na boye maki abubuwan nan ba duk yanda muke dake, but ina son kiyi considering cewar even Mami ban iya na gaya mata ba saboda ban son bacin ranta, kema gudun ɓacin ran naki ne yasa na boye maki, but trust me Nadeeyah kina da special place a zuciyata har kullum har gobe, kiyi hakuri ki tayani mu rungumi kaddarata kamar yanda kika saba min a baya, ni kuma in sha Allah zan zamo me adalci gare ki, i am indebted to you Nadeeyah…. Kamo hannunta yayi sanin fa baxata ce masa komai ba, don in har tana kuka bata iya cewa komai, yayi kasa da murya yace “Send me the amount you need na duk abinda za kuyi da kawayenki na biki in tura maki, if there is anything after that ki gaya min” Mikewa tayi tana goge hawayen idonta tace “Zan yi isha’i” Tana fadin haka ta juya ta bar parlon ya bi ta da kallo, gaba daya jikinsa yayi sanyi, shi kansa yasan bata yi deserving haka daga garesa ba, but ya zai yi shi ma bai taɓa tunanin things will turn out this way ba, yana ta zaune for almost 10 minutes, can ya mike a hankali ya fita daga parlon duk jikinsa a sanyaye. Har khalil ya kusa gida bashi da rest of mind, parking yayi jin Convoy din Janar sun shigo unguwan, ya jira har suka wuce sannan ya ci gaba da driving dinsa a hankali, Ya jima zaune cikin motar bayan yayi parking kafin ya bude ya sauka ya shiga ciki walking slowly, direct ya tafi bangaren Mami, babu kowa first parlon ya karasa daya parlon ya bude ya shiga, Nihad kadai ce zaune ga abinci a gabanta amma bata taɓa ba, daga sama har kasa take kallonsa don fararen kaya ne jikinsa sae zuba kamshi yake, sai kuma ta dauke kai, ya karasa cikin dakin yace “Why are you not eating” Ta hade rai bata dai ce masa komai ba, ya durkusa gabanta ya bude abincin dake tiriri, plate ya dauka ya zuba mata abincin with enough meat, ya dau cokali ya deba ya fara kai bakinsa ya ci kadan sannan ya kai mata baki, dai dai nan Mami ta shigo parlon, makalewa yayi wajen gashi ya kasa sauke spoon din daga kusa da bakinsa, ita kanta Nihad ji tayi kamar ta nutse, ta kasa dagowa balle ta kalli Mami, wayarsa dake aljihu ya fara ring ya ciro da sauri, yaga Abbansa ne ke kiransa, ya ajiye cokalin ya daga ya kai kunne, Janar na gama fadin abinda zai fada ya katse wayarsa, Khalil ya juya a hankali yana satan kallon Mami ya ga ankon lafiyayyen lace na su na iyaye take kirgawa zata fita da shi, mikewa yayi kansa a kasa ya fita daga parlon, bangaren Abbansa ya tafi, ya zauna saman Kujera yana kallon Janar yace “Good evening sir” Janar yace “So now, how did my 800M vanish Ibrahim?” Khalil yace “I don’t know” Janar yace “U don’t know? Kar ka manta u asked for 300M 2 days before and i refused giving you, cause i am still yet to see the outcome of wa enda na baka a baya, bayan kwana biyu kuma my 800M went missing, kai ka shigo min da shi gidan nan ba wani ba, kai kadai kasan da kudin, ko uwarka da Amina basu sani ba, only you have the access to my safe in this house, ba kuma wanda ke shigar min that particular room banda kai, in kudi na baka for joint business sai dai kawai ka salwantar min da kudadena, anyi hakan yafi a kirga, in dai zan dauraka akan Business tohh that business will neva go smoothly….” Khalil yayi shiru yana kallonsa, can a hankali yace “But it’s always not my fault, i do use to try my best but ban san meke faruwa ba” Janar yace “Shi Aliyu kai biyu garesa idan na daurasa kan kasuwancina kasuwancin ke tafiya smoothly ban taɓa daurasa kan abu nayi asaran ko naira biyar ba ko in ga ba dai dai ba, kai ko in sha Allahu sai ka salwantar min da kudade, and now u want me to believe ba kai ka dau min kudina ba?” Khalil bai kuma ce masa komai ba, Janar yace “Toh me kayi da 800M wanda u still have to end up driving daga karshe?” Da sauri Khalil yace “Ni ban san komai kan kudinka ba, and ni ba don na rasa kudi naje driving ba, i can fend for my self for years to come ko da ban yi driving ba….” Janar dake kallonsa keenly yace “With whose money zaka yi fending for ur self bayan ur account was frozen then?” Khalil yace “Mami never left me like that, haka Aunties dina….” Janar ya tabe baki yace “Har gobe bazan daina cewa kai ka dau min kudina ba….” Khalil dai kallonsa kawai yake, can yace “Toh shikenan, ina fatan wataran gaskiya ta bayyana ka gane ban dau maka kudinka ba” Janar yace “I am sending u 20M now, kudin lefen both matan naka…” Khalil na kallonsa yace “Allah ya kara budi” Janar yace “Are they going to be staying together or seperately?” Khalil ya sauke kansa yace “Duk yanda Mami ta ce” Janar yace “Oh ohk, Mamin zata zauna maka da su kenan?” Ya girgiza kai yace “Kawai shawara zan yi da ita” Janar yace “It’s left to you… Zaka iya tafiya” Khalil yace “Nagode” Daga haka ya mike ya fita daga parlon, direct dakinsa ya koma, yana zaune gefen gado with different thought running his mind sai ga Alert din 20M daga Janar, shi bai ma san yaushe ne bikin ba kuma bai san wanda zai tambaya da bazai yi misperceiving dinsa ba, tashi yayi daga karshe ya koma bangaren Mami, ita kadai ya tarar a parlonta tana waya da Aunty Maryam da ta tafi gun dangin mijinta dazu da yamma, yana ta zaune har ta gama wayar ta ajiye, kallonta kawai yake ganin bata ko kalli inda yake ba, can ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace “Mami Abba ya saka min 10M yanzu na lefen Nadeeyah, toh ban san ko basu za ayi ba ko a nan za a hada kayan” Mami tace “Baka da number Nadeeyan ne yanzu?” Yayi shiru yana kallonta, can ya girgiza kai a hankali yace “No… kawai shawara nake yi da ke ne kafin in mata magana” Mami tace “Toh kayi magana da ita ni ba maganar da zaka min” Bai kuma ce mata komai ba, ta dau wayarta da ya fara ring ta daga ta kai kunne, hakan ya sa ya mike kawai ya fita daga parlon, dakin da Nihad ke zama a gidan ya nufa ya bude dakin yaga ba kowa ciki, yana ta tsaye yana imagining inda take, to ko tana bedroom din Mami ne, can dai ya tafi bangaren Mimi to ask her yaushe ne bikin, Knocking yayi kafin ya bude kofar yana kallon cikin dakin, Bai ga kowa dakin ba amma ga trolley din kayan Nihad which means she is here, dai dai nan Nihad ta fito daga bandaki daure da towel tayi wanka, ya karasa shigowa dakin ya kulle kofar, lokaci daya ta hade rai zata dau Hijab dinta yayi saurin daukewa a wajen ya jawota jikinsa murya can kasa yace “Kin ci abincin kuwa?” Taki ce masa komai fuskarta a daure, a hankali yace “Ko an maki wani abu ne?” A takaice tace “Ina ka je da farin kaya dazu?” A tsakiyar kansa yaji tambayar da ta jefo masa kamar dai ba ita ba, he wasn’t expecting such question from her, ya ɗan buda ido yace “Ba inda naje, i… I… I met with a long time friend a cikin anguwan nan, ance maki naje wani waje ne?” Lokaci daya hawaye ya kawo idonta tace “Ban yarda ba” Ya rungumeta so that she won’t see the smile on his face, yana murmushi sosai yace “Toh ina zan je bayan kina cikin gidan nan?” Muryarta na rawa tace “Wajen budurwarka kaje ai na sani” Ya dago kanta ya wara ido yace “Ina da wata budurwar bayan matar da aka aura min dama??” Bai jira tace komai ba ya fara kissing dinta passionately, duk ta rikice tana son kwace kanta ya ki saketa sai ma upgrading da yayi daga kiss din, muryarta na rawa tace “Don girman Allah kayi hakuri kar Mimi ta shigo, yanzu zaka ga ta shigo….” kamar me rada yace “Toh za ki bi ni dakina?” Ta marairaice tace “Ai baxan iya ba, za a ganni” Bai kuma sauraronta ba ya ci gaba da abinda yake mata, tun tana ce masa kar Mimi ta shigo har dai ita ma ta dauke light ta sakar masa jiki. Daga ita har shi suka mance a ina ma suke…. kasa hada ido tayi da shi daga karshe ta rufe fuskarta jikinsa cike da jin kunyarsa, murya can kasa yana rungume da ita yace “U are the best thing that have ever happened to me, and i now appreciate the reason i left home, i appreciate my pass….” Ita dai tayi lamo jikinsa tana jin kamar bacci zai dauketa, Murda kofar dakin aka yi Nihad ta mike zaune da sauri tana zaro ido, wani ajiyar xuciya ta sauke ba tare da tasan tayi hakan ba, ashe yasan ya saka ma kofar makulli shi yasa hankalinsa kwance yayi abinda yake so, ta marairaice zata sauka daga kan gadon ya jawota yace “She is gone, plss tell me the name of ur perfume” shiru tayi ta kasa bari su hada ido, ya dago kanta yana kallon kwayar idonta murya can kasa yace “Tell me” a hankali tace “I will…” Tana fadin haka ta jawo towel dinta ta sauka daga saman gadon ya bi ta da kallo babu ko kiftawa har ta shiga bandaki ya sauke wani ajiyar zuciya yana sauke numfashi a hankali, bai kara minti uku ba a dakin shi ma ya fita ya tafi dakinsa da sauri… Ko da Mimi ta dawo dakin Nihad na kwance ta rufe har kanta da duvet, gani take kamar Mimi zata gane wani abu, Mimi dai bata ce mata komai ba don dakin banda kamshin turaren yayan nata babu abinda yake, ta koma daya side din gadon ganin agogonsa a kasa ta dauka ta ajiye a hankali kan bedside drawer sannan tayi Kwanciyarta ta kashe wutan dakin, Nihad ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya jin bata mata magana ba, don da tayi ma bazata kulata ba she will pretend she is sleeping. Washegari da safe Khalil ya shigo bangaren Mami don gaisheta, Bayan ya gaida Mami ya kalli Aunty Maryam dake kallonsa, sunkuyar da kai yayi ya gaisheta ita ma, ta taɓe baki ta mike tace “Mu koma dakin naka dama yanzu nake son in bi ka can” Ya mike ya bi bayanta suka koma dakinsa, Ta zauna gefen gado tace “Kai yanzu ka kyauta abinda kayi Khalil? Me zai kai ka kayi abu kanka tsaye?” Zai yi magana ta dakatar da shi tace “Daga baya kenan Khalil, ba wani abinda zaka fada da zai yi justifying foolishness dinka, ka riga dai kayi abun ka kai tsaye, ur father is supporting you because he is a Man, kuma dama ku maza mentality dinku daya” A hankali yace “Ku yi hakuri Aunty” Tace “Aa ni dama nayi, duk da yanda daga kai har Nihad din kuka mayar da ni yar iska har nake hadata da wani saurayin su yi waya, to laifi akan ku, don Allah ya gani ban sani ba” Khalil bai san sanda yayi murmushi ba, Aunty Maryam ta jefa masa wani kallo, ya zauna gefenta a hankali yace “Wallahi Aunty ban san ta yanda zan ce ma Mahaifinta a’a ba a sanda ya bani aurenta, kema kinsan da nauyi, kuma kinga ai baxan ce zan kawosa gidanmu ba ga issue that is on ground…” Aunty Maryam ta sauke ajiyar zuciya tace “Toh Allah ya baku zaman lafiya, Mami kuma sai kayi ta lallabata har ta hakura gaba daya, kasan fushin uwa bala’i ne babba, don haka kayi ta bin ta har dai ta sauko, sannan kudin da Janar ya tura maka na lefen Nadeeyah kawai ka tura masu su siya duk abinda suke so, yanzu haka ake yi gaskiya” Khalil yayi shiru sai kuma a hankali yace “Aunty har da na Nihad ya bada amma ban gaya ma Mami bane kawai” Aunty Maryam ta kallesa tace “Nawa?” Yace “Ita ma 10M” Aunty Maryam tace “Maa sha Allah, hakan yayi kyau sosai, ita ma ka tura ma iyayenta su yi mata lefen, ba sai ka sanar ma Mami ba may be daga baya zaka iya gaya mata, but for now don’t say anything to her” Yace “Toh Aunty, and Abba yayi min magana ko hadasu zan yi nace sai nayi shawara da Mami” Aunty Maryam tace “Aa gaskiya baza ka hadasu ba, noo it’s not even possible, ita Nihad ka bar ta a gidanka, Nadeeyah kuma ka nemi gida ka kama mata kawai, bikin ma ai an kara 2 weeks dazu Mami ke gaya min” Yace “Ohk i don’t know about it” Aunty Maryam tace “How will u know dama bayan wannan gurmin da ka hada” Murmushi kawai yayi, Aunty Maryam ta mike tace “Bari in je, za mu fita ne da Mami yanzu” Yace “Toh Allah ya tsare” Tace “Ameen, sai ka kira iyayen nata ka tura masu kudin yanzu” Yace “In sha Allah” Bayan Aunty Maryam ta fita daga dakin Khalil yayi dialing number Aunty Jamila, Aunty Jamila dake zaune parlon Umma tare da Mumy ta shigo yi ma Umma sallama zata koma Jigawa, Inna ma zuwanta kenan ta zo duba Umma da er ayabarta kwaya uku da lemu daya, Jamila ta ciro wayarta ganin Khalil ke kiranta ta daga hade da sallama, bayan sun gaisa Khalil ya sanar mata dalilin kiran nasa, Aunty Jamila ta buda ido speechless at first, sai kuma tayi saurin cewa “Ahhh to maa sha Allah, maa sha Allah, Allah ya kara arziki, zan tura maka account din Mumy” Daga haka suka yi sallama ta katse wayar ta kalli Mumy cike da mamaki tace “Aunty Khalil ne ya kirani yanzu, wai Babansa ya bada miliyan goma a hada ma Nihad lefe, shine zai turo mu hada a nan” Umma tayi kuri tana kallon Aunty Jamila babu ko kiftawa, dama tunda suka shigo ko um bata cewa balle um um, duk ta zama wani iri kamar warce ta dade tana jinya, kana ganinta kasan hankalinta baya tare da ita, tana cikin tsananin damuwa, hatta Mumy har lokacin Abba bai kai ga sanar mata babu aure tsakaninsa da Umma ba don ita ce da girki banda yau da zata ajiye Umma ta dauka, kuma yau din ma sai dare yake da intention din sanar mata, Inna ta mike tana kallon Aunty Jamila tace “Waye Khalil?” Aunty jamila na murmushi tace “Mijin Nihad, wai babansa ya bada miliyan goma a hada mata lefe shine zai turo mana mu hada a nan” Inna ta fashe da kuka ta koma ta zauna, sai kuma ta saki kabbara da karfi tace “Allah mun gode maka, Allah mun gode maka” Mumy na kallon Aunty Jamila tace “Jamila maimakon su hada kawai a can har sai an turo kudi nan, ina ga ba gwara kice kawai su yi a can ba….” Inna ta saki baki tana kallonta, can a fusace tace “Ke dai har yau baki da wayewa Maryam, ai yanzu iyayen mace ake ba kudi su hada mata kaya, salon a bar masu miliyan goma su cuceta su ki siya mata abinda ya kamata saboda bakin ciki? Yo ko wannan figaggiyar baƙar shegiyar ta isa ta raba kudin biyu ta boye rabi, wannan din nan da suka ce uwarsu ce kawai daya da Janar din, su turo kawai nan duk za mu siya mata kaya na gani na fada na kece raini, wanda babu wanda zai ce Ibrahim ne ya haifeta, ai tunda Allah ya tsameta daga cikinmu ya mayar da ita cikin masu fitinannen kudi ita ma shiga zata dinga yi kamar yar sarki, in sha Allahu kayan da za mu siya mata sai ya girgiza su wllh, yanda babu wanda zai raina min jikata a gidan, ana gama hada kayan kuma a hadani da dreba in kai har Abujan, nima zan kara dubu goma ta akan kudin a hada da miliyan goman duk a mata siyayya, da kyar idan ba sai mun siye kwari ba” Aunty jamila tace “Kwarai kuwa Inna, kaya sai wanda bamu gani ba a kasuwa ne baza mu siya mata ba, in sha Allah zamu hada mata kaya na gani na fada….” Aunty jamila na fadin haka ta tura ma Khalil account din Mumy, babu bata lokaci kuwa ya sako masu 10M din, Umma dai ta zama er kallo a parlon sai bin su kawai take da ido ba bakin magana, a zaune take amma dishi dishi take gani….. Wajen karfe sha daya khalil ya koma bangaren Mami, he still wants to tell her he is sorry, fushin nan da take da shi ya sa ya kasa samun nutsuwa, ita kadai ya samu bedroom dinta ya duka kasa ta juya tana kallonsa tace “Lafiya??” Ya marairaice mata yace “Don Allah Mami kiyi hakuri ki yafe min, wallahi bazan samu nutsuwa ba idan kika ci gaba da fushi da ni” Mami tace “Inyi fushi da kai a saboda me, a’a ni ba fushi nake da kai ba, abinda kake so ne fa kayi, don haka bani da wata matsala da wannan, kawai dai abinda na sani gida da Maryam tace maka zaka raba masu babu wannan zancen, ban amince da haka ba, daƙuna biyar ne a gidanka banda biyu da ke downstairs, don haka babu wani gida da zaka kama, they will be staying in the same house….” Khalil ya daga kai yana kallonta ya kasa cewa komai.

 

*Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

Ur evidence via 07087865788

 

Assalamu alaikum
Barkanmu da war haka masoya Khaleesat da Nihad🥰. Nasan kowaccenku na cike da son sanin turarukan da wadannan taurari namu guda biyu ke amfani dashi dake tafiyar da xuciyar maxajensu ya rikita musu lissafi ya kuma goge masu hada😌.
Toh turaruka neh na oil masu kamshi sosai da rike jiki daga scentmania. Wadannan turaruka sunfi kala goma. Dan mace ba’a Santa da xama da kamshi iri daya kullum ba. Dole adinga jin kamshi ma banbanta ajikinta kullum. Ana hada wadannan turaruka biyu xuwa sama asaka alokaci guda dansu bada sihirtaccen kamshin dake tafiyar da hankalin duk wanda ya shaka.
Dan haka muka hada package na wadannan turaruka muna kiranshi da ‘Nihad pack’ 🔥 🔥
Akwai Nihad silver pack: ya kunshi turaruka kala biyar. 6mls guda biyu da 3mls guda uku N5000.
Akwai Nihad gold pack: ya kunshi turaruka kala bakwai. 6mls guda uku da 3mls guda hudu
Sannan akwai Nihad diamond pack: ya kunshi turaruka kala 8. 10mls guda daya 6mls guda hudu 3mls guda uku.
Ga sunayen turarukan nan kamar haka
1. Love letter (na musamman akowani pack akwaishi)
2. Baccarat Rouge
3. Jadore
4. La vie est belle
5. Pink shiffon
6. Pure seduction redplum
7. Versace Eros woman
8. Black Opium
9. Kim Kardashian
10. Love spell
Note that turarukan package a discounted price aka bada, kuma ana hada scents din da sukayi complimenting juna neh yadda xaifi tashin kai in anyi amfani dashi. Amman in kinason kiyi maki choice dinki shima ana badawa standard price dinmu 3mls N800, 6mls N1500 10mls N3000
Akwai 20mls N5000, 30mls N7000 and 50mls N10000. Turaruka araha ina mai tabbatar maki kikayi amfani dasu sai kin dawo. Mudae burinmu kowa tayi kamshi na musamman🥰🥰

Download NIHAAD Complete Novel Document By Khaleesat Haiydar

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

Back to top button