Halysaah Page 131 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 131…Ajay na ta tsaye bakin kofar jin bata yi responding ba, ya sake knocking yace “Jeeddah” Still bata amsa ba, bayan kusan 3 minutes ya juya a hankali ya bar wajen ya koma parlonsa, wayarsa ya dauka ya zauna kan kujera yana dialing number…. Khaleesat ta fito daga bathroom tana kallon kofar dakin don tana wanka taji kamar anyi knocking, fuskarta babu walwala ta kauda ko kuka ta kasa yi balle ta dan ji saukin abinda take ji a ranta, nan ta dinga duba boxes din lefenta daya bayan daya har ta bude wanda kayan bacci ke ciki, ta dau doguwar rigar bacci da inner wear ta ajiye gefen gado, sannan ta bude box din cosmetics ta dau tsadaddun turarurrukan da aka zuba mata, ta dau cream din shafa da hair oil sai sabon comb ta tafi gaban mirror ta zauna, ta gama shafe shafenta ta daure gashinta kenan taji ana knocking kofar dakin, ta juya tana kallon kofar sai kuma taji sallaman Yakumbo, sau uku Yakumbo tayi sallama kafin ta mike a hankali ta tafi ta dau kayan baccinta ta saka sannan ta sa Hijab ta nufi kofar ta bude, Yakumbo ta yi kasa da kai cikin girmamawa tace “Barka da dare ranki shi dade, Allah ya sa baki fara bacci ba na tashe ki” 3:36 Zahra2020 dade, Allah ya sa baki fara bacci ba na tashe ki Khaleesat na kallonta tace “Ban fara ba” ido hudú tayi da Ajay dake tahowa daga babban parlor bayan ya ta bude kofar, ta dauke idonta ta maida kan Yakumbo babu yabo babu fallasa tace “Ina jin ki Mama” Yakumbo na dan kame kame tace “A’a dama ba wani abu bane, zan tambaya ne ko da abinda kike bukata ranki shi dade?” Khaleesat na ganin Ajay ya iso wajen tace “Bana bukatar komai, sai da safe” Daga haka ta juya zata koma cikin dakin da nufin kulle kofar amma taga har ya shigo ciki, tana ganin haka ta nufi hanyar bandaki ya kulle kofar dakin sannan yayi saurin rikota, Yakumbo dai tuni ta juya ta bar bakin kofar sum sum ta fita daga part din, Khaleesat ta ki yarda ta kallesa duk da yana rike da hijab dinta, cikin sanyin murya barin su hada ido, manneta yayi da bango yana kallonta murya can kasa yace “Da aka kawo ki gidan nan dama an shigo dake dakin nan ne?” Kin cewa komai tayi, ya dago kanta yana kallonta babu ko kiftawa, ta fara kokarin barin wajen amma yaki saketa, kamar zata yi kuka ta kallesa tace “Don Allah ka kyaleni pls sallah zan yi fa” yayi kasa da murya yace “Why didn’t you open the door when I was knocking?” Da sauri ta girgiza kai tace “Wallahi ina bandaki ban sani ba” Shi dai kallonta kawai yake, ta sauke idonta a hankali, can ya saketa har sannan bai cire idonsa a kanta ba, ta bar jikin bangon ta tafi ta tsaya kan darduma zata tada sallah, makullin kofar dakin ya cire da na bandaki sannan ya fita, tana sallah ya kawo mata abinci da cup din tea ya ajive mata.





